Showing 75001 words to 78000 words out of 150519 words
Tun Shekaran jiya Munirat ba ta fito ba,
kasancewar ta gama exams
ɗ
inta bata da abun yi da gurin zuwa ne ya sanya ko lek’owa bata yi..
abinci ma bata sauk’a ta ci kuma ko U
mmi ta kai mata ba iya cin mai nauyin take yi ba, sai dai ta yi y’ar kwalamar ta a fridge d’in Ummi ko kuma idan dare yayi sosai ta sakk’o ta dafa indomie ta ci ta koma.
Tun sassafe Yahanasu ta fita dan tana da client kasancewar ta independent lawyer,
ko
da ta gama abun da zata yi bata komo gida ba direct sai ta wuce gidan k’awarta.
Ya’isha itama tana so ta d’an yi wasu aiyyuka dan haka ta fita tare da Kausar domin ta rakata ta yi depending project d’inta daga nan, yayinda
Yasmin take da surgery itakam tu
n 6 ma ta fita.
Yusra da Yadira suma duk suna da exams d’in sassafe
Yadira ƴar level 1 ita kam biyu ne ma da ita safe da yamma….
Yassira itama tun sassafe ta fita aiki !
Dan haka gidan ya rage daga
Mommy sai Ummi Baaba Larai Yassir da Munirat.
Sai waja
jen 2 tukunna da kyar Munirat ta fito ta shiga taya Ummi aiki saboda yau Ummin za ta karb’a girki kuma ta na so ta burge Daddy domin ta samu su sake shiryawa da shi sosai.
Sai kusa da k’arfe 4 tukunna suka samu suka kammala,
kasancewar Munirat tana fas
hin Sallah ne ya sanya Ummi ta barta a kan ta jujjuye a flask ta kai side d’in Daddy ita kuma Ummin ta tafi yin sallah da wanka.
Cikin nutsuwa take juye abincin a cooler suna hira da gwaggo mai aiki dan su Husaina da Asabe y’an Matan (masu aikin) sun tafi
shirin islamiyya….
ji tayi kamar ana kallon ta dan haka ta d’an juya a hankali..
da sauri ta d’auke kanta ta juya ranta a d’an
ɓ
ace sai kuma ta ja kujera ta zauna
saboda riga da wando sai ƴar k’aramar hula ne a jikinta, wandon pencil kuma ya kama ta sosa
i,
sam bata yi tunanin anan yake ba ta d’auka a side d’in Yashjub yake, ta san kuma Ummi ma ta manta ne da bazata bar ta ta zauna a hakan ba…
babu abunda ya fi bata haushi irin yadda ya kafe ta da dara-daran idanuwansa yana k’are mata kallo..
‘’Ina wuni,
d’an albarka’’
Muryar Gwaggo ta katsewa Yassir da Munirat tunani…
a hankali ya k’araso cikin kitchen d’in yana mai cewa ‘’lafiya’’
yayinda idanunsa su ke yawo a jikin Munirat wadda ko kallon inda yake bata yi ba..
ganin da yayi bata da niyyar gaida shi ne
ya sanya shi ya gaida ita ta hanyar cewa’’Anty Munirat,Ina wuni.’’
Da mamaki ta d’ago manyan idanuwanta ta d’an kalle shi dan bata yi tunanin ya san sunanta ba,
sai kuma ta sunkuyar da kanta tace’’ina wuni’’a hankali.
Murmushi kawai yayi daga haka ya juy
a ya kalli gwaggwo ya ce ’’gyaran jiya bai fita ba fa, sannan kinsanni bana son white bedsheets, a cire a saka wani sannan a sake gyara d’akin.’’
Yana dire aya, da sauri gwaggo ta ce
‘’Yanzu kuwa d’an albarka.’’
Ta fad’i hakan tana mai ficewa daga kitche
n d’in, daga nan ta nufi sama d’akin nashi kusa da na Mommy, amma fa a ranta ta gama aiyyana yadda zata zaiyyanewa Munirat halayen Yasir, dan ba zata bari Yassir ya cuci y’ar marainiyar Alllah ba, sarai ta lura da yanayin kallon da yake yi mata!!
bayaga ti
jarar da y’an uwanshi suka yi mata shekaran jiya shine shima yake so zai d’aura mata da nashi kalar cin zalin.
