Showing 96001 words to 99000 words out of 150519 words
Yaran nan, dan yanzu kam babu batun kwana kwana saboda ana ji na tambayi kwatancen gida za a fahimci inda muka dosa…”
Gaba d’aya hankalin Abbakar tashi ya yi, tunda Sir Najeeb ya kira sa ya tambayesa kwatancen
gidan su Manu.
ji yake in
ama bai yi wa sir Najeeb
ɗ
in kwatancen ba…tsabar halinda yake a ciki tashi d’aya idanuwansa suka ka’da su ka yi jajawur.
Ya tsani abunda zuciyarshi ta gama aiyyana masa akan ya yi,
amman kuma bashi da yadda zai yi..
ya san abunda yake shirin aikatawa bai
kamata ba amman fa zuwa yanzu ya fahimci hukuncin da ya yanke kwanakin baya ba shi ne mafita ba!
don tun kafin a je koina ya fahimci idan bai d’au mataki ba tou tabbas hakan na iya zamtowa ajalin sa.
Ba ya so! sam baya k’aunar abunda zuciyarsa take gaya
masa take saka tunzura sa akan ya aikata dan ya san hakan bai dace ba amma kuma babu yadda ya iya, dan haka ya d’ago wayar tasa ya bi number sir Najeeb wadda ya kira sa da ita yanzun ya danna call….
Najeeb yana zaune a office d’inshi yana duba wasu taka
rdu Yashjub ya shigo tare da sallamar sa…
Murmushi kawai Najeeb
ɗ
in ya yi ya mik’e yana kallon sa kafin ya ce ’’na Manubiya bada kanka a sare’’.
Kallon sa kawai Yashjub ya tsaya yana yi, dukda ya ji dad’in furucin nasa amman kuma yadda ya gansa ba a shir
ye chap ba ne ya b’ata masa rai!
Dan haka cikin rashin jin dad’i ya ce ‘’Najeeb, ni da nake tunanin zan same ka a parking lot amma shine kalla ko socks babu a k’afarka ballantana takalmi sannan duba suits d’inka a gefe!
Ina wayarka? Itama na san sai ka nem
o ta ko??’’.
Dariya Najeeb ya yi, sannan ya yi sauri ya saka socks d’in ya d’auka suit d’in da takalminsa ya rik’e a Hannu tukunna ya d’au wayarsa da makullin office d’in ya na me kashe computer ya ce ‘’muje Oga’’
ya fad’i hakan yana dariya.
Suna fita a
office d’in ya samu ya saka takalminsa sannan ya rufe office d’in ya bi bayan Yashjub wanda ya riga ya yi gaba da d’an sauri, yana tafe yana saka suit d’in tasa.
Suna shiga motar, Yashjub yana shirin yi wa motar key kira ya shigo wayar Najeeb….
bai d’auk
a ba dan baya buk’atar takura a yanzu saboda yana so Yashjub ya bashi labarin mai ya faru tsakanin sa shi da Manubiya da ya rikice ya gigice har yake buk’atar zuwa gidansu da gaggawa haka!…
Ganin an kira har sau biyu bai d’auka ba sannan ga na uku ya shi
go ya sanya ya zaro wayar yana mamakin waye ne haka..
ya d’an yi mamakin ganin sunan Abbakar da yayi saving d’azun, dan haka ya d’auka ya kara a kunnensa ba tare da ya ce komai ba.
Daga d’ayan b’angaren Abbakar ya ce “Assalam alaikom, Sir!
Ɗ
azu na ji ka t
ambayeni gidan su Manu, shine ban sani ba ko zuwa za ka yi?’’
Sai da Najeeb ya
ɗ
an juya ya kalli Yashjub wanda ya cilla kan motar ga titi tukunna ya d’an jinjina kai kafin ya ce ’’Eh,muna hanya ma’’
Dum!! Haka k’irjin Abbakar ya buga, ya ma kasa magana,
ya kasa cewa komai..kafin da kyar ya samu ya ce ‘’yanzunnan su ka tafi k’auye, gaba d’aya y’an gidansu, sai jibi
Za su dawo’’.
