Showing 33001 words to 36000 words out of 150519 words
ce miki ba ni da kud’i
hidima kuma da kika gani ba ni
nake yi ba!
Ki yarda ko kar ki yarda wannan ba matsala ta bace ba.
Akwai kud’i a hannun ki na sani ba wai babu ba dan haka idan za ki yi hidimar gida dasu Bismillah…
Duk ranar da na samu zan maida miki,
Idan kuma za ki iya barin
ɗ
an da kika haifa a cikin
ki da yunwa saboda rashin sanin ciwon kai to shima Bismillah…
Sannan idan kinga ba zaki iya ci gaba da zaman ba
nan ma kin san mai za ki ce min inyi
ni kuma in sha Allahu zan yi miki yadda kike so’’
Cikin tsananin b’acin rai
ta ce
‘’Eh lalle Musbahu k
a yi arziƙi, ga alama nan na gani…ai dama ku Maza haka kuke, wato kud’i sun fara zama maka shine ni Baraka yau nice abar wulakantawa ko?
Ka barmu da yunwa ni da d’anka
ka dauko Babarka ka kawo aminity kuma na yi magana ka ce za ka sakeni
Saboda yanzu ka
san kana da kud’in da za ka yi wani auren idan na tafi ko …’’
Cikin katse ta ya ce
‘’Ba wai cewa na yi zan sake ki ba, cewa na yi idan kinga ba zaki iya zama ba to ki fad’i abun da yake ranki ni kuma in aiwatar.
Magana ta ta ƙarshe anan ‘ki yarda ko kar
ki yarda
Ba nine nake hidimar asibitin nan ba, saboda bani da shi.
Dan haka idan zan baki shawara ki d’auka to,
ki je ki siyo kayan abinci ku ci da ke da mai sunan Baba
kar ki damu da cikina
In sha Allah zan samu abun da zan ci, kuma duk lokacin da Alla
h ya bani kud’i zan mayar miki’…’’
Yana gama fad’in haka ya juya ya wuce ciki! Yana adduar Allah yasa Manubiya ba ta ji conversation d’in nasu ba dan shi sai yanzun ne ya lura da ita.
Takaici kamar ya kar Manubiya, sam bata yi niyyar kula Baraka ba, dan h
aka ta zo za ta wuceta da sauri ta na jin wani takaicin ta na musamman yana rufe ta!.
Ita kuma Baraka dai-dai ta juya dan haka suka yi kici
ɓ
us!!!…
Wani tsaki Baraka ta jaaa!
Kafin ta ce
‘’Ni kam wannan aure,
a cuce ka kuma ka yi magana aji haushi!
Sanna
n ga ido ta ko ina…’’
Har Manubiya ta
ɗ
an yi gaba
sai kuma ta juyo ta dawo ta sha gaban Baraka, ta tsaya.
Gyara tsayuwa kawai Baraka ta yi itama ta shiga watsa mata kallon wulaƙanci.
Cikin takaici Manubiya ta ce
‘’Wallahi kin bada Mata, ai ko kishi d
a rashin hankalin ma yanzu an daina yayin irin wannan.
Duk abubuwan da kike yi zuba miki ido kawai muka yi ba wai dan bamu san me kike yi ba ne
sai dan
a kullum adduar mu itace ki shiryu.
Haba Baraka
Mahaifiya fa?
Itace abar kishi?
Inda ace ma lafiyar
ta ƙalau tou da da sauk’i
amman bata fa da lafiya, a kwance take, a gani na idan baki taimako ba to bai kamata ki d’agawa kowa hankali ba.
Kaico!!Wallahi Ya Musbah bai yi sa’ar Mace ba.’’
Yadda Baraka ta zazzaro Idanuwa waje duk wanda yagansu a wajen zai
yi zaton daddanawa Iyayenta zagi Manubiya ta yi…
Ta san dama Manubiya bata da hak’uri amman bata tab’a tunanin zata iya gaggaya mata magana har haka ba.
