Showing 99001 words to 102000 words out of 150519 words
ta d’ebi abinci ta nufi sama, wasu ma har an sa
ka su a fridge haka ta d’auka ta yi warming a micro wave..
tana hawa saman ta nufi hanyar side d’in su kenan ta ji Yassir ya ce ’’Munirat’’
A zuciye ta juyo amma sai ya yi sauri ya rufe mata Baki da tafin hannunsa, ya karb’e plate d’in nata ya ajjiye a
kan centre table na parlourn saman kafin ya ja ta zuwa d’akinsa….
ko da suka shiga sai da ya sa ta yi masa alk’awarin ba za ta yi ihu ba tukunna ya cikata, ya cika mata Baki ya matsa gefe.
Duk masifar da Munirat take ji, tashi d’aya ta b’ace
ɓ
at!!
Sakam
akon abunda ta gani a gabanta……
Sosai ya yi decorating d’akin da candles, gashi an rubuta “I love you Munirat” da ballon’s, gwanin ban sha’awa…
cikin sanyin jiki ya ce mata ‘’dama surprise d’in da na ke so na nuna miki kenan…
Ina so in gabatar miki da ka
ina a matsayin masoyi kuma me neman aurenki, amma kuma na rasa a ina zan yi dan na san ba za ki yarda ki bi ni mu je wani wajen ba, kuma ba zai yiu na yi miki a cikin gidan ba…”
Daga nan ya durƙusa a gabanta a hankali, sannan ya yi mata sahihin proposal.
Duk yadda Munirat ta so ta d’an ja aji kasawa ta yi dan tashi d’aya ta ce masa ‘yes’ sai kuma ta juya da sauri ta fita,
dan duk sai ta ji wata kunyar shi ta lullub’eta.
Ko abinci nata bata tsaya ta d’auka ta ci ba dan tashi d’aya ta ji ta a ƙoshe…
Tana fita Yassir ya saki wani kalar murmushi a ransa ya ce
‘’Allah sarki! zuciyar Mace bata da wuyar samu.
very innocent soul(mai tsarkakakkiyar Zuciya)’’.
‘’Na san kin san ta fita ko?
so za ki iya fitowa,
Sannan nan gaba dan Allah ki daina motsi da k’
ofa
wajen yin lek’en, dan kad’an ya rage ba ki yi drawing attention d’in ta towards inda kike
ɓ
oye ba
(ba ki ja hankalinta zuwaga inda ki ke
ɓ
oye ba).’’
Yassir ya fad’i hakan ba
tare da ya juya ya kalli k’ofar bathroom d’in ba, kafin a hankali ya durk’usa
ya fara d’auke candles d’in yana kashewa.
Dai-dai nan Kausar wadda ta fito daga toilet d’in ta k’araso kusa da shi itama ta sunkuya ta fara tayashi, suna kwashewa suna kashewa a tare.
….
Ganin ya ƙi kulata ne ya sanya ta ce
‘‘Haba dear!
wai har yanzu f
ushin ne?’’
Mik’ewa ya yi fuskarsa babu alamun wasa ya ce
‘’Kausar!it’s either you talk (ko dai ki faiyyace min komai) ko kuma in yi fatali da wannan plan
ɗ
in naki gaba
ɗ
aya wallahi!.
kin san dai yin hakan ba k’aramin aiki na bane ba ko?’’
Murmushi ta
yi kafin ta ce
‘’ka tabbata?
Na fa san halinka,
Kuma take-taken ka ma akan Yarinyar na gani shiyasa na zo maka da wannan tayin, domin mu samu mu jefi tsuntsu biyu da dutse d’aya.
Are you sure(ka tabbata) za ka iya yin fatali da mission d’in nan (manufar
nan tamu) ba tare da ka samu abunda kake so ba?’’.
