Showing 66001 words to 69000 words out of 150519 words
sai da ya d’an nutsu tukunna ya ji yana cewa
‘’I just want to see your face get to know u(fuskanki kawai na ke ao in kalla sannan in san wacece ke) shikenan na san inshaaAllah zan samu nutsuwa, pls ki fad’a min
komai game da ke da rayuwar ki sannan ki nuna mini fuskarki, ina so in san ki’’.
Sai da ya sake nutsuwa tukunna ya ji ta ce “Ka kwantar da hankalin ka jibi inshaaAllah za ka ganni’’
Cikin katse ta ya ce
‘’Manubiya ba ki san ya nakeji a raina game da ke
ba, ki nuna min fuskarki yanzu dan Allah.
ɗ
azu raina a b’ace yake amma da na fara tunanin ki a take na ji fushin ya fara raguwa….
na san ina ganin fuskarki b’acin ran zai b’ace gaba d’aya’’.
Ya k’arashe maganar tasa yana k’ok’arin sanya hannu da niyyar j
anye nik’abin nata.
A hankali ta ce
‘’Na ce maka fa jibi za ka ganni..‘’
sai kuma ya ga ta d’an yi shiruuu
kamar mai tunani ko sauraron wani abun kafin ta d’ago ta tsare shi da kyawawan idanuwanta tukunna ta ce
‘’Answer your phone
(Ka amsa wayarka)’’.
Da d’an mamaki ya ke kallon ta sai kuma ya yi murmushi yana shirin yi mata magana, ya farka daga baccin.
Wani wawan tsaki ya ja dan ya manta rabon sa da yayi bacci da mafarki mai d’an karan dad’i irin wannan, da sauri ya lumshe idanuwan sa ya shiga
add
u’ar Allah yasa ya samu ya koma baccin ya cigaba da mafarkin
kawai ya ji
wayarsa ta fara k’ara…
Shiruu kawai ya yi yana sauraron ringin tone d’in har ta katse.
He just wish Ina ma ace itan ce,
although mafarkin da yadda ta ce ya amsa wayar shi kuma ya fa
rka a ka fara kiran sa is a little bit wired (ya
ɗ
an yi abun al’ajabi)
Amma
Shi fa a halin yanzu a yadda yake ji ko da ace aljana ce to zai iya zama friend d’inta muddin za ta dinga ba sa wannan nutsuwa da kwanciyar hankalin da yake ji a ko da
da yaushe
in yana tunanin ta.
Yana wannan lissafin
Ya ji wani kiran ya sake shigowa
Gudun kar ta sake tsinkewa ne yasanya shi ya d’an juya ya d’auki wayar da ta ke k’ara a cikin wayoyin da ya zube a gefen gadon tun farkon shigowar sa d’akin…
business phone d’i
nsa ne shiyasa bai yi
mamakin ganin bak’uwar lamba ba.
Ahankali ya
ɗ
aga ya kara a kunnensa ya koma ya gyara kwanciyarsa ba tare da ya ce komai ba.
Tashi d’aya ya ji gabansa yayi wani irin mahaukacin fa
ɗ
uwa sakamokon jin muryarta da ya yi tana cewa
‘’
Ke ya isa haka, ba ki ga dare yayi ba, mutum Babba da matarsa kin dame sa da kira haka ki bari gobe ma sake gwadaw……’’
Tsit kuma sai ya ji ta yi shiruu..
A hankali ya d’an runtse idanunsa
yana jin k’irjinsa yana bugawa
a ransa ya ce ’’is she really the o
ne?(da gaske ita
ɗ
in ce?)
ta ya aka yi ta samu number na?,noo it can’t be (ba zai yiu ba)”
tabbas yanzu ma gizo take yi masa har a waya ga kuma mafarkin da yayi
Innalillahi wa inna ilaihirrajiun
Ya Allah na yi gamo da aljana amma wallahi bana son rabuwa d
a ita,Ya Allah ka sa ba muguwa wadda zata cutar da ni bace ba.’’..