Gwaggo tana fita Munirat ma ta mik’e zata fita, da sauri Yassir ya ce’’We haven’t met(ba mu samu
mun ha
ɗ
u sosai ba sai yanzu) sunana Yassir,3rd
born (
ɗ
a na uku) na wannan family d’in, I’m an architect
C.E.O
Yassir Limited’’
Ya fad’i hakan yana mik’o mata Hannunshi alamun su gaisa yana d’an murmushi.
Ba tare da ta kalle sa ba ta ce ’’nice to meet you(madalla da ha
ɗ
uwarmu)”
ta fad’i hakan tana k
’ok’arin wucewa
Da sauri ya sha gabanta yace
‘’Am..dama Ina so in baki hak’uri a kan abunda su Ya’isha suka yi miki the other day…’’
Cikin katse sa tace
‘’Dan Allah ya Yassir ka bar maganar, za mu yi resolving (sasanta) a tsakanin mu, girls(Mata).’’
Murmushi yayi yana yi mata wani irin kallo kafin kansa tsaye yace “you don’t like me,Y?
(Kamar kin tsaneni! Amma Maiyasa?
kar ki damu ki fad’a min ba zan ji haushi ba’’
Cikin k’aguwa tace “a gajiye nake, sannan Ina da damuwa, kai kuma ka zo kana ta magana
, bana son yawan magana.’’
A hankali yace
“Sorry dear!
Na fahimta, kuma ban ji haushi ba.’’
ya fad’a hakan yana mai matsawa sannan ya nuna mata hanya da hannunsa ya d’an rissinar da kai yana wani kalar murmushi.
Da sauri ta wuce ta fita tana waiwayen sa
kamar wanda akace zai biyo ta ya kama ta ne.
A Chan corridor ta lab’e sai da taga hawan shi sama da juice da cake da alamun su ya zo d’auka, tukunna ta fito ta koma
kitchen d’in ta k’arasa zuba abincin ta kai d’akin Daddy,bragowar kuma ta jere musu a k
an babban dining table d’in tukunna ta zuba nata ta ci a kitchen d’in dan sai yanzun ne yunwa ta fara kwak’ular ta saboda rabon ta da abinci mai nauyi tun shekaran jiya….
Gwaggo ta riga ta gama wanke wanke shiyasa itama tana gama ci ta shiga d’auraye plat
e d’in da ta b’ata.
Tana cikin wankewa
Ya’isha da Kausar suka shigo
suna hira…
ko kallon ta ba su yi ba haka suka ci gaba da hirar su kamar ba su ga mutum a kitchen d’in ba, suna hira suna shewa Kausar ta d’auko pizza a fridge ta sa a microwave ta d’auko
cake da drinks suka nufi d’an mini dining d’in da ke a cikin kitchen d’in suka zauna.
Su ne ya kamata su kula Munirat duba da abunda ya faru a tsakanin su tunda itace bak’uwa, sannan yanzu ma ita suka tarar a cikin kitchen d’in….Amma basu ko kalle ta ba.
.gudun magana ne ya sa har
Munirat ta juya za ta fita sai kuma ta koma inda su ke ta tsaya
tace
“Am..Ya’isha sannun ku da zuwa, dama tun jiya ina so mu yi magana, amma sai ban samu ganin ku ba sai yanzu…
dama a kan abunda ya faru ne, ku yi hak’uri mu fa
himci juna, a samu komai ya wuce.”
Dai-dai nan Kausar ta mik’e ta nufi microwave d’in da ta fara k’ara Ya’isha kuma ta d’auko wayarta ta hau daddannawa.
‘’Ya’isha’’
Munirat ta sake kiran sunanta tana mai k’ok’arin danne zuciyarta.
