Showing 126001 words to 129000 words out of 150519 words

Chapter 43 - Mannubiya Complete

ji daga

bakin Yasira da wanda ta fahimta yanzu a take gaskiya ne to kuwa tanada babbar matsala a gabanta!

A take k’irjinta ya shiga dukan uku uku, ta shiga add’ua a ranta akan ‘’Allah dai ya sa bata riga ta makara ba’’

A take kwakwalwarta ta fara lissafawa tana h

aska mata yadda abubuwanta da shirye-shiryenta na sama da shekaru za su zagwanye

a gaban idanunta, muddin bata tashi ta tsaya ta yi da gaske ba!.

A chan k’asan ranta ta ce

‘’Wacce irin shuumar Yarinyace wannan? Da zata shigo mana bagatatan haka ta tarwat

sa min duk wasu taka tsantsan d’ina’’.

Tsabar rud’ani da rikici Mommy bata san lokacin da a fili a hankali kamar me mumbling ta fara cewa “ba zai yiu ba, ba zai yiu duk wasu sadaukarwar da na yi su tafi a banza ba….’’

Da sauri Baaba Larai ta matso ta rung

ume ta, a cikin kunnenta ta ce mata ’’ana dai kallon ki, ki zo mu je sama tukunna, sai mu yi magana’’

Jinjina Kai Mommy ta yi kamar ta fahimta sai kuma ta d’ago ta kalli Baba Larai ta ce ’’kikace Mace ce a rayuwarsa ko? kin tabbatar d….’’

‘’Innalillahi!

!! Na ce ki zo mu je sama ko?!!’’

Baaba Larai d’in ta fad’a mata hakan da d’an zafi.

Sai a sannan tukunna Mommy ta samu ta

ɗ

an dawo cikin haiyyacinta.

Ba tare da ta kalli kowa ba,

ta juya ta wuce sama jiki ba lakka..

Baaba Larai na bin ta a baya.

Anan

suka bar Yahanasu wadda ta bisu da ido kawai a tsaye. “hmmm’’ kawai ta ce, kafin ta juya ta nufi d’akinta,

ba tare da ta kalli su Yassira ba.

Ummi ma bayan Mommy ta bi

dan gaba d’aya duk sai ta ji tausayinta ya lullub’e ta..

A gaskiya Yashjub bai kyaut

a ba,

taya za ka dinga yi wa uwar da ta haifeka irin hakan?…..

Da wannan tunanin ta haye sama ta bi bayan Mommy da Baaba Larai dan tana so ta d’an taya Baaba Laran tausar Mommyn.

Achan parlour k’asa kuwa, wata hirar su Yassira suka shiga yi gaba d’ayans

u suna raha suna dariya….Yayinda Munirat ke tsaye a gefe tana mamakin yadda basu damu da damuwar mahaifiyar tasu ba, suka hau hira haka. sai da tafiya tayi tafiya tukunna ta fahimci ashe don ita da ummi suka kafa hirar dan babu komai a cikinta sai habaice

habaice, tun suna habaici har suka fara sako sunayen su suna zagi suna dariyar rashin mutunci dukkansu banda Kausar wadda tun d’’azu ta yi shiruu.

Nazartar ta (kausar

ɗ

in) kawai shi kuma Yassir yakeyi shiyasa ya ƙi tashi a wajen.

Munirat ce ta katse masa

tunani ta hanyar nufar sama da wani irin sauri dan ita sai yanzun ne ma ta yi tunanin ‘to me ma ya tsayar da ita a wajen ne tun fako?’

Wani irin wawan tsaki Yassir ya jaa, dan bai riga ya gama fahimtar Kausar ba amma kuma dole ya tashi ya bi bayan Muni

rat.

Cikin had’e fuska ya mik’e ya bi bayanta a ransa yana aiyyana ‘’gaskiya shi fa yana gama samun abunda yake nema a wajen ta to zai yi fatali da plan d’in Kausar…

baya son damuwa, bayajin zai iya ci gaba da jurar yarinyar nan muddin ya samu buk’atarsa

ta biya.’’

yana tafe yana mita a cikin ransa fuskar nan tamau haka ya haye saman….

A hankali Kausar itama ta mik’e ta nufi sama jiki ba lakka.