Cikin fushi ya mik’ar da ita tukunna ya ce ’’and you are not even jealous!(Kuma ba ma kya kishi!!)…
tabbas yanzu na sake tabbatarwa
raina min hankali kike son ki yi..kin ga Kausar i’m not your pet (ni b
a abun wasanki bane ba)
sannan ni ba k’aramin Yaro baneba…..
Kwanakin baya da suka shu
ɗ
e kin nuna kin tsaneni, yanzu
kuma a cikin kwana biyu kawai kin dawomin!.
Idan kin san wasa za ki yi min da hankali saboda ki samu ki cimma wata manufa taki to walla
hi tun wuri ki janye!!
Idan kuma ba ki janye ba to this time around (wannan karon) zan ba ki mamaki!!
bar ganin wai Ina son ki wallahi I can be your worst nightmare(wallahi zan iya zame miki babban masifarki)…
Ba wanchan Yassir d’in da kika sani baneba h
ar yanzu,
Yanzu na chanja.
Sannan
kin ce akwai reason d’in (dalilin) da ya sa kukayi calling off auren mu ke da Mommy(da ya sa kuka janyo aka fasa aurenmu, ke da Mommy)…..
Inaaso in ji dalilin da komai, inaso ki fad’amin komai, inaso in san menene shirin
ku dan ba zan yi participating a game d’in (ba zan bada gudummawa a wasan) da ban san inda aka dosa ba…
Ba zai yiu ki dinga yi min abu ta bai bai ba, akwai abubuwa da dama da na ke so ki fahimtar dani
If not (idan kuma ba haka ba to)
kawai inaga gara abar
……’’
Rungumeshi tayi wanda hakan ya sanya ya kasa ci gaba da magana..
sun d’an jima a haka
tukunna ta d’ago ta na kallonsa ta ce
‘’Yassir ba zan iya gaya maka dalilin mu ni da Mommy ba, ka yi haƙuri.
Na fad’a maka mun fasa ne saboda Kai da kuma farinc
ikinka duk abunda mukayi mun yi shi ne saboda Kai!
Idan ni ba ka yarda da ni ba!
na san ka san dai Mommy ba za ta tab’a nemo bak’in cikinka da hannnunta ba dai ko?
You just need to trust us on this one
(Naka shine kawai ka yarda da mu a wannan lamarin)
Saboda ba zan iya fad’a maka ba.
Abu na biyu kuma kai nake so Yassir, Ina sonka tun farko..
fushin da ka ga Ina yi da Kai kwanakin baya kawai Ina yi ne saboda ina so ka bani space (iska) a samu a fasa auren mu da gaske.
Ba za ka tab’a samun abunda kake
so ba tare da ni ba!
Dan haka ka taimakemu, ko kuma in ce ka taimakeni in samu in
fitar da Ummi daga cikin gidan nan!
In gyara tsakanin Daddy da Mommy!
ta yadda za mu samu mu yi maka gatan da muke son yi maka, daga nan in ya so sai a yi maganar aurenmu.
k
a fahimceni?’’.
Kanshi tsaye ya girgiza mata Kai kafin ya matsa daga Jikinta da inda take sannan ya juya mata baya tukunna ya ce ’’ban fahimceki ba Kausar!
not untill you tell me (har sai kin gaya mini)
ko da ace d’an single hint(ƙaramar alama) ne.
Ba z
an tab’a fahimtarki ba idan ba gaya min kika yi ba kuma in ban fahimceki ba
ba zan taimake ki ba.”
Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin ta ce
“shikenan Yassir, amma kar ka bari Mommy ta san ka sani dan Allah’’
‘’I promise
(Na yi alƙawari)
kawai yace,
yana ma
i juyowa ya kafeta da idanuwa.
Sai da ta sauk’e numfashi tukunna ta fara magana
‘’Ka san tun lokacin da aka haifi su Yahanasu,
Daddy ya bawa Yashjub rabin dukiyar shi ko?’’.
