Showing 69001 words to 72000 words out of 150519 words
mu d’auki alhak
in Ummi da y’arta bayan kai ne ka yi alk’awarin za ka zame mata uba.
Sannan magana ta biyu su Ya’isha ya kamata a taka musu burki tun yanzu, kar su saka Yarinyar nan a gaba, and also tun daga kan Yasir har izuwa kan Yadira gaskiya Daddy ya kamata a yi wan
i abun saboda kwata-kwata basu san ya kamata ba, ko ni da na tashi a Uk ba zan yi abubuwan da suke yi ba, na san muna iyakar k’ok’arin mu wajen basu tarbiyya amma abun nasu kullum k’ara gaba yake yi!..
Kalli abun da suka yi wa Munirat da Ummi yau sannan
Yassir yau da na je gidan da ya ke abunda na gani ba zan ma iya sake maimaitawa ba saboda k’azantar ta yi yawa….
da shi da Abokansa guest house guda suka ware suke zaune da y’an Mata abun babu kyan gani, ya kamata a tsawatar musu tun wuri Daddy,
B4 it’s t
oo late
(Kafin lokaci ya ƙure).”
Shiruu Daddy ya yi yana nazari
‘Tabbas shima sai da ya shigo ya nutsu yanzun tukunna ya fara ganin rashin kyautarwar sa, kawai dai itama Ummin bai kamata k’iri-k’iri ta bi bayan y’arta ba, ya san wannan dalilin ne ya sake
fusata shi.
Sannan bai san daliliba
amma tana yawan bashi haushi, haka kurum wani lokacin ko magana in ta yi sai ya fusata!!!
Saddik’a ba ta da laifi tana da
biyayya ga tsafta shiyasa ya ke ta k’ok’arin danne zuciyarsa a samu su zauna lafiya sannan ya k
e danne duk wani takaicin ta da yake ji, ya ke kuma kyautata mata amma duk da haka bata appreciating sam kalli yadda yau ta bad’a masa k’asa a ido a gaban jama’a, yana fad’a tana fad’a’.”
‘’Assalama alaikom’’
Sallamar Mommy ta katsewa Daddy tunani.
Ciki
n nutsuwa ta k’araso, Yassir yana biye mata a baya…
A kan one seater Yassir ya nemi guri ya zauna Mommy kuma ta zauna akan 2 seater,
daganan parlourn ya yi shiru.
Da kyar sannan ciki-ciki Yassir ya ce ‘’Daddy ina wuni’’.
Ko kallon shi Daddy bai yi ba ins
tead sai ya juya ya kalli Mommy sannan ya ce ’’Kin san d’anki a guest house ya je ya zauna yana shed’ana?
Ya ce ki yi masa aure kin k’i bada had’in kai kin tarwatsa abun,
to gashi yanzu ya nuna miki kalar b’arnar da zai yi idan aka k’i a yi masa auren.
Ma
i yasa ba kya so ya auri Kausar?’’
Daddy ya k’arashe maganar tasa da tambaya, kansa tsaye yana mai sake fuskantar ta.
Gaba d’aya diriricewa Mommy ta yi, tana mai jin takaicin
yadda Daddy ya ke k’ok’arin
had’a mata bomb tsakanin ta da Yassir, har ma da Y
ashjub.
Cikin katse mata tunani Daddy ya ce
‘’Anyways shikenan, ku kuka sani!
na riga na cire Hannuna a lamarin kuma wallahi I’m very glad about the fact that (na yi farin ciki sosai da)
Yassir bai auri Kausar ba!!
Dukda cewa shima naga alamun ya zama
d’an duniya
amma duk lalacewar giwa ta fi kare…..
yanzu dai abu biyu zuwa uku nake so in yi miki magana kuma in ja miki kunne akai, ki saurara ki jini da kyau…
Ki san yadda za ki yi ki gyara d’anki ‘Yassir’ idan kuma ba haka ba to zan kwace company d’in
da na bud’e masa, saboda na ga sai ya shafe morethan one month ma bai je ba dan haka a gani na babu amfanin a bar masa…
akwai Yaran Abokaina architecture’s da yawa, zan iya bawa d’aya daga cikin su!!