*MANNUBIYA*

*43*

Sai da su Mommy suka kusan shiga d’akinta tukunna suka lura da Ummi a bay

ansu…

Mommy ji ta yi kamar ta zurma uban ihu, dan a halinda take ciki bata buk’atar ganin kowa da yin magana da kowa in ba Baaba Larai ba….ayanzu da ya kamata ace sun keb’ance daga ita sai Baaba Larai shine wannan matar zata kama ta wani biyo su.

Da kyar

kuwa ta d’an sake ta bata fuska suka shige d’akin nata gaba d’ayansu.

…..

‘’Babe!Babe!!’’

Muryar Yassir ta katsewa Munirat tunani.

Da kyar ya samu ya d’an daidata fuskarshi, dai dai nan ita kuma ta juyo…

dama ta san sai ya biyota dan haka tana juyawar ta

ce ’’i’m okay,sai da safe.’’

Ruk’o hannunta ya yi, dan

haka ta juyo ranta a b’ace ta ce ‘’Yassir na ce ka daina tab’ani ko??’’

Cikata yayi yana mai d’aga hannuwansa sama kafin ya maidasu k’asa ya zura su duk biyun a cikin aljihu tukunna ya ce ’’kin tabba

tar?’’

Murmushi ta yi tukunna ta ce ’’eh, i’m okay!

Ina buk’atar hutu, sai da safe’’

Bata jira jin me zai ce ba ta shige ciki ta banko k’ofar!.

Runtse idanunshi ya yi da k’arfi sosai, ya dunk’ule hannunsa, a ransa ya raya ’’ Tabbas idan burinsa ya cika

akan yarinyar nan sai ya ci uban ta Wallahi’’.

Gyaran muryar da Kausar ta yi ne ya sanya shi bud’e idanuwan nasa, kafin ya juya ya zuba mata idanu yana kallon ta har ta k’araso inda yake, sai da ta kalli k’ofar da Munirat d’in ta banko tukunna ta kallesa

tace “Rashin kunya fa kenan”

Sai da ya furzar da iska tukunna ya matsa kusa da ita sosai ya ce “kuma dole in jure duk wannan abun nata ba, tunda kin had’ani yin soyayyar dole da ita’’

Murmushi ta yi kafin ta ce

‘’Shiyasa k’aunarka take sake nunkuwa a

cikin zuciyata…

Ammafa dukda haka Yassir ba fa ka yin yadda ya kamata da kyau, dan ni dai bana ganin wani shak’uwa a tsakaninku’’

Motse Bakinsa yayi ya d’an chuno lips d’inshi, still idonshi yana akan Kausar d’in ya ce ’’ko d’azu ma kamar za mu cinye jun

a a waya, kawai dai tanada attitude ne sannan bata iya danne

ɓ

acin ranta ba ..na lura idan ranta ya b’aci a kaina take hucewa’’

Cikin katseshi ta ce

‘’Ko kuma haushi ta ji akan baka tsaya mata agaban su Yasira ba’’

Murmushi ya yi ya d’an sunkuyar da kan

sa tukunna ya d’ago ya ce ‘’Tabbas hakan ne ma.

Kinga,

ni yanzu mu bar maganarta haka, ke mene ya ke damu ki?’’

Yayi mata tambayar yana me tsare ta da idanuwa.

Itama idon ta zuba masa na y’an dak’ik’u..tashi d’aya ta fahimcesa tsaff dan haka ta ce

‘’Mo

mmy ce take bani tausayi, ko kai baka lura da ita tun d’azu ba?

In nufin lokacin da taji labarin Yashjub ya bar office.’’

Sai da ta d’an sunkuyar da kanta ta fesar da iska tukunna ta d’ago ta ce ’’muna tunanin yana tare da wata ne, kuma ka san dama na gaya

maka yadda take ji game da batun aure a lamarin Yashjub batare da mun samu mun karb’o dukiyar gidannan daga hannunshi ba……d’azun baka lura da yadda ta yi kuka ba kafin su hawo?’’

Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin ya ce ’’yeah na lura’’

A ranshi kuma yana ji

n wani sauƙi yana zuwar masa dan shi kansa baya so zargin da yake yi akan Kausar ya tabbata, saboda bai san me zai zama ba kuma.

