Showing 45001 words to 48000 words out of 150519 words
maganar tasa cikin b’acin rai.
A hankali
Baba ya d’ago gajiyayyun idanuwansa yana kallon Yayan
nasa, bai bashi amsar tambayoyin sa ba
maimakon hakan sai shima ya jefa masa tashi tambayar ta hanyar cewa
‘’Menene yake damun Matar tawa?’’
Cikin rashin fahimta Uncle ya ce
‘’Ban gane ba’’
Cikin son fahimtar da shi
Baba ya ce
‘’Wanne kalar ciwo ne
yake damun matata wanda har ta shafe sama da wata d’aya a kwance a gadon asibiti?.
Kai d’an uwana ne dan haka na san ka je ka duba ta kuma ya kamata ace ka san abubuwan da suke damun ta’’.
Cikin kame-kame
Uncle ya ce
‘’Magana za ka gaya min?
baka san y
anayin tsarin aikin banki ba ko? to bari ka ji Matana ma hak’uri suke yi da ni!
Ni kaine bani da lokacin kaine
balle kuma..’’
‘’Balle kuma wani ni,ko?’’
Baba ya k’arashe masa maganar tasa cikin sanyin murya.
Cikin d’an fad’a-fad’a
Uncle ya ce
‘’Kaga
Musa, ba ta wannan muke ba yanzu, kar ka zille ta wannan hanyar, ka fito ka fad’i ta yadda akayi ka karb’i kud’in yaro da kuma dalili, ni kuma in gayawa su Baba Habu daga nan mu ga abun da za mu iya’’.
Kamar Baba ba zai yi magana ba sai kuma ya yi murmush
i tukunna yace
‘’Ba zillewa zan yi ba, amsar da zaka bani ita zata sa ka fahimci yadda akayi na kar
ɓ
i kud’in.
Ciwon k’oda ne ya ke damun Amina wanda saida ta kai ga an cire (guda
ɗ
aya).
sannan ta samu stroke!!
hawan jini, ga kumburin zuciya..
Iyakar all
urai da magungunanta kad’ai aiki ne.
Ba daban Al’ameen
ɗ
in ba to da ban san ya zan yi ba’’
Ya k’arashe maganar wasu zafafan hawaye suna zubo masa….
A hankali ya share hawayen kafin ya kalli Uncle ya ci gaba da cewa
‘’Waennan sune abubuwan da suke damun
Matata suka sanya har na karb’i kud’in Al’ameen
Saboda ya nuna kwad’ayin yanaso ya taimakeni sannan shi kad’ai ne ya zo mini ya kuma taimakeni.
Inaso ka gayamin
In da ace kaine a matsayina
shin,
‘Ba za ka amshi kud’in ba’?”.
Uncle ya dad’e yana kallon
Baba kafin ya ce
‘’Anjima za mu had’u a parlourn Kaka Mallan, a nemo mafita
tsakanin kai da Ammi!.
Sannan a tabbatar da maganar Jiddah da Yusuf dan ta hakanne kawai ja’irar Yarinyar nan ba zata sake nemo mana magana ba’’
Ya fad’i hakan yana mai kallon
direction d’in da Jiddan take,
kafin ya juyo ya kalli Ya Musbah ya ce
‘’Har ga Allah ina jin tsoron Matarnan(Ammi), fad’a da mahaukaci sai sarki, ka fahimtar da su dan Allah.’’
Ya na gama fad’in haka ya kama hanya ya fice .
Sai a lokacin Manubiya ta samu
ta saki kukan da take ta k’ok’arin dannewa.
A hankali Jidda ma ta ci gaba da nata kukan.
BULAMA ✍
️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*15*
Cikin rashin jin dad’i Baba ya ce
‘’Ban yi tunanin zan kafa miki doka ki shallaketa
ba Jidda,
yaushe har kika yi wayo da girman da za’a raba ki da shi ki kasa hak’ura?
Ashe dama ziryar da yake ta yi wajen ki ya ke zuwa a b’oye? Kenan har yanzu kuna tare? Amman shine da ke da shi kuka ce mini babu komai tsakanin ku, kun rabu ko?. Ni kika
yi wa k’arya Jiddah?’’.
