Showing 138001 words to 141000 words out of 150519 words
Yashjub ya yi, sannan ya janye d’ayan Hannunshi wanda ya d’aga da niyyar goge mata hawaye, tukunna ya d’an matsa kusa da su ya kalli Yassira, fuskarshi ba yabo ba fall
asa
Yace
‘‘Lafiya dai ko?’’
Da kyar Yassira ta samu ta iya cewa ‘’eh!lafiya, mun zo wajenka ne, sai dai na ga kamar kana busy….”
‘’Eh kam, very busy”
Ya bata amsar kanshi tsaye, kafin ya ce
‘’Ki jira in mun had’u a gida sai mu yi’’
Ya k’arashe maganar t
asa cikin takaici, dan sam bai so su ka ga Manubiya yanzu ba.
Daga haka ya fara k’ok’arin juyawa ya ji ta ce
‘’Akan Mommy ne fa. Ba zai yiu mu yi a cikin gidan ba dama shiyasa muka biyo ka nan’’
Wannan karon had’e fuska Yashjub yayi tamau kafin yace “Yas
sira, i’m busy, ki jrani ko ma menene, idan na dawo gida sai in ji ko?!.Thankyou’’
Shiruu Yasirar ta yi kafin
daga baya ta d’an k’ak’alo murmushi, a hankali ta ce
‘‘Okay Yash’’
Jinjina Kai yayi, still fuskarshi a had’e ya ce
‘’sai anjima’’
har ga
Allah
Allah Allah kawai yakeyi su yi su fita, saboda gaba d’ayanta Kausar! Da ita da shigarta! Da kwalliyarta!
Duk juya mishi kai kawai takeyi.
Sai da Yassira ta sake kallon Manubiya wadda ta juya baya tun shigowarsu tukunna ta kamo Hannun Kausar wadda it
ama tunda suka shigo ta yi ido biyu da Manubiya ta sunkuyar da kanta k’asa ta k’i cewa komai.
Ahankali Yasira ta ce mata
‘’mu je!’’
Ganin da ta yi kamar ma Kausar d’in bata jin abunda take ce mata ne ya sanya kawai ta ja
Hannunta suka fice daga office d
’in .
Suna fita Yash ya zagaya ya d’auki wayarshi ya turawa Yassira massage
…’idan kika sake zuwarmin da ita office
ɗ
ina,
I’m going to humiliate the two of you like hell….
(Sai na ha
ɗ
a da ke da itan na yi muku wulaƙancin da ba za ku ta
ɓ
a mantawa ba)…..’
*MANNUBIYA*
*46*
Yana gama turawa Yassira message ya ga
Manubiya ta sak’ala jakarta, tana shirin juyawa ta tafi.
Dan haka ya k’arasa da sauri ya tare gabanta.
Kasa magana ta yi shiyasa kawai sai ta kawar da kanta gefe.
Cikin sanyin
murya ya ce ‘’nima ban shiryama hakan ba…ki yi hak’uri, ba zan sake rik’e miki Hannu ba, yanzun ma mistake ne..let’s start a fresh (yanzu, mu sake farowa daga farko)
InshaaAllah ba zan sake ba.’’
Ya fad’i hakan yana kallonta, shi a karon kanshi yana mamaki
n yanda ya koma, dan sam bayar da hak’uri baya daga cikin tsarinshi, bai ma iya ba! Amma a iya yau a iya shigowarta cikin office d’insa kawo yanzu ya bata hak’uri ya fi a k’irga.
…….’’sam ba su yi kama da d’ayar ba dan tama fi kama da y’an china. Har
gara ma d’ayar ita sun d’an yi kama wataƙila ko cousin d’inshi ce, to ita kuma d’ayar fa wacece?
Dan sarai ta lura da yadda idanuwanta suka cicciko lokacin da suka had’a ido, wacece ita? Su waye su?
Sannan wacece Mommy!?
Dan ta tabbatar inda ace wadda aka
ambata da Mommy Mahaifiyar sa ce to da ba zai k’i tsayawa ya saurari abunda suka zo takanas fad’a masa akanta ba”….
Manubiya ta aiyyana hakan a cikin ranta.
