Showing 108001 words to 111000 words out of 150519 words
gaba d’aya tashi d’aya ta rikice sannan tsoro ya lullube ta daga ganinsa!
Ba abunda ya fi d’aga mata hankali irin zanen bak’in macijin da ya fito tarr!!
wanda yake nan a
kwance a hannunsa na dama…tun daga kwanjinshi har kan bayan tafin hannunshi
kamar na gaske
ga wasu uban sark’ok’i a jikinsa wuya da hannu da wani burgujejen wando shima mai sark’ok’i a jiki amma kuma rigar jikinsa armless(marar Hannu).
Wata mahaukaciyar
dariya ta ga ya kwashe da, ga mamakinta kawai sai ta ga ya nufota aikuwa kafin ya k’araso tuni ta shige bayan Ya Musbah ta b’uya.
Da mamaki ya kalleta ya juya ya kalli Jidda sai kuma ya juya ya kalli d’aya daga cikin bodyguards d’in nasa ya ce
‘’John!da
ma ita biyu ce?’’
‘’A’a ai dama Kabir d’in ya ce tanada sister, remember(ka tuna)?’’
Dariya ya yi kafin ya juya ya shiga yi wa Manubiya wadda ta b’uya a bayan ya Musbah
wani irin kallo har da lek’awa yake yi yana sakewa saboda a yadda Abokin Ya Yusuf y
a yi masa bayani tabbas Yarinyar ta fi haka kyau a fili..
Ya Musbah ya kalla ya kalleta
kafin ya yi wani kalar murmushi..
Ba su gama fahimtar ma’anar murmushin nashi ba suka ga ya yi fito!.
Da sauri
ɗ
aya a cikin body guards d’inshi ya zo ya hankad’e Ya
Musbah ya fisgo Hannun Manubiya ya dawo da ita gaban black snake ya tsayar, tukunna ya juya ya koma ya je ya tsaya a wajen tsayuwarshi.
Cikin d’an d’aga murya ya Nafi’u ya ce
‘’Me ye haka wai?’’
Ba wanda ya ko kalle sa balle su bashi amsa, a hankali bla
ck snake d’in ya sa Hannu ya d’an kamo hab’ar Manubiya ya d’ago yana mai k’are mata kallo.
Da sauri ta kawar da kanta gefe, tana wani irin kuka…dan gaba d’aya a tsorace take
ga tashin hankalin da take a ciki tun farko dama ga kuma zuwan wannan abun tsoro
n
shiyasa duk ta bi ta sake duburcewa,
in banda karkarwa babu abunda jikinta yake yi.
‘’Mallan kana haukane!’’
Ya Musbah wanda ya taso yanzu ya fad’a a Zuciye yana shirin yin kan black snake d’in…
A take wani a cikin bodyguards d’in nashi ya saita masa
bindiga..
Da sauri Baba ya ce ’’dan Allah kar ku yi musu komai, dan Allah”
sai kuma ya fashe da Kuka.
Shi kam black snake gaba d’aya hankalinshi ya tashi
da ganin Manubiya!..
Babu k’asar da bai je ba a rayuwarshi sai dai in da ba’a rasaba, amman ba zai
yi k’arya ba duk yawonsa da gane ganensa bai tab’a ganin Mace mai kyawu sannan Macen da ta d’auke hankalinshi lokaci guda kamar Manu ba.
Kallonta kawai yake yana sakewa
kamar ya samu television….
Sai da ya lashe Bakinshi tukunna ya kamo hijabinta ta k’asa
bata yi auni ba kawai ta ji ya d’ago shi ya zare ya yar a gefe…
Tabbas ba k’aramin zafin tozarcin da ya aikata mata ta ji ba, dukda kuwa doguwar riga ta Abaya ce a jikinta amma ji ta yi kamar ta kurma ihu.
Tashi d’aya ta ji wani irin bak’in ciki
ya lul
lub’eta, bata san lokacin da ta d’aga Hannu za ta kifa mishi mari ba.
