Showing 63001 words to 66000 words out of 150519 words
ya ce
‘’Wacce irin Mace ce ke?
Eh?
Ash
e son kan naki har ya kai haka?’’
‘’Yarinya ta yi laifi k’iri-k’iri amma kina k’ok’arin b’oyewa?’’
Sai da ya kalle su tukunna ya juya ga Ummi ya ce
‘’To laifi mana, in ba haka ba lokacin da ta je ta ji ya fara yi mata maganar banza ai kamata yayi ta ba
r gurin ko?
A matsayin shi na wanda yayarta za ta aura’’
Yadda yake mata ihu da hargagi da kuma tuhumar Munirat akan abunda bata tab’a tunanin zai yadda ta aikata bane
ya sanya wasu zafafan hawaye zubo mata cikin d’acin zuciya ta ce ’’Daddy tuhumar ta ka
i ma kakeyi?
wanne kalar asiri ne zai juyar da lissafin Mutum mai
kimanin shekarunka a cikin lokaci k’ank’ani haka?’’
Cikin b’acin rai da d’acin zuciya ta share hawayenta kafin ta d’aura da cewa
‘’Maybe sai dai ko irin wanda akayi maka aka juyar da kanka
daga gare ni ne kwana biyu’’.
BULAMA ✍
️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*22*
‘’Babu irin wannan a tsarin mu,
ke kan ki kin san inda ace muna irin haka Wallahi da baki Isa shigowa ki taho har da agola cikin gidan nan
ba.
Sannan duk abun da za ki yi, ya tsaya a iyaka kanmu amma kar ki kuskura ki sako Mommy’’
Cewar Ya’isha.
Cikin jaddada mata Kausar ta ce
‘’Tabbas, dan in dai kika tab’o Mommy to kuwa muma ba za mu ji shakkar rama mata ta ko wacce hanya ba…
yanzu dai
a komawa maganar da ake yi tun farko dan naga alamar so kike yi a rufe lamarin Munira.”
Da mamaki Ummi take kallon Daddy wanda sam ya kasa tsawatarwa ya’yan nasa.
Su kansu su Yashjub sun d’an ji
mamakin sa.
Yusra ce ta k’arasa ta juyo da Munirat wadda
take ta faman kuka ta ce
‘’Munirat tun muna shaidar juna mu da ke….’’
Cikin fushi Munirat d’in ta fincike hannunta sanann ta katse ta ta hanyar cewa
‘’Kar mu shedi juna daga yau dan Allah ki yi duk abunda kika ga dama, ki illatani ta yadda ba ke kad’ai b
a kowa ma ba zai iya sheda ni ba’’
“Munirat wai ya ana k’ok’arin gyara abu kina turjewa ne?
kin fi kowa Baki da Zuciya ne? we are all the same (duk
ɗ
inmu
ɗ
aya ne) anan, so kar ki yi tunanin wai ko ana k’ok’arin nuna miki bambanci ne, ko waye a cikin sist
ers d’ina yayi irin abun da kikayi dole irin haka za a yi mata!!!!
We all love Yahanasu (duk
ɗ
inmu muna son Yahanasu) dan haka ya kamata mu tsaya mu fahimci juna a samu a gyara abun da kike son ki b’ata’’
Yasira ta ce tana mai k’arasowa inda
Munirat d’in
su ke tsaye ita da Yusra.
Ta bud’e Baki za ta yi magana kenan cikin d’an d’aga murya suka ji Yahanasu tace’’Ya isa haka’’ sanann ta k’arasa inda Yasirar ta ke ta saka Hannu ta juyo da ita tukunna ta fara magana “Da ni da ke da kowa duk an san daga ke har
Kausar d’in ba ku wani damu da ni ba!
Infact har su Ya’ishan suma duk ba damuwa suka yi da ni ba!
Dan haka
na rok’e ku da girman Allah kar ku yi amfani da ni wajen baiyyana abun da yake a ranku game da su Ummi…
Alh Bashir da farko ya ce yana so na yanzu
kuma ya ce ya fasa Munirat yake so!!!
