Showing 51001 words to 54000 words out of 150519 words

Chapter 18 - Mannubiya Complete

sannan ya bud’e yana mai kallon ta ido cikin ido

tukunna ya ce

‘’Duk abun da kike buk’ata ki turomin Yadira anjima, tashi ki fita.’’

Ganin yadda ta kafe sa da idanuwa ne ya sanya kawai ya mik’e ya d’au briefcase d’insa ba tare da ya sake bi takanta ba ya nufi hanyar fita.

Da sauri ta sha gabansa cikin

d’an gudu ta ce

‘’Ya Yash Mommy ce fa ta aiko ni wajen ka’’

Ta fad’i haka tana k’ok’arin matsawa jikinsa sosai sannan ta saka Hannu zata kamo briefcase

ɗ

insa.

Duk kalar tsaurin idonta sai da ta ji tsoron kalar kallon da yayi mata dan haka ta d’an ja ba

ya kad’an ta sunkuyar da kanta k’asa.

Da kyar Yashjub ya samu ya d’an rarrashi kansa, kawai ya wuce ba tare da ya yi mata komai ba ya fice ya barta anan wajen

amma da farko yadda zuciya ta taso masa so yayi ya d’an wanke ta da mari watakila zata dawo sa

iti!!!

Idan akwai abunda ya fi tsana a rayuwar sa bayan cin amana to shine Mace marar kamun kai!

tabbas Kausar y’ar uwarsa ce

amman kwata-kwata jininsa bai d’auke ta ba tun filazal, gashi yanzun kuma rashin kamun kanta ya sanya ta kuma fita a kansa ko ga

nin Yarinyar baya son yi,wallahi.

Da wannan tunanin ya k’arasa motarsa ya shiga ya zauna ya

lumshe idanuwansa….

A take idanunta waenda izuwa yanzu abun ya zame masa jiki suka hau yi masa gizo.

A ransa ya ce

‘’Ga inda ake Mace nan, gaisuwar ta ma tsada

ne da ita, sannan ta yi laifi amman tsabar sanin darajar Kai

bata yi gigitar da d’ayan Namijin ya yi yana bada hak’uri ba….

Ana ganinta kuma za a fahimci yadda itama take a ru

ɗ

e amma ta dake sam bata yarda ta zubar da class d’inta ba….”

A hankali wani lal

lausan murmushi ya sub’uce masa

A fili ya ce

‘’Sai shegen kukan shagwab’a kamar wata y’ar baby’’…

Yana nan zaune yanata tunani

kira ya shigo wayarsa…

Ba k’aramin fad’uwa gabansa yayi ba a lokacin da ya d’auko wayar zai amsa idanuwansa suka sauk’a akan

time,

‘Wato zaman sa anan har ya yi 30 minutes kenan??’

ya yiwa kansa tambayar ba tare da ya samu mai basa amsa ba.

Ganin kiran yana shirin tsinkewa ne yasa yayi sauri ya d’auka ya kara a kunnensa ahankali ya ce

‘’Daddy Ina kwana,sorry wani abu ya

ɗ

an ts

aida ni,gani nan zuwa’’ .

Yana gama fad’in haka ya kashe wayar ya kunna motar ya bata wuta ya wuce….

A ransa yace

‘’I really need to see Najeeb.(tabbas dole zan ga Najeeb)

Zuwa yanzu ya fahimci in dai ba son Yarinyar nan yake yi ba

to tabbas akwai dali

lin da ya sanya Ubangiji ya turo ta cikin rayuwar sa, ya san ma ba zai you ace yana son ta ba tun da bai san ta ba…

ya kuma yi addu’o’i dan haka definitely ba aljana ko mayya bace ba tunda gashi har yanzu bai bar tunanin ta ba!

Tun yana k’ok’arin yakice t

unanin nata ma har ta kai ta kawo zuwa yanzu ya daina saboda in yana tunanin nata wani

nutsuwa, annashuwa da farin ciki na musamman ne suke dirar masa wanda har ya kan ji

baya k’aunar abun da zai gilma ko ya gifta a tsakanin sa da tunanin nata….