Ya aiyyana hakan a ransa.
Yana wannan addu’ar ya ji an ce
‘’Adda Manubiya an d’auka fa, ki yi magana mana.’’…
A hankali ya lumshe idanuwansa ya rintse pillow d’in da ya d’aura akan k’irji
nsa yana mai sake tabbatarwa da kanshi
tabbas ita d’in ce…….
BULAMA ✍
️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*23*
Da kyar Manubiya ta samu ta tattaro gaba d’aya courage d’in ta (kwarin guiwarta) ta ce
‘’Assalama alaikom si
r
Good evening.
Sir Najeeb ya ce zaka bani aikin da zan dinga reporting maka duk sati, he gave me your card and ask me to call you for more information(ya bani card
ɗ
inka ya ce in kira ka za ka yi min cikakken bayani)…’’
Kitt!! Haka suka ji an katse kira
n.
Da sauri ta d’ago tana kallon su Jidda waenda suka zuba mata ido su ka yi mata k’urr,
A hankali Muhsin ya sauk’e ajiyar zuciya ya koma ya zauna daga tsugunnon da ya yi domin lek’a wayar tukunna ya ce
‘’Adda kema kin kwafsa, ya za ki yi masa mix d’in
Hausa da turanci..’’
Da sauri Jidda ta ce
‘’Eh! Nima ina tunanin Hausar da kika yi ce ta b’ata masa rai.’’
A hankali Manubiya ta ce
‘’Allah yasa ba Matar shi ce ta d’auka ba’’
Daga haka ta koma ta jingina da jikin bango..
A b’angaren Yashjub kuwa tun
da Manubiya ta fara magana
ya ji numfashinsa yana shirin d’aukewa, the fact that ‘tana yi masa magana referring to shi ka
ɗ
ai’ ne ya sanya nishad’i da annashuwa suka mamayesa sannan ga zuciyarsa wadda ya ji tana shirin tarwatsewa, tsabar uban gudun da take
yi.
Ganin Yarinya k’arama tana shirin sumar da shi ta waya ne yasanya shi yanke shawarar ya kashe wayar idan ya nutsu ya yi calming down tukunna sai ya fahimci wanne irin aiki take magana akai dan kwata kwata
kwakwalwarsa ta ƙi ta d’auki charji, kuma ya
san in ya ce zai yi mata magana a haka to tabbas za’a samu matsala.
A hankali ya runtse idanuwansa ya na maida numfashi kamar wani wanda ya yi y’ar tsere…….
Ya fi mintina goma a haka
sam ya kasa tab’uka komai….
yana nan kwance a hakan ya ji ana knockin
g k’ofar d’akin nasa…..
Sai da aka yi sau wajen uku tukunna ya ce ’’come in’’.
Ya riga ya san wacece shiyasa tana shigowa ya ce ’’Mommy kar ki damu fa, i’m fine’’.
Murmushi ta yi kafin ta k’arasa
bakin gadon ta nemi waje ta zauna sannan ta ce ’’in kai k
ana ganin ka yi girman da za ka b’oye min damuwar ka to ni har gobe ganin ka nake yi kamar yau na haifeka.
yanzu tashi in zauna sai ka kwanta in yi maka massage a goshinka na san ciwon kan zai ragu ko?’’
Bud’e idanunsa yayi ya kalle ta na y’an sakanni k
afin ya mik’e ya zauna a kan gadon sanann ya sake kallonta yace
‘’Mommy da gaske nake miki fa
I’m okay now.’’
Sai da ta d’an k’ura masa idanu na y’an sakanni kafin ta ce
‘’How? ko aljannar da na ji kana maganarta kwanaki a d’akina ce ta kwantar maka da
hankali?’’
Wani sassanyan murmushin da Yashjub ya saki a take sai da ya sanya Mommy a al’ajabi.
