Showing 120001 words to 123000 words out of 150519 words

Chapter 41 - Mannubiya Complete

Musbah ya nuna ya ce musu yana ciki…

kawai suka afka ciki.

Shi kuma Ya Musbahn ya tsaya a wajen Baba da ya Nafi’u wanda bai dad’e da fitowa daga wajen Abbakar

ɗ

in ba, yake sanar musu

‘’ su Yashjub sun riga sun biya ko

mai’’

Baba yana shirin yin magana suka jiyo maman Abbakar ta kurma wani irin ihu….

Da sauri su Ya Musbah suka nufi inda suke suna addu’ar Allah dai yasa ba wani abun ne ya samu Abbakar d’in bayan fitowar su ba.

A durk’ushe a bakin gadon suka hangeta tana

wani irin masifaffen kuka.

Kafin daga baya ta (maman Abbakar) mik’e ta nufi Manubiya gadan-gadan, tana zuwa ta shak’o ta ta mik’ar da ita tsaye tukunna ta cikata, cikin fushi da kuka ta ce ‘’ai duk ke ce kika janyo komai!

munafuka! muguwa! kawai, haka kur

um kin maidamin Yaro kamar wani boyi-boyin ki…’’

‘’Haba mama, baki yarda da

k’addara bane?’’

Ya Nafi’u yayi mata tambayar cikin rashin jin dad’i.

Cikin fushi ta ce ’’ai dama na san ba za ku ga laifinta ba, to wallahi ku jirani a kotu dan ba zan yarda

ba sai mun yi shari’a da ku.

Amman kafin nan inaso in ja miki kunne!….

Manubiya in dai har kin haifu cikin Musa da Amina tou kar in sake ganin ki a kusa da d’a na.

Kalli cikin azabar da kika jefa sa da ke da y’an uwanki da iyayenki…masifa ce ku wallahi!

!!

shiyasa duk wanda ya rab’e ku sai ya shafa, na yi k’ok’arin nunawa Abbakar ba so d’aya ba ba sau biyu ba amman dayake kin riga kin shanyemin Yaro kalli sai da kika kusan kai shi lahira…’’

Kukan da ya kufce mata ne ya sanya ta d’an dakata, kafin ta sak

e d’agowa a zuciye ta ce ’’na gaya miki yanzu zan sake maimaitawa ‘in dai kin haifu cikin tsinannun iyayen k…’’

Nufar matar Ya Musbah yayi da niyyar kai mata duka amman sai maman Baraka ta shiga tsakiya ta rik’e sa, zafin zuciyar da ta ciwo sa ne ya sany

a cikin rashin sani ya yi cilli da ita, ya sake yin kan maman Abbakar

ɗ

in…

Ganin yana shirin yin b’arna ne yasa ya Nafi’u ya taresa ya ce

‘’Musbahu ka yi haƙuri ka kyaleta ba dan itaba, ka duba fa Abbakar shi ne ya kira su Yashjub, ka rabu da ita, ta ci

albarcin d’anta.’’

Daga haka ya juya ya ce mata

‘’mu za mu wuce yanzu.

Ga Abbakar nan, zan dawo in duba shi inshaaAllah zuwa anjima…muna buk’atar mu yi mishi godiya.

An biya duk wasu charges,

abinci kawai zaki dinga basa,

Allah ya basa lafiya.’’

Daga h

aka ya cewa su Manubiya “su wuce su tafi’’.

Sai da kuwa yayi da gske tukunna shi da Jidda suka samu suka janye Manu dan ta tsaya kawai tana kallon maman Abbakar ne, so take yi ta maida mata da martani amman kuma darajar d’anta ya sanya ta kasa yin magana.

Aikuwa har suka fice maman Abbakar ba ta yi shiru ba…babu kalar zagin da batayi musu ba…

Maman Baraka itama tana tsomo Baki

A cewarta ‘’sirikinta ya hankad’eta, ta fad’i kuma ko

kallon inda take bai yi ba

kamar ba y’a ta d’auka ta basa ba!!!!

‘Saboda

shi

ɗ

in d’an marasa tarbiyya ne…shiyasa bai san darajar ta ba’.”

