Showing 123001 words to 126000 words out of 150519 words

Chapter 42 - Mannubiya Complete

ya kasance shiruu kowa da abunda yake tun

ani har aka yi dinner aka watse babu Yashjub babu alamar sa.

Zuwa wannan lokacin Daddy ya sauk’o daga duk wani fushin da yayi da Yashjub!

dan duk hankalinsa ya tashi,

shiyasa ya yanke shawarar idan k’arfe goma ta yi Yash bai dawoba tou zai kira y’an sa

nda da sojoji su saka Hannu a nemo masa d’anshi.

Tunda sukayi dinner kowa ya bar dining ya koma cikin parlourn ya zauna….

In banda safa da marwa ba abunda Ddaddy ya ke yi, a kallo d’aya ake iya hango tsantsar damuwa da tashin hankali kwance akan fuskars

a, ya kasa tsaye ya kasa zaune…tabbas yau ya sake tabbatarwa Yashjub shine rayuwarsa.

*MANNUBIYA*

*42*

Tun asalin farko baya k’aunar ganin fushi ko b’acin ransa wannan dalili ya sanya hajiya Mama ta d’auke shi ta maida shi gabanta dan ta

ce ‘muddin ta bar masa shi a yadda yake tsananin son nan nashi to ba zai iya yi masa tarbiyya mai kyau ba.’

Daddy ya kasance Mutum mai tsananin k’aunar ya’yanshi amma son da yake yi wa Yashjub wani irin so ne na daban wanda bai tab’a jin kwatankwacin kal

ar son akan kowa ba bayan uwar da ta haifesa sai ga Khadijah mahaifiyar Yahanasu.

Bayaso ya yarda da cewa ya fi son Yash dan baya son ya samu banbanci a tsakanin Ƴaƴan nasa amma yau kam ya yarda ya tabbatar, dan gashi kwata-kwata ko awanni 12 ba ayi ba am

ma rashin sanin inda Yash

ɗ

in ya ke yana neman haukatasa, ji yake yi kamar ya d’aga Hannu ya zunduma ihu.

Gashi dai laifi ya yi masa amma

zuwa wannan lokacin har laifin ya gogu a idanun Daddy…..kawai shi matsalar da ke a gabansa a halinda ake ciki itace

ya san inda Yashjub d’in yake da lafiyar sa.

Gashi ya kira gidan su Najeeb shima ance bai Isa gida ba kuma duk wayoyinsu a kashe, hakan ya sanya tashin hankalin nasa ya sake hauhawa.

Mommy kuwa za’a iya cewa tashin hankalin nata ya kusan k’etare na Dad

dy dan dai kawai ita

ɗ

in tana iya danne nata ne.

Babban tashin hankalinta shine ‘wannan Yarinyar da ko sunanta basu saniba ballantana su samu su fara bi takanta, dan indai har ita ce ta kira Yash ta sanya shi ya yi wannnan dogon zango haka to kuwa sunada b

abbar matsala, dan haka abar a fara bi takanta tun da wuri.

Kausar itama daurewa kawai ta ke yi amma had’iyar zuciya ne kawai ya rage batayi ba….

basu riga sun gama tabbatarwa ba amma tabbas in dai maganar Baba Larai ta zamto gaskiya ce! To wallahi sai t

a nemo yarinyar nan a duk inda ta ke ta halaka ta!

Bata da wani za

ɓ

in da ya wuce ta kaita lahira dan ba a halicci Macen da ta Isa ta shiga zuciyar Yashjub ba wallahi!

Ko ta shiga sai ta fito…..

A b’angaren Yassir kuwa,

ba k’aramin sake hawa ya yi ba, ya

dda hankalin Daddy ya tashi ne ya fi komai d’aga masa nashi hankalin….duba da yadda laifi fa Yashjub d’in yayi fushi ya kamata ace Daddyn yayi da shi

amman ya b’ige da damuwa akan rashin sanin inda yake sai kace wani jinjiri.

Zuwa wannan lokacin shi kam b

a ya buk’atar wasu shaidun da za su sake tabbatar masa da ‘Yashjub na musamman ne a cikin gidan nan’ dan ya riga ya yarda sannan ya aminta da hakan….

Ya tabbatar inda ace shine ya b’ace haka to da babu wanda zai damu..kwanakin da suka shu

ɗ

e lokacin da ya

yi fushi ya tafi, Daddy bai san inda yake ba amma bai damu ba!

haka aka share kwanaki ko neman sa bai yi ba, kuma bashi da niyyar neman nasa….