Ni har ga Allah ban ga wani abun tashin hankali anan ba…
iyaka kawai mu yi musu addu’ar Allah ya basu zaman lafiya shikenan magana ta k’are!!!
Dan Allah kar wanda na sake ji yayi amfani da bak’in jini na da bad luck d
’ina wajen nuna real face d’in shi!!…
ku bar ni in ji da abun da yake damu na’’
Ta fad’i hakan wani irin kuka yana sub’uce mata da mugun k’arfi.
A hankali Yashjub wanda ya k’araso yanzun ya sa Hannu ya juyar da ita ya rungume ta yana jin wani tsananin b’
acin rai da takaicin senator Bashir suna taso masa.
Cikin kuka ta ce
‘’Yash dan Allah ka ce su daina maganar nan, su bar shi ya auri Munirat d’in su dena maganar bana so, suna rubbing salt a wounds d’ina (suna fama min gyambon da ke a zuciyata) ne, sana
nn dan
Allah kar wanda ya sake ce min in yi aure, dan Allah dan Annabi’’
Wani kalar kuka abun tausayi take yi wanda yasa gaba d’aya jikin Daddy wanda ya harzuk’a ya fusata ya yi sanyi haka ma Mommy da Ummi duk sai jikin su ya yi sanyi.
Munirat kuwa ji t
ake kamar ta je ta chakawa senator wuk’a!
Yahanasu is the most nice calm and friendly person da zata ce ta tab’a had’uwa da a rayuwarta, gashi jinin su ya had’u matuka …..
A hankali Yashjub ya ja ta tana a rungume a jikinsa suka wuce d’akinta.
Suna wuc
ewa Ummi ta ja hannun Munirat suka wuce sama suma.
Gaba d’aya kuma kallo sai ya koma kan Yassir wanda tun
ɗ
azu da suka shigo ya gagara janye manyan idanuwansa daga kan Munirat.
Ganin duk sun tsura mishi ido ne ya sanya ya d’an sunkuyar da Kai ya fara so
sa k’eya kafin da kyar yace’’Daddy I’m sorry for..”
Kafin ma ya rufe Bakinsa tuni
Daddy ya zo ya wuce shi ya fice daga gidan gaba d’aya dan a wuya yake dama Ummi, bata san a cike yake da itaba kwana biyun nan dama, haka kurum yake jin takaicin ta!
yanzu
kuma ji abun da ta yi,
ta wani bud’e Baki tana cewa ai itama Munirat marainiya ce
sannan har tana da Bakin cewa wani an juya mishi tunani akanta,duk irin yadda yake k’ok’arin bata kulawa amma sam ita bata gani how dare she!!!!
tunda yake da Mommy bata tab
’a yi masa irin haka a gaban Yara ba amma ita ta iya bud’e Baki yana fad’a tana fad’a….
y’ar shi tana cikin wannan halin kalli yadda Mommy take tausaya mata amma ita tata y’ar kawai ta sani.
Yahanasu batayi deserving haka ba y’arshi mai hankali nutsuwa da
sanin ya kamata, cikin fushi a fili ya ce
‘’Allah ya tsinewa Alhaji Bashir’’
……
Daddy yana fita Mommy ta k’arasa inda Yassir yake tsaye ta hau duddubashi kamar wani k’aramin Yaro, idanuwanta suna kaiwa kan wuyansa wanda har zuwa wannan lokacin yake nan j
ajir ta rikice ta hau tambayar sa abun da ya same shi.
‘’A hankali ya ce ‘’Mommy I’m fine, favorite son d’inki da kika tura ne ya je ya jiwa Abokai na ciwo ya sumar da d’aya sannan nima ya shak’eni da kyar aka kwace ni daga hannunsa, da tuni yau sai dai ki
ga gawa ta.”