Shiruu Sir Najeeb ya yi, yana d’an nazari kafin ya ce ‘’okay shikenan, ma zo jibin idan sun dawo’’
Daga haka ya kashe kiran ya
juya ga Yashjub wanda yake tambayar sa “kai da waye ne?”.
Shiruu Najeeb ya
ɗ
an yi, yana so ya fahimci wani abun game da Abbakar…kafin kawai ya kalli Yashjub sosai, sannan ya ce’’ba fa sa nan, yanzunnan suka tafi k’auye’’
K’iiiiii!!!! haka Yashjub ya ja
burki, tukunna ya juyo a d’an fusace ya cewa Najeeb d’in ‘’kuma shine ban ji ka tambayi wanne k’auye ne ba?ko ka san k’auyen?’’
Ɗ
an ƙuraa masa idanu Najeeb ya yi yana kallon shi kafin chan ya ce
‘’idan na tambaya zuwa za mu yi?’’
‘’Ba tare da b’ata lo
kaci ba ma kuwa’’
Yash d’in ya ba sa amsa ya na me matsar da motar tasa gefen titi dan ya tare hanya har ya fara tara goslow.
Sannan ya sake cewa Najeeb
‘’Wai tunanin mai kake yi ne?, ka kira da wuri mana mu samu mu kama hanya time is against us(bamu da i
sashshen lokaci)’’ ya fad’i haka yana kammala parking d’in sannan ya juyo ya zubawa Najeeb lumsassun idanuwansa!.
Sai kuma cikin fushi sosai ganin Najeeb d’in still shi yake kallo sannan yak’i ya sake kiran wayar ya ce
‘’Bani number in kira su, bani man
a da wuri ‘’
ya fad’i haka yana mik’awa Najeeb hannunsa.
A hankali cikin kwantar da murya Najeeb ya ce ‘’dan Allah, ka d’an nutsu ka sarrafa komai ko da ace na mintuna biyar ne a cikin kwakwalwarka,
saboda ita kanta idan ka wanke k’afa ka bita har k’auyen
su a haka tou akwai matsala,
ka tsaya ka fad’a min abunda ya faru sai a san abun yi, dan Allah.’’.
Shiruu Yashjub yayi, kafin kawai ya d’auke kai!
dan in ya biyewa jayayya da Najeeb yaga alamar ransa ne zai sake b’aci…
A hankali ya kwantar da kansa a ji
kin seat d’in da yake zaune a kai…
sun kusa mintuna talatin a haka kafin Yashjub ya gyara zamansa ya kunna motar ya ja suka koma inda suka fito.
Har ya sauk’e Najeeb bai sake kallon inda yake ba haka nan ya juya ya wuce ko sallamar Najeeb d’in bai tsaya
ya amsa ba,
girgiza kai kawai Najeeb yayi daga haka ya nufi tasa motar ya shiga yayi mata key shima yayi gaba yana mamakin Yashjub da zazzafar soyyayar Manubiya wadda ya lura ta d’an fara tab’a masa Aboki…
Zuwa wannan lokacin Najeeb ya fahimci k’arya Abb
akar ya yi masa dan sai yanzu ya tuna suna da exams ma yau da safe around 9 yanzu haka ma maybe sun shiga, but baya so Yashjub ya je wa manubiya a haka dukda bai san me ya had’a su ba, zai bari in Allah ya kaimu gobe sai ya je ya lallab’a Abokin nasa ya fa
d’a masa me ya faru daganan su san abun yi dan a yadda suka rabu da Yashjub ya san ba zai tab’a sauraron sa yau ba.
Lamarin Abbakar kuma akwai sark’ak’iya.. ya lura Manubiyan kanta tana ji da shi, shiyasa yake so ya nemi bakin zaren ya san abunyi dan ya s
an idan Yashjub ya san wani abun tou abun ba zai yi dad’i ba shi kuma bayaso Yash ya samu matsala da Manubiya saboda wani Abbakar…..