Tunanin ta ne ya katse jin ya ce
‘’Mannubiya’’
A hankali
Ajiyar zuciya ta sauk’e tukunna ta d
’ago ta d’an kalleshi.
Kalar tausayi ya yi mata kafin ya ce
‘‘Plsss’’
Ya fad’i hakan yana k’ok’arin durk’usawa a wajen
Ita kanta ba ta san lokacin da ta ce “a’a dan Allah kar ka sunkuya’’
Ba tare da ya damu ba ya ce ’’ai ba ki ce ya wuce ba’’
Ya fad’i
hakan yana me durk’usawa a gabanta.
Gaba d’aya kunya da takaicin kanta ne suka lullub’e ta, bata san lokacin da ta ce ’’ya wuce! nima sai yanzu na lura baka ma sani ba, dan Allah ka tashi’’
Murmushi ya yi kafin ya mik’e a hankali yana kallonta sannan ya
ce ’’ashe dai ana so na!’’
Da sauri ta runtse idanunta a ranta ta ce ‘’Tabbas Ina sonka Yashjub!’’
Dariya ya yi kafin ya ce ’’dole ki runtse ido mana’’
A hankali ta sunkuyar da kanta k’asa ta yi shiruuu, kafin chan ta ce ’’wacece Mommy?’’
Murmushi y
a yi kawai…
a hankali yake kallon fuskarta yana karantarta, yana jin wani sanyi yana ratsashi….
Sai da ta sake cewa ‘’um?’’
Tukunna ya ce
‘’Sisters d’ina ne dukkan su,
Mommy kuma is my mom(mamana ce).”
Bai bata damar cewa komai ba
Ya ce “mu bar wannan
maganar, yanzu mu yi maganar da ta shafe mu’’
Ahankali ya ji ta ce
‘’Kuma ita ta haife ka?’’
Lumshe idanunsa ya yi ya bud’e tukunna ya ce ’’ki bar maganar mana, um??’’
Girgiza kanta kawai ta yi
kafin ta ce ’’kawai na ga yadda ka yi ne
kamar baka wan
i damu ba
Wanda hakan sam bai dace ba!.
Na san bai kamata in shiga cikin abubuwanka na kashin kai ba
amman uwa ta fi k’arfin wasa..
Indai har wadda suka kira da Mommy Mahaifiyarka ce to a gaskiya abunda ka yi bai kamata ba.
Ni yanzu haka so nake ace Innat
a ta turo wani ya bani sak’o ko mu yi magana Baki da Baki ma ni da ita
amman ba ni da damar yin hakan.
Shawara ce nake baka
dukda na san na yi maka shishshigi amman na kasa haƙuri ne tunda naga abun ya shafi Uwa!
dan babu abunda yake
ɓ
ata mini rai kamar
inga ana d’aukar Mahaifiya ba da muhimmanci ba
Dan haka
dan Allah idan zai yiu ka yi k’ok’ari ka gyara hakan,
Once again ka yi hak’uri idan na zarce iyakata.’’
Shiruuu kawai ya yi yana sauraron ta, tunda ta fara har ta dasa aya.
Jin ya yi shiru yasa
ta d’an d’ago ta kalleshi…ganin kawai ita ya ke kallo ne yasa ta d’an kauda idanunta daga garesa a hankali.
A lokaci d’aya ta ji ya sauk’e ajiyar zuciya kafin ya ce
‘’Thankyou! inshaaAllah na yi
miki alk’awarin zan gyara.
Kawai dama mun d’an samu ras
hin fahimta ne amman inshaaAllah
komai ya wuce daga yau!
Na yi miki alƙawari.
Sannan
Kar ki sake cewa kin zarce iyakar ki a cikin rayuwata ko hurumi na kashin kai na saboda Mannubiya kece rayuwar tawa ba ki da iyaka a komai nawa
duk abunda ya shafe ni t
o ya shafe ki….
Inaso ki yi kutse, ki shiga, ki yi duk yadda kika ga dama, dan tabbas in kikayi hakan zai sanyani farin ciki.
A yanzu amincewarki gare ni kawai nake jira, daganan idan mun zama d’aya komai nawa ya zama naki.