Tijara da Zuciya da suka ciyota ne suka sanyata ta figo Hannun Manubiya da dukkannin k’arfin da Allah
ya bata suka yi ciki tare.
Tun daga bakin k’ofa ake kallon su, ga security ya biyo su yanata faman yi wa Baraka magana
Yana cewa “ta sakar mata Hannu”
amman sam Baraka bata da niyyar sauraren sa,
ita kuma Manubiya taso yin tirjiya ko kuma ta fisge Hannu
n nata amman kuma a ranta sai ta ce ‘bara kawai ta barta’ gudun kar su yi kokawa ta sake tada wani case d’in a tsakiyar asibitin..
Ta fahimci d’akin da Inna take take shirin kaita shiyasa ta gama rayawa a ranta ‘suna shiga d’akin in ta cika ta ita kuma za
ta fice ta barta’ dan ta lura burin Baraka tabbas bai wuce ta ga gawar Inna ba…
Da k’arfi ta tura k’ofar suka shiga tare ita da Manubiyan.
Da sauri su Jidda su ka mik’e tsaye saboda a yadda Baraka ta shigo kamar wata mahaukaciya sun yi zaton wani gagarumi
n abu ne ya faru.
Duk yadda Manubiya ta so ta cika mata Hannun sai ta kiya,
ta rik’eta gam!
Sai a sannan Manubiya ta yi dana sanin k’in kwace Hannunta tun a waje su yi ta ta k’are dan tana shigowa d’akin da Inna ta fara tozali ta bud’e idanuwanta sab’anin
ɗ
azu da ta barta tana bacci.
Da kyar Ya Musbah ya samu ya had’iye wani k’ululun takaici wanda ya tokare masa maƙoshi tukunna ya k’arasa wajen su.
Ba tare da ya kalli Baraka ba ya cewa Manubiya
‘’D’auki jakarki ki wuce gida’’
Dan ya fahimci akan maganar
da Manubiyan ta ji suna yi ne shi da Baraka, ta yi wa
Barakan magana
shine ita kuma ta janyo ta nan domin ta d’agawa Inna hankali.
Cikin d’aga murya, hargowa da hayagaga Baraka ta ce
‘‘Ka san me ta yi mini ne
da za ka ce ta tafi haka kawai,
wato ta zag
i banza ma kenan ko?.
Allah na tuba in banda k’addarar aure da ta kanainaye ni a gidanka
Manubiya ta isa ta taka inda na taka?
Ballantana har ta kalle ni ta fad’a min maganar banza?
A hankali Ya Musbah ya lumshe Idanuwansa waenda su ka yi jazirrr!! Kafi
n ya bud’e su ya zubawa Baraka ya ce
‘’Baraka saki Hannun Manubiya ta wuce gida.
Zan yi mata magana.’’
Cikin gurb’atacciyar Hausa security d’in da ya biyosu shima ya matso ya ce
‘’Madam, cika mishi Hannu, ki bar fad’a, ba’a hayaniya, kalle patient fa”
Y
a yi maganar yana nuna Inna wadda ta kafesu da Idanuwa.
A hankali Ya Musbah wanda ya ke ji kamar ya nutse a cikin ƙasa ya
ɗ
an waiga ya kalli Innar
kafin ya juya da
ɗ
an zafi ya ce
‘’Baraka ki sake ta, ta wuce nace, ko?’’
Cikin tsananin tsiwa rashin kun
ya sannan da ƙarfi ta ce
‘’Kaga rufe Bakinka, tunda ba za ka yi adalci ba!
Ƙ
anwarka ta zage ta zuba mini rashin kunya sannan ko bin ba’asi ma baka yi ba kace kawai in cika ta ta tafi?
wato ban isa bama kenan ko?