C’e’o kawai zan chanja cikin k’ank’anin lokaci za a c
hanja suna da komai.
Sannan idan bai shiryu ba to ba k’aramin aiki bane in kore sa a cikin gidana gaba d’aya!!
Saboda
ba zai yiu ya dinga yin yadda ya ga dama anyhow ba!!!
Ban ga dalilin da zai sa ya je yayi iskancinsa kuma ya dawo min nan ni kuma in ba
shi shelter ba!!!!
Ya nuna zai iya rayuwa shi kad’ai, tunda gashi ya fi 1 month (wata
ɗ
aya) ba ya tare da mu, dan haka idan na sake jin wani shirme daga garesa wallahi sai na baku mamaki…..
Amma for now a matsayina na ubansa zan saka a yi masa sauk’a, a r
aba sadak’a, a saka shi a addu’a
‘Allah ya shirye shi..’
daganan kuma idan bai shiryu ba ya nuna min ya fi k’arfina to sai dai mu raba gari ni da shi..”
Daddy ya k’arashe maganar cikin tsananin fad’a da takaici.
Yassir ji yake kamar ya tashi ya rufe Ya
shjub da duka, tabbas ya san shi ne ya zo ya had’a masa munafurci a wajen Daddy.
Saboda Allah d’an k’aramin company d’in nasa da aka bud’e masa shine yake so a kwace ko yaya?
it’s obvious shi ne (a baiyyane ya ke Yashjub
ɗ
in ne) favorite d’in Daddy ya san
Daddy ya fi son shi, shi kuma ya san Daddy ya tsane sa.
Already Yashjub ya fi shi a fannin kud’i da
ɗ
aukaka da komai ma tou amma dan me yasa zai saka masa ido ya sakawa d’an business d’insa ido sannan ya sake hura wutar k’iyayyar sa a zuciyar Daddy!!!
“A
nya kuwa jininsu d’aya da Yashjub?”
Yassir ya yiwa kansa tambayar yana jin yadda zuciyarsa take sake tafarfasa.
A hankali Mommy ta ce
‘’InshaaaAllah Daddy za a gyara, kuma za mu kiyaye, ba za mu baka kunya ba.’’
Dai-dai nan Ummi ta shigo, har za ta koma
dan tana ganinsu ta fahimci meeting suke yi amma sai Daddy ya ce mata “ta zo ta zauna ba komai..”
Cikin nutsuwa ta gaida Daddy daganan ta juya ta gaida Mommy suka amsa ba yabo ba fallasa Yashjub kuma ya gaida ita…
sai da Daddy ya zabgawa Yassir harara t
ukunna ya ce ‘’Ina wuni’’
Ba tare da ya kalle ta ba…
da
kulawa ta amsa kafin ta kalli Daddy cikin sunkuyar da kai ta ce’’
Ka yi hak’uri Daddy akan abunda ya faru
ɗ
azu,
In shaaAllah hakan ba zai sake faruwa ba’’
A hankali Daddy wanda duk ya ji jikinshi y
a yi sanyi ya ce ‘’ba komai’’.
Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin
ta fara magana
‘’Alhaji Bashir, ya san Munirat 3 years back, sun had’u a instagram ne, tun kafin ya ganta in person (ido da ido) suke tare.
tunda ya zo suka had’u kuwa sai ya fara maganar aur
e.
Cikin watanni biyu, komai ya k’ullu, aka saka ranar auren su wata uku.
A ranar hennah party d’inta ne muka ji labarin ashe matarsa psyco ce (tana da ta
ɓ
in hankali), ita ta kashe y’arsu ta farko ma amma da
yake mahaifinta influential person (babban mu
tum) ne, sai aka rufe abun aka ce depression ne yake damun ta shi yasa take hauka…
daga baya ma aka ce ba ita ta kashe yarinyar ba.
