Showing 78001 words to 81000 words out of 150519 words
rayu, to a kan wanne dalili ne za ki tilastamana yanzu akan dole sai mun kula y’arki?.
Sannan last warning gareki ‘kar ki sake cewa za ki tara mu da ni da siters
ɗ
ina ki yi mana fad’a ko kuma ki bamu wani useless labarinki
wanda mun riga mun san shi dan an fad’a mana tun d’azu da safe…
and one more thing(sannan abu
ɗ
aya da nake so in sake jaddada miki)….
Idan kina son magana da Yasira ko Kausar to kin san hanyar inda d’akunan su yake, kar ki sake cewa za ki aikeni tunda ni
ba y’ar aiken ki bace ba…”
Tana gama fad’in haka ta wuce ta bar wajen fuuu kamar za ta tashi sama….
Tana wucewa Yusra itama ta mik’e ta bi bayanta haka ma Yadira.
A hankali Yasmeen ta mik’e
ta ce ’’Mommy good night, muna da wani surgery d’in gobe da sass
afe…
Baabaa Larai a yi min faten doya irin na jiya pls’’
Ta fad’a hakan tana langab’ar da Kai.
Murmushi Baaba Larai ta yi, daga nan ta ce ‘’inshaaAllah y’ar albarka, Allah ya taimaka.
sai da safe.’’
‘’Na gode Baaba Larai d’inmu’’
Yasmeen ta fad’i hakan
da murmushi akan fuskarta kafin itama ta wuce abunta ba tare da ta kalli inda Ummi take nan a daskare ba.
A hankali Yahanasu ta lumshe idanuwanta a ranta ta ce’’inama Bashir bai shigo cikin rayuwarta ba,”
Tunda gashi dai yanzu ba auren ta zai yi ba amman
kuma ya zamto silar da zai tarwatsa auren Daddy da Ummi wanda take addu’ar a samu ya d’auree har abada.
Da gudu Munirat ta mik’e ta bar wajen ta na hawaye….
wannan shine duka biyu!!! ga cin mutunci gashi kuma Ummi ta hanata yin magana.
A hankali Mommy t
ace ‘’Sai da safen ku’’
Daga nan ta mik’e ta bar wajen.
Ummi za ta bar wajen kenan
Yahanasu ta mik’e ta matso ta kamo Hannunta tace “Ummi dan Allah ki yi hak’uri, ko da ace kowa bai fahimce ki ba to ni na fahimce ki, tun a jiya Yash yayi min bayanin koma
i ta waya, nima kuma a jiyan duk na yi wa Yasira bayani kuma na ji suna maganar Yassira ta tura a group d’in su dan haka kinga sun san labarin kenan kawai dai gaskiyar ce ba sa so kuma suke k’ok’arin dannewa tunda dama abunda ya farun ba shine asalin dalil
in su na kyarar ku ba.
kawai ki yi hak’uri Ummi, ki daina k’ok’arin had’a kansu da Munirat dan ba zai tab’a had’uwa ba…
ki zuba musu ido kawai.
ki kwantar da hankalinki Munirat is not alone (ba za ta ji ka
ɗ
aici) a cikin gidan nan ba, tunda ina nan, ba za t
a yi zaman kad’aici ba, inshaaAllah…’’
Cikin takaici Ummi ta ce
‘’Na gode Yahanasu, amma ko ba komai ya zama dole in ji takaicin yadda Mommy ta ke yin burus akan lamarin nan…
ki duba ki ga yadda nake bata girmanta amma ita in Yaran nan za su wanka min ma
ri ba za ta tab’a hanawa ba.’’
Cikin katseta Baaba Larai ta ce
‘’Ummi, sai dai fa ki yi hak’uri, duk cikin Yaran nan ki gaya min waye kika ga yana jin maganar Mommy a cikin su? Tun daga kan Yassira har izuwa kan Yadira
Yahanasu kada’i ke yi mata biyayya am
man ragowar duk binsu kawai take yi.