Inaa, gaskiya da sake! dan ba zai yiu a dake shi sannan a hana shi kuka ba..ba zai kuma yiu ace uwa d’aya uba d’

aya su haifesu ba amma ace ya fi shi fada !kud’i!farin jini!jama’a!ilimi

sannan ya d’auke soyayyar iyayen su…ya zama dole ya gyara hakan, in kuma ba zai gyaru ba to dole ya bi ta ko wacce hanya ce yayi maganin wannan matsalar tun kafin bak’in ciki ya kas

he sa!!

Dan shi kad’ai ya san me yake ji a cikin zuciyarsa…a halinda ake ciki k’ok’ari kawai yake yi yana danne kansa amma ji yake yi kamar ya had’a Daddy da Yashjub d’in ya saka musu bomb!! Musamman ma da ya tuno da abunda Kausar ta gaya masa ‘’ace wai Ya

shjub yanada 50% (kaso hamsin) shi kuma wai 1 %’’

wannan rashin adalcin har Ina haka!?.

••••••

A chan b’angaren su Manubiya kuwa, tun tafiyar Baraka…

tsabar b’acin rai tsakanin Aisha Jidda da Manubiya babu wadda ta iya cewa komai, ko abincin da Aishar ma t

a kawo duk kasa ci suka yi.

Inna kuwa ta lumshe idanuwanta kawai dan bata so ta bud’e hawaye su fito ta sake d’aga musu hankali, shiyasa kawai ta lumshe idanun nata ta yi shiruu iskar fiffitar da suke yi mata su duka ukun tana ratsata.



Suna a zaune Y

a Musbah ya shigo,

shi da mai sunan baba wanda yaketa faman zabga ihu da shure-shuren shi sai ya bi mamansa….

Ganin khairat abokiyar wasan shi ne ya d’an rage zafin abun, kafin dare sharr Yaron ya sake ya shiga mutane yanata wasa.

Ba su dad’e sosai ba

, ya Nafi’u ya zo, dan haka gaba d’ayansu suka nufi gida bayan ya Nafi’u ya sanya su Manubiya sun yi mishi alk’awarin ba za su gayawa Baba komai game da zancen Baraka ba tukunna.

A ranar Baba ya ga gata,

har da kwallar farinciki sai da yayi.

Kamar koma

i bai faru ba

haka suka zauna har Ya Nafi’u da Aisha aka sha hira,

aka

ɗ

an kwantarwa da juna hankali.

Sun jima tukunna Ya Nafi’u da Aisha tare da khairat suka yi shirin tafiya, dan haka Baba ya cewa Ya Musbah shima ya tashi ya bisu kar a bar Baraka ita k

ad’ai.

Da “to” ya amsa shi, daganan ya yi musu sallama suma suka fice shi da mai sunan baba.

Su Ya Musbah suna fita su Jidda suka sanarwa Baba

‘ai d’azu ma Siyama ta kira, lokacin suna asibiti, wai mamanta ba lafiya, shiyasa ma bata je ba.’’

Ba tare da b

’ata lokaci ba ya ce musu

“su mik’e su je su dubota,

ai da sun fad’a tun d’azu, Allah yasa su Siyaman ba su riga sun yi bacci ba.’’

Da “to” suka amsa, daga haka suka fita….bayan fitar tasu ne Baba ya matsa kusa da Inna…

duk abinda ya faru yau ba abunda y

a b’oye mata, saboda yanaso ta sani domin ta fahimce sa kuma ta goya masa baya akan aurar da su Jidda da yake shirin yi cikin gaggawa.

Yaga alamar amincewa kuwa a fuskarta dan har lumshe masa idanuwa ta yi ta bud’e, dan haka ya sake jin dad’i ya kuma samu

kwarin guiwa….hakanan yayi ta mata magana dukda ya san ba za ta mayar masa ba amma ya san tana sauraronshi, kuma ta fahimcesa.

Jikin anty Umma kam ba sauk’i sam, sannan har gara Baba ma shi an samu an kaishi asibiti

Ita kuwa ko asibitin ma ba a samu me

kaita ba.

Siyaman ce take gayawa su Jidda cewa “babu wanda ban kira a cikin manyan gidan nan ba, amman kowa sai dai yace min ba shi da ko sisi.