A ranar d’aurin auren Munirat da Bashir ne matar tasa ta d’auki karamar y’ar tasu wadda ta rage ta tafi da ita Cairo, ta tu
ro masa video tana treatning d’insa (yi masa barazana) akan ‘ko dai ya fasa auren Munirat, ko kuma ta kashe wannan yarinya wadda ta gudu da ita sanann itama ta kashe kanta’.
Sai a lokacin ne muka ji labarin ashe haukar tata tana tashi ne idan Bashir d’in y
a kula wata ko kuma yayi yunk’urin k’ara aure, shiyasa shi kuma yake b’oye mata.
Ko ba komai a wannan lokacin mun fahimci yadda Bashir yake k’aunar matarsa duk da a lokacin ya ce saboda y’arsa yayi abun da yayi amman yadda matar ta hanasa dawowa bayan taf
iyar sa despite (dukda kuwa) yadda ya bar Munirat ya ci ace an fahimci yadda yake gudun b’acin ranta.
Bai tashi fad’ama wakilinsa ma ya fasa auren ba sai da ya isa airport ya tabbatar ya samu jirgi tukunna ya iya nutsuwa ya turawa wakilin sa da na Munirat
message….
Watan Munira d’aya tana rashin lafiya saboda yadda k’awayenta makwafta da kuma y’an uwa suka dinga gulmace-gulmace, gashi ko ba komai itama na san tana son
Bashir a wannan lokacin.
Tun wannan lokacin bai tashi dawowa ba sai after five months (
bayan watanni biyar) bayan ya gama theraphy d’in matarsa ya gama lallab’ata ta zauna achan Cairo d’in, sai gashi ya
dawo da niyyar auren Munirat
ba tare da sanin matar tasa ba ni kuma nace a’a Munirat ma tace a’a ta hak’ura.
Da farko lallab’a mu ya f
ara yi
da yaga dai mun dage, sai ya
fito mana da asalin fuskarsa…..
Duk da mun maidawa gidan su
duk wasu kayan lefe da na Al’ada sannan an janye batun bashi itan da akayi amma sai ya dage akan cewa ‘shi fa an riga an bashi danhaka a duk lokacin da ya ga
dama ko muna so ko bama so zai je a d’aura musu aure.!!’
A lokacin Munirat har ta yi wani saurayin ana shirin saka rana
amma sai da Bashir ya shiga ya fita ya raba ta da wannan Yaron.
Ganin yana neman takurawa rayuwar mu kuma dama na gama sabon gini na
ne
Ya sanya na d’auke Munirat muka tafi chan garin mu,
muka yi wattanni bakwai kuma da muka tashi dawowa bamu tare a gidan da ya sanmu ba.
Yayarta itama cewa ta yi sai da mijinta yayi da gaske tukunna Alhaji Bashir ya d’aga musu k’afa dan da ya neme mu y
a rasa kanta ya koma wai sai ta fito masa da fiancé(matar da zai aura)…….’’
Sai da Ummi ta sauk’e ajiyar zuciya tukunna tace ‘’
Munirat bata da niyyar cutar da Yahanasu, kuma daga ita har ni kwata kwata ba mu ta
ɓ
a kawowa a kanmu shine wanda Yahanasu za t
a aura ba, dan Allah kar abun da aka d’an samu misunderstanding sannan ya riga ya wuce ya zama silar samun matsalar mu’’.
Ahankali Daddy yace
‘‘InshaaAllah Ummi, kema kuma ki yi hak’uri ke da Munirat d’in bamu san da haka ba kuma shima Bashir ko da na y
i masa magana
ɗ
azun bai yi min wannan bayanin ba, zan samu
samu lokaci in saka su Yasmeen d’in su baku hak’uri a fahimci juna komai ya wuce inshaaAllah’’.
A hankali Mommy ma ta ce
‘’Allah yasa mu dace’’.
A tare Daddy da Yashjub da Ummi suka ce’’Ameen’
’
Daganan Ummi ta mik’e ta ce
musu ‘’sai da safen su’’.
Tana fita,Daddy shima ya mik’e ya ce’’we are done here,Allah ya bamu alheri.’’