Ya Musbah da Ya Nafi’u ma duk nufar sa suka yi dukda bindigar da ke saite a kan Ya Musbah bai ma san lokacin da ya motsa ba.
Abbakar shima yana ganin haka ya yi kansu cikin fushi.
A lok
aci guda black snake ya zaro pistol daga cikin aljihun wandonshi
ya saita k’afar Abbakar ya sakar mishi bullet sannan ya rik’e tattausan Hannun Manubiya da d’ayan Hannun nashi.
‘’Innalillahi wa inna ilaihirrajiun’’
gaba d’ayansu suka ce, sai kuma suka yi
kan Abbakar wanda ya fad’i a wajen, ya yi suman wucen gadi, tsabar azaba ya ma kasa kuka ya kasa magana
Yanajin azabar da tunda uwarshi ta kawoshi duniya bai tab’a ji ba tana ratsashi.
Black snake bai huce ba sai da
ya kuma harbin d’aya a cikin bodygu
ards d’insa a kafad’a wanda d’azu ya saitawa Ya Musbah bindiga
Cikin dakakkiyar murya ya ce ’’da ka saita masa bindiga ka ga ya motsa harbesa ya kamata ka yi, next time you should take note
(Ka
ɗ
auki darashi saboda gaba)!’’.
Ba tare daya cika Hannun Manu
wadda taketa k’ok’arin kwacewa tana kuka tana kallon Abbakar ba
Ya kalli kowa a wajen tukunna
Ya ce ‘’yanzu na samu attention d’in kowa ko?
Perfect(dai-dai kenan) bari ayi magana’’
‘’My name is black snake (suna na Black snake)
wanda ya kamata ace kuna
jin tsoro amma na ga ku da Babanku kun raina ni, wanda hakan ne ya nuna min cewa ba ku san wayene ni ba ba kuma kusan what i’m capable of ba(abunda na kan aikatawa ba).”
“Baba na nan kwance’’
Ya yi maganar yana nuna Baba, Kafin ya d’aura da cewa
“ya ci k
ud’ina!.
Ban san ta ya aka yi this old man (wannan tsohon) ya samu guts da audacity d’in (ƙarfin guiwar) cin kud’ina ba but duk nan mun san ya ci min kud’ina, sannan a statement d’inshi ya rubuta in yi mishi duk abunda na ga dama idan har bai biyani ba.’’
Dariya ya yi kafin ya d’aura da cewa ‘’sai da na saka aka dubamin aka tabbatar min da mutumin nan ba mahaukaci baneba
Tukunna
Saboda na yi mamakin mutum mai hankalin da zai yi wannan rubutun a statement na tsakanina da shi
I’m the black snake
(Ni ne fa
black snake)”
Ya fad’i hakan yana d’aga hannuwanshi biyun sama
still yana rik’e da hannun Manubiya, kafin ya ci gaba da cewa “ni mutum bai ce in azabtar da shi ba ma na azabtar ballantana kuma ya fad’a?!.
Anyways I was overseas
(Ko dai yaya ma, ina ƙas
ar waje)
ba na k’asar aka fara case
ɗ
innan.
Ni da Kabir a friend
of your nephew Yusuf (Abokin
ɗ
an wanka Yusuf)
muka tafi and ya ji ni a waya ina magana akan hargitsin
shine ya bani labarin da na ji dad’i kuma da idanuwana suka gani na sake jin dad’i….
Da farko ya ce min
‘wannan Baban ko kashe shi zan yi ba zai biya ni kud’ina ba saboda bashi da kud’i!
Amma akwai wata hanyar da zan iya fanshewa….
Baba yanada kyakkyawar yarinya fara k’al! akwai wata rana da ya je a gidan su Yusuf d’in ya ganta ya cew
a Yusuf yana sonta to ashe
wai budurwar Yusuf d’in ce’.”
