Showing 105001 words to 108000 words out of 150519 words
su Manubiya dan rufarwa Ya Yusuf sukayi, suka yi masa
dukan mata ta koina kamar sun kama b’arawo.
H
aushi da takaici ne suka sanya Baba Habu yarfawa Ya Yusuf mari bayan ya d’ago sa,
A cewarsa ta ya zai tsaya su Manubiya su dake sa.
Da kyar! dan ya jigata ko gani bayayi sosai saboda Ya Musbah ya fasa masa gefen ido..ya samu ya iya cewa Baban nasa “ai ha
r da Musbahu..
shine ma ya fara kai masa dukan da ya kai sa k’asa.”
Cikin fushi Baba Habu ya juya ya kalli Ya Musbah, kamar zai ce wani abun sai kuma kawai ya ja hannun Ya Yusuf suka wuce wanda gaba d’aya jikinsa! baki! hanci da gefen ido suke fitar da j
ini, gashi ya kasa mik’ewa ya tsaya sosai yanata faman rik’e ciki alamun sun dake sa a wajen….
*MANNUBIYA*
*35*
*BARKAN MU DA BABBAR SALLAH,UBANGIJI ALLAH YA KARB’I IBDUNMU YA MAIMAITA MANA.*
Suna wucewa Ya Musbah ya dafe kansa..
ya
fi second ashirin a haka tukunna ya d’ago ya ce
‘’bari in kai Inna gidana, sai in zo mu tafi wajen Baba.
Muhsin dama tun d’azu na mik’a sa gidan Nafi’u.’’
Da sauri Jidda ta ce ‘’Ya Musbah kar ka je su ganka kai ma namiji su kamaka.
A ganina gara ka bari
mu Mata mu je…dan kai ba lallai su d’aga maka k’afa ba, inaga shiyasa Baba bai nemi ka je d’in ba ya ce ‘mu gudu’!.
Ka bari za mu je na san idan suka ganmu Mata za su tausaya mana su d’aga mishi k’afa.’’
Ajiyar zuciya Ya Musbah ya sauk’e yana mai kallon
ta ya ce
‘’D’azu Baban ne suka sanya ya kira ni da kanshi.
Na ji tsoro tare da firgici mai tsananin a cikinnmuryarsa.
Shin wanne irin d’a zan kasance idan na gudu na barshi a wannan halin saboda ni in ceci kaina?
Jidda babu inda d’aya a cikinmu zai gudu
ya je, ko da kuwa za su d’auke ni a matsayin fansar kud’in da Baba ya ci ne.
Inna ma zan kaita gidana ne saboda kar a barta ita kad’ai anan,
Dan gaba d’aya mu ukun nake so mu tafi tare.”
Cikin katseshi Manubiya ta ce
‘’Ya Musbah ka san dai Baraka ba z
a ta kula da ita ba ko’’.
A hankali ya ce ‘’Manu na sani.
Yanzu haka Muhsin yana wajen Matar Nafi’u, so idan na kai Inna zan tura mata shi kuma zan ce masa in Inna tana buk’atar wani abun da ya san ba zai iya ba ya je ya kira matar Nafi’u.
Ina so mu tafi
mu dukan mu mu uku saboda Baba yana buk’atar mu dukkan mu, sannan kinga ni ban iya karatu ba dan haka ba zai yiu in je ni kad’ai ba…
Jidda ba zai yiu mu je da ita
kad’ai ba, kema kuma ba zai yiu in je dake ke kad’ai mu bar Jidda anan ba hankalinta ba zai
kwanta ba,
Ni kuma ba zan barka ku tafi iya ku biyu ba.
Ba za mu bar Inna anan ba,
kar mu tafi Yusuf ya shiga ya yi mata wani abun dan izuwa
yanzu na gama tabbatarwa Yusuf babu abunda ba zai iya aikatawa ba….na Kira Nafi’u ya ce yana hanya, ku zo mu j
e mu had’a k’arfi da k’arfe mu hud’un tunda ba mu da wanda zai tsaya mana, na san Allah zai taimakemu, shi zai tsaya mana
InshaaAllah…
In ma sunk’i yarda su hak’ura ni zan bada kaina a matsayin fansar kud’in ba komai, a samu Baba ya dawo gida”.
