Showing 81001 words to 84000 words out of 150519 words
jiki da ni ga shi kuma k’addara ta had’a mu zama guri d’aya,ya kenan?’’
Ta k’arashe maganar tata da tambaya tana murmushi.
Murmushi Manubiya ta yi
kafin a ranta ta ce
‘’Tabbas k’addara ta had’a ni zama guri d’aya bama da ke kad’ai ba har da wanda nake
gudun ki domin shi.’’
A fili kuma sai tace
‘’Ba komai Maama ba gudun
ki nake yi ba kawai dai abubuwan ne suka d’an yi min yawa,shiyasa.’’
Cikin rashin jin dad’i Maama tace’’Ayya!na ji Ammi tana cewa mamanki ma ba lafiya ko?’’
Ahankali Manubiya ta d’aga kanta alamun’’eh’’
Cikin tsananin jin tausayin ta
maama ta ce
‘’Al
lah ya bata lafiya Allah ya sauwwak’e, ku yi ta addu’a za ta warke inshaaAllah, kin ji ko?’’
Ahankali ta jinjina mata kai tukunna tace ‘’nagode Maama’’
ta fad’a hakan tana mai Jin tsananin k’aunar matar na shiga ranta.
Murmushi Mama ta yi, ta matso ta d
’an shafa fuskar Manubiya
tukunna ta ce
‘’Allah ya yi miki albarka”
daga nan ta wuce ta fita daga kitchen d’in..
so gamon jini!!
ita dai haka kurum Ubangiji ya d’aura mata k’aunar Yarinyar,
tana jinta ne har cikin ranta…….
BULAMA ✍
️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*28*
Har wajajen 11 shiru babu Daddy ba Yasira a company.
Baƙin da suka yi
ma Yashjub ne ya yi handling d’insu shi kad’ai, gashi yana ta kiran number Daddy amma baya d’auka ita kuma Yasira nambobinta duk ba s
a shiga.
Dan haka Baƙin suna tafiya
shima ya kamo hanyar gida.
Sai k’arfe 10 tukunna likitocin da su ka karb’i Yasmeen suka fito,
cikin son fahimtar dasu
Babban Likitan ya kalle su ya ce
“It’s nothing serious(ba wani babban abu bane ba), dan bai tab’a
komai ba kawai dai d’an kurjewa ta yi shiyasa kuka ga jini.
abun nata dama ina so in bata sabo shine kawai muka tsaya aka d’an yi dressing wajen na bata sabo na bata drugs da 1 week off ta huta a gida,
Allah ya kare gaba.’’
Cikin samun relief dukkan su s
uka ce ‘’Ameen’’ sai a lokacin tukunna Yasira ta d’au waya ta kira Mommy take gaya mata komai.
Office Yasira ta wuce
Yusra da Ya’isha da Yadira kuma school, yayinda Daddy da Kausar suka kama hanya domin maida Yasmeen gida.
Suna shiga Daddy ya cewa Kausa
r ta kai Yasmeen d’akinta shi kuma ya nufi b’angaren Ummi…..
Bai same ta a d’akin nata ba ashe ya baro ta a k’asa a d’akin Yahanasu wadda zazzab’i ya rufe tun jiya da daddare ba wanda ya sani.
Munirat ya tarar tana share d’akin, cike da girmamawa ta durk’
usa har k’asa ta gaida shi, ba yabo ba fallasa ya amsa
kafin ya ce mata “Ina saddik’a?’’
A hanakali tace masa
‘’Tana d’akin Adda Yahanasu wadda batada lafiya’’
A ranta tana mamakin Allah dai yasa lafiya dan bata tab’a ganin shi a dai dai wannan lokacin
a gida ba,
kuma a side d’in Ummi.
Cikin fushi ya juya da niyyar fita, a bakin k’ofa suka yi kicibis da Ummi wadda ta ji shigowar su ta biyo domin ta ji ya jikin Yasmeen d’in….
tunda suka fita ta ke trying numbers d’insa, saboda ita shi kuma ya saka wayoy
inshi gaba d’aya a silent..