Cikin yin k’asa da murya ya ce
“ban gayawa Yusuf komai ba, bai ma san na dawo Nigeria ba as we speak(yanzu haka), dan
Kawai
Ina jin maganar budurwa na hayo private jet na na taho
Na zo in yi bet
raying d’in shi (in ci amanar shi)’’
Ya k’arashe maganar yana mai kwashewa da dariya
haka suma guards d’in shi duk suka kwashe da dariya.
…
‘Da kyar Abbakar ya iya zaro wayarshi ya fara k’okarin kiran sir Najeeb.
…
Sai da suka gama dariyar su tukunna Black snake ya ci gaba da cewa
“da farko ina
ɗ
an tantama but yadda na ga Kabir ya rikice yana zuzutamin kyawun Yarinyar ne ya sa na amince na bi shawarar da ya bani na zo
Akan
‘Baba ya auramin ita ni kuma
in bar mishi
1 million,
na yafe har intrest d’in’!‘’.
Manubiya bata san tanada k’arfi ba sai da ta samu damar fincike hannunta daga cikin na black snake
dan ba k’aramin girgiza ta maganar sa ta k’arshe ta yi ba.
Dariya ya kwashe da ita
kafin ya ce
‘’Ai ba ki ji best part d’in ba ma
(Ai ba ki ji mafi ƙayatarwar shirin nawa ba ma),’’
Bai jira jn magana ba ya d’aura da cewa ‘’na yi zaton ke d’aya ne, to kuma da na zo sai na tarar ku biyu ne kyawawan matan, shiyasa na zo da better
plan(shirin mafi dac
ewa)
‘Zan auri
ɗ
aya in ajjiye d’aya mistress(ƙwara)’.
What a smart boy am i, ko??
(Ni
ɗ
in mai wayo ne, ko???’’)”.
Ya k’arashe maganar tasa da tambaya yana d’an rawa kad’an-kad’an sai kuma gaba d’ayansu suka sake kwashewa da dariya.
Kasa ma motsi Manubiya
ta yi dan gaba d’aya kanta ya d’au zafi,
In banda ambaliyar hawaye ba abunda take yi kamar an kunna famfo.
Su Blake snake sun jima suna dariyar da su Manubiya suka kasa fahimtar abunda yake sakasu yin dariyar kafin black snake ya d’aga bindigar sa ya h
arbi window dan haka duk suka yi shiru suka nutsu..
su Manubiya kuwa in banda karkarwa ba abunda jikinsu yake yi,
Addu’o’i kawai su ke karantowa
dan tabbas black snake masifa ne.
A kan Baba ya k’arasa ya tsaya tukunna ya ce
‘’Okay Baba,
komai yana Hannu
nka yanzu, kaga dai na
harbi mutane har biyu…
But bafa wai na yi releasing gaba d’aya temper d’ina bane ba(ammafa a hakan ba wai na saki gaba
ɗ
aya fushina bane), dan na yi iyakar k’ok’arina wajen danne Zuciyana shiyasa ka ga na harbesu a wajen da na tabba
tar ba za su mutu ba!
saboda bana so in yi mugun abu a gabanka a matsayinka na father inlaw d’ina(surukina)
Amma, na yi maka alƙawarin muddin ka yi mini gardama! musu! ko taurin kai! to zan kashe maza guda ukun nan
Sannan in tafi da matana!
Ruwanka ne
ka yarda ko kar ka yarda, kuma
ba za ka sake ganinsu ba
sai wataƙila bayan shekaru sha biyar in sun tsufa sai su dawo maka.
Dan haka idan ni ne kai Baba to zan yi wa black snake biyayya in aura masa mata d’aya in bar masa d’aya kamar yadda ya ke so
kowa
ya tafi safe….
A rabu ba tare da wani fad’a ko grudges (riƙon haushi) ba, kaga ta hakan sai mun fi kare dangantakar da ke a tsakaninmu a samu ta zamto lafiyayyiya kuma dauwwamammiya.
Sannan wani hanzari ba gudu ba,
Inaso ku san cewa ba za ku iya sharia
da black snake ba!