Kamar zai kurma ihu ya d’aura da cewa “da kika san yana da anger issue da sai ku taho tare ke da shi ta yadda ko haukar tasa ta motsa za ki iya shiga tsakanin mu, na san in kina nan
maybe ya d’an nutsu’’.
Cikin rashin jin dad’i Mommy ta ce
“Subahanallah, wallahi Yassir ban san zai yi haka ba…
I was so worried ne (na damu ne sosai) shiyasa na barshi ya je.
ga shi naga Daddynku yana neman mantawa da kai ma gaba d’aya tun da yayi aure
komai ya lalace bai damu da ni ba ma kai kam ko zancen
ka baya yi,wannan Matar da ka gani auntyn ku ce ….’’
Cikin katse ta ya ce
‘’Yeah na fahimta daga shigowata da kuma scene d’in da na yi witnessing (abunda na gani)”
A hankali ya kama lips d’inshi na k’asa ya d’an ciza kafin ya d’ago idanuwansa ya sauk’e
a kan k’annen nasa waenda sukayi cirko-cirko.
A hankali Baabaa Larai ta k’araso ta ce
‘’Ka ji maganar mahaifiyarka ka ji d’an albarka, duk abun da
Babba ya hango Yaro ko ya hau kan dala ba zai gani ba!
kar ka sake yunk’urin barin gidan nan.
Yanzu loka
ci ne da ya kamata ace kun had’a kai da mahaifinku kun shiga jikin shi sosai, dan duk wanda ya yi gangancin yin nesa da shi to kuwa kanshi yayiwa.’’
Tana gama fad’in haka ta kama hanya ta wuce d’akin Yahanasu.
A hankali su Yadira Yusra da Yasmeen suka mat
so kusa da su suka ce
‘’Welcome home Ya Yassir(Sannu da zuwa Ya Yassir)’’
Sannan Yasmeen ta ce ‘’we missed u(mun yi kewarka)’’ tana d’an murmushi.
Kallon su kawai ya yi, daga nan ya maida duban sa ga Kausar wadda ta d’an tsura masa ido tana
mamakin rama
r da ta ga yayi.
Yana kallo ta ya ce
‘’Mommy bara in je in watsa ruwa as usual nobody cares about me (kamar ko yaushe babu wanda ya damu da ni) na tafi kuma na dawo da kaina ba tare da an yi min abunda na buk’ata ba,a tunani na Inada loved one’s waenda z
a su damu da damuwata…
I guess i was wrong(inaga tunanin nawa ya bani ba dai-dai ba kenan).’’
A hankali ya d’auke dubansa daga gareta ya maida kansa k’asa ya fesar da wani numfashi
Sannan ya ce
‘’Bara in je in d’an watsa ruwa.’’
Tun kafin ya juya Yashj
ub wanda ya fito yanzu daga d’akin Yahanasu ya ce
‘’Yasir, wait!.’’
Lumshe idanuwansa ya yi ya d’an bud’e tukunna ya ce
‘’Wanka zan je in yi”
ya fad’i hakan yana mai kallon cikin idanunsa.
Ba tare da Yashjub d’in ya sake kallon sa ba ya juya ga Momm
y ya ce
‘’A gyara masa d’aki a sama kusa da side d’inki.’’
Gaba d’ayan su a tare suka ce
‘’Whattt!!!!’’
Cikin b’acin rai Yassir ya ce
‘’Look here,Man!( ka ga Mallan kalli nan)
tura ta kai bango fa, haba mana wanne cin fuskar ya rage ba ka yi min ba???
Ka je ka ce in biyo ka na biyo ka bayan b’arnar da ka yi min sannan yanzu kuma za ka saka ni a tsakiyar Mata? To gaskiya baka isa b…..’’
Kallon da Yashjub yake yi masa ne ya sanya ya d’auke Kai ya kalli mommy
Ya ce
‘‘Mommy, ki yi min tsakani da shi fa
, idan kuma ba hakaba to wallahi za mu kwashi y’an kallo.’’