Ba tare da Ya’ishan t
a d’ago ta kalle ta ba ta ce “Ni fa, waya zan yi da boyfriend d’ina, so pls leave..dan na tabbata turare ko wankan da kika yi shekaran jiya bai gama barin jikinki ba!!
Najeeb is a very handsome and nice guy (Najeeb kyakkyawa ne kuma ya na da kirki) sannan
ina son shi, dan haka ban shirya bar miki shi ba…’’
Ya’isha ta fad’a mata hakan tana mai daddana wayarta
ba tare da ta kalli Munirat d’in ba, kamar ma ba da ita take maganar ba.
Dai-dai nan Kausar ta dawo da pizza ta ajjiye musu suka shiga ci.
Har Munir
at za ta ce wani abun
sai kuma ta juya kawai ta fita zuciyarta tana wani irin tafarfasa.
Tana fita Kausar ta kalli Ya’isha ta ce “na san ni cousin d’inku ce amman a yadda muka taso
Ni kamar sister nake a wajen su Yash da Yassir, sab’anin Munirat dan ha
ka ya kamata mu yi wa Ummi magana ta daina barin katuwar y’arta tana yi mana yawo tib’ir-tib’ir a gida, dan naga kamar ma tallar y’ar tata take yi.’’
Kausar ta k’arashe maganar cikin tsananin takaici tana addu’ar Allah yasa ba a yi
rashin sa’a Yashjub d’i
nta ya shigo by mistake ya ga Munirat a haka ba.
Murmushi Ya’isha ta yi cikin kamo hannun Kausar d’in tace’’
Kausar ki dena cewa ke cousin d’inmu ce saboda you are more than a sister ma to all of us, muna son ki muna k’aunar ki fiye da zaton ki,’’
cikin
sake ruk’o hannunta ta ce ‘’bara in baki misali,‘’
sannan ta d’aura da cewa “in da ace wata ce ta yi breaking heart d’in Yassir a tunanin ki ya za mu yi mata?
k’iri-k’iri kika ce bakya son Yassir on top of that kika ce Yashjub kike so amma mu ka goya miki
baya
ɗ
ari bisa
ɗ
ari ba tare da mun ji haushin ki ko mun tuhume ki ba dan haka dan Allah ki daina cewa ke cousin d’in mu ce,
ki yarda ki saka a ranki
You are part of this family and we love you,always &forever(kema ƴa ce kamar mu a cikin wannan Ahali n kum
a har abada muna sonki).
ita kuma wachchar ki bar ni da ita, zan san maganin ta soon, in dai ina numfashi sai ta bar gidan nan da k’afarta walllahi..d’azu ai Yasira ta turo message a group akan labarin da uwar tata ta bayar, kin gani?’’
Tab’e Baki kausar
ta yi sannan ta ce ’’eh!na gani,amman hakan ba zai chanja komai ba, dole sai ta bar gidan nan tunda babu gadon ubanta a ciki.’’
‘’Ita da uwarta’’
Ya’isha ta k’arashe mata maganar tata tana dariya.
Dariya duk suka yi kafin su ci gaba da cin abincinsu sun
a yi suna tattaunawa.
Duk yadda Munirat ta so ta hana kanta kuka sam sai ta kasa, tana fita hawaye suka fara tsiyaya daga idanuwanta.
Abun yayi mata ciwo sosai…
gashi Ummi tace kar ta sake mayar musu da magana, maimakon rikice tana so a ko da yaushe ta n
emi zaman lafiya da su..tana tafe tana hawaye a haka har ta k’arasa d’akin Ummi…
bata tarar da ita a d’akin ba dama abunda take so kenan
dan haka ta zaro akwati ta je d’akinta na b’angaren su ta jido kayanta ta had’a komai tana gama had’awa ta kira sister
d’inta ta ce mata “za ta zo ta yi mata kwana biyu…”
yayar tata tanata murna a haka suka yi sallama ta zauna zaman jiran Ummi ta samu ta yi mata sallama daga nan ta kama gaban ta..sai dai kuma Ummin tana zuwa tace bata san zance ba!!!
