Showing 114001 words to 117000 words out of 150519 words
lissafen ta.
Ba k’aramin burge Yash su Manubiya sukayi ba…yadda suke da kunya da kamun kai
tabbas ya san iyayen su sun yi k’ok’ari wajen tarbiyyar su,
dan ko ba a fad’a mishi ba
ya fahim
ci jiddda k’anwar Manubiya ce sakamokon tsananin kamanni da ya ga suna yi..
Banbancin Jidda da Manubiya
yanayin girman jiki, kalar fata da ido ne kawai..Manubiya ta fi Jidda tsayi da jiki kad’an, kalar
fatar Jidda fara ce ita tass sosai Manubiya kuma ba
b’aka bace ba kuma ba fara bace sosai,
Idanuwan Jidda sun fi na Manubiya girma sosai amma na Manu sun fi na Jidda kyau da d’aukar hankali..a ransa ya ce ’’ idanuwan da suka kusan haukatani”
sai kuma ya d’an yi murmushi kad’an.
Shiruu duk suka yi kafin Ya
sh ya katse shirun ta hanyar cewa Manubiya
‘’Sister d’inki ce ko?’’
A hankali ta d’an jinjina kanta sai kuma tace ‘’eh’’daganan shiru ya sake biyo baya.
Still shi ne ya sake kawo k’arshen shirun ta hanyar cewa ‘’Baba zai samu sauk’i, inshaaAllah.
kar k
i damu komai zai daidaita. inshaaAllah’’
A hankali ta ce
‘’InshaaAllah,’’itama Jidda tace’’inshaaAllah’’a cikin ranta.
A hankali Manubiya ta lumshe idanuwanta, tana mamakin yadda k’iri-k’iri ta gagara yi masa godiyar da take ta zumud’in son yi…
gaba d
’aya duk sai ta ji ba dad’i ta inda ko ishashshiyar gaisuwa ta gagagara shiga tsakanin su..
Yo ta inama zata iya? itafa tunda ya zo ya zauna a kusa da ita shikenan ya sakawa tunani, kuzari da duk wasu lissafe-lissafenta full stop.
Ganin rashin kyautuwar ab
unda ta yi ne yasanya ta yi da gaske da kyar ta samu ta d’an d’ago kanta da niyyar ta kalle shi ta yi mishi godiya, suna had’a ido ta yi sauri ta fara kallon gefen kunnensa sakamokon wani irin kallo da ta ga yana yi mata gashi sai wani tsadadden murmushi y
ake zuba mata.
Babu yadda ba ta yi ba amma da ikon Allah sai ta gagara cewa komai, ga wani mahaukacin bugu da zuciyarta ta shiga yi…
ganin da ta yi ba zata iya bane ya sanya ta yi sauri ta sunkuyar da kanta tana tunanin ta yadda zata aro jarumta ta yi masa
magana ko da ace bata kalleshin ba dan zuwa yanzu ta fahimci abun kamar da wuya,a ranta ta ce ’’wannan wanne irin abu ne haka, wanne irin feelings ne wannan?’’
ta yiwa kanta tambayar ba tare da ta san waye zai bata amsar ba.
A b’angaren Yashjub kuwa kad’
an ne ya rage bai fashe da dariya ba a ransa ya ce ’’.to wai menene nata na k’in kallon cikin idonshi ne?’’ yadda take yi
tana kallon gefen fuskarshi abun ba k’aramin burge shi da bashi dariya ya ke yi ba.’’
Murmushi kawai yayi yana kallon yadda ta sunku
yar da kanta yana jin wani sanyi yana ratsatsi…
baisan wanne Hali zai shiga ba in da an yi rashin sa’a black snake ya tafi da ita ko yayi mata wani abun, ganin ransa yana shirin b’aci ne ya sanya ya yi saurin kawar da tunannin cikin taushin murya ta ji yac
e “Allah ya ci gaba da karemin ke, tare da family d’inki a duk inda kike’’.
Dumm!! Haka ƙirjinta ya buga,a take ta runtse idanunta tana jin yadda kalaman nasa na yanzun suke ratsa zuciya da dukkkannin sassan dake a jikinta tare da sauk’ar mata da wata sab
uwar kasala mai tafe da fad’uwar gaba…
cikin mutuwar jiki a chan k’asan ranta ta ce ’’Not again Yashjub,plsss
(Kar ka kuma, Yashjub, dan Allah!)”.