A hankali Yashjub ya matsa daff da shi ya kamo kafad’unsa ya juyo da shi sannan ya ce
‘’Yassir, kar ka ga wai muna a gida kuma a gaban su Mommy ka ce za ka yi min shirme…
Raina already a b’ace y
ake kar ka sake provoking d’ina(fusata ni).
Ka wuce masu aiki za su gyara maka d’aki a chan sama kusa da side d’in Mommy ta yanda za ta fi saka maka ido saboda ni fita nake yi kuma yanzu zan dinga kai dare sosai, sannan ina so in yi tafiya dan haka ba zan
iya kula da kai ba! Tunda ka nuna har yanzu ba ka yi hankali ba, dan haka dole za ka zauna a inda za’a saka maka ido a kuma kula da kai.
Anjima kuma za mu zauna
da ni da kai da Mommy da Daddy a yi magana akan abun da na gani a gidan da kake cewa na yi mak
a b’arna.
for the last time Yassir, ka wuce sama’’.
Iya k’uluwa Yassir ya k’ule, ya san tsaf Yashjub zai iya sake fad’in wata maganar da zata sanya Kausar ta d’an fahimci wani abun tunda gashi har ya fara dan haka kawai ya yanke shawarar wucewa sama
amm
a tabbas zuwa wannan lokacin yayi girman da zai gyarawa Yashjub zama, da sake!!!
Dan gaskiya ba zai yiu a dinga juyashi da girman sa ba.
A hankali Mommy wadda ta fara firgita da yanayin Yashjub ta kamo Hannun Yassir ta ce
‘’Son!mu je,mu je saman. anjima
ba ya ce za mu zauna ba! sai mu zauna d’in, amma for now mu je ka ji ko’’.
Ta fad’i haka tana k’ok’arin janye Yassir d’in daga ruk’on da Yashjub ya yi wa kafad’unsa..
Ai kuwa da kyar sai da ta d’an tab’a Yashjub d’in ta ce mishi
‘’Cika shi za mu wuce’’
T
ukunna Yashjub ya samu ya janye idanuwansa waenda su
ka yi jazir daga kan Yassir ya cika sa da kyar, daga haka kuma ya juya ya fice kamar zai tashi sama.
A hankali Kausar ta ja numfashi ta bi bayansa da kallo har ya wuce tukunna ta lumshe idanuwanta tana
ji a ranta’tabbas bata da hutu bata da sukuni bata da nutsuwa muddin bata samu Yashjub ba!!!
yanzu ne wasan zai fara dan ko ta halin k’ak’a ne
wallahi sai ta mallake shi, bata ga dalilin da zai sanya ta rasa shi ba.’.
Su Mommy suna wucewa sama ita ma t
a bi bayan su haka ma su Yadira.
Yasira kuma ta wuce d’akin Yahanasu…
bata damu da cewar ‘shirin aurenta ya tarwatse a karo na takwas ba’
dole ta kora mata warning, Wallahi.
..
Wani irin karkarwa jikin Yashjub ya ke yi tsabar takaici!
Abun zai yi wani ir
in banbarakwai idan ya je ya samu senator Bashir da fad’a ko da rarrashi dan zai ga kamar yana neman kai da y’ar uwarsa ne…..
Ya jima rabon da ya shiga b’acin rai irin wannan a rayuwarsa, baya so ya dinga jin ma
ɗ
aukakin
ɓ
acin rai irin haka amma yau senato
r Bashir da Yassir sun kai sa bango!!
Da wannan tunanin ya k’arasa part d’in nasa yana zuwa ya fad’a bathroom ya sakarwa kan shi ruwa mai sanyi…
Sai da ya ji ya fara atishawa tukunna ya d’auro alwalla ya fito ya chanja kaya zuwa jallabiya…
ya na shiriin
yanata faman tsaki
dan yana fitowa ya ji ana idar da sallah a masallaci.
A nan d’akin nasa ya yi sallarsa ya idar ya zauna zaman addu’a.