Hakanan Baba ya tsawatar musu yace ‘’kar wanda yace uffan, su rabu dasu’’

dan haka suka tartara yanasu yanasu suka fice bayan ya Musbah ya je ya karb’i magungunan Baba.

K’arfe shida dai-dai

suka bar harabar asibitin suka nufi gida.

A gida suka fara tsayawa

suka ajjiye Baba, tukunna Baban ya ce musu “su duka su je su d’auko inna, kar su damu ba komai zai iya zama shi kad’ai’’.

Da ‘’to’’ suka amsa shi, daga haka suka nufi gidan Ya Musbah gab

a d’ayansu domin su je su d’auko Innar. ce ’’dalla ni cikan….’’

*MANNUBIYA*

*41*

Suna fita Baba ya saki hawayen da yake ta k’ok’arin dannewa…

Dama baya so ya yi kuka a gaban su gudun kar ya karya musu guiwa ya d’aga musu hankali..shiyasa

yace su tafi gaba d’ayansu.

Da ace yana da yadda zai yi to da ba zai tab’a aurar da su Jidda yanzu ba,

ya so ƴaƴansa su yi karatu, yaso ace Jidda ta gama ko da level one ne tukunna, amma yanzu kam sai dai ya bita da addu’a da fatan alkhairi tare da rok’on

Allah ubangiji ‘ya had’a Manubiya har ma da Jiddan da surukai na gari, ya sa su so

su’

Dan kasancewar ya san mahaifin Yusuf ba shi zai sa ya k’i yiwa y’ar sa wannan addu’ar ba!

yana rok’on Allah ya sa su jata a jiki bayan auren, Manubiya kuma Allah ya bat

a na gari, a samu kowacce ta zauna lafiya a gidan ta, dan tabbas abunda su maman Baraka sukayi musu yau a asibiti ya tab’a shi sosai, ya ji zafin abun.

A k’ofar gidajen nasu biyu motar Ya Nafi’u ta yi parking, dan haka suka fara firfitowa…..

Ya Musbah n

e ya fara shiga cikin gidan nasa, su kuma suna biye da shi a baya.

A k’arshen soro kafin ya k’arasa shigewa cikin gidan sukaga ya ja ya tsaya chak! Ya ƙi yayi gaba sannan yak’i yayi baya.

K’arasawa kusa da shi ya Nafi’u yayi yana mai cewa

‘’Ya dai? kar

ka…’’

A take maganarsa ta tsaya chak sakamakon hango Inna da shima yayi a yashe a tsakar gidan.

Da farko tunanin su basu ya yi

’watak’ila ko ta yi k’ok’arin tashi ne sai Allah ya bata iko,

shine da ta fito kuma sai ta fad’i a wajen’…

amman kuma yadda suka

ga an shimfid’a mata zani sannan aka d’aura kanta akan pillow ne ya basu tabbacin wannan aikin Baraka ne.

Cikin d’aga muryar Ya Nafi’u ya hau kwala kiran ‘’Aisha! Aisha!!’’

Sai kuma ya juya zai fita dai-dai suka yi kicib’is da Aishar

dan tana jin tsayuw

ar motar tasa a k’ofar gidan ta d’auko kular da ta gama juye abinci a ciki ta janyo hannun y’arta suka yo gidan.

Cikin fushi ya ce ’’ya akayi kika barta kika fita? ina Muhsin??’’

Inda-inda ta fara yi, tana shirin yin magana ta ga su Manubiya sun yi cikin

gidan da gudu, wanda yadda ya Nafi’u ya d’an gota suka wuce ne ya bata damar hango Innar itama dan haka ta yi ciki da sauri tana salati.

A take

Jidda da Manubiya suka fashe da kuka saboda yadda suka ji jikin Innar ya d’au zafi sosai! hatta kayan jikinta

ya d’au zafi! ga ranar la’asar da ta kusan fad’uwa ta haske mata fuska sosai gashi babu damar motsawa…….

Dishi-dishi ya Musbah ya fara gani tsabar tsananin b’acin rai da tashin hankali…da kyar ya samu ya iya cewa

‘’Baraka!!’’