In banda ciwo ba abunda kan Yashjub yake yi, tashi d’aya idanuwansa suka kad’a suka yi ja,
in da ace zai san inda Manu
biyan take to da sai yaje….
Kawai dai ya tabbatar tunda Najeeb ya masa haka to fa ba zai tab’a fad’a masa ba shiyasa kawai ya hak’ura ya yanke shawarar ya tafi gida yayi sabon shiri……
Yau ma kamar kullum haka Manubiya ta tartara Abbakar ta zuba a kwandon
shara, tak’i kula shi.
Ya riga ta kammalawa dan haka yana gama submitting ya yi sauri ya d’auke jakarta daga inda ake tara jakankuna ya fice ya tsaya jiran fitowar ta.
A wajen ta same shi yana tsaye yana jiran fitowar tata.
‘’Ba ni jakata’’ shine kaw
ai abunda ta ce da shi cikin tsare gida.
Murmushi ya yi ya k’arasa inda take tsaye kafin ya ce
‘‘Ki yi hkr tou, dan Allah’’
‘’Ba komai ya wuce Abbakar,
kawai dai na ji haushi ne..bai kamata kai, musamman kai ba wai ace ka b’oye min abu irin wannan ba .s
hiyasa na ji zafin
abun, yanzu kuma na huce
so ba komai ya wuce.’’
A hankali cikin sanyin murya da mutuwar jiki sannan idanunsa a kanta kyam ya ce
‘’Sure?
ba za ki tambaye ni dalilinna na yin hakan ba??’’
Da sauri ta ce ’’komai ya riga ya wuce, in da
ace bai wuce ba da ko kallon ka ba zan yi ba kai ka san halina, tunda har ka ga na kula ka tou ya wuce kenan, kuma bana so ka sake yin maganar’’
Ajiyar zuciya ya sauk’e, ahankali yace ‘’Thankyou’’
‘’Um’’
kawai ta ce, daganan ta yi gaba shi kuma ya bita
rike da jakartata a hannunsa, suna tafe suna d’an tab’a hira.
Gaba d’aya Abbakar haushin kansa yake ji na k’aryar da ya yi wa sir Najeeb sannan bayaga hakan ga ta nan a gaban sa amman ya kasa fad’a mata abunda yayi, shi sai yanzu ma ya yi tunanin watak’i
la fa sir Najeeb d’in zai iya ganin su a cikin makarantar kuma tare dan haka yayita addua Allah yasa har su fita kar su had’u da shi.
Kafin su k’arasa gida har sun shirya kamar basu tab’a yin fad’a ba.
Manubiya ta lura da waensu ƴan change-change daga Ab
bakar tun ba ma da ta ba sa labarinta da Yashjub na yau ba!
dan tashi d’aya ta ga
gaba d’aya hankalinshi ya tashi kuma ransa ya b’aci, saboda sam ya kasa danne kansa wannan karon…
ta so ta tambaye shi sai kuma kawai ta kawar ta basar da zancen ta sako wa
ta hirar..
Da kyar Abbakar ya dinga yak’e har suka isa gida, ya yi mata sallama tare da fatan hutu mai albarka daga nan
ya wuce gida shima.
Dakyar ya iya k’arasawa ya tsaya ya gaisa da mamansa wadda take zaune a tsakar gida daganan ya koma d’akinshi
da ke a soro, yana shiga ya tura k’ofa ya sak’ala sakata tukunna ya saki zafafan hawayen da yake ta k’ok’arin dannewa tun a makaranta…
bai yi tunanin ba zai iya hak’ura da Manubiya ba sai yanzu, tsananin k’aunar da yakeyi mata ne yasanya ya hak’ura yayi s
aurin had’a ta da Yash.
