Showing 111001 words to 114000 words out of 150519 words
Najeeb ya d’auka, a d’an riki
ce ya ji muryar Najeeb d’in sannan kamar ma driving yake yi, dan yana amsa kiran ya ji Najeeb ya fara magana
“kaga message d’ina ko?
Abbakar ne ya kirani yanzun, ban samu na d’auka ba shine ya turomin message, inaga shima yana wajen.
Ina ganin message d’in
na kira shi, an d’auka amma ba a magana..
Babban abun tashin hankalin kamar muryar black snake na ji a wajen, kuma Yash kamar maganar aure su ke yi
da shi da Manubiya!
Amma
ka kwantar da hankalinka
ganinan na ma kusan ƙarasawa police station
ɗ
in.’’
K
ashe wayar kawai ya ji Yashjub yayi…..
A yadda ya nufi k’asa sai da ya bawa wasu
tsoro da mamaki, dai-dai nan Daddy yana fitowa dan akwai
speech wanda Yashjub zai bada kuma lokaci ya yi.
Cikin fushi Daddy ya bi shi a baya amman kafin ma ya gama sauk’
a k’asan ya hango tashin motar Yashjub ta glass
ɗ
in dake ajikin gefen stairs d’in…
‘Tabbas zai ci uwar Yashjub kam yau!’
Daddy ya raya hakan a cikin ransa,
amma yanzu bari ya koma ya gama da waennan mutanen,first.
Kafin ya koma cikin hall d’in ya turawa
Yasira message ya ce ta shirya ita za ta bada speech d’in a madadin Yash…
hakan kuwa aka yi Allah ya taimaka Yasirar ta san kan abun, dan haka ta d’an had’a abubuwan da za ta iya ta bayar taron ya watse.
Daddy kamar ya fashe saboda tsananin takaici, dan
ko da ya koma kiran Yashjub ya ci gaba da yi amman sam bai d’auka ko d’aya ba, k’arshe ma message ya yo masa wai ‘’wani abu mai mahimmanci ya taso masa, su k’arashe meeting d’in babu shi kawai!’’.
Me zai fiye mishi wannan meeting
ɗ
in da su ke yi mahimma
nci?
Menene har ya fi mahimmanci a wajensa sama da kare mutuncin company da kuma mutuncin shi kansa Daddyn.
Har wanne
irin abu ne zai sanya ya tafi ya bar shi stranded (babu madafa) cikin bak’in mutane haka ya kunyatashi…..
….
Tun kafin ya k’arasa polic
e station d’in ya kira babban office na dss yace ‘yana
buk’atar su,
Black snake yana Nigeria, kano.’
Sannan ya fad’a musu sunan police station d’in.’
Ashe dama neman sa ake yi, ruwa a jallo.
Sun tab’a yin case da Yashjub ta inda ‘black snake
ɗ
in ya so
ya cinye masa filinsa, da kyar ya kwato filin nashi’
a ta dalilin hakan ne Yashjub ya san wayene black snake da kuma record d’insa dan ko satin da ya shige ma sai da suka yi maganar sa da Najeeb akan ‘ya je ya gina hotel a filin wani yace filin nasa ne,
ana tsakiyar yin case d’in da ya ga za a damk’e sa shine ya gudu’.
Kuma still an banka’do ‘yayi sanadiyyar sace y’an mata, y’an secondary school guda ashirin’.
Shiyasa da yaga za a yi masa tunb’ir a tona masa asiri sannan a kamasa shine ya gudu zaman Nige
ria ya gagare sa, ya bari akan in komai ya lafa sai ya dawo.
..
Yash yana gama waya da DSS
ya kira AIG yace ‘’a dakatar da duk wani abu da ake gudanarwa a police station d’in da Najeeb ya gaya masa su Manubiyan su ke”
sannan yace’’ kar a bar kowa ya fit
a,dss suna hanya za su kama black snake’’.