Da d’an k’arfi, dan jikins

a wani irin karkarwa yake yi, hatta muryar tasa rawa takeyi.

Tun lokacin da suka shigo ta jiyo su…..dan ta gama watsa ruwa a jikinta kenan sakamokon zafin da akeyi

ta ji tsayuwar motar ya Nafi’u.

Dan haka ta d’auro zaninta, ta yafo mayafinta ta rik’o k

ayanta a Hannu ta fito fuskarta a had’e tamau!.



Tana fitowa Ya Musbah ya k’arasa inda take ya tsaya..so

ya ke yayi magana amman sam sai ya gagara, in banda karkarwa babu abunda jikinsa yake yi, dan haka kawai sai ya kafeta da idanu, ya shiga karanto add

u’o’i a chan k’asan ransa yana mai neman tsari daga shaid’an saboda a yadda yake jin zuciyarsa a halin da ake ciki ya san muddin ya ce zai

ɗ

auki mataki ko ya yi wani abun to ya san wallahi kashe Baraka zai yi!

sai ya kaita har lahira.

Tunda Baraka take a

rayuwarta bata tab’a ganin Ya Musbah a irin wannan yanayin ba, babu abunda ya fi tsoratata irin yadda taga idanuwansa sun yi jajawur hatta farar fuskarsa ta yi jaa!

gashi jikinsa sai wani irin karkarwa yake yi…

Shiyasa gaba d’aya duk sai ta ji tsoro ya lu

llub’eta, abunda bata tab’a tunanin za ta ji ba kenan dan ko a mafarki bata tab’a kawowa akwai ranar da zata zo ace wai’ta ji tsoro ko shakkar Ya Musbah a rayuwar ta ba’.

A lokacin da suke soyayya

soyayyarshi kawai ta sani, da suka yi aure kuma..hak’uri j

uriya da lallashin sa kawai ta sani. Shiyasa a yanzu da ta ga asalin fushinsa abun sai ya bata tsoro matuk’a.

Sai da ta d’an yi k’asa da kanta tukunna ta ce

‘’feshi na yi a d’akin, shine na fito da ita waje…..’’

Basu ga k’arasowar Ya Nafi’u ba, sai sa

uk’ar gigitaccen marin da ya d’auke Baraka da shi kawai suga gani.

Da sauri ta d’ago ta kallesa sai kuma ta kasa cewa komai kafin hawaye sharr ya wanke mata fuska, tama kasa maganar.

Dakyar da mugun kyar Ya Nafi’u ya yi k’ok’ari ya danne zuciyar da take

tunzura sa akan ya rufe Baraka da duka, yana wani irin huci ya

juya ya kalli Ya Musbah

Ya ce

‘’Yi hak’uri Musbahu’’

Daga haka ya wuce ya fice daga cikin gidan da sauri, dan ya san in ya cigaba da tsayuwa to tabbas sai an samu matsala.

Yana fita Baraka

ta juya tana kallon Ya Musbah wanda yake nan tsaye ya kafeta da idanuwa…

A ranta tana mamakin yadda yana gani Nafi’u ya d’aga hannu ya zabga mata mari amman bai tab’uka uwar komai ba, sannan ba shi da alamar yin komai a kan hakan har yanzun, dan haka ta bu

d’e Baki zatayi magana kenan shi kuma ya riga ta ta hanyar cewa “ki tafi na sake ki! saki biyu’’

Dede nan Manubiya wadda suka gama kai inna cikin d’aki ta fito ta yo kan Barakar da niyyar ko dai ta illatata ko kuma su illata juna.

Da sauri Aisha wadda da

ma ta lura da abunda Manubiyan take shirin yi ta taho da gudu ta rik’e ta.

Sai yanzu Baraka ta samu ta goge hawayen da suke zubo mata babu k’ak’k’autawa tukunna da kyar ta ce

‘’Cika ta, cikata ta dakeni tunda ita mahaukaciya ce, nace muku

Feshi na yi am

man hakan bai ishe ku ba, uwar taku gwal ce?’’

Cikin fushi Aisha ta ce

‘’Mahaukaciya! Jahila! Dak’ik’iya!

