Showing 117001 words to 120000 words out of 150519 words

Chapter 40 - Mannubiya Complete

d’aya jikinsa yayi sanyi, yayinda zuciyarsa take wani irin tafarfasa!!!

tabbas Hausawa sun yi gaskiya da sukace’’munafuki in ya rigaka shiga d’akin uwarka, to ko ruwa baka isa ka sha ba.’’

Allah kad’ai ya san me da me Yusuf ya gayawa Baba shi

kuma ya hau

kai d’aram ya zauna.

Gashi ya san halin Baba da wata iriyar rikitattiyar kafiya, dan haka ya riga ya san ko ta ya zai yi masa bayani ba zai tab’a yarda ba.

Gashi yanzu ya saka shi a gaba yana kuka, shiyasa tashi d’aya gaba d’aya jikin Ya Musbah

ya yi sanyi, dan jin kukan Baba yake yi har cikin ransa, ji yake yi kamar ya je ya samu Yusuf ya d’aga shi sama kawai ya goce…

zai bar maganar yanzu, ya samu ya lallab’a Baba amma inshaaAllah ba zai ta

ɓ

a bari Jidda ta auri Yusuf ba’’.

A hankali ya mats

a ya shiga rarrashin sa shima yana mai bashi hak’urin abunda ya yi masa yanzun…

Cikin sanyin jiki Baba ya ce’’mutumin nan ya gudu, basu kama shi ba. ku bar ni in aurar da su Jidda tun kafin wani abun ya sake faruwa, na san inshaaAllah idan sunada aurensu

darajar aure da kariyar ub…..”

Shiruu ya yi sakamokon shigowar da su Manu sukayi.

cikin nutsuwar su, suka k’arasa suna zuwa wajen ya Musbah ya juya da sauri yace ‘’bara in duba jikin Abbakar!”

Ya fad’i hakan yana nufar labulen da aka saka a tsakanin baba d

a abbakar d’in.

Doga jin haka ya Nafi’u ma ya biye masa baya.

Ya Musbah na gaba ya Nafi’u na biye da shi a baya yana tafe yana dialing number Aisha dan sai yanzu yaga misscalls dinta birjik, haka suka shiga inda Abbakar d’in yake a kwance.

Suna shiga ya M

usbah ya naushi iska da k’arfi, jikinsa har wani irin karkarwa yake yi tsabar takaici.

Dasauri ya Nafi’u ya rik’e shi yace’’haba Musbahu! kayi hak’uri a bi komai a hankali, lokaci zai sa komai ya yi daidai inshaaAllah.’’

Kamar zai fashe da kuka ya ce



’Astaghfirullah, Nafi’u wacce iriyar rayuwa ce wannan? kalli family d’ina! kalli halin da suke a ciki!

amma wai ace banida yadda zan yi in taimakesu?

ka duba kaga yadda ake shirin aurar da su Manubiya kamar wasu Kaji?

kuma a yadda Baba yayi bayanin nan tab

bas yana da gaskiya ta wani fannin tunda daga ni har shi

ɗ

in ba za mu iya karesu ba..

amma dukda haka bai kamata Jidda ta auri Yusuf ba, kuma ya kamata ace na yi wani abun amma banida……’’

Kukan da ya kufce masa ne ya sanya shi kasa ci gaba da magana.

Ya

Nafi’u ji yayi kamar shima ya fashe da kuka, dan haka cikin sanyin jiki ya matsa kusa da ya Musbahn ya rungumesa, sannan

cikin sigar rarrashi ya ce ’’kuka da k’unci ba shine mafita ba

Musbahu, kar ka dasa ayar tambaya a kan k’addararka ka je garin hakan

ka kauce hanya, sannan kar ka karaya ka ce wai dan baka da k’arfi ba za ka

Iya yin komai ba. inshaaAllah za mu fahimtar da Baba kuma zai fahimcemu, dan ko da ace za’a aurar da su Jiddan to ni

kaina ba zan goyi bayan a aurar da su da wuri haka ba kuma ba

zan bari Jidda ta auri Yusuf ba inshaaAllah.

kawai dai yanzu abunda nake so ka fahimta shine ‘Baba ya d’au zafi!. Sannan hankalinsa a tashe yake!’