Na dad’e da gama tsarawa ‘mata
ta ita ce ni
nine ita.’
Kawai ina fatan za ki bani damar da zan nuna miki how much I love you (yadda na ke son ki)…….’’
Manubiya ji take yi kamar ta ce mishi “eh, itama tana son shi. amman kuma tana buk’atar shawara da su Jidda kafin ta ce komai, dan i
ta kanta ta san kuma tana gani kamar Yash ya fi k’arfinta amma dukda hakan tana buk’atar shawara da wani nata
wanda zai bata izinin ta kulashin saboda itama a karon kanta abunda take so d’in kenan.
Abu na biyu kuma ko da ace zata ce masa tana son shi har
ga Allah ba za ta iya kallon cikin idanunshi ayanzu dai ta fad’a mishi ba,
dan wata tsananin kunya kwarjini da girmansa take ji take kuma gani.
Abu na uku kuma abunda yayi mata yanzu ta ji zafi dukda kuwa ya bata hak’uri kuma ita kanta ta lura dagaske ba
i sani d’in ba amman tanaso ta sake jaddada mishi sannan su fahimci juna sosai akan
‘Ko bakin hijabinta bata yarda ya sake tab’awa ba’….’’
Dan haka kawai sai tace masa
‘’once again (Har ila yau), mun gode kwarai.
bari in wuce gida’’
Murmushi kawai ya
yi kafin ya ce
‘‘Okay ranki ya da
ɗ
e! duk yadda kika ce hakan za a yi.
In kai ki? Ko in saka a maidake?’’
Yayi mata tambayar yana mai tsare ta da idanuwa.
A hankali ta girgiza Kai kafin ta ce ’’na gode’’ daga haka ta juya ta wuce
Numfashi ya fesar sann
an yace
‘’Ina jiran amsata’’
Tsayawa ta yi i ta kasa gaba ta kuma kasa juyowa
Bata san lokacin da ya matso kusa da ita ba sai da ta ji maganarsa a setin kunnenta
A hankali yana cewa ‘’pls dear, don’t keep me waiting‘’
Da sauri ta yi gaba ta fice daga
office d’in tana mai sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya……
Shima ajiyar zuciyar ya sauk’e sannan ya fesar da iska yana wani sihirtaccen murmushi kafin ya koma ya zauna a fili ya ce ‘’Alhamdulillah’’
Kamar kuma wanda ya tuna wani abun sai ya mik’e, ya b
i bayanta da sauri…..
Sai da ya nemi adaidata sahun da ta kwanta masa ya sakata tukunna hankalinsa ya kwanta…haka nan suka rabu kamar basa so bayan ya ce mata ‘akwai ƴar uwarsa ta musamman da zata kirata, mai suna Yahanasu.’
Sai da suka k’ule ya daina ga
ninsu tukunna ya juya ya koma buil
ɗ
ing d’in, har ya isa shi kad’ai sai faman murmushi yake ta yi..
Ba drivers ba hatta securities na company d’in nashi sun sha mamaki yau, dan haka sukayi ta y’an ƙus-ƙus d’in su a tsakani shi kam Yashjub bai ma san sunay
i ba.
Sai da suka yi nisa da company d’in tukunna Manubiya ta samu ta shak’a sanann ta fesar da wani bahagon numfashi, dan tun d’azu ji takeyi kamar an shak’e ta,
gaba d’aya kunya!k’auna!shauk’i!da asalin mamakin Yash sun hanata sukuni…
Yashjub yana zam
a a office, aikin Yassir wanda ya saka a gaba ya d’an tab’a, kafin daga baya ya fad’a duniyar tunani….
Ya kuwa dad’e yana lissafe-lissafenshi kafin ya mik’e ya fice daga company d’in gaba d’aya dan dama saboda Mannubiya ne ya zo yau…..
A b’angaren su K
ausar kuwa, suna fita ta samu gaban company d’in chan da d’an nisa ta yi parking.