To Bari ka ji
bayan cin kashin da kake yi
mini da azabtar dani
ɗ
in da kake yi wallahi ban shirya sake d’aukar rashin kunyar k’annenka ba, dan haka ba zan cika ta ba kuma sai ta bani hak’uri yanzu ba sai anjima ba sannan ka kora mata zazzafan warning idan kuma ba haka ba to wallahi sai mun kwashi
y’an kallo ni da ita’’
Da mamaki Manubiya ta ke kallon Baraka…
ba abunda ya fi bata mamaki irin yadda Barakar ta ke ihu bayan ga Inna a kwance sannan ta bi ta wani dage akan wai an yi mata rashin kunya
bayan ita Manubiyan ta bata wata biyu a duniya!
Yanz
u haka ita ta cika shekaru ashirin da biyu
ita kuma Barakar sai watan gobe….
Security ya yunk’uro kenan zai yi magana
Maman Abbakar ta mik’e ta ce masa
‘’Yi hak’uri, je ka.
Za su yi shiru, bara in yi musu magana’’
Ba dan ya so ba ya juya ya fita dan
ya k’ule sosai da Baraka.
Yana fita Baba yana shigowa rik’e da Hannun takwaransa, Muhsin na biye a bayan su.
Dama tun kafin ya k’arasa ya ke jiyo hayaniya gashi kuma ya tadda su cirko-cirko
dan haka ya hau tambayar su ko lafiya….
Maman Abbakar ce ta ce
‘’Tou Baba Musa, ka san dai Manu da Baki da kuma rashin kunya!
To inaga yau abun nata ya biyo ta kan yayar tata ne,
dan gashi har janyo ta ta yi ta kawo k’ara shi kuma Musbahu ya ma k’i ya bari a yi maganar, sai cewa yake ta yi Manubiya ta wuce ta tafi k
awai zai yi mata magana’’.
A cikin ransa Baba ya shiga karanto sunayen Allah.
Tsit haka d’akin ya d’auka.
Sai da Baba ya ji ya d’an dedeta tukunna
Ya ce
‘’Musbahu ya ce Manubiya ta tafi za su yi magana saboda nan d’in d’akin mai jinya ne wadda take fa
ma da kumburin zuciya, hawan jin, k’oda da kuma mutuwar b’arin jiki.
Ina fatan kun fahimci dalilin da ya sanya ba ya so a yi wata rigimar a gaban Idanunta kar ku yi masa mummunar fahimta,
ba wai son kai yake shirin gwadawa ba ….’’
A hankali
ya juya ya ka
lli Baraka tukunna ya ce
‘’Me kike so Manubiya ta yi miki yanzu?’’
A hankali ta sunkuyar da kanta ta cika Hannun Manubiya tukunna ta ce
‘’Baba ta bani hak’uri, karta sake kuma’’
‘’InshaaAllah” Baban ya ce
Sannan ya juya ga Manubiya har
Idanuwansa sun
yi jajir suna kyalli tsabar
ɓ
acin rai,
zai yi magana da sauri Manubiyan ta ce
‘’Ki yi hak’uri, sharrin Zuciya ne, ba zan sake ba, inshaaAllah’’
Ajiyar zuciya Maman Baraka ta sauk’e sannan ta mik’e,
Baba kawai ta cewa
‘’Allah ya k’ara sauk’i’’ daganan
ta taho kamar zata bangaje Manubiya
ganin haka yasa tayi sauri ta matsa
Itakuma ta bud’e k’ofar ta fice.
Baraka ma Hannun Baba k’arami kawai ta kama suka fita bata cewa kowa uffan ba.
Maman Abbakar ce ta d’an tsaya ta yi musu sallama daga nan ta saka kai
ta fice
Jidda da Baba suna masu ce mata sun gode.
A hankali Baba ya ga wasu hawaye suna tsilalalowa Inna ta ido d’aya
da sauri ya k’arasa ya sunkuya dai dai fuskarta ya shiga share mata hawayen nata yana girgiza mata kai alamun ta yi shiru….
Sun jima
a haka kafin
ba tare da ya juyo ba
ya ce
‘’Manubiya ki kwashi duk Kayanki da suke anan,
Ki wuce gida.’’