Ba ta san lokacin da ta ce
‘’Akwai ta kenan da gaske, a ina take? talk to me(yi min maganar), ka fad’amin, kar ka b’oye mini komai’’
This time around (wan
nan karon) dariya Yashjub ya yi kafin ya juyo ya kalle ta sosai sannan ya ce
‘’Relax! Mommy…
Idan lokacin sanin nata ya yi za ki santa amma ba yanzu ba, kuma na san tunani kike yi akan wai ko budurwata ce ko kuma ina son ta wanda sam abun ba haka yake ba,
she’s just my friend (ƙawata ce kawai) ko kuma ince za ta zamto ƙawar tawa, soon(nan ba da jimawa ba)”
Ya fad’i hakan yana komawa ya kwanta kamar yadda ta shigo ta same sa.
Ganin da yayi kawai ta yi shiruu ta fad’a duniyar tunani ne ya sanya shi cewa “oka
y!bye.
bara in d’an huta kafin in shigo anjima’’.
A hankali ta ce ’’Byee’’
ba tare da ta motsa ba.
Kamar ba zai yi magana ba
sai kuma yace
‘’Your mood?(na ga yanayinki ya sauya?)mai ya faru?’’
Ya yi mata tambayar yana kallon ta sannan ya sake mik’ewa
ya zauna.
D’an murmushi ta yi a hankali daganan ta ce
‘’Bye, sai mun had’u anjiman’’
Tana gama fad’in haka ta mik’e za ta fita, da sauri ya ce
‘’Yauwa’’
sai kuma ya mik’e ya k’arasa drawer da ya ajjiye wayoyi da atms d’in Kausar ya d’auko envelope d’i
n da ya saka komai nata a ciki ya kaiwa Mommyn ya ce ‘’ga shi”.
Dukda hakan bai ga chanji a mood d’in nata ba(yanayin nata ba), dan kawai karb’a ta yi ba tare da ta kalle sa ba ta juya ta fita.
Ya dad’e yana nazarin Mommy
daga k’arshe ya yanke wa mood d
’in nata (yanayin nata) hukuncin ‘wataƙila ta d’an ji zafin yadda ya ƙi tsayawa ta yi masa massage saboda wata friend wadda ya sani jiya-jiya already ta riga da ta kwantar masa da hankali.’
Daga haka ya janyo wayarsa ya turawa Manubiya message
kafin ya da
nna kiran Najeeb…
Yana d’auka kuwa ya kwashe da dariya.
Shiruuuuu Yashjub ya yi yana sauraron shi sai da ya yi mai isar sa tukunna ya ce “ya aka yi ne?’’
ya yi masa tambayar still yana dariya k’asa-k’asa.
‘’Iyakar plan d’in naka da idear taka kenan? wan
ne aiki to zan bata?’’
Yashjub yayi masa tambayar kai a d’aure.
Cikin dariya Najeeb ya ce
‘’Iyaka taimakon da zan iya yi maka kenan wallahi, tunda kaga ka zo mini da sharud’a, my hands are tied ta ko ina (ka
ɗ
aure ni ta koina) shiyasa na barka ka yi figu
ring out komai da kanka, cikin sauk’i.’’
Ajiyar zuciya Yash ya sauk’e kafin ya ce
‘’To ai ni aikin da zan bayar a dinga zuwa duk sati sau d’aya ne ban san shi ba’’
Yadda Najeeb ya yi wa Abbakar tak’aitaccen bayani akan aikin haka ya yi wa Yashjub, dag
anan ya d’aura da cewa “chatting nake yi da k’anwarka ka kira ni, kar ka ja min in je garin gyara maka ni kuma madam ta yi fushi, sai anjima.”
Yashjub yana shirin yin magana ya ji Najeeb ya katse kiran…
shiruu ya yi yana tunani kafin kuma ya fara wani kal
ar murmushin da ya dad’e bai yi ba….
….