Idan baki saniba to yau ki sani Baraka

‘uwa ta fi gwal’.

Da bata haife shi ba to da baki same shi ba, dak’ik’iya kawai.

Ya Musbah ya ce ya sakeki,

dan haka za ki iya tafiya.

ki tartara kayanki ki koma gida a sake yi miki tarbiyya wataƙil in kin gyaru ya dawo dake, dan tabbas ko ni ba zan bada goyon bayan

aci gaba da zama da ke da wannan halin da wannan zuciyar taki ba.’’

Tana gama fad’in haka ta juy

a ita da Jidda suka ja Manubiya da kyar suka shige d’aki dukkan su Manubiya tana kuka sosai kamar ranta zai fita! dan ji takeyi idan bata daki Baraka ba yau tou sai ta mutu!.

Ita kanta Aisha ta san

tabbas in ta tsaya tsaf za su kwashi y’an kallo ita da Ba

raka kuma a ganinta in bata kwantar da husuma ba to bai kamata ta iza wutar ba, dan haka ta za

ɓ

i su zauna a

ɗ

aki sannan ta duk’ufa tausar Manubiya.

Duk bakin Baraka yau kasa cewa ko yin komai ta yi

daga k’arshe kawai sai ta juya

Fuuuuuu ta wuce d’akinta….

Ya Musbah ma bai ci gaba da zama a gidan ba!

Baraka

tana wucewa d’aki ya lek’a ya cewa su Manu “kar wanda ya kulata a cikin su,su barta da duniya’’

daga haka ya juya ya fita.

Baraka tana shiga d’aki ta fashe da kuka marar sauti mai

tsananin cin rai!

Bata tab’a

tunani ba bata tab’a kawowa a ranta Ya Musbah zai iya sakinta ba!!

“to me ya faru, ya akayi har ya iya sakinta! Yanzu ya za ta yi kenan???”

Ta yiwa kanta tambayar ba tare da ta san wa zai bata amsar ba.

Ta jima tana kuka tana tunani kafin ta

share hawayenta a ranta ta shiga aiyyana

“Tabbas sai ta nunawa Musbahu kuskurensa wallahi!

sai ta jaa shi a k’asa.Kallifa kalar cin mutuncin da suka taru sukayi mata,inaa!bazaiyiu ba wallahi da sake dole ta sake shiri zai ga ikon Allah, bama shi ka

ɗ

ai ba

gaba d’ayan su sai ta nuna musu wacece Baraka’’.

Da farko da ta yanke ne akan babu inda zataje, sai kuma ta bawa kanta shawarar ta je ta samu su mamanta itama, a yadda su Ya Musbah suka hayayyak’o sukayi mata wannan aika aikar

tabbas bai kamata ta yanke

shawara ita kad’ai ba….

Tana wannan tunanin ta had’a kayanta kaf, ko d’an kunne bata bari ba a ganinta in tayi haka Ya Musbah zai ji tsoro ya zo biko da wuri.

Su Manubiya suna d’aki sun zagaye inna suna yi mata fiffita sukaji fitowarta tana ta jidar kay

a.

Babu wanda ya ce mata ci kanki a cikinsu,haka suna

jinta ta dinga kwasar kayanta

tana fitarwa one by one

har ta gama……

Ya Musbah yana fita direct wajen Baba ya nufa, dan ya gama rayawa a ransa

‘Idan ma za su maida Inna gida tou sai dare, dan so ya

ke yi ya nunawa Baraka iyakar ta! Ta yadda tana ji tana gani sai dai ita ta fita ta barwa Inna gidan Wallahi’.

A hanya ya had’u da Muhsin da mai sunan baba sun dawo daga siyo madara, dan haka suka wuce wajen Baban da su…

Dama bayaso Baraka ta tafi akan i

don me sunan Baba gudun kar yayi ta kuka ya ce sai ya bita.