Tafiyar mintuna goma ce ta kai shi police station d’in dan bashi da nisa da su, sannan bai bi k’a’idodin hanya da titi ko guda d’aya ba sakamokon uban gudun da ya tsula kamar ba gobe.
Motarsa tana yin parking ta
wani dss shi d’aya ko uniform babu a jikinsa ta yi parking, da sauri ya k’araso ya nunawa Yashjub id card d’in sa kafin yace ‘’kai ne ka yi waya ko? ina kusa sosai na ga assignment d’in shine na k’araso da wuri but mota biyar tana hanya, yanzunnan zaka ga
nsu inshaaAllah. “
Sam Yashjub bai ji dad’i ba, dan so yayi ace tawagar su ce tazo da wuri haka saboda ya san black snake baya yawo shi kad’ai,
dan ga police station d’in ma yanzu haka ya cika tapp da motocin da ya tabbatar nasa ne da shi da Jama’ar sa.
Kamar yadda jami’in dss d’in ya nunawa Yashjub Id card haka ya k’arasa ya nunawa ragowar y’an sandan dake harabar wajen id card d’insa dan haka a take suka sara masa suka bi bayan sa su ka yi ciki gaba d’ayan su……
…..4 minutes before now.
(Mintuna hu
ɗ
u d
a suka shu
ɗ
e)…
Ana shirin fara d’aura aure
Dpo ya fita domin amsa waya,
kafin minti d’aya sai gashi ya dawo…jikinsa har yana d’an karkarwa.
Da mamaki black snake ya ke kallon sa yana shirin yin magana Dpo d’in ya k’arasa inda yake ya ce
‘’Muna da probl
em fa! an san kana nan’’
Dariya black snake yayi kafin yace
‘’Relax(kwantar da hankalinka), babu wanda ya Isa ya yi arresting ko ya iya dakatar da ni’’
Cikin yin k’asa da murya dpo ya ce
‘’Ban san ya akayi ba, amman Dss ne a hanyar zuwa nan fa black s
nake, sun san kana nan gurin
Sun kusan ƙarasowa ma yanzu haka, sannan oga kwata kwata ya kirani ya ce
In tsayar da koma me ake yi anan
ɗ
in sannan in kama ka!!
da farko ma da suspending d’ina ya yi, sai da na rantse masa akan ban san da case d’in ‘ana ne
man ka’ ba tukunna ya bar ni yace in tabbata na kama ka!’’
Take a alokaci d’aya fuskar black snake ta chanza daga jin batun dpo, cikin fushi ya d’ago yana kallon kowa….sai kuma yayi lissafin ai mutanen nan basu da ƙarfi da hanyar da za su kira someone in
fluential (babban mutum) haka.
Wataƙilan dai wani Abokin hamaiyyarshi ne ya ji labarin zuwan sa shine akayi masa chune!.
Bayaga hakan ma ai tun d’azu yana tare dasu Manubiyan kuma babu wanda ya ga yayi waya a cikin su.
Yana wannan tunanin ya ji dpo yace
‘’Sir,wannan ba lokacin tunani baneba,u need to leave, now!(ya kamata ka tafi, yanzu yanzu).
ka san su kamar aljanu, yanzun nan za ka ga sun k’araso.’’
Cikin fushi black snake d’in ya juya buguzun-buguzun
Ya je shi ya damk’i hannun Manu ya fara janta sa
nnan ya cewa yaran nasa su kamo
Jidda
duk wanda kuma yayi yunk’urin hanasu to su kaishi lahira.
Ya Nafi’u ne ya danne zuciyarsa da kyar ya iya rik’e Ya Musbah dan ya san muddin suka shiga to kashe su mutanen nan za su yi kuma in sun mutu ba za su samu
su kwato su Jiddan daga hannunsu ba.
Da kyar Baba ya iya had’a gaba d’aya k’arfinsa da ragowar kuzarin da ya rage masa ya samu ya mik’e tsaye,jikinsa
yana karkarwa ya tsaya a inda black snake yake k’ok’arin bi ya wuce,yace’’ka kashe ni kawai!