Dalilin da kika ga yasanya bata saka muku Baki
Shine
Bata so ta shiga fad’an kuma su disgata a gaban ki, dan itama ba jin maganarta akeyi a cikin gidan nan ba!!
hatta shi kanshi Daddy d’in ba bi ta kanta yake yi ba
kuma na san kin san me ke faruwa a tsakaninsu shi da ita tunda ta ce min rannan a gabanki ya koreta…….
Ba wai Ina gaya miki hakan dan ki raina ta ba, A’a ina gaya miki ne dan ki daina jin haushin ta, ki yi mata uzuri ki barta da abunda ya ke damunta….
Dan
haka idan zan baki shawara ki d’auka to ki daina k’ok’arin tilastawa Yaran nan akan dole sai sun bi ki dan hakan da kike yi kamar kina sake rura wutar rikici a tsakaninki da su ne.
Sannan wani abunda na lura kamar baki sani ba
shine
ko dambatuwa kuka yi
da ke da Yaran nan to fa idan ubansu ya zo bayansu zai bi, dan babu abunda ya tsana a duniyar nan kamar ka tab’a masa ƴaƴa…
Dan haka tunda har kika ga uwarsu ma ba ta tilasta musu to kema ki koma gefe ki zubawa kowa ido.’’
Tana gama fad’ar haka ta
wuce, t
a nufi sama wajen Mommy..
..
A d’akinta ta sameta tanata faman safa da marwa…
tana ganin shigowarta ta yi maza ta k’arasa wajen ta, a d’an rikice ta ce “yauwa Larai, ke nake ta jira, ya ake ciki?
Ajiyar zuciya Baaba Larai ta sauk’e kafin ta ce
‘’Na barta
a k’asa, ita da Yahanasu’’
Cikin katseta Mommy ta ce ‘’Ba maganarta nake yi miki ba, maganar Yashjub nake yi..na gaya miki tun jiya ai..maganar ki gaskiya ce, da Bakinsa ya tabbatar min amman har yanzu ban ji kin ce komai ba.’’
Murmushi Baaba Larai ta yi
kafin ta nemi waje ta zauna sannan ta ce ‘’Tunda kika ji na yid shiru akwai dalili….
yanzu
Yahanasu ce naga Bakinta ya fara bud’uwa, kina ganin ba matsala kuwa?.
Na lura da ita, bata shakkar kowa kwana biyun nan, yanzu haka a gabana ta gama aibanta su Ka
usar sannan k’iri-k’iri Ina kallon idanunta tana kallon nawa amma ta bi bayan Ummi ta bata gaskiya…
shiyasa na ke ganin gara a yi wani abun tun kafin ta je ta b’allo ruwa.”
Ajiyar zuciya Mommy ta sauk’e kafin ta ce
‘’Larai bar batun Yahanasu tukunna, Ina
tunanin shurun nata da rashin fitar da take yi ne ya shafe ta har a ta b’angaren aure fa, ko ke ba ki yi wannan lissafin ba?
Ba ki fahimci komai ba?.
Saboda har ga Allah na fara jin tsoron zalintar Yahanasu da nake yi dayawa har haka saboda nawa gain d’in
(ribar)’’
Shiruu Baaba Larai ta yi kafin ta ce ’’gaskiya ni kam ba zan bi ta taki ba Khadija, saboda idan Bakin Yahanasu ya bud’u ba ke kadaice a wahala ba, bari ki ji in gaya miki yau tun safe da ta bar gidan nan bata dawo ba sai magrib.’’
Cikin rashin
jinn dad’i Mommy ta nemi guri ta zauna itama a kusa da ita kafin a hankali ta ce ‘’shikenan Larai, ki yi abunda kike ganin ya dace.’’
Murmushi Baaba Larai ta yi
kafin ta gyara zama ta ce
‘’Ita kuma Ummi………..’’
BULAMA ✍
️
0903 441 32
52
*MANNUBIYA*
*27*
Sai da Ummi ta yi da gaske tukunna Munirat ta fasa zuwa gidan yayarta…da fad’a da rarrashi duk ta ha
ɗ
a tukunna ta samu ta d’an kwantar mata da hankali, dukda kuwa ita ma hankalin nata ba a kwance ya ke ba…
abun tausay
i haka itama Munirat d’in ta shiga kwantarwa da mahaifiyar tata hankali.
sun jima suna magana kafin Ummi ta mik’e ta nufi wajen Daddy jiki ba kwari.