Da kyar Daddy ya iya cewa
‘’Munirat give us a moment
(Munirat bamu waje)”
ya fad’i hakan idanuwansa a kan Ummi, ba tare da ya kalli Munirat d’in ba.
Da sauri ta ajjiye parker da abun sharar ta fice daga d’akin, tana tafe tan
a waiwaye gaba d’aya hankalinta a tashe
tana mamakin me ya had’a su haka dan ita Ummi bata ce mata komai ba tun
ɗ
azu, gashi
ta ga ran Daddy a mugun b’ace!!!
ba abunda ya fi d’aga mata hankali irin yadda ta ga mood d’in nasa, tsoronta kar ta je ya bugi U
mminta…
tana tafe tana lissafi tana waiwaye haka ta fice a parlourn, bata yi auni ba kawai ta ji ta afka kan Mutum,
da sauri ta ce ‘‘Innalillahi’’
sai kuma ta fara k’ok’arin kwace kanta daga rikon da Yassir ya yi mata.
Tunda ta taho tana kallon baya ya gan
ta dan lokacin dai-dai shi kuma ya fito daga corridor na side d’in Mommy ,
ahankali ya wani lumshe ido ya bud’e saboda yauma riga da wando ke jikinta na bacci irin me bin jikin nan, rigar iya cinya wandon kuma har k’asa,dan haka a ransa ya ce ‘’lucky me’’
Ganin bata gansa ba ne ya sanya shi sake nutsuwa ya ƙi motsi gudun kar ya ankarar da ita,ai kuwa da ikon Allah ta afka jikinsa!!!
Without thinking twice shi kuwa ya rungume ta gamgam….
tana d’agowa su ka yi ido biyu da shi, cikin tsananin firgici ta ce ’’g
et off me, (ka cika ni) baka da hankali ne’’
Ta k’arashe maganar cikin tsawa.
Wani irin murmushi ya yi kafin ya ce
‘’Munirat yo ai ko malaikan mutuwa ne ya zo d’aukar raina
to
Sai ya d’aga min k’afa na gama appreciating moment d’innan (godewa lokacin
nan)
tukunna ..’’
Wani irin kuka ta saka kafin ta fara k’ok’arin kwace kanta tana magiya tana kai masa duka, ganin tana neman cika masa kunne ne ya sanya ya fara k’ok’arin kissing d’inta…..
A gigice ta kwala wata mahaukaciyar k’ara dai-dai shima Yashjub y
a ce
‘’Yassir’’
Cikin tsawa
………….
Achan d’aki kuwa, Munirat tana fita
Daddy ya cewa Ummi ‘’Ki had’a kayanki, duk wani abunda kika san naki ne, ki tartare, ki bar min gidana’’
A hankali Ummi ta ce
‘‘Daddy har me ya yi zafi haka?
Wallahi Kausar k’arya
take yi, ban san Yasmeen tana da matsala a Kunne ba!
Sannan ya kamata ka tsaya ka ji abunda Yaran nan su ka yi min kafin ka yanke wannan d’anyen hukunci hak….’’
Cikin katseta Daddy ya ce
‘’Na san k’arya Kausar ta yi miki, na san basu gaya miki Yasmeen ta
na da matsala a kunne ba.
Kinsan abu na farko da ya fara had’ani da ke?’’.
Cikin zubar kwallah Ummi ta girgiza kanta alamun’’a’a’’
Cikin fushi Daddy ya ce
‘’Ranar da kika zo d’akina kika bamu asalin labarin Munirat da Bashir, me na ce miki ??’’
Cikin in
da inda saboda duk ta rikice ta ce
‘’Cewa ka yi komai ya wuce,
amman Daddy su Kausar basu..’’
Cikin tsawa ya ce ‘’ba wannan ba!d’ayar maganar tawa ta k’arshe, me na ce miki Saddik’a?’’
A gigice ta ce
‘’Cewa ka yi zaka saka su su bani hak’uri’’
‘’Good
’’
Daddy ya furta yana mai sake matsowa kusa da ita
wanda hakan ya sanya Ummi ta d’an ja baya dan ba kad’an ba ta tsorata da Daddyn, bata tab’a ganin shi a haka ba tunda su ke.