Sai da safe su Yashjub suka yi musu suka fice, yayinda Mommy ta mik’e ta bi bayan Daddy amma tana shiga yauma kamar ku
llum ya sallame ta, haka nan ta fito hankalinta a tashe!!……
Tabbas ita kanta ta san tana da kissa amma bata jin wannan karan she can keep on hiding her pain,(za ta iya ci gaba da
ɓ
oye damuwarta,),
abubuwan sun yi mata yawa,
abunda ta raina yana k’ok’arin
fin k’arfin ta. Ga shi yanzu zargin su a kan Yashjub ya tabbata, dukda ya ce mata friend d’in shi ce amma ita bata wani yarda ba bayaga hakan ma shin a ina ake wani k’awance tsakanin mace da namiji, tunda ya gaya mata d’azu har yanzu hankalinta bai kwanta
na second d’aya ba….
‘kar dai fa ace wannan ita ce Yarinyar da zata zamto obstacle d’in (shamakin) nasu…….’
Mommy ta aiyyana hakan a ranta.
Bayan kwana d’aya,(Monday!.)
Da asubah Manubiya ta tashi, tana idar da sallah ta yi karatun Qur’ani ta idar, dag
a nan ta d’auki handout d’inta ta hau karatu bayan ta je ta d’aura ruwa.
Sai da garin ya d’an yi haske tukunna ta mik’e ta je ta d’an d’ebi ruwan ta watsa ta barwa su Jidda nasu.
Tunda Baba ya fita sallah bai dawo ba har ta gama shirin ta,
ta san kuma dal
ilin da ya hana shi dawowar! Dan haka ta hau tunani tana lissafin ‘ko dai su hak’ura da zuwa office d’in mutumin nan ko kuma su je a k’afa idan za su iya in yaso d’an kud’in motar da suka tanada sai a siyawa inna kununta su Muhsin suma su ci abinci’
dan
ta san shima Ya Musbah ba lallai a samu wani abun daga wajen sa ba.
K’arfe 7 dai-dai ta fita zuwa gidan Ammi tana addu’ar Allah yasa yau d’aya dai ta samu ko da
left over d’in jiya ne.
Kamar yadda ta yi expecting (zato) kuwa
sai da suka fafata ita da Am
mi…dan jiya basu had’u ba wai ta tafi sunan k’anwarta tun sassafe so manubiyan bata samu ta tambaye ta akan fitar da za ta yi yau ba!!
Sai da Mama ta saka Baki yau ma tukunna Ammin ta barta akan nan da k’arfe goma za ta zo.
Abincin da ta yi tunanin sam
u kuwa san bata samo ba, haka nan ta dawo hankalinta a mugun tashe dan bata san mai za su ci ba.
Da ikon Allah tana shigowa
ta tarar Ya Musbah ya zo musu da koko Jidda har tana bawa inna nata..
ba k’aramin dad’i ta ji ba kuwa dan haka ta yi wa Allah godi
ya, itama ta karb’a ta sha nata daga nan Baba ya yi musu addu’a su Jidda suka yi musu a dawo lafiya, su kuma suka fito ita da Ya Musbah kowa a d’akin yana musu fatan alkhairi.
Lokacin karfe 7:36.
A hanyar bakin k’ofa suka tarar da ya Yusuf yana tsaye yana
daddana waya sanye cikin suite.
da murmushi Ya Musbah ya k’arasa ya mik’a masa Hannu yana mai cewa
‘’Yusuf ina ta so in lek’a in yi maka murna…
Na ji Baba yana cewa ya ji Kaka mallan a masallaci yana gayawa Abokinsa ka samu aiki a banki ko?
Allah ya sanya
alkhairi’’
Ya k’arashe maganar tasa da tsananin murmushi kwance akan kyakkyawar fuskarsa.
Ko kallon sa Ya Yusuf bai yi ba ballantana ya yi tunanin zai bashi Hannu su gaisa!
A hankali Ya Musbah ya janye hannunsa kafin cikin rashin kuzari ya sake cewa “Al
lah ya sanya alkhairi.’’