A ganin sa da lissafin sa…
na farko Manubiya ta fi k’arfin sa!
sannan kusan age mates suke (shekarunsu
ɗ
aya) shi da ita dan ko kwak’kwaran watanni biyu bai bata ba,
sannan a kalar matsin rayuwa da wahalar da Manubiya ta sha ya kama
ta ace ta auri mai arzik’i ta yadda zata kula da kanta da ahalinta itama ta samu ta huta ta ji dad’in rayuwa,
Waennan dalilai su suka sanya ya hak’ura da ita domin ta samu ta ji da
ɗ
in rayuwa kuma ya yi saurin had’ata da Yash dan a tunaninsa zai iya saka fa
rin cikinta a saman nashi kuma ya zauna ƙalau sannan yana zaton idan ya had’a ta da wani ya ga tana farin ciki tou zai hak’ura ya samu zuciyarsa ta samu salama
sai dai kuma a tashi d’aya a iya yau kad’ai ya fahimci abun ba haka yake ba!!
kuma ya fahimci
ya tafka babban kuskuren da in dai bai gyara ba to shine ajalin sa….
Tunda gashi tun yanzu ya fara shiga tashin hankali Ina kuma ga in soyayya ta yi nisa tsakanin ta da Yash….?..
…
Ya yi kuka ranar kamar ransa zai fita, kafin daga baya ya yi shiru ya shig
a duniyar tunanin nemawa kansa mafita
dan tabbas da sake…..
*MANNUBIYA*
*33*
Manubiya Tana shiga gida ta d’auki kud’in da Baba ya bata na Ammi ta nufi gidan, dan bata samu ta tsaya sun yi magana ba d’azun.
Tana shiga ta tarar da aiki
birjik!!
Ammi ta hana d’ayar mai aikin nata tab’awa, dan hadda natan ma tace duk ta ha
ɗ
a ta barwa Manubiya yau duk ita za ta yi ..
Wai punishment d’in lettin da ta yi kenan..
haka nan suka zauna babu wanda ya had’a tsinke da tsinke a cikinsu, ana jiran Ma
nubiya ta zo ta yi, dan Ammi ta fusata yau da lettin da Manubiyan ta yi ba da wasa ba, hakan ha sanya ko da Maama ma ta saka Baki wannan karon Ammi ba ta saurare ta ba dan haka itama maman sai ta kyaleta dan ta lura yau matar tijara take ji.
Ba k’aramin
tashi hankalin Ammi ya yi ba, da ta ji wai su Manubiya za su bar aiki…..
babu damar ta ce bata yarda ba tunda dai ga kud’in ta an riga an bata..
dan haka ta shiga gaggaya mata maganganu, ta hakan ne ta samu ta d’an rage takaici kuma tace sai ta yi aikin
yau!!
Manubiya so take su rabu lafiya dan haka ta yi aikin ta gama tsaf ta je ta yi mata sallama…
Bak’in ciki a gun Ammi kamar ta d’aura Hannu aka ta yi ta kurma uban ihu.
Har k’ofa maama ta rakota, matar ta ji dad’in aikin da Manubiyan ta bari saboda ta
lura Ammi so take ta wahalar da yarinyar dan ko Muhsin k’iri k’iri ta hana sa shigar mata cikin gida idan ya zo ko Manubiya baya samu ya gani dan iyakar sa tsakar gidan, yayi shara ya tafi,a cewarta ba ta so namiji ya shigar mata cikin parlour da kitchen
ba…….
•••••
Zuwa yanzu Yassir ya warke garau, dan har ya koma office ma.
Ba k’aramin tashi hankalin Mommy ya yi ba ganin yadda
Yassir ya k’ulla gaba da Yashjub!
gashi Daddy ya ƙi ya sa Baki….
Ita ta rasa wanne irin dak’ik’in Yaro ne Yassir wanda ba a isa
a gaya masa ya ji ba,
sam ya k’i yarda da ita akan ‘ya hak’ura ya kula d’an uwansa..’
ta san muddin Yashjub ya tsame Yassir a lamarin shi Wallahi in ba da kyar ba
sun rabu kenan har abada.
Gashi yanzu ita kanta Yashjub d’in fushi ya d’auki yi da ita g
adan-gadan tunda ta mare sa sannan ta yi waennan furucin garesa duk akan Yassir, shikenan
ko sunanta baya kira!