Dan haka ka bari nan da kwana biyu inshaaAllah idan ya d’an sak’k’o mu ka lallab’a shi na san zai fahimce mu.

Ubangiji yana tare da mu, komai zai yi dai-dai inshaaAllah’’.

Cika shi Ya Musbah ya yi, ya je jikin window ya dawo ya sake komawa…yana yi yana share hawayensa, kafin da kyar ya samu ya tsayar da kukan nasa

tukunna ya ce ‘’Allah ya dafa mana. Allah ya tsa

ya mana. Nafi’u na san zafin rashin dace da Abokin rayuwa, idan akayi rashin sa’a Baba ya k’i amincewa da mu ya je garin neman mafita ya

ɓ

urma su Jidda a Hannun mugaye shin ya kake tunani kenan?

Kar mu je duk mu ukun mu k’are da…..’’

Da sauri ya Nafi’u ya

ce ‘‘Musbahu, ka kyautata zato dan Allah…think positive!.

inshaaAllah hakan ba za ta faru ba’’.

Shiruuu, ya Musbah ya d’anyi da farko!

yana me sauk’e ajiyar zuciya a

jere a jere, kafin ya jinjina kai kawai, daga haka ya k’arasa bakin gadon da Abbakar ya

ke nan a kwance ya zubawa guri d’aya ido ya yi shiruuu.

Numfashi Ya Nafi’u ya fesar, kafin ya d’ago wayarsa da sauri dan shi sai yanzun ne ma ya tuna ya yi dialing number Aisha tun d’azu,

yana d’ago wayar kuwa ya ga timer tanata tafiya alamun ta d’auka k

enan tun d’azun.

Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin ya kara wayar a kunnensa ya ce ’’lab’e kika fara kenan!’’

Murmushi ta yi, sannan ta ce ’’na d’auka sai su khairat suka fara fad’a ita da mai sunan Baba, shine na ajjiye wayar na je raba su da ke hankalina y

a yi gaba a tunanina na kashe. amma kuma dukda haka da na d’auka d’in da farko kafin in ajjiye na ji maganar da ta d’an kid’ima ni shiyasa ma na manta ban kashe d’in ba tsabar kid’imar da na yi’’….shiruu ta d’an yi kafin ta ce ’’da gaske Manubiya aure ta y

i???”

Dafe Kai ya Nafi’u ya yi kafin yace’’kinga irin ta ko, baki tsaya kin ji kan zance da k’arshen sa ba kawai daga kin ji ance aure shikenan ke har kin je ga ƙarshen zancen.’’

Fahimtar da Aisha ta yi kamar ran maigidan nata a d’an b’ace yake ne yasa

nya cikin kwantar da murya tace ‘’Allah ya huci zuciyarka, ba zan k’ara ba.

Dama na ga kamar Inna tana jin yunwa ne shine na kira inaso in tambaya a bata madara ne ko abinci, to kuma sai baka d’auka ba, a lokacin kuma wayar Manu bata shiga amma na same ta

ma har ta yi min bayani tun d’azu mun gama magaana.”

‘’Okay, sannu Aisha, Allah yayi albarka’’ ya Nafi’u ya fad’i hakan cikin sanyin jiki.

Ahankali tace ‘’ameen’’ daganan suka yi sallama bayan yace mata ‘ai sun ma kusan dawowa’

Dan haka ta bari akan ida

n sun dawo sai ta ji koma mene ya kaisu suka dad’e har haka.

………….

Tun lokacin da Ya Musbah ya kai Inna gidansa ya fita!

Baraka ta kumbura, ta rasa Ina za ta saka ranta. Tashi d’aya ta ji gaba d’aya

duniyar ta yi mata zafi…ita fa dama tun farko abunda ta

ke ta tsoro kenan, dan ita babban tashin hankalinta kar rikon Inna ya dawo hannun Ya Musbah! Dan wallahi ita bazata tab’a iya jurar ganinta a cikin gidan ba!….dad’in dad’awa kuma gata liability, saboda Allah in banda rashin adalci ta yaya ma za’a had’ata d

a jinya, ai ba dan haka aka aurota ba!.