Dan haka

kawai ya gama yankewa akan zai ajjiye b’oye-b’oye a gefe ya fuskanci Najeeb akan maganarta yau yau d’innan inshaaAllah, tun kafin a samu matsala, yana da buƙatar ya santa.

BULAMA ✍



0903 441 3252

*MANNUBIYA*

*18*

Da wannan tunannin

Ya ƙarasa makeken company d’in Daddyn nasu.

Sanin da yayi suna da bak’i ne yasanya bai wani tsaya ko ya biya ta office d’insa ba, kai tsaye kawai ya wuce in da ake meeting d’in…

Bai samu sun kammala

komai ba kuwa sai wajajen k’arfe biy

u, duk saurin sa bai samu damar k’arasawa office d’in Najeeb ba sai pass 3.

A parking lot suka had’u da Najeeb d’in yana shirin fita shi kuma ya shigo.

Tunda ya hango Yashjub d’in ya taho ya tsaya daga k’okarin bud’e k’ofar motar tasa da yake yi ya zuba m

asa ido yana murmushi yana girgiza kai a ransa ya ce ’’Allah mai halittar kowa da yanayin nasa halin,

ya san zai zo kuma ya san ba lallai ya same shi ba amma ya d’auki waya ya ce masa ‘ya jira sa’ kawai, shine yake ganin aiki, ya gwammaci ya zo

ɗ

in in bai

same shi ba ya juya’’.

‘’Kai lafiyar ka kuwa!’’

Yashjub wanda ya k’araso kusa da shi yayi masa tambayar cikin tsare gida.

Y’ar guntuwar dariya Najeeb ya saki kafin ya ce

‘’Mamakin ka nake yi, ka san wani abu ne ya d’an rike ni, ba dan haka ba da na da

d’e da fita daga nan’’

‘’Hmmm’’ Yash

ya ce

kafin ya d’aura da cewa

‘’Ka kyauta kuwa, bani key d’in in shiga idan ka gaji da tsayuwa ka same ni a office d’in.’’

Murmushi Kawai Najeeb yayi daganan ya mik’a masa key d’in ya wuce shi kuma ya bud’e motar

sa ya zuba kayayyakinsa a ciki ya rufe tukunna ya bi bayan Yashjub d’in.

Kusan a tare suka shiga

Office

ɗ

in wanda ya ke nan k’all gwanin ban sha’awa sai faman tashin ƙamshi yake yi.

Fridge Yashjub ya nufa ya d’auki ruwa da cup tukunna ya nemi guri ya

zauna akan sofa kusa da Najeeb d’in, yana zama ya b’alle marfin ruwan ya zuba a cup ya kafa a Baki yayi bismillah ya shiga sha…..

Ajiyar zuciya Najeeb ya sauk’e kafin ya ce

‘’Uncle ya ce in baka hak’uri,

In sha Allah nan da sati biyu za’a gama ginin esta

te

ɗ

in..

k’ofofin ne suka d’an yi wahala

gashi ka ce dole sai irin na estate d’in Abuja da Kano za a saka shiyasa abun ya d’an yi musu tsauri amma yanzu haka an samu an yo order, ya ce kawai za’a fara fenti da fixing electronics in ya so idan an kawo ƙofo

fin sai ya zamana shine last aikin da za a yi kawai.’’

Kallon da ya ga Yashjub d’in yana yi masa ne ya sanya ya ce ‘’Menene kuma? Yash!..Uncle d’ina ne dai, ido ya san na gida.’’

Murmushi Yashjub yayi kafin ya ce

‘’Kallon da kaga Ina yi maka na mamakin

yadda ka hau zuba ba tare da ka ji dalilin zuwana ne,ba.

Ko ce maka aka yi akan maganar estate na zo nan?’’

Yayi masa tambayar yana me kafesa da ido.

Ajiyar zuciya Najeeb ya sauk’e kafin ya ce

‘’To naga ai shine priority d’inka a yanzu mu kuma muna ta y

i maka delay’’.