Cikin fashewa da wani irin kuka ta ce
‘’Baba dan Allah ka yi hak’uri…
Cewa yayi zai samu right time ya yi maka bayani ta yadda zaka fahimce mu’’.
Cikin fad’a sosai Baba ya ce
“Bayanin me? Ni za ku yaudara?.
yanzu shi Al’ameen as
he ba zai iya taimako na saboda Allah ba sai in da wani dalilin kenan, yaushe aka haifeku
daga ke har shi da zaku raina min wayo?’’
Ya k’arashe maganar cikin fushi.
A hankali Ya Musbah ya ce
‘’Baba ka yi hak’uri dan Allah, bara in fita in ga yadda za’ay
i da kud’in Matar nan, gara kawai a rabu lafiya.’’
A hankali Manubiya ta share hawayenta ta ce
“Zan je mu yi lissafi da ita, ta lissafa kud’in ta zan biyata ta hanyar yi mata aiki!
A gidan ta.”
Da sauri Ya Musbah ya ce ‘’za mu san yadda za mu yi ni da Ba
ba ki maida hankali akan karatunki ki yi shiru,kawai.’’
Murmushi ta yi kafin ta ce
‘’Ka bari nima in taimaka dan Allah, in kuka kawo naku sai a had’a ragowar da bai cika ba
In yi mata aiki na Iyaka kwanakin, kud’in suna da yawa fa ka barni inaso in tai
maka nima.
Makaranta kuma ba matsala zan iya had’a aikin da makarantar karka damu.’’
A hankali Muhsin ya ce
‘’Za mu dinga zuwa tare, sai in dinga tayaki da wani abun’’.
Jinjina Kai ta yi alamun ‘to’
Tana kallon sa tana murmushin da ya fi kuka ciwo.
Ka
fin ta kalli Ya Musbah
Ta ce
‘’Bara in je tun da wuri mu ji ko zata amince’’
Sai a sannan Jidda tace
‘’Adda da kin bari na….’’
Cikin katse ta ta ce
‘’Ba komai Jidda, kar ki damu, zamu gyara komai, inshaaAllah’’.
A hankali Jidda ta matsa ta rungumeta
ta na kuka sosai kanta fal da na sani, ba tare da Baba ya gani ba ta saka mata wayar da Al’ameen d’in ya siya mata Kafin ya tafi a Hannu, ita kuma karb’a kawai ta
ɗ
an jinjina Kai, daganan ta d’auki hijab d’inta ta sake sakaya wayar sannan ta cewa Muhsin y
a taho.
…
A gaban Baba ta je ta durk’usa tana addu’ar Allah Ubangiji yasa kar yace a’a…
cikin kwantar da murya tace’’Baba,dan Allah ka bar ni inje, kar ta zo ta tozarta Mutane ka ga inna bata da lafiya, kar a kuma d’aga mata hankali, gara mu bi ta a sannu
a rabu lafiy….’’
Yafi mintuna biyu bai yi magana ba kafin chan ya had’iye wani k’ululun bak’in bak’in ciki da tashin hankali tukunna
ya jinjina mata kai alamun amincewa.
Chan k’asan ranta ta ce
‘’Alhamdulillah’’.Sannan suka mik’e da niyyar fita, har sun
d’an gota ta ji yace
‘’Manu’’.
Sai da ta lumshe idanunta tukunna a hankali ta ce
‘‘Na’am Baba’’
Ahankali yace
‘’Kar ki yi ja’inja da ita sannan ki yi mata magana da tattausan lafuzza’’.
‘’InshaaAllah Baba’’ tace
Daganan ta jaa Hannun Muhsin suka wu
ce.
Suna fita Baba ma ya juya ya fita.
Chan bayan gidan inda ba kowa yaje, yana zuwa ya fashe da wani irin kuka, ya manta rabon da yayi feeling
helpless irin yau, ba irin wannan rayuwar ya so ƴaƴansa su yi ba,ba irin wannan uban yaso ya zamto ba amman ba
yadda zai yi ba shi da yadda zai yi,ko wacce hanya ko ina ya juya a toshe yake gani..