Takaici da bak’in ciki ne ma suka saka ta kasa tab’uka komai a cikin gidan, dan haka ta fito tsakar gidan ta zauna akan y’ar kujerar tsugunno tanata faman cika tana batsewa, ko d’akin da aka ajjiye Innar bata lek’

a ba tunda su ya Musbah suka kawo ta suka fita…

Muhsin ne da me sunan Baba wanda tunda ya gansu yaketa murna ya shige d’akin shima

suke ta yiwa innar hira.

Baraka kuwa tana tsakar gida ta d’aurawa kanta bala’i in banda tafarfasa babu abunda zuciyarta tak

eyi…a haka Aisha ta shigo ta same ta.

Sama-sama suka gaisa da Aishar daga haka ta tambayeta d’akin da innar take, ta nuna mata,

Aishar ta shige.

Tana shigewa Baraka ta mik’e tsaye dan zuwa wannan lokacin ta ma kasa zama kwata-kwata, kamar wata wadda aka

aikowa da rikitaccen sak’o haka ta shiga safa da marwa a tsakar gidan ta kasa tsaye ta kasa zaune….itafa ba zai yiu a maida mata gida asibiti ba wallahi!

Tunda gashi y’an dubiya har sun fara zuwa, wannan ya shigo wanchan ya fita shikenan ita ba ta da sirr

i a cikin gidanta kenan?

Gashi har yanzu su Ya Musbah shiru, ta kirasa kuma ya k’i d’agawa,

Itafa wallahi Inna ba za ta kwanar mata a cikin gidanta ba yau.!.

Sama-sama ta fara jiyo muryar

Aisha kamar tana waya da ya Nafi’u dan haka ta je ta lab’e…..

wan

i irin gumi ne ya shiga keto mata sakamokon kunnuwanta da suka jiyo mata lokacin da Aisha take cewa “da gaske Manubiya aure ta yi???’’.

Tashi d’aya Baraka ta shiga cikin ma

ɗ

aukakin tashin hankali, a ranta ta ce

“Manubiya ta yi aure!

Abunda suka je yi ken

an?

To ina batun

Baba kuma dan d’azu maman Abbakar ta kira ta take gaya mata cewar “kamasa akayi!

Shiyasa suka kawo innar suka tafi gaba d’ayansu, itama ta so ta

tsaida Abbakar amma yana gaya mata an kama Baban ya fice a gigice har yanzu shiru babu shi

babu labarin shi tanata kiran wayar sa kuma baya d’auka’’



“Wato Shiyasa aka kawo mata inna da Muhsin tun yanzu kenan…

Manubiya tana tarewa a gidanta ta san jidda ma nan za ta dawo!

Kut!ai wallahi bazaiyiu ba, wannan abu ba zai t

ab’a sab’uwa ba, ba za ta zauna a gida d’aya da su ba wallahi!

Sannan

yanzu haka ma ya aka k’are,

tayaya ya Musbah yake iya ciyar da su biyu kawai

Ina kuma ga in nauyi ya sake yi masa yawa.’

Waennan sak’e-sak’en da Baraka take ta yi ne ya sanya ta fara ji

n jiri, dan bala’i har wani dishi-dishi ta fara gani!

dan haka ta koma ta zauna a kan y’ar kujerar ta tana ji kamar zuciyarta zata kama da wuta.

Bata dad’e da zama ba, Aisha ta fito ita da khairat ta ce mata ‘’ta d’aura girk, bara ta je ta duba’’

‘’To’



Kawai Baraka ta iya ce mata shima kuma da kyar, dan wani irin tafarfasa zuciyarta takeyi.

Aisha tana fita Baraka ta mik’e.

Ta ma rasa me yakeyi mata dad’i! ta rasa Ina zata saka ranta ta ji sanyi…

Tabbas idan fa ta yi sake tou wallahi ruk’on inna ya d

awo hannunta kenan har abada tunda ko

da ace daakwai Jiddah ai

Jiddan in dai ta ci post utme d’inta to makaranta za ta fara zuwa!!!