‘’Yeah, days ago shine priority d’ina amma yanzu kam ba shi bane ba, kawai dai tunda ka taso da maganar tou ka gayawa waenda ka ce sun ce suna son guda d’aya rent su jira sai nan da one month idan za su iya.’’

Yash ya fad’a hakan yana sake

zuba ruwan a cup sannan ya kai Baki.



‘’Ok’’

Kawai Najeeb ya iya cewa

yana mai k’ok’arin fahimtar mood na Yashjub d’in.

Wani d’an guntun murmushi yaga Yash yayi, ba tare da ya kalle sa ba Ya ce

‘’Ina Manubiya?’’

Da d’an k’arfi Najeeb ya ce ’’what!’’

Kafin ya d’aura da cewa “wai dama da gaske kake kenan, kuma amma ka tsaya ka na ta yi mini kwana-kwana da fulatanci?

Ba fa a zurfin ciki a harkar nan dan in ka tsaya wasa tsaff sai dai ka ji sold out!wallahi.

Kaii amma na ji dad’i, ni zan fara kaiwa Mommy

good news

ɗ

innan.

Alhamdulillah ‘dutse’ is in love finally’’.

Najeeb ya k’arashe maganar yana mai fashewa da dariya.

Tsayawa kawai Yashjub ya yi yana Kallon sa bai ce masa uffan ba.

Haka nan Najeeb ya tisa shi a gaba yayi ta zolayar sa, sai da ya gaji

dan kan sa yayi shiru tukunna Yashjub ya ce masa

‘’Ka gama?

Za ka iya saurarata yanzu mu yi abun da ya kawo ni, ko in tafi kawai?’’

Cikin dariya k’asa-k’asa Najeeb ya ce

‘’Sorry, Ina jin ka Angon Manubiya’’.

A hankali ya lumshe lumsassun dogayen idanuw

ansa ya bud’e tukunna ya ce

‘’Najeeb ba wai son Yarinyar nake yi ba…..’’

Cikin tarar numfashinsa Najeeb ya ce

‘’Yet(tukunna..)

Amma ta burgeka ai ko?.

ai dama abunda za ka ji kenan yanzu tunda kwata-kwata sau d’aya ka tab’a ganin ta,haka abun yake ai.

Ka yi ƙoƙari ka santa ku shaƙu!

InshaaAllah nan da ƴan watanni za mu sha biki…’’

‘’Ya Allah,

duk wani iri abun nan ya ke sa ni ina ji’.

Yash ya fad’a yana mai sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya.

Dariya Najeeb ya saka kafin ya ce

“Ai yanzu zan baza ka a

groups, kaff friends d’inmu sai sun san aljannar da ta aureka ta rabu da kai finally ko kuma ta mutu, wannan abun farin cikin har walima zamu had’a.’’

‘’Pls don’t (dan Allah kar kayi hakan), haba Najeeb ya kake yi min haka?

Na zo maka da matsalata a mats

ayin ka na Abokina kai da ya kamata ace ka tsaya ka saurare ni amma sai faman shirme kake yi min,shikenan kawai bara in tafi…’’

Yashjub ya fad’a yana k’ok’arin mik’ewa da alama ransa ya d’an sosu.

Da sauri Najeeb

Ya ce

‘’Yi haku’uri’’ yana mai rik’o hann

unsa sannan ya yi serious face ya ce ‘’na daina,

Talk to me friend(mu yi magana Abokina).”

Sai da Yashjub ya d’an k’ura masa ido tukunna ya koma ya zauna.