Yanzun ma bai ko kalle sa ba sai wayarsaa da ya ci gaba da dannawa.
Juyawa Ya Musbah ya yi, ya kalli Manubiya wadda ta k’ule ta zo iya wuya, ya ce mata ‘’Manu,mu je’’daga nan ya sa kai ya fice daga gidan jikinsa a mugun sanyaye.
Manubiya har zata fita itama
sai kuma ta juya ta kalli Yusuf d’in dai dai shima ya d’ago yana kallon ta, a hankali k’asa-k’asa ta ce’’Jidda ce dai,ba za mu bayar ba!
dan Allah in kaga dama ka zama sarkin gaba.’’
Tana gama fad’in haka ta fice da sauri tana
mai jin takaicin yana d’an raguwa.
…..
Ƙ
arfe 7:56am
Adaidaita sahun su ta yi
parking a bakin ‘Yashjub Limited’.
Sunayen su kawai masu gadin suka tambaya, Manubiya tana fad’ar sunanta suka shiga yi musu sannu da zuwa, suka bud’e musu k’aramar k’ofa su k
uma suka shiga.
A reception suka zauna bayan sun je sun fad’i sunayen su an ce ‘su d’an jira.’
Cikin nutsuwa Ya Musbah yake kallon gurin yana adduar ‘Ina ma ace ya samu aiki a gurin, ko da masinja ne, in dai zai samu abun da zai ciyar da Inna da Baba da
y’an uwansa da kuma Baraka da d’ansa to Alhamdulilla…’
aikin gini da wanki da gugan nan da ya ke yi ba k’aramin wahala yake sha ba sannan ogannin nasa basa biyan sa sosai, ga shi kullum a gajiye ya ke!!!,
Baraka har ta fara yi masa mitar baya sauk’e mata
hakkinta na aure wanda yake a kansa saboda kullum yana zuwa gida ya ke bajewa sai barci, tsabar gajiya.
A nan kam ya san ba zai dinga yin gajiyar da yake yi a wankau ba, ga gurin ko Ina AC….
‘’Ya Musbah dan Allah ka daina kula Ya Yusuf, tunda bashi da mut
unci.’’
Muryar Manubiya ta katse masa tunani, murmushi kawai ya yi kafin ya kalle ta tukunna yace’’Manu,idan na biye masa ai sai zumuncin namu ya fi yanzu lalacewa…’’
‘’Miss Manubiya, pls follow me(taso mu je).’’
Wata baturiya cikin suite da skirt ta ce d
a su kafin ta
juya ta nufi hanyar sama.
A tare suka mik’e ita da Ya Musbah suka bi bayan matar….
a bakin lift matar ta tsaya,
sai da ta juya ta tabbatar suna bayan ta tukunna ta danna lifter ya bud’u sannan ta shige ta kallesu ta ce ’’come in,pls(ku
shigo)’’
A hankali suka shiga k’irjin Manubiya yana dukan uku-uku,dan bata tab’a shiga ba, ta dai san menene amma bata tab’a shiga ba.
4th floor dama Matar ta danna wanda shine last floor dan haka suna isa lift d’in ya tsaya k’ofar ta bud’u matar ta fice
suma suka bi ta a baya.
Sai da numfashi su ya kusan d’aukewa saboda tsananin had’uwa da kyawun wajen, ko ina glass! dan kana iya hango har chan waje har titi, ga wasu fitilu da suka haska wajen suka sanya yayi wani irin haske tarr….
Hijabin idi
ɗ
inta na
last year ne a jikinta brown colour,
a wanke tass a goge har k’asa, sai shek’i yake yi, dan tun sallar da ta saka bata sake sakawa ba!
Ya Musbah shi kuma yana sanye da jallabiya bak’a da hula fara (tashi ka fiye naci)….
kayan Jikin duk su biyun a goge su
na shek’i amma duk da haka sai suka raina kansu saboda had’uwar wajen da kyawun shi
sai ya fito da rashin kyau da tsadar kayan nasu.
Apart from wannan baturiyar da take yi musu