Dan haka idan ma kuna tunanin court ne
na wuce nan tun tun tun tuni….
I have my ways!
(Inada hanyoyi da dabaru na).’’
..
Da kyar Abbakar ya iya d’ago wayarshi ya kira sir Najeeb,
bai d’auka ba dan haka ya samu ya tura mishi message
d
a taimakon Ya Nafi’u wanda ya tambayeshi ‘’mai zai yi?’’ shi kuma ya ce masa ’’wanda zai taimakesu ya ke so ya kira’’
Daga nan ya gaya mishi shi kuma
ya rubuta;
‘Manubiya tana buk’atar taimakon Yash da gaggawa’
Da
Address d’in police station d’in da suke
a k’asa.’
Daga haka suka tura ba tare da an gansu ba.
Kishi haushi da kuma takaicin abunda ya sake aikatawa wanda ya yi wa kansa alk’awarin ba zai kuma ba ne…suka taru suka sake zuzutamasa azabar da ya ke a ciki…dishi-dishi ya fara gani, daga haka idan
uwansa suka rufe, ya sume a wajen yana mai addu’ar Allah ya sa Yash d’in ya zo, dukda kuwa kishi da takaicin sake had’ashi da Manu da yayi a karo na biyu yana ta addabar zuciya da ruhinsa amman kuma ba zai iya barin Manubiya a cikin wannan bala’in ba, baya
n ya san akwai hanyar da zai bi ya cece ta.
A chan gefe kuwa, wani
a cikin guards d’in black snake ne ya tak’ark’are yana yi masa
bayanin yadda ake auren Musulmai dalla-dalla, dan bai
gama sani ba kasancewar sa Christian.
A take suka yanke shawarar
za a yi na musulmai
kuma za a yi na Christian’s duk a wajen a yau!
Dan haka ya cewa d’aya a cikin guards d’in nasa ya tafi ya d’auko pastor
ɗ
insu na church ya zo da shi kafin a gama d’aura na musulman.
………
Kuka gaba d’ayansu suke yi,
ga
Abbakar a yashe an ce za a kaishi asibiti
Amma Black snake ya ce ’babu uban wanda zai yi motsi a wajen har sai an gama aura masa Manubiya.’
Zuwa wannan lokacin su kam sun d’auka ma Abbakar d’in ya rasu ne saboda dogon suma ya yi mai nauyi, duk wanda ya g
anshi ba zai yi tunanin akwai rai a jikinsa ba.
Sai da aka sake saitawa Ya Musbah da ya Nafi’u bindigu tukunna suka nutsu!
Baba kuma ya ce “shikenan ya yarda zai d’aura auren”
ya fad’a musu hakan, a ransa kuma yana tunanin ta yadda zai nemi mafita su samu
su zille.
Wani kalar murmushi black snake yake ta zubawa wanda ya ke nuna tsantsar farin cikin da ya ke a ciki…
bai tab’a had’uwa da Macen da ta sace zuciyarsa tashi d’aya kamar Manubiya ba, shiyasa har Allah Allah yake ayi ayi a d’aura musu aure, ya sa
mu cikakken iko a kanta, za ta ga soyayya, ya san za ta yarda da shi, duk da kuwa taurin kanta da yadda ya fahimci tana jin tsoronshi amma ya san idan ta ga ya riga ya zama Mijinta to dole ta yarda da shi sannan zai sameta yadda yake so dan ya san za ta
yi mishi biyayya….
Ga Manubiya matarsa wadda zata haifa mishi y’a y’a ga kuma jidda a gefensa mistress..
wannan wacce iriyar rana ce haka mai sa’a ta riskeshi!
Tabbas ya zama dole ya yi wa Kabir babban kyauta idan komai ya tabbata.