A kan da
i in bari ka tafi da y’ay’ana har biyu a gaban idona, gara kawai ka kashe ni!’’.
Wani wurgi black snake ya yi dashi wanda ya sanya shi ya tafi ya je ya daki gini….
Cikin fushi black snake ya cd
‘’Ban tab’a had’uwa da tsoho mai audacity (tsaurin ido) ir
in ka ba!
kar ka damu ba zan kashe ka ba amma tunda na lura kamar ka fi son wanchan Yaron naka mai kama da kai a cikin y’ayan naka maza to shi zan kashe’’.
Ya yi maganar yana nufin
Ya Musbah.
…Now(yanzu)…
‘’Ba za ka kashe kowa ba black snake’’
Muryar j
ami’in dss d’in da suka shigo taree shi da Yash ta
katsesu, sannan ta maida hankalin kowa gare su.
A take Yashjub ya ji ransa yayi wani irin b’aci na ban mamaki, zuciyarsa ta cunkushe tana tafarfasa sakamokon yadda ya ga black snake ya k’ank’ame Hannu
n Manu,
gashi sai k’ok’arin kwacewa takeyi tana wani irin kuka, kuma ko damuwa ma bai yi ba.
Sannan daga ita sai doguwar riga da hula, wuyanta duk a waje!.
Bai san lokacin da ya k’arasa ya fincike hannunta daga cikin na black snake d’in ba sannan ya ha
nkad’asa gefe.
Wani irin murmushin takaici black snake yayi kafin ya ce
‘’Yashjub!the hero..we meet again!
(Jarumi Yashjub, mun ƙara ha
ɗ
uwa kenan…)”
Banza Yashjub ya yi dashi, kawai ya juya inda ya hango hijabin da ya gani a yashe wanda yake da tabbacin
na Manu ne, ya k’arasa ya je ya d’auko ya mik’a mata yana mai k’ok’arin danne fushin sa.
Dai dai nan jami’in dss tare da dandazon y’an sandan da suka biyo bayan su da shi da Yashjub suka yi kan black snake
Ba tare da tantama ba
Black snake ya harbi s
s d’in a ciki
wanda hakan ya sanya gaba d’aya y’an sandan suka rufar masa, dama rabi a cikinsu duk bakinsu d’aya da dpo ba wai son kama black snake d’in sukeyi da gasken gaske ba.
Ai kuwa hakan ya bashi dama da shi da tawagar sa suka fice da gudu
Bayan
ya kalli Baba ya ce masa “zan dawo d’aukar matata, nan ba da jimawa ba’’
Da sauri Yashjub yayi kan jami’in da aka harba, ganin
yana motsi yasa yace gara a yi sauri danne gurin su kai sa mota a wuce dashi asibiti.
Shi kuma ya bi bayan su black snake da g
udu
amman ya na zuwa
sai k’urar motocin su kawai ya tarar.
‘’Damn it!!’’
Ya furta da k’arfi, yana jin
takaici kamar ya kurma uban ihu.
Dai-dai nan motar Najeeb ta k’araso cikin harabar gurin tare da dandazon motocin jami’an dss.
Najeeb yana k’arasow
a yace
‘’Kar ka damu,rabin motocin sun bi su,za’a kama shi in sha Allah,bai dai tab’a kowa ba ko?’’
Cikin b’acin rai Yashjub ya ce
‘’Ya harbi mutane uku’’
A rikice Najeeb yace’’subahanaallah,da wa da wa?? ina Manubiyan take?’’
‘’Tana ciki!’’
kawai Ya
sh ya iya cewa,
daga haka ya juya ya nufi ciki
bayan ya kira ambulance,
dan wani irin takaici yake ji,ya riga ya san dole ba za a iya kama black snake ba.
Suna shiga polisawan da wasu a cikin ss d’in suna fitowa d’auke da jami’in da aka harba.
Statement
ya tarar ragowar ss d’in suna karb’a a wajen ya Musbah da ya Nafi’u yayin da Jidda da Manubiya suke kuka suna dudduba Baba.