Fashewa ta yi da kuka
Cikin kukan ta ce
‘’Baba dan Allah ka yi hak’uri,
wallahi ban yi tunanin Baraka za ta yi haka ba’’
Still bai d’ago ya kal
le ta ba
ya ce
‘’Ni kuma ban yi tunanin har yanzu ba ki yi hankali ba, ban yi tunanin har yanzu ba za ki iya barin abu d’an k’ank’ani ya wuce ba tare da kin yi magana ba’’
Cikin fushi Ya Musbah ya ce
‘’Ko ma menene ki ka ji tsakanina ne ni da ita!
Dan
mai yasa za ki shiga ciki har ki yi mata magana?”
A hankali tana kuka ta ce
‘’ku yi hak’uri’’
Ya d’an jima yana kallon ta kafin ya ce
‘’Ki kwashe Kayanki ki wuce gida, ki je ki fara karatu
Jidda za ta ci gaba da zama anan,
Ke kuma kya dinga yin girki
daga gida.’’
Za ta yi magana
ya ce
‘’Manubiya ki je a ka ce ko?’’
A hankali ta d’aga kanta alamun ‘to’ tukunna ta k’arasa ta je ta shiga had’a kayanta, har ta gama bata yarda ta d’ago sun had’a ido da Inna ba
dan ta san ita take kallo,
sai da ta zo ta
fiya tukunna ta je ta rungumeta ta ce’’Inna Allah ya baki lafiya’’
Still bata yarda ta kalle ta ba.
Daganan ta yi wa su Jidda sallama, Baba ya bata kudi’n mota ta sa kai ta fita.
Ya Musbah ji yake kamar ya fashe da kuka, tabbas Baraka ta kai shi bango!!!
k’iri-k’iri duba fa yadda ta disga shi ta wulak’anta shi a gaban jama’a harda wani cewa ‘k’addarar aure’!!
babban takaicin sa shine idan ya d’au mataki a wannan ga
ɓ
ar ya san sai ya had’u da fushin Baba saboda cewa zai yi dan mai yasa zai biye mata a case d
’in da ya had’a da su Manubiya, tunda wani abun yana faruwa kowa cewa zai yi ya bi bayan k’anwarsa sam baza’a duba rashin d’a ‘a da furucin da ta yi a gaban iyayensa ba……….
…
Chaaan yamma.
Jidda na zaune ita kad’ai gashi lokacin zuwan Al’ameen ya yi
ta r
asa yadda za ta yi ta fita.
Sai da Innar ta yi bacci tukunna ta samu ta fita, tana ta sauri.
A cikin mota ta same shi yana ta jiran ta
Ba tare da b’ata lokaci ba ta ce ‘’ya zo su je d’akin,
Adda Manu bata nan yau, ta bar Inna ita kad’ai’’
Murmushi y
ayi
Daganan ya fito suka jera suka nufi d’akin gwanin ban sha’awa.
Sun jima kuwa suna hira,
tukunna ya yi mata sallama ya wuce.
Allah da ya taimaki Jidda sam Ya Yusuf bai had’u da Al’ameen ba dan tana dawowa daga raka Al’ameen d’in ta tarar da shi a d’a
kin,
ko waye ma yayi masa kwatance, sai Allah .
Tunda ta shigo ta gan sa sai ta tamke fuska, daga gaisuwa bata yarda sun yi wata hirar kirki ba.
Ita sai da ya fad’a mata ma tukunna ta gane wai ashe fushi ya yi tun ranar da ta gudu
shiyasa shi kuma ya ƙi
zuwa ya duba Innar sai yanzu….
Ganin dai duk yadda ya yi fad’a, fushi da rarrashi sam ya gagara samun fuska a wajen Jiddan ne ya sanya kawai ya tashi ya tafi dan ya riga ya gama tsara yadda zai yi da ita next tunda ya lura bata san a bita ta sauk’i ba.