A bakin k’ofar shiga parlourn
suka had’u da Yasmin, tana shiga Yasmeen d’in kuma tana fitowa..ko kallon
ta bata yi ba
Itama Ummin bata kulata ba.
Da sallama ta shiga, ba ta same shi a parlournsa ba sai a chan cikin d’akinsa a zaune a kan gado,
Ya yi shiruu alamun tunani yake yi.
A kusa da shi ta je ta nemi guri ta zauna kafin a hankali ta ce
‘’Barka d
a dawowa Daddy, ya
meeting d’in?’’.
Ba tare da ya kalle ta ba ya ce
‘’Alhamdulillah’’
Daga nan ya mik’e ya fad’a toilet.
Har ya fito tana nan a zaune,
ta yi zurfi a tunani..
Sai da ya gama shirin bacci tukunna ta ce
‘’Bara in kawo maka abinci’’
Ta fad
’i hakan tana shirin mik’ewa.
Cikin dakatar da ita yace ‘’don’t bother, a k’oshe na ke.’’
Cikin kwantar da murya tace
‘’Daddy, ka d’an ci ko kad’an ne m….’’
‘’Wai Saddik’a ni k’aramin Yaro ne?d’ura zaki yi min ko me?
Na ce miki a k’oshe nake amma kin
bi kin ishe ni…
daga meeting na dawo Ina buk’atar hutu shin baki da fahimta ne????”
A hankali ta ce ‘’ka yi hak’uri,
Allah ya huci zuciyarka’’…
Har zai kwanta sai kuma ya ce
‘’Ki koma parlour ko kuma ki zab’i wani bedroom d’in ki kwana,
ban ce ki fita a
side d’ina ba…kawai ki nemi wani bedroom d’in a parlourn..’’
Sai da ya sake cewa’’bakya ji na ne?’’
Tukunna da kyar Ummi ta ce ‘’to Daddy, sai da safe.’’
Washegari da sassafe ta tashi, tunda ta yi sallar asuba ba ta koma ba, dama tun a daren jiyan ta f
itar da abincin da ya ce ba zai ci ba ta saka a fridge dan a lokacin hatta gwaggo ta riga ta tafi side d’insu na masu aiki.
Had’add’en breakfast mai rai da lafiya yau ma Ummi ta shiga had’awa Daddy…
tana cikin yi su gwaggo suka shigo dan haka ta shiga aka
yi har na gaba d’aya gidan tare da ita.
K’arfe bakwai da kwata suka kammala, dan haka ta d’auki na Daddy ta nufi sama da shi cike da sassarfa.
A bakin k’ofar d’akinshi ta same sa yana gyara zaman necktie d’insa, tun kafin ta gaida shi ya ce ’’koma da abi
ncinki yanzu ma, na k’oshi’’
A hankali ta nufe sa da tray d’in a hannunta da niyyar idan ta je ta durk’usa ta bashi hak’uri, amma tana zuwa kusa da shi tun kafin ta durk’usa ya yi wani irin fatali da abincin wanda ta sanadiyyar hakan gaba d’aya parlourn,
kayan jikinsa da kayan jikinta suka b’aci….
Cikin fushi ya juya ya koma d’aki ya bar ta nan a tsaye cikin tsananin tashin hankali da mamaki, bata san lokacin da wasu hawaye masu zafi suka shiga tsilalo mata ba.
Da kyar ta samu ta goge wajen tana yi tana
kuka haka nan ta je ta chanja kayan jikinta tukunna ta dawo ta tattare kwanukan ta nufi k’asa.
A hanyar stairs ta tsaya ta goge hawayenta tukunna ta k’arasa sauk’a ta nufi kitchen.