‘’Continue
(Ki ci gaba)”
Yassir yace yana mai gyara tsayuwarshi
A hankali Kau
sar ta ci gaba da cewa
“Da wannan rabin dukiyar da kuma taimakon ƙwazo da aiki tuƙurun da Yashjub ya ke da su ne suka zamto silar da a yanzu haka hatta Daddy bai isa ya kamo k’afarsa a kud’i ba!.
Bayan estates d’in da muka sani, Yashjub yanada hannun jari
a companies daban-daban da kuma gidanjen man fetur!…
Ita kanta Mommy bata san da hakan ba sai last two years ago (shekaru biyu baya da suka wuce) ne ta fahimci d’umbin arzik’in Yashjub.
Daddy ne kawai ya san komai nasa amma abunda zai baka mamaki shekara
r nan da ta wuce da ya tashi raba wasiyyar masu Hannun jari a companynsa(shi Daddyn)…
Kamar haka ya raba;
share d’in Yashjub (kason yashjub)a company d’in Daddy
50%ne
(Kaso hamsin a cikin
ɗ
ari)
Na Daddyn 18%
(Sha takwas a cikin
ɗ
ari)
Su Yasira su 6 kow
acce tanada 1%
masu hannun jari
dama nasu already (tuntuni) 5%
ne
Mommy bata da komai ita dama
Mama 20%
naka kai kuma 1%.”
Da k’arfi Yassir ya ce ‘’watt??’’
‘’Kwarai da gaske’’
Kausar ta ce
kafin ta d’aura da cewa
‘‘Mommy ta b’oye maka
ne saboda ta san idan ka sani ba za ka ji dad’i ba.
Yassir
Idan ta ji na fad’a maka ba za ta min da sauk’i ba, ko su Yasmeen basu san da maganar nan ba!
Yasira ce kawai ta sani
Dan haka kar ka fad’awa kowa dan Allah
sannan ina so ka yi min alƙawarin ba
zaka yi komai ba.
A hankali ya ce’’I promise (na yi alƙawari)
Cigaba Ina jin ki .’’
Cikin son fahimtar da shi Kausar ta
ɗ
aura da cewa
‘’Ka san a yanayin tsarin Daddy
Idam Mutum ya yi graduating (kammala karatu) ya fara aiki ma to tsame hannunsa ya ke
yi a kansa
kuma tun ba yau ba ya riga ya ce ‘a cikin ku idan kuka riga kuka yi aure to
tsakanin sa da ku sai dai ku
dinga kawowa gida, dan ya gama baku kwandalarsa,’……
Tuni, ya riga ya gama gina Yashjub ya kafa shi!
Wat about you(kai
Kuma fa)?.
Yassi
r idan ka kuskura ka yi aure a yanzu shikenan ka tashi da 1 percent da kuma company d’inka wanda bana jin a shekara ma yana kawo maka sama da million biyu,
Shin
ta yaya za ka iya ciyar da iyalinka?
kuma na san idan baka kawowa gida kamar yadda Daddy ya t
sara ba
to kuwa ka had’u da tijarar sa kenan.
Ita Mommy abunda take so shine
‘ta samu ta san yadda zata yi ta janyo hankalin Daddy a samu ya k’ara maka wani abun, ko da a cikin share d’in Mama da nasa dana Yashjub ne! A samu ayi maka karo karo kaima ka y
i sama..’
To kuma an d’an fara samun nasara sai Hannun agogon gaba
ɗ
aya ya koma baya tun lokacin da wannan matar Saddik’a ta shigo rayuwar Daddy, shikenan komai ya tab’arb’are!
We need to get her out
(Dole mu fitar da ita)!
mu gyara tsakanin Mommy da Dad
dy, a k’ara mata share ka tsaya da k’afafunka kaima tukunna ayi maganar aure Yassir.
A yanzu balance d’inka na duk shekara wanda Daddy yace yana tarawa kowa nasa
Idan aka tashi baka na shekara ukun da suka wuce ba a baku ba
dai dai fa kake kai da su Yas
ira!