Cikin zafin zuciyar da ya ke ji tana taso masa ya ce ‘’na fad’a miki bara in
sake maimita miki!
dan naga kamar kin manta,
Abu uku na fi tsana a yi min
waenda su ne suke janyowa Mutum ya ga other side d’ina;
A yi crossing d’ina
A ci Amata
na uku, a nuna min ban Isa ba!!
Duk yadda na kai ga son Mutum da ganin girman sa
muddin ya
yi min haka to babu
dalilin da zai hana ni yin kacha-kacha da shi…...
da nace miki ki jira zan sanya su su baki hak’uri dan me yasa kika yi gaban kanki?
saboda kin raina ni?
saboda ban isa ba?..na ji sarai na kuma san me kika yi
Yasmeen ta gaya min yadd
a kika tara su a dining table
kina cewa su zauna lafiya da Munirat, kina gindaya musu sharud’a kina jera musu warning alhalin su already komai ya riga ya wuce a wajen su…..
Me kike so ki yi proving by doing that??(ki nuna ta hanyar yin hakan??)
bari kiji
nan gidan ubansu Yasmeen ne, Munirat kara kawai na yi mata nake bata shelter saboda ke, and if za ki nemi ki takurawa ƴaƴana saboda ita har ta kai ga kina k’in jin maganata kina k’etare umarni na to kuwa ban ga dalilin da zai sanya in ci gaba da zama da i
ta a gida d’aya da ke kan ki ba!!!
Sannan yau har kina da guts d’in da za ki d’aga Hannu ki mari Yasmeen?kin tab’a gani na yi wa Munirat kallon banza???
Ko ma me Yasmeen ta yi miki ko ma menene Saddiƙa
ban ga dalilin da zai sanya ki mare ta ba’’
Cikin s
hare hawaye Ummi ta ce
‘’ko menene?’’
Ciikin fushi Daddy ya ce
‘’Ko uwar ki ta zaga ban baki ikon ki tab’a d’aya daga cikin Ƴaƴana ba!!!
Kin tab’a ganin uwar da ta haife su ta d’ora Hannu akan su??’’.
Wani Irin kuka Ummi ta fashe da shi ta durk’ushe a
wajen, dan ba wanda ya fad’o mata a rai a dai dai wannan lokacin sai
Marigayin Mijinta..
Sam bata bawa Daddy tausayi ba, dan shi wani irin haushi ma ta ci gaba da bashi, ji yake yi kamar ya yi ball da ita.
Kwanakin baya Mommy ta tuno masa da Khadija ya
nzu kuwa Saddik’a ce ta tuno mishi da ita..ta yadda ta nuna masa bai Isa ba, bashi da girma da daraja!!!
ta yadda ta nuna son kanta ta fifita y’arta k’iri k’iri sama da shi.
Cikin fushi ya sake cewa “ki tashi ki had’a kayan ku…”
Maganarsa ce ta mak’ale
sakamokon ihun Munirat da suka jiyo..da gudu Ummi ta nufi waje..kafin ta k’arasa ta fara jiyo na Yassir shima…..
Ummi na fita Daddy ya bi bayanta da kallo cikin takaici….
kafin kuma ya nufi wardrobe d’inta da kansa ya fara firfito mata da kayanta yana
sauk’e akwatunanta sannan ya ja akwatunan ya fitar parlournta
daga nan ya wuce ya fitar dasu daga side d’inta gaba d’aya!! ya nufi chan babban parlourn da ke a saman…
ko damuwa da ife-ifen Yassir bai yi ba kawai shi a halinda ake ciki babban burinshi shin
e Ummi ta fitar masa daga gida, kawai shi dai ta fita, ya san in ta fita shine zai samu nutsuwa…..
…
A chan parlourn kuwa…
Yashjub yana hango su bayan ya daka masa tsawa, sai kuma ya nufe su cikin tsananin tashin hankali.
yana zuwa bai yi wata wata ba ya j
anyo Yassir ya kifa masa wani gigitaccen marinda har sai da ya sanya Yassir d’in ya kai k’asa yana shirin tashi ya zaro belt d’in jikin wandon shi ya rufe shi da duka yana ball da shi.