Ya jima ya na kuka kamar wani k’aramin yaro kafin daga bisani ya share hawayen nasa yayi istighfari sannan ahankali ya ce ‘’Alhamdulillah’’ tukunna ya mik’e ya koma d’a
kin.
A nan ya tarar da Ya Musbah shi da Jidda suna ta lallab’a Inna wadda take ta faman hawaye.
Dan Baban yana fita sukayi la’akari da ita ashe ta farka tun tuni basu sani ba, saida Baba ya fara umartar Ya Musbah akan
ya je gida ya duba Baraka da mai s
unan shi yaga komai kalau tunda tun safe yake asibiti kuma da suka dawo bai je ya lek’a gidan nasa ba.
Ba dan yaso ba ya tafi,
tukunna shi da Jidda suka ci gaba da lallab’a Inna………
Sai da su Manubiya suka kusa awa biyu tukunna suka dawo daga gidan Ammi
duk su biyun jikinsu a sanyaye. Jidda kawai suka samu a d’akin ita da Inna wadda suka lallab’a dakyar daga nan ta sha maganinta bacci ya d’auke ta,Jiddan ce ta ce musu ’’Baba ya fita yanzu bai dad’e ba’’.
A hankali Muhsin ya ce’’Bara in je wajen shi, na
san yana masallaci’’ daga haka ya fice ya bar musu d’akin.
Yanayin yadda Jiddan ta ganta ne ya sanya itama cikin mutuwar jiki tace ‘’lafiya dai ko? na gan ki wani iri’’.
A hankali Manubiya ta ce
“Wai har mun fara yau fa,
shiyasa ma kika ga mun dad’e.
A
ikin ba sauk’i gaskiya kuma a haka kinga yanzu dare ne so na san na safe zai fi wahala…
wanke-wanke da shara mukayi yau, tace kuma gobe har da girki.
Muhsin kuma da muka je da niyyar ya dinga tayani
ta ce shi zai dinga sharar wannan makeken tsakar gidan m
ai uban girma, albashin mu dubu goma goma, a wata dubu ashirin mu biyu.
In Allah yasa su Baba sun samu kud’i masu nauyi watak’ila wata d’aya ko biyu kawai za mu yi muna aikin, na bata har wayar da ya baki ma’’.
Manubiya ta k’arashe maganar tana mai cire hi
jabin jikinta.
Ajiyar zuciya Jidda ta sauk’e kafin tace
‘’Adda Manu ko ni in karb’a ke ki huta ki yi karatun ki cikin kwanciyar hankali’’.
A hankali Manubiya ta koma kusa da ita ta zauna kafin ta ce
‘’Jiddah,a yadda matarnan take jin zafin ki idan kik
aje mata gidan da sunan aikatau tsaf za ta iya cutar da ke, kuma bayaga haka ma bai kamata ke d’in ki je ba so ki bari karki damu ni da Muhsin d’in za mu yi, za mu iya’’.
Cikin zubar hawaye Jidda ta ce
‘’Adda Manu,ta yaya za ayi ni na yi laifi amma ace k
une zaku biya price d’in
A Ina aka tab’a yin haka?’’.
Cikin d’an jan kumatunta Manubiya tace ‘’A gidan Baba, gidan da y’an uwa suke matukar k’aunar junan su, gidan da kai yake a had’e! Har ta kai
Idan abu ya shafi d’aya tou ya shafi dukkan mu, gidan da m
u ke so mu nunawa Jiddan mu tana da gata’’.
This time around fashewa da kuka Jidda tayi ta fada jikinta ta rungumeta a hankali ta ce
‘’Nikam kar ku yi ku barshi zan yi in kuka yi bazan tab’a yafewa kaina ba..
Kullum zan dinga gani kamar na shiga hakkin k
une’’
A hankali Manubiya ta ce
‘Jidda ki kwantar da hankalinki, bau komai kinji ko?
