Showing 147001 words to 150000 words out of 150519 words
neman Kai ne da kanta,
ga kuma abunda Ya Musbah ya gaya mata wanda gaba d’aya ya d’
aga mata hankali…..
A take a lokacin…ba b’ata lokaci, ya kira Baba.
Sai da Baba ya sake yi masa godiya tukunna suka fara tattaunawa…
Baba da so yayi su yi magana a waya kawai amman sai Yashjub d’in ya ƙi amincewa..a ranar suka zo da shi da Najeeb suka ha
d’u a masallaci ya amsa tambayoyin Baban.
Daganan Baba ya nemi da ya tura masa da adress d’in sa, ya ce masa “inshaaAllah bayan kwana biyu, za su neme sa.”
Ba abunda ya fi b’atawa ya Musbah rai irin yadda Baba ya sake d’aura masa alhakin yin bincike ak
an Yash, kuma ya hura masa wuta ko d’aga Ƙafa babu
ko duba halin da suke a ciki ma bai yi ba.
A b’angren Baba kuwa babu abunda zai iya shiga tsakanin sa da maganar Yashjub da Manubiya dan har ga Allah ya yi farin ciki matuƙa da ya ji Yash d’in yana son M
anu
ba wai kwad’ayi ko wani abun ba kawai dai ya san idan Manubiya ta auri Yashjub to hatta Jidda za ta samu kariya daga sharrin black snake….
Tun jiya da suka samu matsala da su Baba Habu hankalinsa yake a tashe dan ya san auren Jiddan da yake gani tan
a da Miji a Hannu ba mai yiwuwa baneba…
Shiyasa gaba d’aya hankalinsa ya sake tashi, sai gashi da ikon Allah Allah ya kawo Yashjub…..in dai aka yi bincike ya ji komai daidai akansa to inshaaAllah a cikin sati biyu kamar yadda ya fad’a zai aura masa ita.
….
.
A cikin kwana biyu Ya Musbah ya yi bincike ya gama, ya so ya ƙi gayawa Baba
amman sai Ya Nafi’u ya soma da yi mishi nasiha, ta inda ya ke cewa
’’ka kalli komai da kyakykyawar fuska, kar ka yi
mummunar zato. Mu bi komai da addua tunda bamu Isa mu hana
Baba yin abunda yayi niyya ba, uwa uba idan Ubangiji ya riga ya rubuta matarsa ce to fa ba mu Isa mu hana ba’’
Kamar ya Musbah zai fashe da kuka ya ce ’’Nafi’u ba fa anan ya girma ba,
taya za ayi amfani da shaidar da aka bayar akansa anan Nigeria??’’
N
asiha da fahimtarwa sosai ya Nafi’u yayi masa, sannan ya masa nuni da rashin son tsananta bincike kafin ya k’are da cewa “mu bi komai da addua, za a ga alkhairi inshaaAllah’’.
Ya Musbah bai iya gayawa Baba komai ba
Ya Nafi’u ne ya same shi yayi mishi bay
ani.
Sai washegari tukunna Baba yana shirin kiran Yashjub d’in shi ya kira sa.
Dan shi Yashjub har ga Allah ya k’agu, abu har kwana uku sun ce za su neme sa amma har yanzu shiru…Ya san ba shi da wani mummunan hali amman ya kasa hana kansa jin fargaba da t
soro.
Dukda ya san za a ga zumud’in sa amman shi fa akan Manubiya aga komai ma bai damu ba.
………Bayan doguwar gaisuwa da tambayar Baba ya jiki da jikin inna kuma sai kuma ya hau kame-kame.
Murmushi Baba yayi yana yaba yanda Yashjub d’in ya ke son Manubiya
, shifa tun lokacin da aka bata aiki dama ya fara tunanin wani abun
Shi a zaton sa ma sir Najeeb d’in ne sai da yaga Yashjub da yanda yayi lokacin da ya ga black snake rik’e da hannunta tukunna ya tabbatar Yashjub d’in ne.