Tunani Yashjub ya fara yi akan ko dai ya sako maganar incidence d’in jiya da safe, dan haka
ya bud’e Baki z
ai yi magana kenan aka bud’e k’ofar d’akin da aka shigar da Baba da Abbakar aka fito, da sauri su Manu da Ya Musbah da sir Najeeb suka rufarwa Doctor d’in da ya fito.
Yayinda Yashjub yake nan a inda yake ko motsi ya gagara yi, bayan Manubiya wadda ta mik
’e da sauri ta nufi doctor kawai ya bi da kallo yana murmushi yana jin wani nishad’i yana ratsashi…ashe haka so yake? shi fa ko wanne irin takaici yake ciki to wuyarta ya yi magana da ita ko ya ganta kai ko tunanin ta ne ya samu ya yi
to fa da yardar Alla
h tashi d’aya sai ya ji b’acin ran nasa ya kau.
Cikin nustuwa sir Najeeb wanda ya gama jin bayanin Likitan ya juya ya nufi inda Yash d’in yake a zaune, har ya k’arasa ya tsaya a kansa sam Yashjub bai lura ba sai da Najeeb d’in ya kyasta ƴan yatsunshi a se
tin fuskar Yashjub tukunna ya d’an d’ago
yana kallon sa.
Murmushi Najeeb yayi ya zauna a gefen sa tukunna ya ce “ya dai?’’
Bai da niyyar b’oyewawa dan haka tashi d’aya ya ce
‘’Najeeb! Manubiya ce rayuwata, adadin yadda nake
numfashi kullum haka k’auna
rta take k’aruwa a cikin zuciyata,
ku yi sauri ku nema min aurenta tun kafin in haukace muku.’’
K’amewa Najeeb ya yi kawai yana kallonshi yana mamaki, a ransa yace “Ubangiji mai’kun fa ya kun’!’’
Kafin ya yi murmushi ya
ɗ
an
bubbugan kafa
ɗ
an Yash d’in ci
kin sigar zolaya yace “Mutumina! Ai ka riga ka fara hauka, kalli yadda ni kaina ka maidani bawan students d’ina..
mun gama duk wasu abunda suka kamata amma ka hanamu tafiya, sannan ka ji yadda kake magana kuwa?..
Gaskiya kam ya kamata mu yi wani abun da sa
uri’’
ya k’arashe maganar yana dariya k’asa-k’asa.
Kafin ya sake cewa “yanzu dai zo mu je ka ga sirikin naka,,mu samu mu wuce, Inada aiyyuka da yawa wallahi.
Doctor yace
Abbakar d’in an cire bullet an yi komai amma bai farfad’o ba tukunna,
Sirikin ka kuma
he’s well and conscious so let’s go say hi
(Ya farfa
ɗ
o yaana lafiya, dan haka mu je a gaisa),
daganan mu wuce ko?’’
Ya k’arashe maganartashi da tambaya yana mai mik’ewa tsaye.
Har ya d’an yi gaba sai kuma yaga Yashjub bai ma taso ba, dan haka ya koma ya
ce “ya akayi kuma?’’
Tunda yake bai tab’a ganin Yashjub yayi kalar tausayi ba sai yau, har da wani karkata wuya…
Dan haka kawai sai Najeeb d’in ya saki baki yana kallon ikon Allah..
Muryar Yashjub d’in ce ta katse masa tunani jin yana cewa
“I’m serious (
da gaske fa nake) Najeeb, ka fara yi wa Hajiya Mama magana ita kuma ta yiwa Daddy, ka san halinta yanzun sai ta birkice a kasa gane kanta, shiyasa bana so ni in yi mata magana da kaina dan na san idan ta ga na damu kuma na rikice akan maganar to ba za ta
taimakamin ba, cewa za ta yi tun yanzu Ina haka ina kuma ga idan anyi auren, ni kuma na san a yadda nake ji d’innan ba zan iya yin komai a nutse ba.
Ka yi mata magana, a samu a fara maganata da Yarinyar nan
Najeeb tun kafin a samu matsala.”