Iyakaci ya ce mata Ina kwana ko Ina wuni ruwanta ne ta amsa ruwanta karta amsa.
Ita kanta ta fara da na sanin marin da ta yi masa da furucin d
a ta yi, dan gashi sun janyo mata ya k’ullace ta!
ita gani take yi ma kamar gaba d’aya ya tsaneta….
kamar ba uwar da ta tsugunna ta haife shi ba!
Shiyasa gaba
ɗ
aya duniyar ta yi mata zafi.
…
Tsakanin Ummi da yaran gidan ma abun ba dad’i sam, d’azu
da safe
har bangajeta Kausar ta yi ..
Yassir ma ya samu gindin zama a wajen Munirat,
tun bata kula shi har ta zo ta fara kula shi sakamokon nacin da yake yi mata, sannan duk wani abunda ya san zai janyo ta so shi to shi ya ke yi tun ba ma da ya lura tanaso ta ga
yayi repenting akan abunda yayi ba dan haka ya maida bata hak’uri d’abi’ar sa ba dare ba rana…
kullum sai sun had’u a wajen dining kitchen har back yard binta ya ke yi in ta fita shan iska.
ta sake da shi kuwa, dan
Munirat irin matan nan ne masu raunin
zuciya ga tausayi,
kuma Yassir ya ci sa’a dan tun a ranar farko kyawunshi ya tafi da hankalinta, yanzu kuma kulawar sa da tausayin sa sun k’ara ingiza ta
zuwa gareshi.
A ranar da Ummi ta ganta ta fito daga d’akinshi, ta ja mata kunne sosai, ta kuma h
anata shiga d’akin shi!
Gaisuwa ta mutunci dai tunda ya nuna yanaso a yi su yi,
amma ta tabbatar mata da ‘kar ta sake shigar mishi d’aki dan yin hakan ba dabi’a mai kyau bace ba…’
Ita kanta Munirat ta yi mamakin yadda ta kasa gayawa Ummi dalilin da ya sa
nya Yashjub ya daki Yassir a wannan ranar….
Wataƙila ko dan bata so Ummin ta tsani Yassir d’in ne, ko kuma ta ce za ta raba su har abada…
Ita kuma Ummi bata tambaya ba, kawai a tunanin ta fad’an su ne ya had’o su shi da Yashjub d’in.
….
Da Allah ya tashi k
ama Munirat kuwa, ranar Yassir ya biyo ta har d’akinta akan ta zo su je d’akinsa yanada surprise d’in da zai nuna mata..kawai sai ga Ummi ta shigo d’akin a daidai lokacin da Yassir ya janyo hannun Munirat
ɗ
in ita kuma mistakenly ta fad’a jikinsa.
Da kyar
Ummi ta
ɗ
an danni kanta ta cewa Yassir ya basu waje, ya na fita kuwa Munirat tana shirin yin magana Ummi ta wanka mata mari sannan ta rufeta da fad’a, kuma ta ce “ta bata sati biyu, ta fito da miji a yi mata aure..”
Ba abunda ya f
i b’atawa Munirat rai irin yadda Ummi ta k’i tsayawa ma ta saurareta, da kuma yadda ta yi zargin wani abun su ke yi ita da Yassir d’in…..
..
Munirat ta ci kuka kamar ranta zai fita, dan bayan Ummi ta tafi da kamar awa d’aya ta kira yayarta za ta labarta ma
ta amman sai ta ji itama yayar tata ta rufe ta da fad’a ashe har Ummin ta kirata ta kora mata jawabi….
sai da ta yi mata fad’a sosai, tukunna ta kashe wayar ko sallama ba ta tsaya sun yi ba..
Ranar haka y’an gidan suka gabatar da dinner d’insu babu Ummi
babu munirat…
Kausar kamar ta zuba ruwa a k’asa ta sha.
Tabbas ta fara hango silver lining(alamun nasara) ba kamar da da komai yayi musu du
ɗ
um!!!.
Sai k’arfe sha biyu na dare tukunna Munirat ta sauk’o k’asa