Ya dafe kansa da Hannu d’aya ya d’an sunkuyar da kan nasa ya lumshe ido a hankali ya ce

‘’Ba wai son

Yarinyar nan nake yi ba Najeeb, saboda wallahi yanzu inda ace za a kawo mata guda goma a kulle musu Iyaka Idanunsu a bar ragowar fuskar a bud’e to ba lalle in iya nuna ta a cikin su ba.

iyakar idanunta kawai na gani that very day(a wachchar ranar) amman

tun daga lokacin na gaza sukuni…

Idan fa na lumshe idona har ganin idanunta nake yi,

sannan haka kurum sai in dinga ji kamar muryarta tana yi mini gizo a kunnuwana..

sannan in ba tunaninta nake yi ba ko maganarta as in(misali) idan na yi forcing kaina in

cireta a raina to gaba d’aya sai in ji Ina neman susucewa kaga alal misali yanzu haka maganar ta muke yi da kai ko?To ni kad’ai na san irin peace of mind d’in (kwanciyar hankalin) da nake samu, wani sanyi nake ji har k’asan zuciyata da annashuwa sannan wit

h each passing second na rayuwata

all i want to do (sannan duk wata daƙiƙar da za ta zo ta shige a rayuwata iyakar abunda na ke ganin ya kamata in yi) shine

In san ta!!!.

Its like (ji nake) kamar akwai abun da yake pushing d’ina (tura ni) akan in je in s

anta in yi bincike akan ta, in zama very close to her, like sooooo close..may be a friend

(In samu mu shaƙu da ita, shaƙuwa sosai, wataƙila kamar ko mu ƙulla Abota haka)”

Ya k’arashe maganar tasa a hankali yana mai d’agowa ya kalli Najeeb wanda ya ga ya yi

shiruu ya k’ura masa ido kawai, sai da ya fesar da iska tukunna ya ci gaba da cewa

‘’Na san me kake tunani amma dan Allah karka fad’a, I can’t love her (ba zan iya in so ta ba) tunda ban riga na san ta kuma na ganta ganta sosai ba, shiyasa ma na riga na

yi concluding abun as (na bar abunda na ke ji a kanta a matsayin) ba so bane ba!!!!.

it’s definitely something else (dole wani abu ne chan na daban, amma ba so ba).

Dan haka

Ka bani shawara, mu tattauna a nemo mafita amma kar ka ce min son Yarinyar nan nak

e yi dan na san ba son ta nake yi ba.’’

Da kyar Najeeb ya samu ya iya danne dariyar da take ta faman taso masa, duk da tausayin da Abokin nasa ya bashi amman kuma ya ba shi dariya duk a lokaci guda.

Gashi dai Yashjub is in love da ikon Allah saboda gaba

d’aya bayanan shi akan Manubiya

amsar d’aya ce tak ‘KAUNA’

although (dukda)bai ganta sosai ba

amma idanuwanta da muryarta da ruhinta sun riga sun hana shi sukuni tun yanzu

Ina kuma ga in sun kasance frnds d’in (abokan)kamar yadda ya ke da buk’ata a ya

nzun,

Lokacin da zai amayar da abun da yake ransa ma ba zai saniba!….

Tabbas kuwa za a yi soyayyar da ba lalle an ta

ɓ

a yin kwatankwacin irin ta a tarihi ba dan ya lura da Manubiyan itama a ranar da suka fara had’uwa da Yash d’in.

‘’Najeeb’’

Yashjub ya ki

ra sunansa.

Kame-kame Najeeb ya fara yana tunanin mai zai ce masa, saboda shi dai ya riga ya gama fahimtar Yashjub d’in tsaff to amma shi kuma gashi yace kar a ce masa yana son Yarinyar ne

Which is the absolute truth(wanda hakan ne haƙiƙanin gaskiyar)…

Dan haka a hankali cikin son fahimtar da shi ta ruwan sanyi Najeeb yace

‘’Mai yasa kake tunanin ba son ta kake yi ba? soboda kai ba Mutum bane?’’

Ganin ya ƙi ma ya kula shi ne yasanya Najeeb cewa

‘’Shikenan bara zan san abun yi

amma gaskiya ni a yanzu b

a zan iya nema maka mafita ba.