Shiruu Najee
b ya yi kafin ya bud’e Baki yana shirin yin magana k’arar wayarsa ta katse shi, dan haka ya cewa Yash d’in “a minute pls
(Ina zuwa dan Allah)’’
kafin ya sanya Hannu a aljihunsa ya zaro wayar.
Yashjub ya kalla kafin ya sake maida hankalinsa ga wayar sakamo
kon ganin sunan Daddy da ya yi a matsayin wanda yake kiran nasa, sai kuma ya sake kallon Yash d’in tukunna ya ce ‘’Ina wayarka??’’
‘’Tana mota’’
Yash ya bashi amsa a tak’aice, yana mai ci gaba da tunane-tunanen sa…’ya riga ya k’arbi har number Baba, zai j
ira ya d’an warke daganan sai ya bawa Daddy number d’in tasa su yi magana a tsakanin su ya san inshaaAllah kafin nan Najeeb kuma ya tsara masa hajiya Mama ita kuma ta yi wa Daddyn magana,
daga nan ya san inshaaAllah komai zai zo masa da sauk’i,
ta b’angare
n Manubiya kuwa yana addu’a tare da yak’inin inshaaAllah za ta aminta da shi da yardar Allah ba zai sha wahalar samun soyayyarta ba, shiyasa ma yake so ya je mata ta koina har ta sama ta yadda zata fi d’aukar sa serious.’….
Cikin nutsuwa da girmama Najeeb
ya gaida Daddy shi kuma ya amsa masa kafin cikin fushi ya ji Daddyn ya ce ‘’kana tare da Yashjub ne??’’
Sai da Najeeb ya kalli Yash yaga sam hankalinsa bama ya gurin ya tafi ga tunanin da yake ta yi tukunna ya ce ’’eh Daddy,‘’
kafin ya d’aura da cewa’’ga
shinan, bara in basa’’
Da sauri cikin katseshi Daddy yace
“A’a barshi. Ka ce masa na ce dan ubansa ko me yake yi ya bari ya zo yanzunnan’’
Daga haka ya kashe wayar kit.
A d’an duburce Najeeb ya kalli Yash dan bai tab’a jin Daddy da irin wannan fushi hak
a ba, kafin yace’’Yash!Daddy fa a zuciye yake, mai ka aikata?’’
A hankali Yashjub ya maida kallonsa da tunaninsa ga Najeeb kafin ya yi shiruu kamar mai tunani sai kuma chan ya ce ’’kash!wallahi mantawa na yi’’
Cikin tarar numfashinsa Najeeb d’in ya ce ’’
me ka manta? yace ka je right away fa(yanzu yanzunnan) tashi mu wuce, na ji b’acin rai sosai a muryarsa’’
Najeeb d’in ya fad’i hakan yana mai juyawa.
Numfashi Yashjub ya fesar kafin ya kalli inda Manubiya ta bi ta shige…
wallahi ba daban Daddy ne ya kiras
a ba to da bai ga dalilin da zai sanya ya fita a asibitin nan ba tare da sun yi sallama da Manu ba, bayaga hakan shi fa bai ma gaji da ganin ta ba.
A gaggauce suka tsaya suka biya duk wasu bills daga nan suka fice suka nufi motocin su Najeeb yanata sauri
yana cewa ‘’ka yi sauri fa Yashjub,kar ka dad’e ransa ya sake b’aci..’’
*MANNUBIYA*
*39*
A zaune su Manu suka tarar da Baba, ana gwada masa sugar dan complete checkup Yash ya biya ya ce a yi musu.
suna had’a ido da shi gaba d’ayansu sai s
uka sake zama emotional(sai raunin zuciyoyinsu ya tsananta)
Tashi d’aya Jidda da manubiya suka fara hawaye, ya Musbah shima sai da ya yi da gaske tukunna ya iya hana kansa kuka…ji yake kamar ya d’aura hannu aka ya yi ta kurma uban ihu!…
Wai akan naira mili
yan d’aya tak!kalli abunda aka yi wa mahaifinsa sannan aka yi shirin tafiya da k’annensa Mata har biyu amma babu abunda ya iya tab’ukawa.