Kuma inaso ki saka a ranki muddin za ki ci gaba da kula Al’ameen tou abunda zai faru damu kenan.
dan Allah Jidda
For the last time ki fita harkar Al’ameen har abada’’.
Ahankali Jiddan ta cika ta ta d’ago tana kallon ta kafin ta ce
‘’na riga na gama yi wa kaina wannan alk’awarin!
InshaaAllah babu ni ba Yw Al’ameen, kawai dai dan Allah kar ku bari a aura min Ya Yusuf,
Wallahi bana son shi’’.
Cike da bata assurance had’e
da kwarin guiwa Manubiya ta ce
“Su su uncle d’in wacce rawa suka taka tun daga haihuwarki har kawo yanzu da kike tunanin zamu bar su su yi miki auren dole?
ki kwantar da hankalinki kin ji ko!
InshaaAllah Yusuf sai dai ya ganki ya bari.’’
Ahankali Jidda
ta sake hugging d’in Manubiya tanajin wani kwanciyar hankali a cikin ranta, harga Allah bata son Ya Yusuf!
bata san ya za ta yi ba
Idan k’addarar Ubangiji ta sanya ya zamto mijin ta ba, da sauri a ranta tace ‘’ya Allah kar ka sa in auri ya Yusuf,alfarmar
annabi s.a.w’’.
Shiruu ta yi tana tunani
kafin ta d’ago ta gyara zamanta tukunna ta ce
‘’duk naga kin yi kalar gajiya
kin gaji sosai ko? bari in je in d’eba miki ruwan wanka, in d’aura
na fanfon ya d’auke’’.
Murmushin yak’e Manubiya ta yi kafin ta ce
‘’Mun riga mun tara ni da Muhsin kafin mu shigo,sai da ma muka d’aura a kitchen tukunna muka shigo nan, na san zuwa yanzu dai bai yi ba’’…
…Tun ranar da ta gan shi notunan kanta suka kwance, sanin da ta yi cewa sam shi d’in ba sa’an ta bane ba ta ko Ina
, hakan ya sanya ta yi wa kanta fad’a! sannan ta dage da addu’a da sallar dare da nafilfili….
Ta samu sauk’i kuwa!
sai dai kuma bata san k’addarar da ta kai ta gidan Ammi ba yau
ɗ
in gidan da tun da take a rayuwarta bata tab’a shiga ba!
Shin wacce irin kama
ce tsakanin Matar da ta tarar tana yi wa Ammi kitso da wannan bawan Allahn da ta gani a office d’in Sir Najeeb sati biyu baya da suka wuce?…
Tunda ta ga Matar kuma tashi d’aya sai tunanin Mutumin ya dawo mata sabo fil.
“Innalillahi wainna ilaihirrajiun!!
Ya Allah kar ka d’aura mini abun da zai zama ajalina, ya Hayyu ya Qayyom kar ka
ɗ
aura mini abunda ba zan iya ba’’.
Ta fad’a a chan k’asan ranta…..
Anya kuwa zata iya ci gaba da aikin gidan Ammi tana karo da wannan Fuskar kullum,dan ta lura matar kamar a
gidan take saboda
inda ace zuwa ta yi tou da da ta gama yi wa Ammin kitso da zata tafi amma sai ta ga ta kama wani aikin kuma na daban, babban tashin hankalita shine
kar ta je shima Mutumin a gidan ya ke!!!
Dan tabbas maybe in dai ba tsananin kamanni ba
to matar nan yayar sa ce. Ta san cewa Ammi d’a d’aya gare su ‘Al’ameen’ to kenan wannan mutumin y’an uwansu ne? da shi da yayar tasa a gidan suke kenan?
Inaa ba zata iya ba, saboda
gani d’aya ta yi masa lissafinta ya kwance shin ina kuma ga idan ta ci ga
ba da ganin shi kulliyaumin?……
‘’Adda Manu, ya kawo ruwan fa’’
Jidda wadda take ta faman yi mata magana bata kula ta ba tun dazu, ta fad’i hakan da d’an k’arfi.