Kallonta kawai Yassira ta ke yi
tana mai jin wani tsananin tausayinta ya na sake lullubeta a lokaci guda kuma tana da na sanin gaiyyatar ta
ɗ
in da ta yi akan su zo nan
ɗ
in,
dan inda ace ta san za su yi wannan mugun ganin to da ita ka
ɗ
ai za ta zo abinta, su tattauna ita da Yash d’in akan Mommy su magance matsalar iyaka su biyu’ kawai! Dan ba zai yiu ace ta zuba ido tana gani yana gaba da uwar su ba’.
Ta lura da yadda Kausar
d’in ta ci uban kwalliyar da ita kanta ta ma manta rabon da ta ga ta yi kwatan kwacin irinta, gashi ta zo amma ko kallonta Yash d’in ma bai yi ba, gashi kuma sun yi mugun gani…..
Yassira tana cikin wannan tunanin ta ga Kausar d’in ta zaro wayarta. Wani cl
eaner wanda su ke shiri kuma suka shirya akan zai ke fad’a mata shige da ficen Yash
ɗ
in! Ta kira.
Yana zuwa ya fara sosa k’eya, bayan sun gaisa kuma yayi shiru, ya sunkuyar da kanshi k’asa dan tun a ranar da yaga Manubiya ta zo an kaita har office d’in Y
ash ya kamata ace ya kira Kausar ya sanar da ita a yadda suka tsara amman kawai shi baya son wannan harkar ne dan ya zama kamar munafurci da cin dunduniyar Yash kenan
Mutumin da wani lokacin in wata ya k’are har k’ari yake yi musu akan salary d’in su…..
‘’Ka san laifin ka kenan’’
Muryar Kausar ta katsewa cleaner d’in tunani
Murmushi yayi ya d’an sosa k’eya, ahankali ya ce
‘’Afuwan hajiya! na d’an yi
tafiya ne, nima yau na fara ganinta da na tambaya shine aka ce min ai ta d’an kwan biyu’’
Sarai Ka
usar ta fahimci k’arya ya shirga mata, shiyasa ta ce ‘’Ina da recording d’in wayoyin da muka yi ni da kai,
ba zan damu ba dan Yash ya san me nakeyi
dan haka idan baka bi min Yarinyar chan ka gano min gidansu ba
tou zan kwashe komai in tura masa.’’
Da sa
uri yace ‘’ki yi hak’uri dan Allah, inshaaAllah zan bi ta, yanzu ma kuwa. Tana fitowa zan bi ta.”
‘’Ka d’auko min number gidan adress d’in ta da sunanta da komai’’
Dasauri yace
‘’To to,angama…’’
Kafin ma ya gama amsawa har ta kunna motar, bata sake bi
ta kansa ba ta figi motar suka wuce.
Sai a lokacin Yassira wadda tun d’azu ta kumbura sannan al’ajabi ya rufeta ga kuma tausayin Kausar
ɗ
in
ta ce
‘’Kausar! me za mu yi da adress d’in ta?
Kin dai san duk abunda kika je kikayi mata zata gaya masa ko??
Ba
ya ga haka ma ba ajin mu bace, sannan bai kamata ace
mun tsaya muna chachar Baki da wannan Yarinyar wadda bana jin ta kai sa’ar Yusra ma.
Kuma idan ya sani ko ya ji labari ina fatan kin san kashinki ya bushe ko?
Ki duba ki gani dai yadda duk ya burkice y
a rikice yake ta faman rarrashinta
saboda kawai ya ga tana hawaye….’’
Mahaukacin burkin da Kausar ta ja wanda sai da Yassirar ta buga kanta kad’an ne ya sanya ta yi shiru, dama Yasira a zuciye take kuma ranta a mugun b’ace yake ‘na ganin Manubiya da ta
yi’ dan haka rai a
ɓ
ace ta d’ago ta ce ’’Girl! Are you crazy? (Ke! Kin haukace ne?)
kallifa ya…’’
Maganar tata ce ta mak’ale sakamokon hawayen da ta gani ya fara zubowa ta cikin Idanun Kausar d’in..