••••
Around 2:OO pm,
yana tsakiyar meeting kira ya shigo wayarshi, kamar ba zai kalla ba sai kuma ya d’an zaro wayar, ganin sunan Najeeb ya sanya shi saka wayar a silent ya ajjiye ta a gefensa, dukda kuwa ya san koma menene tou it’s very important tunda har Najeeb ya yi kiran
shi a dai dai wannan lokacin…dan ba su dad’e da gama waya da shi ba ya ce masa ‘zai sake shiga wani important meeting d’in da su Daddy, bak’in nasu har yanzu basu tafi ba, but in ya fito zai kira shi.’
Ba zai yiu ya amsa wayar ba, dan meeting d’in da su k
e yi mai matuƙar mahimmanci ne, shiyasa ya bari akan idan sun gama meeting d’in sai ya kira Najeeb ya ji dalilin kiran..
Kawai dai yana fatan Allah ya sa dalilin kiran ba abune mai mahimmanci sosai sannan wanda ake buƙatarsa da gaggawa ba, sannan yana fata
n Allah ya sa har zuwa lokacin da za su gama meeting
ɗ
in nasu lokaci bai riga da ya ƙure game da kiran da Najeeb
ɗ
in ya yi masa ba….
*MANNUBIYA*
*37*
Ba zai yiu ya amsa wayar ba, dan meeting d’in da su ke yi mai matuƙar mahimmanci ne, sh
iyasa ya bari akan idan sun gama meeting d’in sai ya kira Najeeb ya ji dalilin kiran..
Kawai dai yana fatan Allah ya sa dalilin kiran ba abune mai mahimmanci sosai sannan wanda ake buƙatarsa da gaggawa ba, sannan yana fatan Allah ya sa har zuwa lokacin da
za su gama meeting
ɗ
in nasu lokaci bai riga da ya ƙure game da kiran da Najeeb
ɗ
in ya yi masa ba…..
…..
Kiran Yashjub Najeeb yake yi yana sake maimaitawa..ganin ya jera masa kira sun fi sha biyar amman bai d’aga ba ne ya sanya Najeeb d’in yanke shawara
r ya tura masa message kawai, dan haka ya rubuta:’Yash, Manubiya tana da buƙatarka, ban san menene ya faru ba amma her friend(Abbakar)ya ce min
It’s very urgent!.’
Daga haka ya tura masa tare da address d’in police station d’in da su Abbakar suka turo, y
ana adduar Allah yasa ya gani ya kira.
A bangaren Yashjub kuwa dama tun d’azu ya nemi nutsuwarsa ya rasa, haka kurum ya ke ta jin wani iri..
so yake ya amsa kiran ko ya yi excusing kan sa ya fita amma kuma ya san idan yayi hakan zai gamu da b’acin ran Dad
dy ba na wasa ba!…
Yana cikin wannan tunanin ya ji k’arar shigowar message dan haka ya juya ya kalli wayar tasa.
Wani Irin bugawa k’irjinsa ya yi!
Bai san lokacin da ya mik’e tsaye ba
sakamokon message d’in sir Najeeb daya samu damar karantawa ta saman n
otification bar.
Da sauri Daddy ya ce
‘’Yash.’’
A d’an rikice ya kalli Daddy
sai kuma ya kalli Yasira da ragowar turawan da ke a wajen kafin ya ce
“sorry,i have to
go, it’s very important
(Ku yi haƙuri, zan je ga wannan kiran, yanada matuƙar mahimmanci)”
Ya fad’i hakan yana mai kallon wayar tasa sannan yana kallonsu, kafin ya tura kujerar tasa baya riƙe da wayar ya fita daga hall d’in gaba d’aya
kamarwalkiya yana mai cewa “pls excuse me(dan Allah a yi min afuwa)”.
Yana fita ya shiga kiran number Najeeb…
in banda bugawa ba abunda k’irjinsa ya ke yi..Manubiya a police station kuma!ta ya?garin yaya!…..
shi da yake ta fafutukar zuwa k’auye wajen ta, mai ya dawo da ita har ya kaita ga zuwa police station.
Yana wannan tunanin ya ji