A matsayinka na
ɗ
a Namiji!….
Daddy ya tartara komai ya damk’awa Yashjub wanda ba shi da wata kyakkyawar alaƙa da
ɗ
aya daga cikin mu
hatta Mommy…
Iyaka Daddyn ne kawai ya san cikinsa kuma ya ke
ɗ
an shiri da shi…
Ka ga kuwa duk ranar da aka ce ya yi au
re to komai hannun matarsa zai koma!
Mu sai dai mu zama y’an kallo a gefe..
Daddy can take care of himself
(Daddy zai iya kula da kanshi)
daga nan har tsufan sa yanada kud’in da zai temaki kansa da shi da Mommy!
Kai fa?
kai da su Yasira….
Allah ya rufa
asiri
Idan ba ayi wani abun ba sai dai mu zama a gefe y’an kallo, abun tausayi!
Gaba d’aya arzik’in gidan nan ya koma hannun shi shi kad’ai daga shi sai matarsa
tunda tun yanzu dama ba kulamu yake yi ba……
Amman idan kuka zamto equal (
ɗ
aya) da kai da
shi, ko ma ace ka fi shi samu to
tanan ne kad’ai komai zai tafi normal!
tunda munsan kuma muna da tabbacin kai za ka kula da su Yasira da ita kanta
Mommyn sannan ni za ka aura ba wata stranger (bare) ba dan haka arzik’inmu yana nan a wajen mu.
Ba abund
a ya fi d’agawa Mommy hankali irin yadda
ya yi maka duka ranar nan!
Kuma ka kasa ramawa saboda baka da power, shiyasa take so ku zama
ɗ
aya a fannin arziƙi da samu,
bata so wani ya taka wani….
kuma tana jin tsoron kar a yi ta zalintar ka ka zo ka ce za
ka rama ta hanyar da bata kamata ba…
Wannan itace gaskiyar magana
Yassir, so muke yi mu taimake ka
amma sai ka bamu hadi’in kai tukunna za mu iya.
sannan dan Allah kar ka bari Mommy ta san ka sani dan bata so kowa ya ji!
Saboda ta san ba lalle a fahimc
eta ba, dan za’a ga kamar ta fi sonka ne akan Yashjub’’.”
Rungumeta Yassir ya yi, kafin
a hankali ya ce
‘’Sorry Kausar, na d’auki alhakinki kwanaki, na yi tunanin gudu na kike yi, ki yi hak’uri, na fahimci komai yanzu.’’
Shiruu ya d’an yi kafin ya ce
‘’Amma ta ya Munirat za ta taimaka wajen case d’in (lamarin)Ummi?
da har kike ta k’ok’arin ha
ɗ
a ni da ita, sannan shin ba kya kishina??’’.
Murmushi ta yi sannan ta ce
“Yassir Ina kishin ka,
amma bana so in zama kamar Ina
controlling d’in ka(juya ka),
s
annan na san duk rintsi ni d’in dai ni ce a cikin zuciyarka.
na riga na san halinka ba wai ban saniba..
na san ko na yi haukar rabaka da ita a yanzu ba zan yi nasara ba!
Inaso mu zama d’aya ni da kai..
Shiyasa
akan ka je ka yi abu a bayan idona gara ka y
i a gaban idona,
daga haka ni kuma in ci moriyar halinda ake cikin….dan
Wannan yarinyar itace lagon Uwarta!
Muddin ka kafa mata k’ahon zuk’a
lokacin da uwartata zata hak’ura ta bar gidan nan tare da ita ma ba za a sani ba…
Ba ka ji a labarin Yahanasu b
a?
saboda senator ta bar garin nan ita da y’ar sai bayan
watanni tukunna suka dawo….
Tuni yanzu ita da Daddy sai dai kallo
We make sure of that
(Mun tabbatar da hakan)
fitar ta a gidan ne kawai matsala,
Wanda godiyar hakan ta tabbata ga Hajiya wadda t
a hana Daddy sakin ta
in dai har ba ita ta tafi da kanta ba.