Shiyasa gaba day’a sai tausayinta kuma ya lullub’e Yas
irar….tabbas ko da ace itace
take da saurayi ya yi budurwa kamar wachchar Yarinyar da suka tarar a office d’in Yashjub
to fa ko dai ta hak’ura da shi ko kuma ta bi ta ko wacce hanya ta rabasu, dan ita kanta tunda ta ganta tashi d’aya sai da ta raina kant
a ga wani irin kishi da ta ji ya taso mata a take duk ya bi ya lullu
ɓ
eta lokaci guda!!
To Ina kuma ga Kausar
ɗ
in?!
Allah kad’ai ya san me take ji!
Bata riga ta samu hankalin Yashjub d’in bama, gashi har wata ta yi wuff da shi, dan a iyakar abunda ta gani a
yau kawai tabbas ta san sunada aiki jaaa! A gaban su.
‘’Yassira har mu je gida kar ki sake cewa komai
Dan Allah’’
Muryar Kausar ta katsewa Yasirar tunanin.
Tana gama fad’in hakan ta ja motar da gudu suka wuce.
Suna zuwa gida ba ta ko kalli Yasira ba,
ta bud’e motar ta fice ta wuce sama.
Kai tsaye fanninta ta nufa, tana tafe Zuciyarta tana wani irin tafarfasa.
Tana shiga parlournta ta yi cilli da wayarta da d’an ficicin mayafinta sai kuma ta fara kai kawo….tana safa da marwa a cikin
ɗ
akin, kafin kuma
ta
fara d’aukar abubuwa tana farfasawa!!!
Wanda hakan ya janyo hankalin Mommy, dan
haka ta nufo side d’in nata.
Tana shiga ta zaro idanu waje, sai
kuma ta k’arasa inda Kausar d’in take ta rik’eta cikin tashin hankali ta ce
‘’Lafiyar ki kuwa?’’
ta yi mata
tambayar tana mai shafa fuskarta wadda ta yi jajawur idanunta suka sake k’ank’ancewa.
Tsabar tashin hankali kasa ma magana ta yi, kuma so take ta yi kuka sosai amma ta kasa dan shima hawayen ya k’afe…
Suna tsaye a haka Yasira ta iso, tun daga bakin k’o
far ta fara cewa “Kausar bani takardun nan akwai wanda ya ke jirana a office kins…’’
Maganartace ta mak’ale sakamokon kutso
kai da ta yi cikin parlourn.
Da sauri ta ce’’Ya subahanallah!’’
sai
kuma ta k’arasa inda suke tsaye su duka biyun.
Tana zuwa ta rung
ume Kausar d’in, sannan a hankali
cikin son kwantar mata da hankali ta ce ‘’kar ki damu, za mu nemo mafita’’
Da sauri Mommy ma ta shiga rarrashin Kausar d’in dukda kuwa bata san dalilin fashe fashen da ta tarar ta na yi ba da
ɓ
acin ran nata amma dama tu
nda Yassira
ɗ
azu ta ce mata ‘’za su je office d’in Yash itada Kausar” ta san za a rina….
Suna nan tsaye wayar Kausar ta d’au k’ara….
Dan haka ta janye Jikinta daga na Yassira a hankalia ta koma gefe ta durk’usa ta d’auki wayar tata
wadda ta duk farfas
he dan tana shigowa dama da ita ta fara yin cilli.
Ganin mai kiran nata ne yasa ta d’auka a take, sannan a hankali
ta ce ‘’ina jin ka’’
Daga chan d’ayan b’angaren ya ce mata “gani nan yanzunnan aka ajjiyeta a k’ofar gidan nasu ta shiga’’
daganan ya fad
’i mata adress da number gidan tukunna ya ce ‘’ban samu
sunan yarinyar ba dai amman
Ina kan bincike.’’
‘’Tam’’
kawai Kausar ta iya cewa daga haka ta zare wayar daga kunnenta ta kashe sannan ta shiga cikin contact d’inta….
Zuwa wannan lokacin Yassi
ra ta fahimci da wa ta gama yin waya dan haka ta matsa kusa da ita ta ce mata’’Kausar me za ki yi ne??’’
Dai-dai nan ta kara wayarta a kunne ta ce ’’Hello!na’am…zan turo maka adress d’in wani gida yanzu!Inaso ku je duk