Cike da kamala Baba ya ce ’’yan
zu nake shirin kiranka’’
Sai da Yashjub ya d’an sosa k’eya tukunna ya ce ’’to Bara inzo yanzun Baba’’…kamar wachchar ranar Baba so yayi kawai su gama a waya tunda ba wata magana mai tsaho bace ba amman sai Yash d’in ya dage akan yana so ya zo d’in….bayan
kamar mintina ashirin sai ga shi….
A masallaci yau ma suka sauk’e shi, Baba ya so ace su Uncle sun d’an shiga maganar amman ko da ya je musu ma ko kallo bai ishe su ba dan gaba suke yi da shi k’iri-k’iri, dan haka suka tari Yashjub iya su uku, Baba Ya Nafi
’u da Ya Musbah.
Cike da fahimtar juna Baban yace ‘’zuwa ko yaushe ya turo!
In ta shi ne yanaso ayi a cikin sati biyu ma amman ko yaushe suka shirya sai su fad’i lokacin da suka ga ya fi musu’’
Godiya da murnar Yashjub saida ta bawa Baba dariya dan kasa
b’oyuwa ta yi, musamman ma da ya ji Baba ya ce a cikin sati biyu!
Abun yayi masa dad’i matuk’a, shiyasa farin cikin sa ya kasa b’oyewa haka yai ta murmushi bayan yayi godiya
kafin daga baya suka yi wa juna sallama tare da fatan alkhairi,ya wuce.
Washe g
ari …..
Yau ya shirya samun Daddy,
jiya kwana ya yi yana sallah, yau
ɗ
in ma sai addu’o’i yake ta yi
tare da fatan ‘Allah kar ya sa a samu matsala ta ko Ina’
Dukda ya san tunda har hajiya mama ta amince to a rubuce yake Daddy shima ya amince, dan ko jiya
sai da ta kira shi suka yi maganar amma
dama shi addu’ar sa ‘Allah yasa su yarda ayi a cikin 2 weeks d’in, sannan Allah ya toshe duk wata matsala da take shirin tasowa.’
Suna gama waya da Manubiya wadda rikicin ta na kwana biyun nan yake basa dariya so
sai, ya mik’e ya nufi parlourn Daddy, dan ya san zuwa wannan lokacin Daddyn ya gama duk wasu aikace aikacensa……
A zaune ya same su shi da Ummi kamar wasu mak’iyan juna! Ita ta juya fuska tana kallon makeken aquarium d’in da yake a parlour ta had’e rai, shi
ma Daddyn ya kauda Kai yana daddanna wayarsa fuskar nan tamau!.
Ko isashshiyar gaisuwa Ummi bata tsaya sun yi da Yashjub ba,
ta mik’e ta ce ‘’sai da safen ku’’
daga haka ta yi wuff ta nufi ƙofa kamar wadda take zaune akan k’aya.
Bin ta kawai Daddy yayi
da kallo har ta fice ta rufo musu k’ofar….sam ya kasa gane kanta gaba d’ayanta, abun nata kamar wata mai aljanu, tun abun bai dame shi ba har ya zo ya fara damunshi…yanzu haka shi ne ya kirata akan su samu su d’an yi magana su d’an dedeta amma tana shigow
a daga gaisuwa ta d’auke Kai ta had’e rai! Shi kuwa wallahi ta yi kad’an ya bita ya rarrasheta!
Idan ma abunda take jira kenan……
Ahankali cikin kwantar da murya Yashjub yace mishi
‘’Daddy, wani lokacin fa muma sai mun d’an sak’k’o tukunna zaman yake yin
dad’i, kuma na tabbatar inda ace rikicin na iyakar kai da ita ne to da tuni komai ya wuce na san da bazata d’auka da zafi har haka ba, amman abun ya had’a da Yara shiyasa ta ji ciwo sosai.’’
K’ura masa idanu Daddyn yayi kamar ba zai ce komai ba sai kuma
ya sauk’e ajiyar zuciya tukunna ya ce ’’Yash!! Ko a gidan giya akwai babba. Ban auri Matar da zan dinga bin ta tana raina ni tana raina min wayo ba, yi haƙuri da abunda zan fa
ɗ
a a gaban idonka..ba wai cin fuska ba amma Yash ko Macen da na so fiye da kowa b
atayi min wannan abun ba.