Nurse d’in tana fita suka rufarwa Baba, har suna y’ar rige-rige wajen k’arasawa tare da tambayar sa “ya jikinsa?”
m
urmushi ya yi dan dukda hali na tashin hankalin da yake a ciki sai da ya ji wani sanyi da fariin ciki suna ratsashi na ganin yanda y’ay’an nasa suka
damu sannan su ke ta d’awainiya da shi, dan haka ya shiga kwantar musu da hankali kafin ya kalli ya Musbah
ya ce ‘’Ina Yaran su ke?
Ai bai kamata ku barsu a waje ba ko?
ku je ku shigo da su da wuri, kar su tafi ban yi musu godiya ba.’’
Jinjina kai ya Nafi’u ya yi suka fita da shi da ya Musbah amma ko da suka fita basu tarar da kowa ba wnda hakan yake nuni da c
ewar su Yash d’in sun tafi kenan, dan haka suka koma ciki!
Suka sanarwa baba…sai da suka ce masa ai
suna da nambobin wayarsu, tukunna ya d’an ji sanyi, sannan ya ce ‘ko da sun Kira su a waya ya zama dole
su je har office d’insa ko gidansa ayi
masa godiya,
dan duk Mutumin dayayi musu alkhairi irin wanda Yashjub yayi musu to tabbas ya chanchanci kulawa ta musamman daga garesu suma.
Ta wayar ya Nafi’u aka kira Yash
ɗ
in wanda gaba d’aya kunya ta lullub’esa sannan duk sai ya ji wani iri na daga godiyar da baban
yake ta yi masa…
Hakanan dai a kunyance suka yi wayar daganan Yash ya yi masa sallama tare da fatan ‘Allah ya basa lafiya, ya kuma kare gaba’.
Har Najeeb sai da Baba yasa aka kira masa shi shima yayi masa godiya tukunna hankalinsa ya kwanta…dukda kuwa Bab
a k’arfin hali ne kawai yake yi amman gaba d’aya abun wani iri yake jin sa ace wai
‘ka ci kud’i har za a tafi da y’ay’anka Mata, amma ka gagara tab’uka komai….’
A hankali ya lumshe idanunsa a ransa ya ce ‘’Innalillahi a inna ilaihirrajiun,’’
Daidai nan
kiran wayar Aisha ya shigo wayar Manubiya, dan haka ta d’an fita waje domin ta amsa…bataso ta yi wayar a gaban Baba dan bata sani ba ko wani abun ne ya taso daga b’angaren Inna, dan ta san yana ji zai ce zai tafi gida, to kuma shima ga yanayin jikin nasa s
ai a hankali….
dan haka ta fita tana mai addu’ar Allah yasa lafiya….
Jidda ma tana ganin fitar Manubiyan itama ta mik’e ta mara mata baya.
Baba yana jin fitar su ya bud’e idanunsa ya zubawa inda su ka bi suka fita idanu yana jin tsananin tausayin su yana
ratsashi dan tabbas shi kansa ya san ba za su ji dad’in hukuncin da ya gama yankewa a kansu ba.
Ya ji dad’in fitar da suka yi dan haka ya gyara zama ya kalli ya Nafi’u da ya Musbah ya ce’’ inshaaAllahu nan da sati biyu nake so in aurar da Jidda da Manubi
ya…’’
Kwarewar da Ya Musbah ya yi ya fari tari a wahale ne ya katse Baba…Da kyar!! Dan sai da ya sha ruwa sosai ya d’an zauna tukunna ya d’an ji dama-dama still yana tarin kad’an-kad’an…
Bai iya jira tarin ya tsaya gaba d’aya ba ya ce ‘’Baba aure a cikin
sati biyu kuma sab….’’
Cikin tarar numfashinsa Baba ya ce ‘inshaaAllahu Rabbi…
Yanzu Manubiya nake so ku nemawa tsayayye wanda yake a shirye tsaf, nan da sati biyu sai a had’a a yi…
Jidda ita dama Yusuf a shirye ya ke, inshaaAllah Ina fita daga nan zan sa
mu Baba Habu mu…’’
Duk yadda Ya Musbah ya so ya danne fushin sa kasawa ya yi,
Dan bai ma san lokacin da ya katse Baban ba.. cikin tarar numfashinsa a hassale ya ce ’’Baba amma dai ba Yusuf d’an gidan Baba Habu na gidanmu kake maganar za ka aurawa Jidda ba
dai ko?!