Yanayin dukan da Yashjub ya ke yi masa ba irin dukan da normal Mutum
zai yi bane ba saboda k’arfin Yashjub d’in na daban ne
shiyasa duk yadda Yassir ya so daurewa sai ya kasa ga shi ya kasa tashi dan yana yunk’urawa zai tashi Yash d’in yake kuma kai masa duka da k’afa ya kwantar da shi.
Kusan a tare Mommy Kausar da Ummi s
uka k’araso wajen….
Kausar ce ta fara k’arasawa kusa dasu da niyyar rabawa ai kuwa itama ya zula mata belt dan dama haushin ta yake ji.
Da sauri Mommy ta matsa ta janyo Hannunta ta mayar da ita gefe, tukunna ta yi kan Yashjub d’in…
Da kyar ita da Ummi su
ka samu suka rik’e Hannun Yashjub wanda idanuwansa suka yi jaa sosai.
Cikin tsananin b’acin rai Mommy ta fashe da kuka ta ce ‘’haba Yash, wanne irin abu ne wannan?
Ko Yaro d’an shekaru sha takwas ai ba ka saka a gaba da duka irin wannan ba’’.
Cikin rashi
n jin dad’i da dauriya Ummi ma ta ce ’’Yash baka kyauta ba, ko ma me ya yi maka bai kamata ka dake shi haka ba.’’
Sai kuma suka juya ga Munirat wadda ke durk’ushe a wajen
Mommy ta ce ‘’me ya faru’’
Gaba d’aya ta tsorata ta gigita daga abun da Yassir ya
yi mata ga kuma dukan da taga Yash yayi masa shiyasa da gudu ta tafi jikin Ummi ta fad’a ta fashe da kuka tukunna ta ce ’’Ummi dan Allah dan Annabi ki zo mu bar gidan nan, idan kuma ke ba za ki tafi ba ni gaskiya zan tafi’’.
Dai-dai nan Daddy wanda ya gam
a janyo akwati ya cillo waje
ya ce
‘’Kar ki damu, yanzun nan za ku tafi’’.
Da sauri Yashjub wanda tun
ɗ
azu yake ta karanto sunayen Allah yana k’ok’arin daidaita kan shi, ya runtse idanuwansa da k’arfi.
Dai dai nan su Yahanasu da Baba larai suka hawo sam
an
sakamokon hayaniyar da suka ji.
Yahanasu ce ma ta lura da yadda gefen kan Yassir ya ke zubar da jini sai kuma taga kamar ma baya motsi da sauri ta k’arasa kansa ta shiga tattab’asa tana kiran sunan shi’’yasssir! yassir!!’’sai
kuma ta juya ta kalli
Baa
ba Larai a rikice ta ce ’’baya motsi fa’’.
Cikin tsananin tashin hankali Mommy ta kalli Yassir itama ta tabbatar ba ya motsin, bata san lokacin da ta juyo ta kifawa Yash wani irin gigitaccen mari ba sai kuma ta sake fashewa da kuka ta durk’ushe a kan Yas
sir,
cikin tashin hankali ta ce
‘’Shikenan ya kashe min Yarana, ya kashe min d’ana mafi soyuwa a gare ni, shikenan ya kashe min gudan jinina….’’
Da sauri Baba Larai ta ce
‘’Haba Khadijah, ki yi shiru mana, bai mutu ba inshaaAllah’’
Sai kuma ta durk’usa
ta mikar da ita, tana tittirjewa tana kuka haka suka jata ita da Kausar suka nufi b’angarenta da ita, tana kuka kamar ranta zai fita.
A hankali Daddy ya k’arasa ya dudduba sa, ba tare da ya kalli Yash ba ya ce ’’kama min shi mu kai sa d’akinsa.’’
Yana ga
ma fad’in haka ya d’auko waya ya kira family Dr.d’insu, daga nan suka fara k’ok’arin kinkimar Yassir.