A kitchen d’in ta tarar da Yasira Kausar Yasmeen da Ya’isha,
da alamun ko
wa fita zata yi kuma masu aikin ba su gama jerawa a kan dining d’in ba shine suka zo suke d’iba anan d’in…
a cikin su ba wanda ya ce mata ci kan ki haka ta wuce ta ajjiye kwanukan ta shiga wanke Hannunta…
Cikin rashin mutunci ta ji Ya’isha na cewa
‘’Dad’
ina da talaka bai iya samun guri ba, a yi employing d’inka amma ka nemi zak’ewa, na rantse da Allah Asabe duk ranar da kuka sake yin letti ba ku jera mana abinci har kuka ja muka makara ba to
ko wacce shegiya sai ta koma inda ta fito, sai ku dinga yin ab
u kamar ku kuka haifi Mutum…..
Mtswwwww’’
Ta k’arashe maganar tata tana mai jan wani uban tsaki,
daganan ta sa Kai ta fice.
Wata dariya Yasmeen ta yi,
Irin wadda ta yi wa Ummi jiya ciki-ciki.
Dariya sosai Kausar ita kuma ta yi kafin tace
‘’Kin ga Mala
ma, ki saki Baki ki yi dariyarki dan babu uban wanda ya Isa ya hanaki.’’
Ahankali amma yadda ta tabbatar Ummin za ta ji Yasira ta ce
‘’Tana jin tsoron a shiga tsakanin ta da Daddy ne’’
Cikin dariya k’asa-k’asa ta rainin hankali
Kausar tace ‘’au,haka ne
fa’’
Daganan duk suka d’auka abincin da suka zuzzuba suka fita suka nufi dining table banda Yasmeen wadda ta tsaya ha
ɗ
a tea a cikin kitchen d’in.
Har Ummi ta fita sai kuma ta tuna akwai flask d’in da ferfesun ciki bai gama zubewa ba dan haka ta juya da n
iyyar komawa ta cewa gwaggwo su juye mai kyau ne…
a k’ofar kitchen d’in suka yi kici
ɓ
us da Yasmeen wadda ta yi kamar irin ta tare k’ofar nan ne..ita ba ta matsawa Ummin ta wuce ba sannan ita bata fito ba..
da mamaki Ummi take kallon yarinyar tana so ta ga
iya gudun ruwanta.
A hankali Yasmeen wadda ta hango Daddy yana sauk’owa daga bene tace “na ga kin shigo da kwanuka a hargitse
kuma idonki kamar kin yi kuka, gaya min gaskiya dukan ki Daddy ya yi?’’..
Dama tun
ɗ
azu da kyar Ummi take danne kanta dan ba
ta so ta kula Yaran amman duk maganganun da suka yi a kitchen d’in ta san da ita suke ga kuma takaici da tashin hankalin da Daddy ya tsoma ta a ciki tun jiya shiyasa duk yadda ta so hana kanta ta kasa dan haka ta d’aga Hannu ta zabgawa Yasmeen wani irin gi
gitaccen mari,
dai-dai nan kuma Daddy ya k’arasa saukk’owa cikin parlourn.
Wani irin kuka Yasmeen ta saka ta durk’ushe a wajen ta dafe kunnnenta tana ihun ‘’Wayyo Allah kunnena’’
Dai-dai nan Daddy ya k’araso wajen a gigice, da k’arfi ya ce
‘’Innalillah
i wa inna ilaihirrajiun’’
sakamokon ganin jini yana zubowa ta kunnen Yasmeen.
Sai a lokacin Ummi ta ji ashe wai ‘Yasmeen tana da abu a cikin kunnenta wanda ya ke zuk’o mata magana sakamokon rashin aiki da kunnuwan nata basa yi sosai.’
kuma ba kunya ba ts
oron Allah a take Kausar har da rantsuwa ta yi tsalle ta dire wai “ai sun gayawa Ummin jiya da ta yi yunƙurin marin Yasmeen d’in amma shine yau sai da ta mare ta, shikenan yanzu in ba da kyar ba ta danna mata abun chan ciki ta lalata mata kunne gaba d’aya.
”
Cikin tsananin gigita Ummi ta ce
‘’Kausar ki ji tsoron Allah, yaushe….
Wata rikitacciyar tsawa da Daddy ya buga mata ce ta sanya ta kasa ci gaba da magana…cikin tsananin fushi ya ce ’’ki b’ace min a wajen nan tun kafin na illataki .’’