Shiruu
duk sukayi kafin
Manubiya ta yi sauri ta wuce
tana share hawayenta tana mai cewa “zan jira ku a titi’’.
Ya Nafi’u yana zuwa suka saka inna a motarshi suka kaita gidan Ya Musbah, kana ganinsu ka san suna cikin tsananin tashin hankali Jidda kam in banda
hawaye ba abunda takeyi, ya Musbah ma da kyar ya ke iya rik’e kwallarsa, dan basu da tabbacin dawowar tasu…
Baraka tana kitchen ya lek’a ya ce mata ‘’za su je wani waje, ga inna nan a d’akin bak’i.’’
Bata ko kalle sa ba ballantana
yayi tunanin zata amsa
shi.
Hakanan ya juya ya bar mata kitchen d’in, ya samu Muhsin yace masa “in yana buk’atar
wani abu ya je ya kira anty Aisha”
daga haka ya kama hanya ya fito ransa duk ba dad’i.
Yana zama a cikin motar, Nafi’u ya lura da yanayin shi dan haka ya ce ’’in
ba zata yarda ba Musbahu kawai mu kai Inna wajen Aisha, tun d’azu da ka kirani dama na kira ta na gaya mata, dan da ni da ita duk mun d’auka a gidana ma za a ajjiye innar a wajenta…shiyasa ma har ta gyara mata d’ayan d’akin bak’in dake a tsakar gida.’’
G
irgiza kai kawai ya Musbah ya yi kafin yace’’karka damu Nafi’u.
ba zai yiu ace ni da
gidana amma mahaifiyata ba zata shiga ba! ba zai yiu ba!.
Ka bar batun Baraka kawai, dan bata da lissafi da ishashshen hankali, mu yi sauri mu yi abunda yake a gaban m
u kar mutanen nan su fara shirme.’’
A bakin titi suka tsaya suka d’auki Manubiya tukunna suka kama hanyar Bankin…
cikin d’aurewar Kai Ya Nafi’u
Ya ce
‘’Ni fa duk ban gane komai ba, wanne irin banki ne za su ranta kud’i iya na kwana uku
kuma su ce za
su kama Mutum tashi d’aya?
Sannan na ji kace Baban ya ce maka da kansa ya je bankin to ya akayi kuma suka kamashi????’’
Ajiyar zuciya Ya Musbah ya sauk’e kafin ya ce ’’wallahi nima kaina a d’aure yake da lamarin nan, na dai san sharrin Yusuf ne bani da
tantama shi ne ya had’a komai.
Shi kuma Baba ya yarda da shi,
kuma ka san shi da b’oye b’oye,
sannan ya ƙi yin shawara da kowa har ta chab’e.
Bara dai mu je d’in, sai mu ji komai, Allah ya shige mana gaba.’’
‘’Ameeen’’
gaba d’ayansu suka ce, daga haka
motar ta d’au shiruuu kowa yana tunani da fargaba, dan haka suka shiga jero addu’o’i a cikin ransu.
Aikuwa da suka je abun da suka yi zato d’in ne, dan ko cikin bankin ma ba su shiga ba a waje ake case d’in, saboda babu bashin banki tsakanin Baba da bank
i.
Bashi!
a tsakanin Baba da wani mai kud’i ne wai shi ‘Black Snake’
wanda k’asa take zarginsa dan a file d’in nashi ma har da case da efcc suna kan yi….
A jikin takardar
….Baba ya tambayi Mutumin aron miliyan d’aya, akan yana buk’ata urgent kud’insa sun
d’an mak’ale amma suna fitowa nan da 2 days zai maida masa har da interest!.
Idan bai maida ba kuma to ya yarda Mutumin ya yi masa
duk abunda ya ga dama…
Su ya Yusuf su suka yi shaida suka tsaya a tsakani da shi da
wasu Abokan shi guda biyu.