Har sun kama hanyar k’ofar d’akin Yassir d’in Daddy ya d’an tsaya ya juyo ya kalli Ummi ya ce ‘’kar ki k’ara minti biyar a cikin gidan nan’’.
Daga haka
suka yi gaba suka wuce shi da Yashjub.
A hankali Munirat ta k’arasa kusa da ita ta rungume ta
cikin zubar hawaye ta ce ’’ sorry Ummi, it’s for the best
InshaaAllah( ki yi haƙuri Ummi, hakan shine mafi alkhairi, in sha Allah)”
Munirat ta fad’a hakan dan
ita duk a tunaninta ita ta sake tunzura Daddy dan taga Daddy ya ji lokacin da ta ce su bar gidan……
A kan gado suka kwantar da Yassir,
Daddy ya sake zaro waya ya shiga kiran Dr domin ya ce masa ya zo da sauri, yayinda Yashjub ya faki idon shi ya juya ya f
ice,
ya nufi wajen su Ummi.
Bai same su a main parlourn saman ba dan haka kanshi tsaye ya wuce side d’in Ummin.
A bakin k’ofar d’akinta ya tsaya yana knocking, lokacin suna tsaye suna mamakin yadda Daddy ya watsar da gaba d’aya kayan wardrobe d’in Ummin
,
ahankali Ummi ta faki idon Munirat
ta goge hawayenta ta nufi k’ofar da ta ji ana bugawa tana addu’ar Allah yasa kar Daddy ya sake creating wani scene d’in a gaban Munirat dan ita a tunanin ta shine ya sake dawowa, amma tana fita sai ta ga ashe Yashjub
ne.
Dukda halin da take ciki haka ta daure ta b’oye tata damuwar ta ce
‘’Yash, dan Allah dan Annabi kar ka sake yi wa d’an uwanka irin wannan dukan,
Dan Allah’’
A hankali Yash ya had’iye wani k’ululun da ya mak’ale masa a mak’oshi yana mai mamakin kya
kkyawar zuciya irin tata
tukunna ya ce
‘’Na ji Ummi, ba zan k’ara ba amma kema kar ki je koina,
I’ll speak with daddy (zan yi magana da Daddy),
In ya huce’’.
Murmushi ta yi kafin ta ce masa
‘’shigo’’
Ta fad’i hakan tana matsawa ta bashi hanya ya shigo
cikin d’akin nata da sallama a bakinsa…
da mamaki shima ya ke kallon d’akin sai kuma ya kalle ta.
Cikin karyewar zuciya ta ce
‘’Ni kaina Yash bana son barin gidan nan, banaso aurena ya mutu, amma kuma kalli abun da Daddy yayi, shiyasa na ga tunda har ab
un ya kai ga haka gara in fita tunda lafiyata da mutuncina..tun kafin ya zo yayi fata fata da ni kamar yadda yayi da kayana, amma Ina so ka fad’a masa ko bayan na bar gidan nan cewa ina son Y’ay’ansa kuma ba zan tab’a cutar da d’aya daga cikin ku ba.’’
Y
adda Ummi take hawaye
da kuma abunda Daddy ya aikata tabbas ya san Ummi ba za ta yarda ta k’ara minti uku ba ma a cikin gidan, shiyasa a hankali ya jinjina mata kai kawai alamun fahimta,
yayi hakan yana mai kallon windunan d’akin da kuma hanyar closet d’
inta har zuwa toilet ya tabbatar babu ta inda za su fita,
ya ji dad’i da balcony d’inta ya kasance a parlour ne
dan wallahi ko shi ne Daddy ya yi mishi wannan tijarar sannan ya ce ya fice mishi a gida to
sai ya fita ko ta window ne, daga baya ya dawo a s
asanta…..
A hankali ya ce
‘’Na fahimci ki, Ummi.’’
Murmushin da ya fi kuka ciwo ta yi ta ce “ka kula da y’an uwanka, Allah yayi maka albarka’’
‘’Ameen’’ ya ce,
daga nan ya juya yana zuwa k’ofar yayi sauri ya sa Hannu ya zare makullin kafin ta k’araso t
a ce wani abun har ya fice ya