‘’Ya akayi?’’

Muryarta ta katse masa tunani

Murmushi ya yi tukunna ya ce ‘’ba komai’’

Ya fad’i hakan yana d’an ruk’ota.

Da

riya ta yi kafin a hankali da style da wayo ta samu ta zille tana mai cewa “ka je ka kira budurwarka ku shirya, bari in je na ji da Mommy’’ daga haka ta wuce ta barshi a nan tsaye.

Yashjub yana fitowa a wanka ko abinci bai ci ba saboda dare ya riga ya y

i….

Ya d’auki waya ya kira Manubiya…dan zuwa wannan lokacin kam ya san ta kunna tunda ya ganta da ita a asibiti.

Lokacin basu wani jima da dawowa daga wajen Siyama ba, suna zaune ita da Jiddah suna shawara…

Ta inda Jiddan ta ke cewa

Manubiyan ‘ta siya ma

sa jallabiya da Alkur'ani, ta kai masa a matsayin gift na godiyar abunda ya yi musu….’

Suna cikin lissafin ta Ina kud’in za su fito ne wayar Manubiya ta

fara k’ara, dan haka ta yi sauri ta mik’a Hannu ta d’auka daga inda take, ta yi saurin saka ta a sile

nt, gudun kar ta tashi su Inna….

Dukda ta goge numbersa tun lokacin da ta yi fushi ta bar masa office

ɗ

insa amma tana ganin number kallo d’aya ta gane shi ne!

dan haka ta zubawa screen d’in idanu tana kallo kawai, yayinda k’irjinta yake bugawa a hankali a

hankali.

Lek’awa Jidda ta yi, kafin ta d’an d’ago ta kalleta tana murmushi ta ce ’’shine ko?’’ sai kuma ta kalle ta ta ce ’’Adda Manu, anya kuwa mutuminnan…ko dai ko dai,

d’azu fa naga irin kallon da yake ta miki’’

Da sauri Manubiya ta d’ago ta kalleta,

sai kuma ta shiga girgiza mata kai alamun ‘A’a’ kamar za ta yi kuka.

Dariya Jidda ta yi ta ce ’’to ki d’auka da wuri kar ta tsinke, in yaso sai ki je ko bakin dakalin gefen k’ofa ne, kar ki tashi su Baba.

Kamar wata Yarinya haka Manu ta d’an jinjina Kai

alamun tou, sai kuma ta mik’e ta fice da sauri dan itanma tanaso ta d’auka d’in…tun d’azu take ta tunanin sa, sam bataji dad’in yadda har ya tafi bata samu ta yi masa cikakkiyar godiya ba,

kar yaga rashin kyautawarta..

Tun kafin ta Ida fita ta d’auka

ɗ

i

n tukunna

a hankali ta maida k’ofar ta rufe, ta nemi waje gefen dakalin ta zauna kafin ta ce

‘’Assalama alaikom’’

A hankali.

Sai da ya lumshe idanuwansa ya bud’e, yana jin wani sanyi yana ratsa shi tukunna ya nemi waje ya zauna a bakin gadon shima. A ha

nkali ya fesar da iska sannan ya ce

‘‘Ameen.

Wa alaiki Assalam’’

Daganan shiru ya d’an biyo baya kafin ta ce

‘’Ina wuni.’’

‘’Alhamdulillah’’ ya ce

tukunna ya sake cewa ’’ya jikin Baba?”

Itama ‘’Alhamdulillah’’

ɗ

in tace,

daga nan suka sake yin shiruu.

A b’angaren Yashjub tunanin kawai yakeyi yana fatan

Inama ace tana gefen shi a yanzu haka.

Manu kuwa ta lumshe idanunta ne kawai, ta jingina da jikin bango

dan zuwa wannan lokacin tabbas zuciyarta ta yi galaba akanta…

wani farinciki da nutsuwa kawai ta

tsinci kanta a ciki.

Bata san meyesa yake son kiran ta ba amma kuma kiran nata da yakeyi

ɗ

in da kulawar sa

gareta da kuma taimakon su dayayi ayau

tabbas sun k’ara bada gudunmawa wajen tsundumata cikin tafkin k’aunarsa.