Babban
abun takaicin
shine yadda Mutumin ya ƙi baiyyana su gansa balle su samu su yi mishi magana!!!
an ma ce musu baya ma k’asar gaba d’aya…
Wasu mutane ya aiko su biyu
bak’ak’e murd’ad’d’u, waenda ana ganinsu kallo
ɗ
aya an san babu d’igon Imani a tare da su.
Ana cikin haka aka ce ‘’ai case ya tashi anan, awa uku da aka bada ta cika dan haka yanzu sai dai a tafi da shi
Police station.
Kamar wani shahararren b’arawo haka aka datsa masa ankwa, aka saka shi a mota.
Gaba
ɗ
ayansu Yaran suna kuka haka aka tafi d
a shi.
Ba tare da b’aata lokaci ba suka bishi a motar ya Nafi’u.
Suna zuwa suka tarar da wani sabon tashin hankali ‘Wai an bada order, a yi masa horo mai tsanani,’
Gashi an k’i a basu bail d’in shi.
D’ayan police d’in ma ce musu yayi “su gudu.”
Saboda
wai black snake d’in tun d’azu ya bada order a kama har family d’in Baban a had’asu waje d’aya..
Suna tsaye a reception suka fara jiyo ihu, babu yadda ba su yi ba amma aka hana su shiga….
d’ayan police d’in ne ya d’an kwantar musu da hankali ta hanyar c
e musu “ai ba ihun Baba baneba” sannan ya basu shawarar ‘su je su nemo kud’in, tun kafin abun ya fi haka lalacewa’
Da kyar dai aka samu suka hak’ura suka yi waje a gigice masu hawaye suna yi
masu kuka sunayi.
suna fita
Ya musbah da ya Nafi’u
kowannensu
ya d’au waya suka shiga neman mafita a rikice.
Sun shafe sama da awa d’aya
suna tambayar jam’ar da suka sani bashi amma daga Ya Musbah har Ya Nafi’un kwata-kwata dubu ashirin suka had’a….
Uncle kanshi dubu uku ya turo ta acc d’in ya Nafi’u ya ce
“su j
ira sa, in ya tashi a aiki zai zo ya duba Baban.”
Gefe Jidda ta koma ta fashe da wani sabon kuka, ji take kamar ta gudu…..
Saboda ita Manubiya ta yi aikatau a gidan Ammi!
sannan yanzu ma gashi saboda ita aka kama Baba!
in ba dakyar ba kuma ta san Ya Yus
uf ne ya ce ayi masa horo mai tsanani, so yake ya rama dukan da suka yi mishi.
Kuka gaba d’ayansu suke yi daga ita har Manubiya…
Su ya Musbah kuma in banda waya ba abunda suke yi dan kaff
d’an kud’in hannunsu ma duk ya k’are a siyen kati.
Suna tsaye a
harabar police station d’in sukaga wasu polisawa sun fito da tray da almakashi da wasu k’arafuna akai duk jini,
sun nufi fanfo suna ƙarasawa su ka hau wankewa….
Tun kafin kwakwalwar Manubiya ta gama d’aukar charjin ‘watakil jinin Baba ne wannan…’
ta kwas
a a guje ta yi cikin police station d’in, da kyar ta iya tsayawa ta shiga tambayar police d’in da ya biyota da niyyar taro ta. Tana kuka ta ce “ka bar ni in ga Baba, saboda Allah da Annabi.”
Tausayi ta bashi dan haka ya nuna mata k’ofar inda Baban yake, ya
juya kawai, a ransa yana mamakin ‘mai ya had’a waennan kamilallun mutanen da Black snake.’
Juyawa ta yi zata koma dan ta baro d’akin a baya, suka yi ido hu
ɗ
u da su Ya Musbah, ashe sun biyota a baya suma, duk a gigice.
sai da suka je bakin k’ofar d’akin
kuma duk sai suka kasa shiga,kowa yana jin tsoron abunda zai shiga ya tarar.