Dukda abunda black snake ya aikata sai da Yashjub ya karb’i acc number d’insa a wajen dpo ya tura masa 1 million d’insa da yake b
in Baba, bayan ya ji bayanin komai da ga Bakin dpo.
Zuwa wannan lokacin gaba d’aya ran Yashjub ya kammala b’aci daga jin bayanin, tabbas in da ace zai ga black snake yanzu to kuwa in bai kashe sa ba sai ya sumar da shi, musamman ma da ya ji cikakken laba
rin maganar auren da ya so a d’aura masa shi da Manubiya!…
‘wato da niyyar auren Manubiya ma yake yi!’
Idan ya yi tunani akan
‘Black snake d’in fa yayi tunanin auren Manubiya, kenan
ta kwanta masa shima son ta
yake yi’,
sai ya ji kamar ya bazama ya ne
mo shi ya chaka masa wuk’a.
Dan mai yasa zai yi wannan tunanin a kanta!.
how dare he!.
*MANNUBIYA*
*38*
Shiyasa har aka gama case
ɗ
in….aka gama karb’ar statements d’in su,
suka nufi asibiti sam fuskarsa babu walwala!
Ya had’e girar sa
ma da ta k’asa, ko magana ma ya daina yi.
Private hospital aka nufa da Baba da Abbakar, suna zuwa aka karb’esu emergency.
……
Wayar da Yashjub ya yi aka tabbatar masa da ‘black snake ya gudu, ba a samu damar kamasa ba’
ne ya sake harz
uk’a shi.
Dukda halin da take a ciki sai da ta lura da shi dama tun
ɗ
azu..
yanzun kuma ta tabbatar wayar da aka yi masa ce ta sake b’ata masa rai…
So take yi atleast (ko ma ƙa-ƙa dai)
ta je ta ce musu sun gode, dukda ta ga su Ya Musbah sun yi musu godiy
a sosai har kar
ɓ
ar nambobin juna ma taga sun yiyyi, amma dai dukda haka ya kamata su je su yi musu godiya suma ita da Jidda, sai dai kuma tana shakkar kar ta je ya maketa!
Dan in ba lokacin da su ke exchanging numbers shi da su Ya Musbah ba to bataga ya
saki fuska dede da na second d’aya ba!…Sannan kuma
tana jin kunyar sa dan in ta tuna abunda ta yi masa jiya da safe gaba d’aya sai ta ji wani iri babu dad’i! duba da yadda yanzu yake tsaye tsayin daka akan al’amarin da ya kusan tarwatsa rayuwarta da ahali
nta.
Gashi yanzun kwata-kwata bata hango walwala a tare da shi ba,
masifa ya ke yi wa kowa hatta sir Najeeb yanayin yadda ta ga yana masa magana kamar zai rufe sa da duka take gani….
waennan dalilan ya sanya ta d’an dakata tana mai tunanin ta yadda za ta
yi masa godiyar.
Sallar la’asar aka kira, dan haka gaba d’aya Mazan suka fita masallaci, su kuma suka nufi band’akin da suka tambaya aka nuna musu…
Sallah kuma suka nemi waje inda babu mutane sosai, suka gabatar da ita cikin nutsuwa.
Bayan sun idar sukay
i addu’oin samun lafiya wa Baba da Abbakar, har ma da Inna.
Basu dad’e da dawowa wajen ba su Yashjub ma suka shigo, shi da
sir Najeeb su Ya musbah a bayansu.
Ba k’aramin dad’i Manubiya ta ji ba, dan bata yi tunanin za su dawo su jira har sai an gama tre
atment d’in su Baban ba,
hakan ya sanya har bata san lokacin da murmushi ya sub’uce mata ba, tana murmushin tana kallon Yash d’in….
dai-dai shi kuma ya d’ago kansa shima da niyyar ya d’an saci kallon ta ai kuwa karaff suka had’a ido da ita tana kallon sa t
ana murmushi.