Muhsin yarone ya Musbah kuma aiki zai ce ze dinga fita, shikenan ita a barta da inna kenan….

Ita kam a barta da talaucin

da ya Musbah ya tsundumata a ciki ma mana

ba sai an k’ara mata da zama gida

ɗ

aya da dangin miji ba!.

Tsulum!

Haka Muhsin ya ga Baraka ta afko cikin d’akin da suke a ciki shi da inna…

Da sauri ya mik’e yana cewa “anty, kin ji yanzunnan

Na ji inna ta c

e ‘Manu’ wallahi!

Ki matso ki tambayeta ki ji’’

Ya fad’i hakan cikin tsananin farin cik, yana Jan hannun Baraka yana dariya…

Wafce hannunta ta yi da k’arfi ta...

*MANNUBIYA*

*40*

Wafce Hannunta ta yi ta k’arfi

ta ce ’’dalla ni cik

ani”

A hankali Muhsin wanda duk jikinshi ya yi sanyi ya ce

‘’Da gaske nake fa’’

Da kyar Baraka ta d’an k’ak’alo murmushi sannan ta ce

‘’Na yarda mana, nima ai tun daga waje na ji lokacin da ta fad’a’’

Da sauri ya ce

‘’au haba! bara mu kira su……”

Ci

kin katseshi ta ce ’’yi maza ka je shagon

Audi ka karb’o mata madara,

Idan ta ce ’Manu’ to madara take buk’ata.

Bari in je in kawo maka

kud’in”

Baraka ta fad’i hakan tana mai juyawa da niyyar fita.

Shiruu Muhsin ya yi, tana shirin fita ya ce mata ’’A’a

fa,bata ma tab’a

cewa Manu ba sai yau!

Adda Manubiya take nufi,

kuma ai yanzun nan muka bata madara ni da anty Aisha.”

Cikin d’an fushi ta ce

‘’Muhsin za ka yi abunda nace ko kuwa??’’

‘’Tam’’

Ya ce mata,

sai kuma ya sake cewa

‘’Akwai madarar da Y

a Musbah ya siya mata me yawa a gida, bara in je in d’auko’’.

Shiruu ta yi, kafin ta nufo sa, tana zuwa ta kama kafad’unsa ta ce

‘’Muhsin su ya Musbah sun rufe d’akin naku kafin su tafi, ka wuce ka je ka siyo mata a shagon Audi yanzu-yanzun nan, bara in

kawo maka kud’in.

Kana sakani yawan magana, kai na ciwo ya ke yi.”

Ahankali ya ce ‘’tou Anty’’

a ransa yana tunanin nisa da tafiyar shagon audin.

Kamar ya ce mata ‘ba zai iya siyowa a shagon kusa ba?’

sai kuma kawai yayi shiru dan ya san halinta

yanzun i

n ya cika ja-in-ja da ita tsaf sai ta makesa!

Dan haka ya ja Bakinsa yayi shiru, ya tsaya ya jirata har ta je ta kawo masa naira d’ari ta ce ’’gashi, ka yi sauri’’.

Da ‘’to’’ya amsata, tukunna ya sa hannu ya karb’i kud’in ya fita…har ya kusan kai k’ofa kam

ar wanda ya tuna wani abun sai kuma ya koma d’akin ya ce ’’Anty in je in kira Anty Aisha? Ta ce idan zan fita in je in kirata, saboda kar a bar inna ita kad’ai.”



Wannan karon cikin fushi sosai Baraka ta yi masa dak’uwa tukunna ta ce’’ ungo naka Muhsin!

I

nnar ita kad’ai ka gani anan? ni ba mutum baceba?.

Za ka wuce ka je min aike ko sai jikinka ya gaya maka?”

A hankali ya kamo hannun me sunan Baba ya ce ‘’zo ka rakani’’

Daganan ya juya kawai ya fita

ba tare da ya sake cewa komai ba.

Yana fita ta kalli I

nna tana raya abunda za ta yi, kafin ta kalli k’ofar da Muhsin d’in ya bi ya fita a ranta tace “sai dai kawai ka dawo ka gani, na san in kana nan tsaf za ka kawo min cikas!