A hankali sanna
n k’afafuwanta suna wani irin karkarwa ta samu da kyar ta juya ta kama hanyar sama zuciyarta tana wani irin tafarfasa.
Yayinda su kuma suka d’unguma kai Yasmeen asibiti, gaba d’ayan su.
••••••
Sai yau Manubiya ta d’auki wayarta a jikin charji daga gidan A
mmi,
dan sai da ta bar wayar ta yi awannin da aka rubuta ana buk’atar ta yi a jikin charjin. Layinta na jiya da suka yi wa register ta saka, bayan kamar 30 minutes ta d’auki wayar ta dudduba daganan ta d’auko katin Yashjub cikin nutsuwa ta juye numbersa t
ukunna ta tura masa sak’o kamar
haka
’’Good morning Sir(ina kwana sir), yau na kunna wayar tawa daga charji, my mail is empty as for today(yau, mail
ɗ
in nawa ba komai a ciki)..idan sun turo I’ll report everything to you on Friday (zan ha
ɗ
a in sanar maka k
omai ranar juma’a)..
InshaaAllah
Thankyou(na gode)...
Manubiya Musa..’’
Fitowar Yashjub daga wanka kenan dan lokacin 7 dai-dai,itama Ammi ce ta ce mata ta tabbata ta je da wuri fiye da yadda take zuwa kullum, wai tana da bak’in da za su zo daga Abuja so
akwai aiki sosai..
Yana fitowa ya ga wayarsa ta yi k’ara dan haka ya k’arasa ya d’auka ya shiga duba message d’in, dama ya saka a ransa maybe ita d’in ce dan tun jiya yake ta jiran ya ga kira ko messge d’inta.
Murmushi kawai ya yi, ya sake karanta sak’on
ya kuma maimaitawa ya sake maimaitawa kafin ya ajjiye wayar da kyar yana mai sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya…
yanzu mene ne abun yi, saboda duk taurin kansa da kauce-kaucen sa ya riga ya sak’k’o, ya fahimci yana mahaukacin son Manubiya..duk yadda ya
yi ta denying yana kaucewa, a iya jiya kad’ai ya tabbatar
k’aunarta yake yi, k’auna ba ta wasa ba, amma kuma ta ya zai fad’a mata abunda ko Najeeb yana tunanin anya zai iya fad’awa kuwa….
numfashi ya fesar ya nemi guri ya zauna a ransa yace ‘’Yashjub a y
adda kake son Manubiya, b’oye b’oye ba naka bane ba,’’
domin
shi kansa ya san yana da buk’atar wani abun ya faru soon…a fahimci juna a yi aure tun kafin sonta ya zautar da shi sannan ga wannan cousin d’in nata da ya ga take-taken kamar shima sonta yake yi
, kasancewar sa na gida ne ya sanya Yashjub yake ganin gara ya d’auke Manubiya tun wuri tun kafin iyayenta su yi abunda zai kai sa lahira ta hanyar aura mata Abbakar.
A part from all these (bayaga duk waennan abubuwan ma) a yanda yake jin Manubiya a zuciya
rsa da ransa to tabbas
ba ya jin zai iya ci gaba da rayuwa daga nan zuwa watanni hud’u ko uku gaba ba tare da ya mallake ta a matsayin matarsa ba…..
Da wannan tunanin ya shirya ya fice office, ko Daddy bai tsaya jira ba dan yana buk’atar ya yi tunani sos
ai sannan ya san ta inda zai fara Kafin Daddyn ya zo su fara aiki,kuma yana da buk’atar lek’awa d’ayan company d’in nasa duk a yau.
……
Manubiya tana ajjiye wayar ta juya kenan su ka yi ido biyu da Maamaa,
da sauri ta sunkuyar da kanta k’asa kafin tace’’Ma
amaa Ina kwana.’’
sai kuma ta fara k’ok’arin fita daga kitchen d’in.
Murmushi Mama ta yi sannan ta ce’’ni kam Manubiya tsoro na kikeyi ne?
naga kwata kwata kin k’i ki yarda ki saki