Sannan nan gidansu Yasmeen ne, abu d’aya wanda na sani kuma ba zan tab’a komawa baya akan maganar tawa ba shine
‘Dole a lallab’amin Ƴaƴana a gidan ubansu, kuma babu wanda ya Isa ya zo nan ya ce zai juya min su!’
Idan ta yarda d
a hakan a zauna lafiya, in kuma ba ta yarda ba
ta je ta yi ta fushi
Itace ita ka
ɗ
ai……’’.
Ahankali Yashjub ya ce
‘’Amman Daddy…’’
Cikin d’an fushi Daddyn ya katseshi ta hanyar cewa
‘’Yashjub bar maganar Matar nan, banaso!’’
Shiruu Yashjub d’in yay
i,
kafin ya sauk’e ajiyar zuciya, sai kuma ya mik’e daga inda yake ya koma 3seater da Daddyn yake zaune akai shimanya zauna,a hankali ya ce ’’am Daddy’’
Murmushi Daddyn ya yi tukunna
yace “za a yi min wayo kenan’’
Dariya duk sukayi sannan Yashjub ya f
ara magana ahankali
“am..Daddy, dama
alfarmar ka da rufin asirin ka nake nema.’’
Bai jira komai ba ya ci gaba da cewa
“na san hakan yana iya zama kamar abu mai wuya amman idan ka yi min wannan gatan to ban san wanne irin farin ciki ni kaina zan shiga ba.
A baya ka sha gaya mana cewa
‘ wacece/wanene muke so a matsayin abokiyar/abokin zama, in dai tarbiyyar su ya kwanta maka to ba za ka yi k’asa a guiwa ba wajen ganin mun mallaki juna.
To Daddy ni a yanzu mahaifin Yarinyar da nake so yana buk’atar d’aurin
auren nan da sati biyu ne,
shiyasa nake neman alfarmar ka
In ba damuwa a d’aura a cikin sati biyun masu zuwan kamar yadda ya buk’ata.’’
Shiruu Daddy ya yi, har sai da Yashjub ya d’ago dan kalar shirun da Daddyn ya yi ya yi yawa,
had’a ido suka yi kamar
an fisgi maganar daga bakin Daddy ya ce ’’yaushe ka yi budurwa ??’’
fuskarsa tana baiyyana mamaki
Sunkuyar da Kai Yashjub ya yi da sauri dan tashi d’aya ya ji wata kunya ta lullub’esa.
Lokaci guda ya ji Daddy ya fara dariya, cikin dariyar ya sake cewa
“Dan Allah dagaske Yashjub ya akayi ka yi budurwa, abun ya bani mamaki ne, Hajiya Mama ta yi min magana tun lokacin dama nake so ka yi min maganr saboda a tunanin na ita ta had’a ka da Yarinyar ashe da gaske kai ka kyallo abarka.’’
Ya fad’i hakan yana dari
ya….
Kamar Yashjub zai fashe da kuka cikin yin kalar tausayi ya ce
‘’Daddy dan Allah ka daina’’
Ai kuwa ya sha tsokana a wajen Daddy, dan har ga Allah Daddyn ya ji tsananin mamaki,
kafin daga bisani kuma ya yi
gyaran murya ya gyara zama tukunna ya ce
’’Yash ka tabbatar kana sonta, itace zabin ka?’’
Ahankali yace ‘’Eh Daddy, da dukkan Zuciyata.”
‘’Alhamdulillah’’
Daddyn ya ce
kafin ya ci gaba da cewa
‘’Yash, tabbas alk’awarin da na yi muku yana nan, babu abunda ya chanza amma ka san ba zan bari ka c
utu ta ko wacce irin hanya ba.
Abu d’aya da na yi mamaki shine ta inda Mahaifinta ya dage akan a yi a cikin sati biyu
wannan shine abunda zan fi sakawa na’urar bincikena akai wanda ina fatan ya kasance ba wata matsala baceba dan nima farin cikin naka nake
son gani.