Ba k’aramin aikinka bane ba ma ka tara min jama’a shegen Yaro mai shegen surutu…”

T

ana gama fad’in haka ta nufi inda innar take.



Tana zuwa ba tare da shayi ko tantama ba ta yaye zanin da aka lullub’ewa innar k’afafu da shi, ta d’auki pillown da ke ajjiye a gefenta ta fita waje…

A nan tsakar gidan da sumintin duk ya farfashe ta yi shi

mfid’a ta zanin da pillown tukunna ta koma d’akin.

Da kyar, da mugun kyar ta samu ta kinkimi Inna, k’arshema da ta ga baza ta iya ba janta ta yi ta fitar ta shimfid’eta anan tsakar gidan

Inda ta shimfid’a zani ta saka pillow.

Tana ganin lokacin da hawaye

suka shiga sintiri a kan kumatun Inna amman ko d’ar Baraka ba ta ji ba!idanunta sun riga sun rufe..

Ita babban tashin hankalinta shine

‘Manubiya ta yi aure kuma da alamun wani wajen za’a tafi da Baba tunda an riga an kama shi wataƙila shikenan ya tafi har

abada, ko me ma yayi oho musu!

Dan haka dole dole ta san gidanta Muhsin Jidda da Inna za su dawo kenan da zama’…

Dan haka

Wallahi ita kuma ba za ta yi k’asa a guiwa ba wajen nuna musu ba su Isa ba…tun wuri ma su nemi gurin zama! yau za su yi ta ta k’are!

garama idan suka dawo su gani sannan su tabbatar da cewa uwar tasa ma bata da wajen zama a cikin gidan ballantana kuma k’annensa.

Dama tun d’azu a k’ule take….saboda da ya tashi kawo Innar ma ko shawartarta bai yi ba

haka nan kawai sai ganin su ta yi.

Ai kuwa yanzu zai gani kuma zai san itama ta Isa wallahi!! taga alama idan ba nuna masa ta yi ba tou ba lalle ya tuno ‘waccece Baraka ba’.

Hakanan ta yi ta zancen zuci tana huci ita kad’ai!!!.

Ko bi ta kan inna bata sake yi ba, ta fad’a band’akin da ke na

n a tsakar gidan tana jin nauyi da zafin da zuciyarta ta yi yana raguwa kad’an-kad’an…..

A ganinta rainin wayon su ya ma yi yawa! A barta taji da hak’urin zaman auren ma da takeyi da shi ba sai an k’ara mata da wani takaicin ba, yau za’a yi ta ta k’are

Wa

llahi

dan bata tsoron uban kowa a cikin su.

…….

Su Ya Musbah suna tsaye a d’akin da Abbakar ya ke, su Jidda suka shigo. a take wani irin tausayin su ya lullub’e ya Musbah, dan haka ya kalli ya Nafi’u ya ce ’’bara in duba Reception, in ji ragowar bill d’in

mu dan a samu a biya…”

Daga haka ya sa kai ya fice…

Sun san su Yash sun biya d’azu amma basu san duka suka biya har da na Abbakar ba.

Yana fita ya Nafi’u ya d’auki wayar Abbakar,

Manubiya ta bud’e musu password d’in shi kuma ya kira maman Abbakar.

Ko mi

ntuna ashirin ba ayi ba kuwa suka k’araso cikin asibitin a hargitse ita da maman Baraka.

A reception suka had’u da ya Musbah wanda yake ta faman sak’a da warwara, sam ya kasa komawa cikin d’akin bayan ya je an ce masa “ai su Yash sun riga sun gama biyan k

omai’’.

Hangosu ya yi a hargitse suna tambayar wani cleaner, dan haka ya k’arasa ya yi musu iso har cikin d’akin.

Dama shima d’in da kyar suka amsa gaisuwar shi yanzu kuma ko kallon baba da yake kwance ba su yi ba haka suka wuce shi suka d’aga labulen da

ya ke tsakaninsu da Abbakar

Inda ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login