Ta san ba lalle ta sameshi ba,

ta

san za ta sha wahala, ta san ya kamata ta yaƙi zuciyarta amman kuma ta san ta makaroo

dan ta san ko ta yi yunk’urin hana kanta ba za ta hanuba!

she can’t help it…

saboda ta riga ta kamu.

sannan abunda take ji a duk lokacin da ta yi tunanin shi ko kuma ta

ke tare da shi

‘aljannar duniya ne’ haka za ta fasalta abun, dan ya ƙunshi duk wani nisha

ɗ

i, farin ciki, annashuwa d.d.s…..

Dan haka bata son ta rasa wannan abun da ta ke jin ko da na second d’aya!

Ita ka

ɗ

ai ta san me take ji….shiyasa a take tausayin kant

a sai ya lullubeta.

‘’Na yi tunanin za ki kirani’’

Muryarsa ta katse mata tunani.

A hankali ta ce ‘’tun d’azu ban zauna ba, sai yanzu’’

‘’Yeah, nima haka…

Na san ai ko da ace kin zauna d’in ma, ba kiran nawa za ki yi ba.’’

‘’Saboda me’’

Ta yi saurin

tambayar sa.

‘’Saboda na lura kamar tsoron kulani kike yi, bakya so mu fahimci juna alaƙarmu kuma ta bunƙasa.

idan kuma na yi making move (wani yunƙurin da zai bunƙasa alaƙar tamu) sai a balbaleni da fad’a, a yi fushi a bar min office d’ina”

Wata iriyar

kunya ce ta lullub’eta, kamar tana gabansa haka ta rufe fuskarta da tafin Hannunta d’ayan,

saboda gaba d’aya kunyarsa da kunyar abunda ta yi masa jiya da safen take ji…

Sai kuma ta yi saurin dafe k’irjinta, dan sai yanzu ne kwakwalwarta ta gama mata lissa

fin abunda ya ke nufi

‘Making move (Bunƙasa alaƙa) kamar yaya?

Ta yi wa kanta tambayar ba tare da ta san wa zai bata amsa ba.

Shiruu ne ya biyo baya kafin

da mugun k’arfi kirjinta ya buga jin a hankali cikin wata kalar murya ya ce

‘’Mannubiya’’

Bata s

an lokacin da ta kashe wayar da wani irin sauri ba,

tana hak’i kamar wadda ta yi y’ar tsere!

Sai kuma ta lumshe idanuwanta, ta sake kishingi

ɗ

ewa a jikin bangon kamar mai shirin shigewa cikinsa, a lokaci guda kuma ta shiga sauk’e ajiyar zuciya a jere a jer

e.

Ta d’an d’auki lokaci a hakan, kafin ta ji kira ya sake shigowa wayar. ta riga ta san shi ne shiyasa ta yanke shawarar k’in d’auka, amman kuma sai zuciyarta ta ƙi bata goyon bayan yin hakan,

dan haka ta amsa kiran…

Tana d’auka ta ce masa “zan duba in

na yanzu, sannan za mu zo da ni da su Ya Musbah mu yi maka godiya,

a office. ban sani ba ko kana nan gobe sunday’’

ta so daga haka kawai ta kashe amma kuma sam sai ta gagara.

Shiruu ya d’an yi kafin ya ce

‘’Ba za a abar godiyar nan ba kuwa? zaku sa in

yi ta jin kunya fa’’

A hankali ta ce ‘’ba komai ai, da har da Baba ma zamuzo’’

Da sauri yace ‘’Innalillahi. dan Allah ku rufa min asiri….

In Baba ya zo yi min godiya da kanshi ai sai in b’ace. d’azu ma duk sai da na ji wani iri da ya min a waya Wallahi.’



Murmushi ta yi kafin ta ce

‘’Eh muma mun lallab’a shi ya hak’ura, amma dai ka bari mu d’in mu zo saboda ba zai yarda ba, ko na ce masa ka ce ba sai mun zo ba! bazai bari ba.

kuma nima ina son in yi maka godiyar, dan ban samu na yi maka a asibiti ba’’

Shiruuu ya d’an yi, har sai da ta zare wayar daga kunnenta ta kalla taga still yana kan layin

kafin ta ji ya ce ’’Ni kam ba godiya na ke buk’ata daga wajen ki ba..