Idan an duba an ga ba matsala sannan aka yi bincike shima akaga ba wata matsala to da yardar Allah sai a d’aura auren a cikin sati biyun kamar yadda suka buk’ata.
Allah ya yi maka albarka.”
Ahankali Yashjub ya sauk’e ajiyar zuciya yana mai jin
wani farin ciki mara misaltuwa kafin a hankali a fili ya ce ’’Alhamdulillah’’
Muryar Daddy ce ta katse shi jin yana cewa “Ka bani adress d’in da wuri, saboda ina gama binciken nake so zan aikawa su Hajiya mama, dan a samu su taho da wuri suma.’’
D’an b’
ata fuska Yash yayi ya d’ago ya ce ’’Daddy yanzu wannan tsohuwar itama sai ta zo?’’
Dak’uwa Daddyn ya yi masa kafin ya ce ’’Dole ta zo, kuma in ka yi mata abunda bata ji dad’i ba tsaf sai ta ce a fasa,
kasan kuma daga ni
har uncle d’in naka dole abund
a tace shi za mu yi,
daganan sai in ga k’arshen soyayya’’
Da sauri Yashjub ya ce ‘’Na gode sosai Daddy, zan turo maka adress d’in yanzu inshaaAllah’’
daga haka ya mik’e da sauri yace’’sai da safe’’ tukunna ya fice
tun kafin Daddy ya sa shi ya nutse cikin
k’asa a take a wajen dan ya lura sarai yau Daddy tsokana yakeji
shikuwa ba zai iya ba.
Hakanan ya wuce zuciyarsa cike taff da farin cikin da bai tab’a tsintar kanshi a cikin kwatan kwacin sa ba….
Bayan fitar Yashjub,
A hankali
Daddy ya lumshe idanuwa
nshi…
Tabbas ya yi matuƙar farin ciki da Yashjub ya samu wadda yakeso, kuma gashi da izinin Allah zai aureta.
Yana tuna lokacin da ya auri Mommy……shiyasa a ko da yaushe yake addu’ar Allah kar ya sa d’aya a cikin ya’yan shi ya
ɗ
an
ɗ
ana kwatankwacin wannan fe
eling
ɗ
in (yanayin), dan shi kad’ai ya san mai ya ji, shi kad’ai ya san zafin aurar wanda ba ka so!.
Har i yau kuma yana tuna lokacin da ya auri amaryarsa Khadijah…farin cikin da ya rayu a ciki shi yake yi wa gaba d’aya ya’yansa kwad’ayin
su samu, shiyas
a ya dad’e da yi musu alk’awarin ko waye sukeso
A ko wanne irin yanayi
InshaaAllah zai shige musu gaba ba zai yi k’asa a guiwa ba wajen ganin sun mallaki juna!!!
Wannan dalilin ne yasa bai takurawa kowa a cikinsu akan yayi aure ba, saboda yana so su nutsu
kowa ya nemi wanda yake k’auna cikin nutsuwa…
Yahanasu itama gani yayi kamar tana cutuwa ne shiyasa yake saka baki a cikin lamuranta ba dan haka ba to da ba zai tab’a cewa komai ba,
dan bashida wani burin da ya wuce yaga gaba d’aya y’ay’ansa sun samu asa
lin ƙauna da sahihin farin ciki na gaskiya
kamar yadda shima ya samu
A
lokacin da Khadijansa take da rai!!
A hankali wasu zafafan hawaye suka shiga bin k’uncinsa…
wannan wanne irin feeling (yanayi) ne?
Ya tsaneta!
Sannan kuma har yanzu yana mahaukacin
sonta da k’aunarta
Kuma
Ji ya ke kamar ya kashe kansa saboda abunda ya yi mata…
Wanda Zuwa wannan lokacin ya gama yanke shawarar
Idan Allah ya ba shi ikon ganin auren hatta Yadira, ya kuma tabbatar da Ƴaƴansa duk sun girma sun kama ƙasa za su iya kulawa
da kansu
to inshaaAllah zai mik’a kanshi ga hukuma!!
Ba zai iya ci gaba da jure wannan rada
ɗ
in ba ,shi kad’ai ya san me yake fuskanta me ya ke ji a cikin zuciya da ranshi!