Da kyar Ya Musbah ya yi ta maza ya tura k’ofar ya shige!
daga haka suma suka samu kwarin guiwar mara masa baya.
Turuss! ya Musbah da ya Nafi’u suka ja suka tsaya….
Su manubiya
kuma suka saki wani irin kuka.
A kwance suka sameshi daga shi sai vest da dogon wando…
In banda karkarwa babu abunda jikinsa yake yi, da alamun bai ma san waye a kansa ba, ga jini a zuzzube a k’asa!
Sai da suka matsa kusa dashi sosai, dakyar, tukunna suka
lura ashe har da faratunsa na k’afa d’aya guda d’aya da na Hannu yatsu biyu suka fara zarewa.
Da sauri suka zauna a gabanshi Jidda ta d’aura k’afafun shi akan cinyar ta Manubiya ta shiga goge masa gumi tana yi masa fifita, suna yi suna kuka a rikice.
A z
uciye ya Nafi’u ya mik’e cikin fushi ya ce
‘’Wanne irin rashin imanine da dak’ik’anci wannan?
A haka zai fito musu da kud’in nasu?’’
Sai kuma ya nufi hanyar waje.
Da sauri Ya Musbah ya sha gabansa ya tare sa.
Cikin fushi ya Nafi’u yace ‘’matsa,matsam
in in je in samesu”
Cikin son fahimtar da shi ya Musbah ya ce ’’Nafi’u idan rai ya b’aci hankali ba ya gushewa…
ka je ka samesu ka ce musu me?
kud’i fa aka basu aka basu order kaga kuwa dole su yi abunda aka ce, kuma baka karanta takardar bane?
mutum b
ai saka hannu bama ya aka k’are ballantana an saka hannu?
Dole su yi abunda aka ce!
Kuma ko Ina za mu je babu wanda zai tsaya mana, idan ka yi fad’a ko kuma ka ce zaka tada rikici yanzu sai a had’a da kai saboda baka da kud’i nima bani da kud’i shima Bab
a bashi da kud’i.
Ka tsaya yanzu mu nutsu mu San abunyi mu ceto Baba, dan hayaniya da rikici ba namu bane ba.’’
Da kyar dai ya Musbah ya samu ya d’an kwantarwa da ya Nafi’u hankali aka samu ya nutsu ka
ɗ
an.
Yana huci ya ce ’’na ji, ka fi ni gaskiya, ba
zan je in same su ba amma wallahi tallahi
duk wanda ya shigo da niyyar sake yin wani hauka anan wajen sai na illatashi.
Ina nan ba inda zan je’’.
Lumshe ido kawai ya Musbah ya yi ya bud’e ya ce ’’ba za su sake ba, in ma bamu samu mun had’a kan kud’ad’en
ba, ba komai ni sai in fanshe sa’’.
daidai nan Abbakar ya shigo wajen shima a rikice. Yana ganin Manubiya da yanayin kukan da take yi hankalinshi ya sake tashi..hankalin nashi bai gama tashi ba sai da idanuwansa suka kai ga Baba.
Da sauri ya k’arasa ya na
salati
sai kuma ya kalli Manubiya, kamar jira take yi kuwa a take ta sake fashewa da wani sabon kukan.Ji yayi kamar shima ya sa kuka, da kyar ya samu ya tsugunna inda take a ahankali
ya d’aga hannu kamar zai shafa fuskarta sai kuma
ya sauk’e hannun ji
ki a sanyaye kafin ya runtse idonshi da k’arfi ya bud’e tukunna a hankali ya ce
‘’Ki yi hak’uri Manu, za mu san yadda za a yi inshaaAllah..
d’azu
ya Musbah ya kirani yake gaya min,
3k ne kawai a acc d’ina na tura mishi yanzu kuma ga 20 na sake nemowa…
ki kwantar da hankalinki za’a samo, kin ji, dan Allah ki daina kuka’’
Da kyar ta samu ta ce
‘‘Abbakar kafin nan mukasan mai za su sake yi masa? kall …..”