Ba yadda Munirat bat
a yi da ita ba amma Ummin ta hana ta tafiya, k’arshema sai ta rufe ta da fad’a, tana ji tana gani haka ta hak’ura ba dan ranta ya so ba…
….
Kamar kullum bayan sallar isha, sai da Ummi ta yi da gaske tukunna Munirat ta yarda ta bita suka sauk’a domin yin d
inner.
Dama sun san yau su Daddy suna da meeting, dan haka shi da Yassira da Yashjub basu zauna dinner ba.
A dining d’in suka tarar da kowa har Yahanasu…
a kusa da Mommy Ummi ta ja kujera ta zauna da murmushi a fuskarta tace ‘’Barka da dare Mommy’’
ba ya
bo ba fallasa da d’an murmushi a kan fuskar Mommyn ta ce’’Lafiya Ummi ya gida ?’’
‘’Alhamdulillah’’ta bata amsa daga nan Munirat ma ta gaida Mommy da Baaba Larai da Yahanasu kafin ta ja kujera ta zauna…
sai da ta zauna tukunna ta lura ashe opposite d’in Y
assir ta zauna,
ta so ta tashi amma kuma in ta tashi duk inda za ta koma to dole sai dai ta shiga tsakiyar su Kausar ne dan a rarrabe suka zazzauna, dan haka kawai sai ta hak’ura ta zauna.
Cikin girmamawa Yahanasu ta gaida Ummi ita kuma ta amsa mata da ku
lawa.
Tana shirin zuba abinci suka had’a ido da Yassir, a hankali ya d’an motsa bakinsa alamun ‘Hi’
D’auke kanta kawai ta yi ta ci gaba da zuba musu abinci itada Ummi.
Murmushi yayi kafin ya juya ya kalli Ummi ya ce “Ummi ina wuni’’
Da sauri Ya’isha da
Baaba Larai suka kalle sa, sai kuma suka d’auke Kai suna mamaki.
Cikin jin dad’i da murmushi
Ummin ta ce
‘’Lafiya Alhamdulillah,Yassir.”
Wata kalar dariya Yasmeen ta yi ciki-ciki kamar irin Mutum yana k’ok’arin gimtse dariyarsa d’innan amma kuma ta yad
da ta tabbatar da Ummin za ta ji.
Ta kuwa ji!
amma sai bata kulata ba, daga haka kowa ya shiga cin abincinsa.
Yassir ne ya fara mik’ewa yayi musu sai da safe yana ta satar kallon Munirat,
ita bata ma lura da shi ba amma Ya’isha da Yadira sun lura.
Yadir
a tana shirin mik’ewa
Ummi ta ce ‘’Yadira d’an zauna ina son magana da ku’’.
Kamar ba za ta zauna ba, sai kuma ta koma ta zauna ba tare da ta kalle ta ba, ta wani had’e rai ta d’auke Kai.
Kausar ko rabin abincinta bata ci ba bata da niyyar tashi da farko
amma tana jin Ummi ta ce ‘tana son magana da su’
Kawai sai ta mik’e ta wuce sama.
Shiruu Ummin ta yi, kamar ta ce kowa ya tafi kawai sai kuma ta fesar da numfashi kafin ta ce
‘’Ya’isha in kun hau sama sai ku gayawa Kausar da Yassira abunda na ce…’’
Daga
nan tiryan-tiryan
haka nan Ummi ta zaiyyano musu labarin senator da Munirat kamar yadda ta gayawa su Daddy kafin ta d’aura da cewa ‘’Munirat ba za ta tab’a auren shi ba, dan in da ace zan bari ta aure shi to da tun lokacin da ya dawo an d’aura musu aure,
ballantana kuma yanzu da yake a matsayin saurayin Yahanasu.’’
cikin lallami Ummi ta ce
“Dan Allah komai ya wuce, let bygones be bygones(a bar baya ya zamto baya).”
‘’Ummi komai ya riga ya wuce,
what more do you need from us(me kuma ki
Ke sake buƙata daga
garemu?)’’.
Yusra ta yi mata tambayar cikin tsare ta da Idanuwa.