Babu wanda ya lura ba kuma wanda ya sani amman a ko wacce rana ta duniyar nan yana
fuskantar azaba mai tsanani ne.
……..
Tun ranar da Yassir ya je d’akin Kausar ya tarar da ita suna magana da Yassira…..tun daga wannan ranar bai sake saka ta a Idanunsa ba dan wasan y’ar b’uya ta hau yi da shi gadan-gadan.
Sai yau ne tukunna ta daure da
kyar ta ce ‘bari dai ta lek’a sa’.
Sai chan dare wajajen sha biyu, tukunna ta samu ta lek’a d’akin nasa, ita ala dole za ta yi mai basaja gudun kar ya fahimci komai…
Ba yabo ba fallasa ya karb’eta, dan haka ta samu kwarin guiwar zama a kusa da shi suka g
aisa tukunna ta ce “kwana biyu ka ji ni shiru, sorry mun d’an sake samun matsala ne ni da Daddy shiyasa ka ga Ina kuka ranar da ka zo, to kuma tun daga ranar bani da lafiya sai yau ne na d’an ji dama-dama,’’
Ta fad’i hakan tana mamakin yadda tun ranar da
ya zo ta rufe k’ofa bai nemeta ba, sannan bai sake lek’a d’akin ta ba, ko a waya bai ce mata hi ba, yau kwanaki hud’u kenan.
Murmushi kawai ya yi mata ya ce ‘kar ta damu ba komai’
daganan ya d’an ja ta da hira…
faram-faram dai haka ya yi mata kamar ba ko
mai.
Abu d’aya ne ya bata mamaki ta inda ‘ta nuna za ta kwana a d’akin nasa’ amman sai ya ce mata ‘’its fine(ba komai), ta tashi ta tafi kawai, ita da bata da lafiya ma’’
Itanma daman hakan take so,
dan haka ta yi masa sallama
daganan ta fice, tanata
mamakin sa.
Sai kamar bayan mintuna goma da fitar tata tukunna ya d’auki wayarsa ya shiga ya kira wata number, tana fara ringin ya mik’e ya fice ya tsaya a balcony d’insa wanda yake opposite inda ake parking motocin gidan….
Har ga Allah bai shirya yin ha
ka tun yanzu ba!
Ya so ace ya bashi wahala ya kassara shi tukunna sai yayi shawara abunda zai yi
masa a gaba
amma Kausar ta janyo komai,
ya lura barin shi a doran k’asa yana numfashi had’ari ne a garesa ta ko wanne fanni!!..dan haka dole a yi gama kawai.
Dakyar yana jin yanda tunanin ya sake tunzura zuciyarsa ta fara tafarfasa ya ce ’’ba kowa
ta nan, cameras d’in ma na tsaida su
Ka yi sauri kafin su yi zagaye.’’
Yana nan tsaye a wajen a yadda ya ke d’aya
daga cikin masu yi wa gidan hidima wanda suka
gama wayar dashi kenan
Ya lallab’o ya je shi jikin motar da Yashjub yake fita aiki da ita kullum ya kunce tayoyi biyu ba duka ba…ya kunce su ta yadda ba za ayi tafiyar mintuna biyu da motar ba tayar gaba da ta baya waenda ya kunce d’in za su fita .
Sai
da Yassir ya ga Mutumin ya kammala komai ya koma inda ya fito tukunna
shima ya koma d’akinshi ya rufe k’ofar balcony d’in, yana jin wani nauyi yana sauk’a daga kan k’irjinsa.
Addu’arsa d’aya ‘Allah yasa kar Yashjub ya bashi mamaki gobe ta hanyar chanza m
otar hawa’
Yayinda a d’ayan b’angaren zuciyarsa yake mamakin Kausar da kuma tunani da lissafin abunda zai yi mata idan zarginsa a kanta ya tabbata, hatta Yassira itama sai ta karb’i rabon ta wallahi,
dan ya lura tabbas itama ta san wani abun daman tun ba
yau ba!
Za su san sun yi wasa da hankalin shi kuwa.