Su Manubiya har sun cire rai suna shirin maidawa Siyama wayarta kawai suka ji message ya shigo..
Da farko kamar ba za su duba ba dan basu sani ba ko na siyaman ne sai kuma suka ga kamar number da suka kira ce dan hak
a suka duba.
Suna bud’ewa suka ga an turo Time da Adress d’in inda zata same shi, jibi Monday da safe inshaaAllah…
A take suka turawa Ya Musbah message d’in ta wayar Siyaman, duk da sun san gobe za su had’u, amma duk cikin su Baba ne kawai mai waya dan h
aka gara su ajjiye message d’in a wayarsa, in ya so goben sai su shirya komai, jibi su tafi tun da ya ce 8 na safe za ta je.
Suna gama tura masa Jidda ta maidawa Siyama wayarta ta dawo ta zauna ita da Muhsin suka shiga surutu da murnar aikin da Manubiya t
a samu,
tun Manubiyan bata kula su har ta d’an fara saka musu Baki a hirar tasu wadda duk suna yi ne a kan albashin Manubiyan: za su siya kayan abinci da na farko, idan an sake biyan ta kuma sai su siyawa inna da Baba kayan sakawa, sannan suka ce za su biy
awa Muhsin ya yi jarabawa ya wuce ss1 ya ci gaba da karatunsa shima….
Kusan duk a lissafin nasu ba su sako kan su ba kawai komai su iyayen su sai Muhsin wanda yake ta murnar ya ji an ce zai ci gaba da karatu..
wannan dalilin ne ya sanya hawaye suka b’alle
wa inna wadda ta farka daga bacci ba da dad’ewa ba..
da kyar ta samu ta rarrashi kanta ta yi shiru.
A haka Baba ya shigo ya same su hannunsa rik’e da bak’ar leda.
sai da suka yi masa sannu da zuwa tukunna Manubiya ta mik’e ta d’auko faranti ta na zuwa y
a mik’a mata ledar ta karb’a ta yi godiya tukunna ta bud’e….
Kunun tsamiya ne a ciki d’an sachet guda d’aya sai gurasa guda hud’u mai gishira an d’an yayyafa mata mai.
Jidda ce ta karb’a kunun tsamiyar ta je ta ta damo wa inna ta dawo Manubiya da Muhsin ku
ma suka d’auki
gurasar d’aya d’aya su ka ci bayan sun yi sun yi da Baba akan shima ya ci amma ya ƙi, ya ce musu “ya ci tasa a waje kafin ya shigo”
ba dan sun yarda ba sai dan basu son yin ja in ja da shi ne yasanya suka hak’ura suka d’auki tashi guda d’a
yar suka sake raba ta gida uku suka barwa Jidda wadda take bawa inna kunu nata su kuma suka ci nasu suka sha ruwa, daganan Manubiya ta d’auki bargon Baba da Muhsin ta yi musu shimfid’a ta ajjiye musu abun rufuwa…
dai dai nan ita kuma Jidda ta gama bawa Inn
a kunu, dan haka ta zauna zaman cin tata gurasar Manubiya kuma ta je ta d’an d’umamo ruwa ta dawo ta kaiwa Baba rabi toilet rabin kuma ta zo ta shiga gogewa Inna jiki.
Cikin sanyin jiki Baba ya mik’e ya je ya gasa k’afar sa wadda ta addabe sa kwana biyun
nan, daganan ya yi uzuri, brush da alwalla ya fito ya zo ya yi addua ya kwanta yana tunanin mai gobe kuma zata k’unsa….
babbar damuwar sa itace ‘abinci’ dan wannan ma a bashi aka basa da kyar, dan haka ya san ba lalle wanda ya
basa bashin ya kuma basa gob
e ba…..
Yana jin su (Yaran) suka shiga one by one kowa ya yi brush ya yi alwallah ya fito daga nan Manubiya ta kunna musu mosquito coils Jidda ta yi musu shimfida suka nema waje suka kwanta..