Sun d’an jima a wajen Baba bayan ya ce mishi

‘’Sunje sun tarar Aisha tana bawa innar abinci ne shine aka tsaya ta gama tukunna a kawo ta’’

Sai da suka kuma d’aukar lokaci tukunna ya bar Muhsin

anan, shi kuma ya kama Hannun me sunan Baba suka nufi gidan nasa…

bai yi tunanin tarar da Baraka har zuwa wannan lokacin a gidan ba amma yana karya kwana ya tarar da ita da adaidaita sahun ta har uku tanata loda kayayyakinta ita da masu napep d’in a ciki

.

Ko iskar da ta d’ebo ta bai yarda ya kalla ba, ya sake rik’e hannun Yaron ya zo zai shige cikin gidan…suna zuwa da

Yaron ya gane ashe uwarsa ce tare da masu adaidaita sahun ai kuwa nan ya hau ihun sai ya bi ta.

Tana gani ya fara tsalle ana jan shi ya

na tirjewa ta dawo ta kama kunnesa ta ja tukunna tace

“in na sake jin sunana a bakinka sai na ci uban ubanka! shegen Yaro kawai sai kace dashi na zo’’

daga haka ta juya zata wuce

ta ji Ya Musbah ya ce ’’Babana yi

hak’uri, mu wuce mu shiga gida,

yawo a

titi bai kamace ka ba’’

Ai kuwa cikin fushi Baraka ta juyo

‘’Ai sai ka bari in gidan naka ne sai ka yi tink’aho da shi, talaka mara matsugunni kawai,

gara ni idan na tafi yawo a titin ba’a gidan haya zan k’are ba!

kai kuwa nan da y’an kwanaki za a zo a

yi waje da kai dama darajata yasa mai gidan yake d’aga maka k’afa yanzu kuwa na san ba zai barka ka cigaba da zama daga kai sai uwarka b……”

Da sauri ya d’auke me sunan baba, ya wuce ciki ya banko k’ofar dan bai shirya biyewa Baraka a k’ofar gida ba…

Ta ji

ma kuwa tana ta tijara ita kad’ai sai da masu mashin d’in suka ce mata “in bata shirya tafiya ba, zasu sauk’e mata kayanta su yi gaba’’

tukunna ta shiga ta zauna a take kuma sai ta fashe da kuka.

To dai Baraka tun kan aje koina sai da ta ji dama bata fito

daga gidan mijin nata ba saboda d’ayan mai mashin d’in bai rik’e mata amana ba…dukda kuwa tafiyar da sukayi bata wuce ta mintuna biyar a tsakani ba

amma

da yayi wura wura ya ga babu ido a kansa

chan ya chanza hanya.

Sai da ta Isa k’ofar gidansu tukunna

ta lura babu napep d’aya.

••••••••

Tun lokacin da Yashjub ya bar office Daddy ya k’ule, ganin la’asar har ta gota bai kira kuma bai zo ba ne ya sanya shi ya kira Najeeb a fusace ya bashi sa’ko amman gashi har bayan Magrib Yashjub d’in bai iso ba.

Yassi

ra ce ta guntsawa su Mommy abunda Yashjub d’in yayi yau a office, gashi kuma har yanzu bai dawo ba..hakan kuwa ba k’aramin sake d’aga musu hankali yayi ba dan tashi

d’aya suka yanke cewa

‘’wannan yarinyar da suke zargi ce ta kirasa’’

Saboda Yasirar ta ce

musu ko bayan da aka tashi daga office sai da suka biya d’ayan company d’in Yash d’in ita da Daddy amma akace musu yau throughout bai je chan ba.

Ta tambayi Racheal kuma, ta ce mata ‘’batun estates d’insa komai stable(dai-dai)’’

dan haka matslar ba anan t

ake ba kenan.

Shiyasa suke da tabbacin wannan yarinyar ce kenan…tabbas kuwa zama bai kamasuba dan Indai har matsalarta zata sanya ya mik’e tsulum ya fice ana tsakiyar meeting sannan ya ƙi d’aga wayar kowa har yanzu saboda tsabar yadda ya bata mahimmanci, t

o hakan ya nuna da akwai babban bound (abu) a tsakanin sa da ita wanda ya zame musu dole su tarwatsa shi tun wuri su yakiceta daga cikin rayuwarsa, tun kafin ya k’ak’abo musu k’adangaren bakin tulu!.

Hakanan gidan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login