Ba dai Yusuf d’an iska wanda ya jefa mu a cikin wannan bala’in za ka d’auki Jidda ka aurawa ba ko?!
Dan in dai shi kake nufi to a gaskiya Baba ba zan tab’a barin Jidda ta aure sa ba…’’
Cikin fushi da fad’a Baba ya ce ‘’a kul
ɗ
in ka Musbahu!!!
Wa
nnan iftila’in da ya fad’o min babu ruwan Yusuf a cikinsa! Dan haka kar ka d’aura masa laifin da ba nasa ba.
eh! Na san muna yawon samun sab’ani
da su amma na san ko
Hauka Yusuf ya ke yi ba zai tab’a yi mini abunda zai jefani cikin wannan halin ba,’’
Cik
in fushi Ya Musbah ya ce ’’baba habu fa shi y…’’
Cikin tarar numfashinsa a hasale Baba ya ce “Musbahu bana son rashin kan gado fa?
So nawa nake ce maka ko da wasa kar ka yarda ka k’ullaci ƴan uwana da y’ay’ansu akan abubuwan da suke yi?
Idan ka k’ullace
su kaima ai ka zama su kenan!!
Ka ga sai ka bada gudummawar tarwatsewar zumuncin namu cikin sauk’i.
In ba rashin kirki ba Musbahu har kai ne wai za ka kalleni kana cewa wani bazaka bari Jidda ta auri Yusuf ba Kaine ka haifa min ita???”
Sai yanzu Ya Nafi’
u ya fesar da iska ya k’arasa gaban Baba ya zauna akan kujerar da ke a bakin gadon tukunna ya ce ’’Baba ka yi hak’uri, kar ka yi (wa furucin Musbahu fahimta ata bai bai) misunderstanding d’in sa,
maganar gaskiya Baba Yusuf bai cancanci a bashi Jidda ba dub
a da yadda….”
Cikin katseshi Baba ya ce ‘’Bari ka ji Nafi’u!
Dama na san za ku yi
Tunanin wai ko ata sanadiyyar Yusuf ne na fad’a wannan halin, wanda sam abun ba haka yake ba!
Yusuf taimakona ya yi amma sai abun (taimakon) ya zo da tangard’a!
Ya yi min
i bayani kuma na fahimci komai dan haka bana son jin komai daga Bakin kowa illah ku ce mini ‘to’ kawai.
Yusuf zai auri
Jidda nan da sati biyu, Manubiya kuma ku nema mata Miji, wannan shine kawai abunda nake so ku fahimta sannan ku yi mini biyayya a kai.’’
Shiruu Ya Nafi’u ya yi kamar ba zai ce komai ba sai
kuma ya ce ‘’amma Baba auren gaggawa da….”
Cikin katse shi Baban ya ce
‘’Nafi’u baka ji abunda Mutumin chan black snake ya fad’i mun kafin ya tafi ba?
Idan ba ka ji ba bari in maimaita maka.
Ce min yay
i ‘sai ya dawo d’aukar Matansa’!’’.
Shiruu Baba ya yi kafin zafafan hawayen da yake ta k’ok’arin rik’ewa suka samu nasarar zubo masa, cike da rauni ya ce ‘’Nafi’u tunda na haifi Yaran nan ban jiyar da su dad’i, farin ciki da walwala ba!!
Allah ya rufa asi
ri amma idan aka ce yau ga black snake ya dawo kamar yadda ya fad’a
ɗ
in ya d’auki Yaran nan ban san ta ya zan fuskanci ni karan kaina ba ballantan asu kansu yaran, Mahaifiyarsu, uwa uba ubangijina, Nafi’u ban san da wannne Bakin zan yi masa bayanin yadda n
a kula da amanar da ya bani ba’’
Baba ya k’arashe maganar tasa yana mai fashewa da wani irin kuka.
Jiki a sanyaya Ya Nafiu ya shiga ƙoƙarin ganin ya lalla
ɓ
a Baba dan a samu ya yi shiru…
shi kansa ya Musbah ya ji ba dad’in kukan da mahaifin nasa yake yi
shiyasa gaba