Da mugun sauri ta sunkuyar da kanta k’asa, ta fara wasa da y’an yatsun hannun ta…
murmushi sosai ne ya kufcewa Yash wanda har sai da sautin murmushin ya fito fili!
Dasauri sir Najeeb ya d’ago yana kallon sa…
ganin inda yake kalla yana murmus
hin ne yasanya Najeeb d’in yin wata y’ar guntuwar dariya kafin ya ce ’’Romeo, a asibitin ma ba za’a d’aga k’afa ba?’’
‘’Hmm’’
Kawai Yashjub ya iya ce wa Najeeb, dan gaba d’aya Manubiya ta sanya shi a wani yanayi, shiyasa ko iya juyawa ya kalli Najeeb d’i
n ma bai yi ba, saboda gaba d’aya idanuwansa da hankalinsa kacokam suna akan ta ne!
So yake ta sake d’agowa ya kalleta amman sam tak’i, ta ma yi k’asa da kanta sosai.
Ganin ta ƙi d’agowa shi kuma zullumi yana shirin susuta shi ne ya sanya kawai ya nufi i
nda take.
Dama kuma yanata so ya d’an yi mata maganar ‘ko akwai wani abun bayan wanda dpo ya gaya mishi’ amma ya lura tanata kuka, shiyasa ya d’aga mata k’afa saboda jin kukan nata yake yi har cikin ransa a lokacin da take yi….dan har ga Allah ya san in ya
je kusa da ita tana wannan kukan to tsaf za’a iya samun matsala, kukanta yana cikin abubuwa mafi munin da baya buk’atar gani a duniyar nan…….
A take Manubiya ta fahimci inda take yake nufowa, dan haka tashi d’aya fargabarta ta k’aru, dama ga fargabar jik
insu Baba dan ma an tabbatar musu da jikin na Baba
Ba wani abu me muni bane
Abbakar kuma yanada rai.
Tana wannan tunanin ta ji shi a tsaye a kanta, ji ta yi kamar ta mik’e tsaye ta ruga a guje.
Ba ta ida jan numfashin da ya mak’ale take kokawar janyoshi
da kyar ba ta ji yace’’in zauna??’’
Dakyar da mugun kyar dan sai da ya sake maimaitawa tukunna ya ga tad’an matsa kusa da Jidda sosai sannan ta ce masa’’eh’’ a hankali.
Murmushi yayi kafin a hankali ya nemi gefenta da d’an tazara kad’an ya zauna cikin
nutsuwar sa bayan yayi bismillah.
Yanayin zaman da ta yi sai da ta bashi dariya,
ya lura da yadda ta wani zabura lokacin da ya zauna d’in ma sannan ta kuma matsawa jikin Jidda sosai.
Murmushi kawai yayi, ya amsa gaisuwar Jidda yana mai kallon ta
a hankali
ya ji tace’’Mun gode sosai, Allah ya saka da alkhairi’’
Murmushi ya yi kafin ya ce ’’ba komai, Allah ya kare gaba ya ba su lafiya’’
‘’Ameen’’ ta ce,daganan ta yunk’ura zata tashi dan ta lura kamar yana d’an bukatar space da Manubiyan amma sai ta ji Manub
iyan ta yi saurin damk’ar Hannunta ta rik’eta gam.
A hankali Jiddan ta gyara ta zauna a wajen ba dan ta so ba,
itama ta sunkuyar da kanta ta shiga wasa da bakin hijab d’in jikinta…
Har ga Allah ta jinjinawa Yashjub da abunda ya yi musu,
dan tun d’azu da
Manubiya ta ce mata ‘ai shine wanda take yi wa aiki’
Jiddan take ta mamaki, dan a ganinta a zamanin nan na yanzu wanne employer (Oga) ne yake damuwa da matsalar employee d’insa (ma’aikatansa) har haka, a take wata zuciyar kuma sai ta ce mata ‘’kodai!kodai!
!’’ dan haka ta d’an yi murmushi ita kad’ai, ta ci gaba da lissafe