Ita ma kuma na lura idan ba sakin nata aka yi ba to ba zata tafi cikin sauƙi ba!
Shiyasa
Muke so mu sakata ta bar gidan da k’afarta daga nan
Daddy ya rakata da takardarta.’’
Wani zazzafan
numfashi Yassir ya fesar kafin a hankali ya ce ’’Na fahimci komai yanzu”
daganan ya sake k’ank’ame ta
A ranshi yace
“Na gode Kausar..
ke da Mommy
ku saka Daddy ya k’ara min share(kasona)
Ni kuma zan shiga cikin dukiyar Yashjub..
In kwashi rabi
In tarw
atsa rabi
Idan kuma abun ya zo da tangard’a in dagargaza komai, kowa ma ya rasa!.
Bayan na gama da shi kuma
zan dawo gareki,
sai dai kawai ki ji ana d’aura mana aure!
Saboda
duk da bayanin nan da ki
ka yi min
I still don’t trust you
(ban gama yarda da
ke ba)
Dan
Inda ace da gaske kina sona to
da zan ga ko da d’an guntun kishina ne a cikin idanunki da aiyyukanki,.
Allah dai kawai yasa ba yaudarata
kike yi ba!
sannan ba ki da shirin shiga hanyata ki taremin abunda nake son cimmawa…dan cikin duk Mutane
ke kad’ai ce banaso ki shiga hanyata saboda
a shirye nake in bi ta kan duk wanda ya yi k’ok’arin tare min hanyar cimma abunda nake so in cimma….’’
Tunda Kausar take a rayuwarta bata tab’a jin shakkar Yassir irin na yau ba, dan kamar yadda ya fad’a mata
tabbas ‘wannan ba shi ne Yassir d’in da ta sani a baya ba’!
Idanuwanshi sun tabbatar mata da hakan,
Hakan ya sanya ta d’an tsorata da shi dan ta san idan ya fahimci gaskiyar lamari to akwai matsala, dan ita har ga Allah baya gabanta!
asalin gaskiya ma ita
so take ta yi getting rid of him (ta kawar da shi a hanyarta) cikin sauk’i, shiyasa ta zo suka shirya….
Da gaske, akwai shiri maganganun da ta gaya masa ba wai babu ba! kuma duk gaskiya ne, da batun arziƙin yash da batun yadda Daddy ya kasafta kason comp
any
ɗ
insa duk gaskiya ne, amma ko su Mommyn kawai biye su take yi saboda ita a cikin zuciyarta bata da mu Yassir ya ji dad’i ko kar ya ji ba dan ba shine a gabanta ba…
ita kwata kwata babu shi a cikin tsarin ta na asalin gaskiya ma…
…shirinsu ita da su Yas
sira shine
su fitar da Ummi.
…shirinsu ita da Mommy da baba larai kuma
Shine
su saka a bawa Yassir kaso mai tsoka sannan
hatta Yash suna so ya janyo shi ya saka shi a cikin company d’in shi.
…Ita kuma shirinta shine ta yi wa
Yassir wayo, gudun kar ya
je ya yi mata wani shirmen…
ta samu ya bata lokaci da iska
ta samu ta shiga jikin Yash shi kuma ta kwak’uma masa Munirat
daganan sai dai kawai ya ga ana d’aura mata aure da Yash.
Amma yanzu kam dole ta chanja taku!
Saboda Ta san Yassir tun suna Yara ida
n zuciyarsa ta motsa babu abunda ba zai iya aikatawa ba! Dan haka ya zame mata dole ta yi betraying (ci amanar) Baba larai da Mommy dan ba za ta tab’a bari
Yash ya ja Yassir a jikinsa saboda
a yadda Yassir yake a zuciyen nan tsaf zai iya cutar da Yash ko
dukiyarsa.
Kuma dole ta yi sauri ta ko wachche hanya ta auri