A d’an firgice Manubiya ta yi firgigit ta d’ago tana kallon ta kafin ta samu da kyar ta had’i
ye wani abu wanda ya tokare mata mak’oshi tukunna a hankali tace’’Ok‘’.
kafin ta kalli Muhsin wanda ya dawo daga mik’a ruwan band’akin ta ce
‘’Na gode auta,bari in yi in rage maka’’.
Tana gama fad’in haka ta mik’e
ta d’auki abubuwan da zata buk’ata ta fad’
a band’akin. …
BULAMA ✍
️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*16*
Tana fitowa daga wanka,
aka aiko kiran su daga wajen Kaka Mallan.
Muhsin kawai suka bari a wajen Inna su duka suka d’unguma.
Uncle,Ya Yusuf,Baba Habu Anty U
mma sai Kaka Mallan suka tarar.
Ko gaisawa Uncle bai bari an yi ba dan yana lura babu Ya Musbah ya d’au waya ya hau kiransa yana mitar ‘ya an ce za’ayi meeting, amma an bar shi ya tafi,bai zo ba’.
Sai da aka jira ya zo ya fara bud’e taron da addu’a tuk
unna Uncle ya bari ma aka gaggaisa.
Ba tare da b’ata lokaci ba
Kaka Mallan wanda ya amsa gaisuwar su Baba da kyar ya kalli Baba ya ce
‘’Musa’’!
Sai da Baba ya lumshe Idanunsa ya bud’e tukunna ya ce ’’Na’am,Kaka.’’
Sai ya d’an nisa tukunna ya ce
‘’Dazu
d’an uwanka ya zo ya same ni akan batun Matar senator da y’ar wajen ka, an yi part 2 kenan?’’
Shiruu Baba ya yo kafin chan ya ce
‘’InshaaAllah hakan ba zata sake faruwa ba, na tsawatar mata’’.
Cikin d’an daka tsawa Kaka Mallan
ɗ
in ya ce
‘’Kai dallacha
n gafara, ka tsawatar kuma na yaushe, kwanakin baya ba an tsawatar matan ba amman ka ga alamun ta yi amfani da tsawatarwar?.
kuma tsabar cin fuska da rashin sanin ya kamata
MUSA, Yusuf fa da Mahaifinsa suna cikin gidan nan amman kuka barta take kula wani
‘Al’ameen’.
Dama na fahimce ka tun ba yau ba,komai naka daban yake…..
Duk wata hanyar da zaka bi ka salwantar da had’in kan zuri’ar nan tou ka sani, kai kenan ace komai naka a botsare? kuma duk in ka je ka dawo baka ganin dai-dai sam amma taurin kai ya ƙi
bari ka saduda?
Ka duba kaga yadda ka kafe akan kasuwanci kana ganin babu riba amma dukda haka sai da ka d’aura Musbahu akan kasuwancin shima, kana gani y’an uwanka suna karatu amma kai ka nacewa abu d’aya gashi yanzu a ta dalilin botsarancin ka kai da i
yalin naka gaba d’aya kun zama abun tausayi.”
Da sauri Manubiya ta mik’e ta juya za ta fita.
Cikin karsashi Kaka Mallan ya ce’’Wallahi zan ci ubanki, ni zaki mik’e ki fitarwa ina tsaka da magana, saboda na fad’i gaskiya?dawo ki zauna tun kafin in saka Yu
suf ya ladaftarmin da ke’’.
Ko gezau Manubiya bata yi ba,
bata fitan ba kuma bata koma ta zauna d’in ba, har sai da Ya Musbah ya daka mata tsawa ya ce ’’Wai ba da ke ake magana ba?’’Tukunna ta koma ta zauna tana ji kamar ta fashe tsabar takaici.
Baba,
K
aka Mallan ya kalla kafin ya ce
‘’Ka gani ko?
kalli ka ga!!
Wannan ƴar sai ta gagare ka wallahi’’
ya fad’i hakan yana nuna Manubiyan kafin ya d’aura da cewa
‘’Babu yadda ba a yi da kai akan ka aurar da ita ba amma ka nace akan karatun da aka kwad’aita mak
a tun