Cikin rashin jin dad’i Ummi ta ce ’’Yusra zumunci da zaman lafiya nake so a tsakanina da ku, sannan a lokacin da Daddyn ku ya aure ni ya yi alk’awarin zai rik’e Munirat kamar y’ar cikinsa,
ya ce za ta ji dad’i a tsakanin ku…
zaman gidan nan ba zai tab’a yi mata dad’i ba indai kuna yi mata irin haka…
Ɗ
azu fa tarar da ita na yi ta had’a kayanta zata bar gidan nan, kinga ai hakan bai yi dai-dai ba, pls ku zauna lafiya, dukkanmu a k’ark’ashin mu
tum d’aya muke…
duniyar ma duka duka nawa take?d’an zama ne fa na k’anƙanin lokaci bayaga haka ma na tabbata nan da five years ba lalle a tarar da hatta Yadira a cikin gidan nan ba..
Ya’isha ki gayawa Kausar in kin hau sama ki yi mata bayanin da na yi mu
ku ita da Yasira tunda su ne ba….’’
Da k’arfi Ya’isha ta dire kofin juice d’in da ke Hannunta wanda hakan ya katsewa Ummi maganarta!
Allah ya so cup d’in unbreakable ne da tuni ya fashe saboda yadda ta wani buga shi.
Cikin tsananin b’acin rai ta mik’e ta
kalli Munirat wadda ta d’ago itama tana kallon ta, zuciya a wuya ta ce
‘’Dan girman Allah yadda kika had’a kayanki kar ki kwance ki kwashe su ki yi gaba yau! kar in sake ganin k’afarki anan.’’
Sannan ta juya ta kalli Ummi
tace’’Ummi do you know wat your
problem is?
(Ummi kin san menene matsalarki?)”
bata tsaya jin mai Ummin zata ce mata ba ta ce’’Son kai!.
son kai shine matsalar ki…
kalli yadda kika tisa mu a gaba kina mana maganar dole sai mun so y’arki!! dole sai mun yi zaman lafiya da ita, shin wai ana
dolene!??.
kuma na ga ita ta janyo komai tun asalin farko tunda tun da ta zo gidan nan babu wanda ya Kyamaceta
Despite the fact that
She’s not even our class but (dukda kuwa cewar ita
ɗ
in ba ajinmu bace ba amma) a hakan muka ja ta a jiki duk dan a zaun
a lafiya amma duk bataga wannan ba haka nan ta zo ta tafkawa Mutane shirme…
Kasancewar wani wai saurayintane tun farko ko ma mijinta ne tun farko hakan ba zai goge laifinta ba tunda ai dai yanzu Yahanasu ya zo zai aura
amma bataga wannan ba tsabar cin fus
ka haka ta biye masa..
Although (dukda)Yahanasun ta ce babu ruwanmu da case d’inta amma yadda ki ke supporting y’arki kike k’ok’arin goge laifinta k’arfi da yaji ni shine matsalata da ke!!!!!
sannan bari ki ji in gaya miki ni kam har abada i’ll never be f
riends with her (babu zaman lafiya tsakanina da ita) tunda na lura ba ki san mutunci,kawaici da arzik’i ba ke kawai naki kika sani, you are morethan selfish (kin fi son kai son kai) dan haka babu zaman lafiya a tsakani na da ke da y’arki har abada wallahi…
ba da irinku ake zaman lafiya ba dan naga idan aka baku fuska next time sai kun yi abunda ya fi wannan,
dan haka dole mu taka miki burki mu nuna miki matsayinki a cikin gidan nan tun yanzu,
ke ba kowa bace ba, you are just holding a place here(cike waje
kawai kike yi a cikin gidan n…..)’’
Cikin tsawa Ummi ta mik’e tsaye ta ce
‘’Ya’isha!!’’
Itama Ya’ishan cikin tsawar da ta fi ta Ummi ta ce
‘’Kar ki sake d’aga mini murya!!!
gaskiya ce dole in fad’eta.
kuma naga da farko ba ku san mu ba muma bamu san ku
ba amman ai mun rayu kuma kun