K’arar bundugun da suka ji ba k’ak’k’autawa tare da hayaniya da k’arar motoci ne ya sanya duk suk
a yi tsit.
Basu gama tunanin mai ya faru ba suka ji an banko k’ofar da mahaukacin k’arfi an shigo da gudu…
*MANNUBIYA*
*36*
K’arar bundugun da suka ji ba k’ak’k’autawa tare da hayaniya da k’arar motoci ne ya sanya duk suka yi tsit.
Bas
u gama tunanin mai ya faru ba suka ji an banko k’ofar da mahaukacin k’arfi an shigo da gudu…
Body guards ne bak’ak’e k’irin da su sanye da bak’ak’en kaya da bak’in glass…
biyu na farkon suna rik’e da manya manyan bindigu, ragowar na bayansu kuma k’anana n
e a sak’ale a gefen k’ugun ko wannensu.
Yanayin wajen suka kalla dan haka d’aya a cikin su ya juya ya fita da gudu, ya je ya kawo kujera ya ajjiye, kafin ya koma ya shiga cikin layi biyun da suka yi a jere tundaga bakin k’ofar har izuwa inda suka ajji
ye kujerar a gaban Baba.
Tsayawa kawai su Manubiya suka yi gaba d’ayansu suna kallonsu..
Basu kai ga gama tunani da lissafin abun ba, tashi
ɗ
aya suka fara jiyo wata iriyar dariya ana yinta cikin
wani kalar sauti da kuma murya marar dad’in sauraro….
Ya
dda ake dariyar ne zai sanya tashi d’aya a
fahimci rashin kamala da rashin sanin ciwon kan mamallakin muryar…Yana magana da turanci yana dariya sosai kamar wani tab’abb’e!.
Yadda su ke jiyo muryar tana matsosu ne ya sanya suka fahimci Mutumin nan cikin
d’akin zai shigo..
Ta tsakiyar body guards d’in nashi waenda suka hau layi ya bi ya shigo…
Ƙ
ato ne sosai, dogo, lukuti, fari sosai..farin nasa irin jaaa!! Ɗinnan.
Babu gashi ko
guda d’aya tun daga scarf d’insa (fatar kansa) har gemun sa da gashin baki d
uk babu gashi!
Iya kar girar sa da gashin idanunsa ne kawai masu gashi a kaf ilahirin kansa zuwa fuskarshi wanda hakan ne ya basu damar ganin asalin yanayin fuskartashi
wadda take d’auke da
k’ananan Idanu jajaye, da
ɗ
an
guntun Hanci, yayinda Bakinsa y
a kasance madaidaici.
Yadda dpo yake binsa yana russuna masa yana yi masa magana kamar zai kwanta
abun dole ya k’ular da jama’a…
dariyarsa kawai yake ta yi shi kam at the same time yana bawa dpo amsa, har ya iso inda Baba ya ke!.
Shiruu ya yi ya tsayar
da dariyar tasa kafin ya kalli dpo tukunna ya ce ’’ku ka ce yana kan karb’an punishment (hukunci)
But (amma
nagani he’s still conscious,Y(har yanzu yana cikin haiyyacinsa, mai yasa?)?’’.
Yayi tambayar yana mai zubawa dpo jajaye idanuwansa.
A take dpo d’i
n ya rikice ya fara kame-kame ya shiga
karanto addu’o’i daban-daban a k’asan ransa yana mai neman tsari daga sharrin ‘Black Snake’!
Dan kasancewar yanzunnan ya gama raha da dariya da shi
ba shi zai hana shi sauya masa kamanni a take a wurin ba!..
kamar
kuwa ya sani dan tashi d’aya black snake ya gama rayawa a ransa ‘zai sanya body guards d’in shi su yi wa dpo asalin horo, a yanzu a gaban kowa, ta yadda next time zai fahimci mai ake nufi da horo!!’
dan haka ya d’an d’ago kansa da niyyar juyawa ya kira biy
u a cikin body guards d’in shi amma sai
Idanuwanshi suka sauk’a akan Manubiya
wadda