Har bacci ya kwashe su gaba d’aya amma shi ya gagara kawai dai y
a lumshe idanuwansa ne kamar mai bacci ….
•••••••
Ummi bata cewa Munirat komai ba har suka k’arasa d’akin Ummin.
Sai da suka shiga ta rufe k’ofar d’akin nata tukunna ta juyo Munirat tana shirin yin magana Ummin ta kwashe ta da wani kalar gigitaccen mari, c
ikin fushi ta ce ’’na baki minti biyar ki yi mini cikekken bayani. Munirat kina haukane?
Yahansu fa?
Ba wai ina zargin ki da yi mata snatching (kwace) ba amman kamar yadda Daddy ya fad’a da Mutumin ya fara yi miki zancen banza da sai ki yi fitar ki ki bar
shi, a iya d’azun yana ganin ki kawai ya ce miki zai aureki ko kuwa ya abun ya ke?’’
Cikin kuka Munirat ta ce
‘’Ummi alhaji Bashir ne fa kuma tare mun hanya yayi, amma wallahi Ina ganin sa na so in juya amma sai ya tare min hanya…’’
Shiruuu
Ummin ta yi
ta kasa cewa komai kafin chan ta cewa Munirat d’in ‘’je ki yi alwallah ki yi sallah ki kwanta,’’
Daga haka ta juya ta fice daga d’akin.
Ko da Ummin ta fita a parlournta ta zauna ta yi tagumi, ta jima sosai a haka kafin daga baya ta mik’e ta nufi side d’
in Daddy..
A d’akin Munirat ta ci y’an biscuits da apple
ɗ
in da ta tarar a fridge ta sha ruwa bayan ta yi sallah ta kwanta tun tana tsammanin ganin Ummi har bacci ya kwashe ta tana sheshek’a tana ajiyar zuciya.
…
Kamar yadda Yashjub ya fad’a,sai da ya h
uta ya tabbatar Daddy ma ya gama duk wasu aiyyuka da uzururrukan sa tukunna ya nufi cikin gidan, bai tarar da kowa ba dan gidan yayi shiruu, dare yayi kowa yana d’akin sa.
yana tafe ya turawa Mommy massage daganan ya nufi sama side d’in Daddy yana k’arasaw
a k’ofar parlourn ya d’an yi knocking tukunna ya shiga da sallama.
Yana shiga ya hango sa ya rafka tagumi ya zurfafa a tunani, sai da ya je kusa da shi sosai ya zauna a kan 1 seater d’in da take facing 3 seater da yake zaune akai ya ce
‘’Daddy’’
Tukunna
ya yi firgigit ya d’ago yana kallon sa
BULAMA ✍
️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*24*
Numfashi Daddy ya fesar kafin ya gyara zama ya bawa Yashjub dukkannin attention d’insa tukunna ya ce’’kana da buk’atar wani abu ne?’’
G
anin Yashjub d’in ya yi shiru ya gagara cewa komai ne ya sanya Daddy d’in sake cewa’’ina jin ka, akwai matsala ne?’’
A hankali Yashjub ya sunkuyar da kanshi yana tunani, sai da Daddyn ya sake basa dukkannin hankalinsa ya ce’’Talk,mana.’’
tukunna Yash d’i
n ya sauk’e ajiyar zuciya cikin nutsuwa da sanin kan zance ya fara magana
‘’Daddy..
Allah ya huci zuciyarka akan abun da zan fad’a maka yanzu,
Idan ya yi maka zafi ka yafe min”
sai da ya d’an yi shiru tukunna ya ce
‘’Daddy abun da aka yi wa Ummi a gida
n nan yau bai kamata ba, sannan su Yasira a gaban ka suka dinga yi mata rashin kunya amma aka kasa tsawatar musu, bayan ba ma laifin Yarinyar nata bane ba, tunda ba ita ta ce tana son Mutumin ba…
kar so da tausayin Yahanasu ya rufe mana ido