Yana zaune sai ga Kausar ta yi knocking, ta shigo da zumbulelen hijabinta.
ta zo ta zauna kusa da shi wai Mommy ta c
e tunda course d’aya suka karanta ta zo ya k’ara duba mata project d’in ta gobe time zai cika
kar a sake dawo da ita wannan shekarar ma,sannan ya manta bai bata wayoyin nata ba.
A yadda ya ke jin kansa tabbas inya ce zai kula Kausar tou zai iya ji mata r
auni, wacce irin mahaukaciyar Yarinya ce wannan mai shegen tsaurin ido haka.
Mik’ewa kawai yayi ba tare da ya ko kalle ta ba ya koma kan sofa ya nemi guri ya zauna.
Duk da tsoron da take ji hakan bai hana ta matsawa dai-dai wajen k’afafunsa ta zauna ba,
s
annan cikin wata kalar murya
mai tsananin had’ari ta ce
‘’Ya Yash dan Allah’’
Gaba d’aya tashi d’aya sai ya ji tsigar jikinsa yayi wani iri…
Kallon ta ya yi da rinannaun idanunsa cikin b’acin rai ya ce ’’Tashi ki fita, in kuma tsaurin ido zaki gwada Bis
millah ki k’ara second goma a nan za ki ga ikon Allah’’ ya riga ya san k’arya take yi ba Mommy ce ta turo ta ba.
A hankali ta ce ’’ka yi hak’uri’’ daga haka ta mik’e ta fita tana jin zuciyarta k’all dan ta san ko dai hijabin ko kuma muryar ta da salon ta
tabbas akwai abun da ya ba ta ko da k’ank’anuwar nasara ne akan shi yau!!.
‘’Slowly but surely
(Sannu sannu bata hana zuwa)’’
Ta furta hakan tana murmushi a lokacin da ta fito daga b’angaren nasu.
A ranta tace ‘’kwalliya ta biya kud’in sabulu, next level k
am zan girgizaka!!
ai da na d’auka kai d’in dutse ne.’’
..
Shakka babu idan kausar bata fita a hanyar shi ba tou zai bar gidan nan, baya son tab’a lafiyarta kwata kwata amma kullum sake pushing nashi (tunzurashi zuwa) bango take yi..
Yarinya ba jan aji ba
nutsuwa
ba sanin darajar kai kamar ba tarbiyyar Hausawa ba!!!.
Kalli yadda ya ke korarta kullum amma sam ba ta damu ba!!
shak’iyyiyar Yarinya ji irin muryar da ta yi amfani da ita…
Yash ke aiyyana hakan a ranshi..
A fili kuma sai ya yi tsaki ya ce ‘’Alla
h wadaran naka ya lalace’’..
A hankali a hankali tunanin Manubiya ya fad’o mishi….
jingina ya yi da jikin gadon ya lumshe idanuwansa,
nan muryarta da idanunta suka fara yi masa gizo, da kad’an da kad’an ya ke jin b’acin ran nasa yana sauk’a har ya samu
ya d’an ji dama dama tukunna ya mik’e ya koma kan gadon ya kwanta ringigine yana mai kallon sama yana mamakin ta yadda tunanin ta yayi maganin anger d’insa a cikin lokaci k’ank’ani haka..
Kad’an-kad’an ya fara jin bacci dan haka ya jawo pillow ya d’aura a
kan k’irjinsa ya d’an rungume a fili ya furta ‘’Alhamdulillah’’
saboda ya san in yayi baccin ya farka b’acin ran nasa zai ragu sosai da yardar Allah.
Bai dad’e da lumshe idanuwan nasa ba kuwa bacci yayi awon gaba da shi….
Mafarki ya fara mai masifar dad
’i da annashuwa….
‘Ga shi ga Manubiya a zaune a cikin wani lambu mai cike tabb da korayen ciyawa, yana sanye da farar jallabiya yayin da ita kuma ke sanye cikin baƙar Abaya da niƙabi, iyaka idanuwanta kawai yake iya gani.
Suna zaune suna fuskantar juna su
na hira amma sam ba ya iya jin me suke cewa,