Katamau!! Haka shima ya wani tamke fuskar nan tukunna ya fice bayan ya ajjiye musu dubu d’aya akan gadon, wai su sayi abun da basu da shi…..
BULAMA ✍
️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*10*
Ko da Baba ya koma gida da daddar
e sai da Manubiya ta sake roƙon sa akan ‘ya barta ta je asibitin washegari’ amman furr ya
ƙ
i amincewa illa ya ce mata’’ta yi karatu ta dinga zuwa makaranta akai-akai” kawai.
Da asubah ta tashi ta shirya musu breakfast, har lunch, ta cewa Muhsin “ya d’uma
ma miyar idan an zo kaiwa” daganan ta wuce makaranta saboda tana so su yi karatu da Abbakar yau sosai, gashi lecture
ɗ
in Sir Najeeb gare su da sassafe shiyasa take ta sauri saboda ta san baya bari a shiga muddin ya riga ya shiga.
Duk saurinta kuwa sai da
ta yi
rashin sa’a, dan ta na karya kwanar inda k’ofar tafkeken hall d’in ya ke ta hangoshi yana shiga dan haka ta k’ara sauri amma dukda hakan kafin ma ta k’arasa bakin k’ofar har ya rufe.
Haka nan ita da ragowar d’aliban da suka yi letti suka ja suka ts
aya a bakin k’ofar hall d’in dan waatak’ila idan sun ci sa’ar shi
In ya fito ya karb’a sunayen su da Matrc number
ɗ
insu ya raba musu ko da half half maki ne.
3 hours ne lecture d’in kuma Sir Najeeb d’an ƙa’ida ne shiyasa sai da ya cike 3 hours d’in sa tsa
f tukunna ya fito.
Bai yi musu kamar yadda suka yi zato ba dan kamar ma ransa a b’ace yake lokacin da ya fito d’in dan ya had’e girar sama da ta k’asa fuskar nan tamau!!! Kamar bai tab’a dariya ba,
shiyasa kowa a wajen ya sha jinin Jikinsa.
Ko da wani a
cikin su ya je yana k’ok’arin gaya masa uzurin sa
ma, a take ya daka masa tsawar da ta ƙarasa ru
ɗ
a su!
Dan haka duk sai suka ƙarasa rikicewa, kowa kuma ya jaa ya yi tsit suna ganin sa ya wuce ya tunkari parking lot.
Har ya nufi inda ya yi parking motars
a, sai kuma ya juyo, dan in dai ba gizo ta yi masa ba tou Yarinyar da yake nema ya hango a cikin dandazon ƴan letti.
Ya na juyawa kuwa su ka yi ido biyu shi da ita dan itanma bayansa ta raka da harara saboda ba kad’an ba ta ji haushin tsawar da ya dakawa w
annan wanda ya zo zai ba sa uzuri, sosai.
Da sauri Manubiya ta sunkuyar da kanta ƙasa tana adduar Allah ya sa bai fahimci hararar sa take yi ba.
‘’Manubiya Musa, follow me’’
Ya fa
ɗ
a ba tare da ya damu ta ji ko bata ji ba, haka kawai ya sa Kai ya wuce ya
shiga motarsa ya jaa ya nufi building d’in da office d’insa yake, a nan cikin BUK
ɗ
in.
Bata ji d’in ba kuwa, ragowar Mutanen da suke wajen ne suka ce mata ‘’ya ce ta bi sa’’.
Dan haka hankalinta ya gama tashi a take saboda laifi a makaranta wanda zai janyo
su Baba su sake yin fushi da ita is the last thing da take tunanin za ta yi involving kanta a ciki.’’
A take ta gama yanke shawarar tana zuwa zata durk’usa ta basa hak’uri sannan ta ce masa
Itafa haka Idanuwanta suke, ya yi hak’uri ba hararar sa take yi
ba.
Tana shirin barin wajen Abbakar na fitowa daga cikin hall
ɗ
in, kana ganinta ka san a rikice take, a haka ta k’arasa kusa da Abbakar