Akwai abunda nake da buk’ata amman sai ido da ido tukunna zan gaya miki.

Allah ya kaimu gob

en.

inanan.

Akwai aiki dama, kinga goben sai ki nuna min, daganan idan mun kammala ni kuma sai in gaya miki tukuicin da nake so a bani,’’

Shiruu ta yi har sai da yace ‘’Mannubiya’’

Tukunna ta ce ‘’to.

amma fa babu aiki mutum d’aya ne kawai, sannan ya aka

yi ka sani?’’.

Murmushi yayi yace ‘’aikin nasa yana da matuƙar muhimmanci.”

Shiruu ta kuma yi kafin ta ce

‘’Ai be kamata ka tambayi tukuici da kanka ba, ni ce zan ga dama in bayar kuma bai ma gama zama ready ba (bai ma gama kammaluwa ba).”

Dariya ya yi,

yana jiyo wauta a cikin maganar tata kafin ya ce ’’banaso ki siyamin komai…

In ma wani abun kike shirin siya, dukda kuwa na ji da

ɗ

i kuma na gode

amman da gaske ba na son ki siya min komai.

Ni a

ɗ

a

ɓ

i’ata idan na yi abu aka yaba to ni zan fad’i tukuicin da

nake so a bani.”

Sai da ta

ɗ

an juya maganar a Bakinta tukunna ta ce masa

“Iyakar maidamin zuwan nawa sau biyu da ka yi a wannan satin, a ganina ai ya ishi tukuici to”

‘’Um um bai Isa ba, sannan ai ba iya wannan satin nace ba, zuwan ki gaba

ɗ

aya ya daw

o sau biyu kenan Friday and Sunday’’ yace hakan yana murmushi.

Turo Baki ta yi gaba kamar tana gaban sa, sai kuma ta yi shiruu tana tunani kafin ta samu tayi kokawa da zuciyarta wadda take ta faman d’aurata akan tunanin abunda zai fad’a mata goben…..

ahan

kali tace ‘’bara in duba Inna, sai da safe’’

Sai da ya d’an d’auki lokaci tukunna ya ce “dare bai yi sosai ba ko?

in ba damuwa inaso za mu gaisa’’

A hankali ta sauk’e ajiyar zuciya kafin ta ce ’’ai bata da lafiya’’.

‘’Eh, Najeeb ya fad’a min kuwa…Allah

ya bata lafiya. ki

kai mata wayar in yi mata ya jiki’’

Ya sake nanata mata batun gaisawar, a karo na biyu.

Sai da Manubiya ta d’an lumshe idanuwanta ta bud’e tukunna ta ce ‘’ai bata magana, bata iya yin komai’’

Da sauri ya ce ‘’subahanallah,

Stroke?’’

Ya yi mata tambayar a d’an rikice.

A hankali ta ce masa “eh’’

Shiruu ya yi yana nazari kafin ya ce ‘’wanne physiotherapist d’in take gani?’’

A hankali ba dan ta so ba tace mishi ‘’in mun kaita tana ganin normal Dr’’

Zuwa wannan lokacin ya fara fahimtar

wani abun dan haka a hankali ya ce ‘’wanne asibiti take zuwa, da magungunan da take sha?’’

Sai da ta sauk’e y’ar siririyar ajiyar zuciya tukunna ta ce ‘’asibitin murtala’’.

Ahankali ya lumshe idanuwan shi, yana mai jin tsananin tausayin ta yana ratsa sh

i….ji yake yi kamar yayi mata kuka.

Sai da ta ce bara in je, sai da safe. tukunna dakyar ya ce

‘’Ok’’

sai kuma ya sake cewa ‘’zan iya kiran ki nan da 3O minutes haka, dare bai yi ba?’’

A hankali ta ce ‘’tam, ba damuwa’’

daganan suka yi sallama..

A ran

ta tana mamakin tsantsar tausayin ta itada ahalinta tare da kulawa da ta jiyo ƙarara a cikin muryarsa.

Ba a cikata mintuna ashirin ba ya kirata, ya sanar mata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login