Frnds d’in dai da ka ambata inshaaAllah zan had’aku friendship (Abota) dukda ni ban ma san ta Ina zan fara ba tunda kaga ni Malaminta ne amma in sha Allah zuwa gobe za ka ji ni, zan nemo idea soon, bari zan jira dan kamar sun

a da exams d’in Dr Auwal”

Shiruu Najeeb d’in yayi daga magana kafin ya sake cewa

“bari zan san yadda zan yi kar ka damu, na ma nemo idea’’.

‘’Ok’’

Kawai Yashjub ya ce

Kafin ya sake cewa

‘’Kuma wannan wanda na gan su tare kana tunanin akwai wani abun

a tsakanin su’’?

Dariya najeeb yayi a ransa yace

‘’Ga wani sign din ‘kishi ‘

A fili kuma sai ya ce

‘’I don’t think so, amma dai zan yi finding out’’

Shiruu Yashjub yayi dan sai kuma ya d’an fara jin haushin kansa na tambayar da ya yi wa Najeeb d’in t

a yanzu.

Ganin yayi shiru ne

Yasanya Najeeb kawo wata hirar daganan suka hau tattaunawa…

..

Kiran sallar laasar ne ya tashi zaman nasu

Yashjub ya wuce

Najeeb kuma ya nema wani ya aika shi inda su Manubiya suke exams yau yace masa ya kira mishi Abbbakar

.

Daganan ya wuce masjid…..

••••

Tun rabuwar Kausar da Yashjub da ta shige d’akinta ta rufe bata bud’e ba!

Mommy ta je har sau biyu…

Jin ta yi knocking ba a bud’e ba

yasa ta yi tunanin ko ta fita ne maybe

dan haka ta hak’ura ta

hau zaman jiran ta.

Ganin

har yamma ta yi bata ganta ba yasa ta sake komawa domin ta sake dubawa dai-dai nan ita kuma Kausar d’in tana shirin fitowa daga side d’in nata.

Kana ganin fuskarta ka san ta ci kuka ba kad’an ba.

A hankali cikin rashin jin dad’i Mommy ta ce

‘’Haba Kau

sar, yanzu ashe tun

ɗ

azu kike ta faman kuka, mai ya faru haka, mai ya sameki?’’

Ta yi mata tambayar tana mai tsare ta da idanuwa.

Fad’awa ta yi jikin Mommy ta sake fashewa da wani irin kuka

cikin kukan ta ce

‘’Mommy ko kallo ban ishi Ya

Yash ba, ni gan

i nake ma kamar yq tsane ni,

tayaya kike tunanin zai kalle ni ma

Talkless of ya bani time da chance d’in da zan kafa kaina a cikin Zuciyarsa?.

Ke da Baaba Larai kullum sai cewa kuke yi in jira in jira yau an fi wata d’aya kuna cewa in jira, so kuke yi in

yi ta jira har sai lokacin da ya had’u da wata ya fara son ta tukunnna ni kuma in nuna mishi ra’ayina?.

nikam a gaskiya Wallahi ba zan sake bin ta maganar ku ba ko zai

ko zai kasheni da duka zan gaya masa in yaso ke da Baaaba Larai ku san abun yi daganan

.’’

Da kyar Mommy ta samu ta zaro ta daga jikinta cikin son fahimtar da ita ta ce

‘’Kausar gaggawa aikin shed’an ne, ki tsaya ki nutsu!!!

Na gaya miki na san abun yi kin ji ko? saurin me kike yi ?

Yash naki….’’

Cikin ture Hannun Mommyn daga jikinta tana

kuka sosai ta ce

‘’Mommy dole in yi sauri, baki san ya nake ji game da shi a cikin zuciyata ba, ina tsoron kar ya sub’uce min sannan ga fargabar kar Yasir ya sanya Daddy yayi min dole…

Ko da yaushe fa a cikin fargaba nake. Kar in rasa Ya Yash

In ya sub’

uce min mutuwa zan yi, wallahi mommy inban aure sa ba”………

Tsit maganarta ta katse ganin Yash d’in yana hawowa sama cikin main parlour d’in saman

Cikin zuciyarta kuma sai ta ce

‘’Ai da ban yi shiru ba gara kawai in fad’a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login