Uncle shi kam ma rufe ni yayi da fad’a!

wai yanzu Ya Musbah ya kira shi, ya tura masa kud’i shine nima zan kum

a kira…

gaskiya shi fa an saka mishi ido!Ɗan shige da ficen da aka ga yanayi shine ake ganin kamr wani k’arfi ne da shi. Daga yau in dai na san maganar kud’i ne tou kar ma in sake kiranshi yana wajen aiki, shima bashida shi…’’

Muryarta ce ta katse ta dali

lin kukan da ya taho mata.

Cikin kulawa Manubiya ta shiga rarrashinta tana bata Baki…..

duk da damuwar da su Manubiya suke a ciki basu yarda sun bar parlourn ba sai da suka d’an kwantarwa da y’ar uwar tasu hankali, suka ga ta d’an ware, tukunna suka yi w

a anty umma ‘Allah ya k’ara sauk’i’

suka mik’e za su tafi.

Mik’ewa itama Siyaman ta yi ta cewa Umman nata “bari in d’an raka su’’

‘’To’’

kawai anty Umman tace daga haka ta yi musu sai da safe tace su gaida Baba.

Suna fita Siyaman ta ce

“Manu, akwai

abunda nake so in gaya muku, kar ku ji a Bakin wani gara ku ji a Bakina’’.

Tsayawa su ka yi duk suna kallonta, dama sun lura kamar akwai

abunda take son fad’a!

Anty Umma kuma sai gargad’i take ta yi mata da ido.

Cikin sanyin jiki Siyaman ta sanar musu

’ashe Suraj..wanda zai aureta ne ya fasa. wai akan an zab’a masa y’ar uwarsa…

shine ma dalilin da ya sanya Anty Umma ta d’aga hankalinta har ta kwanta rashin lafiya.’

Tausayin ta ne ya lullub’e Manu

dan haka sai tama kasa cewa komai.

Jidda ce ta iya ce

wa ‘’Siyama dan Allah ki kwantar da hankalinki kema karki wani d’aga hankalinki.

InshaaAllah hakan shine mafi alkhairi,

Allah ya riga ya rubuta dama ba mijinki baneba, inshaaAllah shi zai baki wanda ya fi shi.”

Ajiyar zuciya Siyama ta sauk’e kafin ta ce

‘’Jidda sam ban d’aga hankalina ba wallahi ni kaina ina mamakin yadda abun bai wani dameni sosai ba, amma yadda Umma take yi ne bana so, sannan Itafa har yanzu ta ƙi ta hak’ura, shiyasa ma kika ji bata gayawa kowa ba, ni kuma na riga na san tunda har suka

ce sun fasa to sun fasa d’in kenan saboda matsalar daga b’angaren mahaifinsa ne fa tun da y’ar k’anwar mahaifin nasa aka basa ashe shiyasa suke ta ja mana rai wajen kawo kaya su ce yau su ce gobe.

Amman wai duk da wannan abunda suka yi wa mutane in kika ga

yadda Umma take waya da mahaifiyarsa tana wani lallab’a ta abun sai ya b’ata miki rai, sai kace irin ana neman kai da ni

ɗ

innan….

Da ya ke itama mahaifiyar tasa ba so take ya auri ita wachchar Yarinyar ba.’’

‘’Haka iyaye mata suke Siyama,

gani takeyi ka

mar za ki shiga damuwa…

Duk abunda za ki ga ta yi domin ke ne take yinsa”

cewar Manubiya wadda gaba d’aya jikinta yayi sanyi.

Cikin sanyin murya Siyama ta ce

“da wannan kam gaskiya, sannan kuma na lura kamar tana so ma ta nunawa kaka mallan iyakar sa,

a n

awa tunanin kenan. saboda kin san ai ya yi wa makwaftanmu magana akan karb’ar kaya, tou yanzu duk ya je yanata yayatawa wai an fasa auren nawa…

A bakin yayata fa da take aure a illorin mukaji, wai wata makwafciyar mu anan ta kirata takanas dan ta tabbatar

, kinga kuwa ai ya gama yayatawa kenan. Amma dukda haka ni ban san me yasa Umma ta ji haushi ba, dukda a yanayin da yaketa sanarwar bai dace ba amman kuma ni a ganina gara ma a sani tun wuri,

tunda dole dai za’a fasa d’in, kuma kowa zai ji.’’

Ajiyar zuciy

a ta sauk’e cikin son kawo k’arshen zancen ta ce

‘’ko ma dai menene…

mai faruwa ta riga ta faru.

Ni kuma Ko ba komai yanzu da na yi muku maganar na d’an samu sauƙin abun wallahi’’.

Murmushi Manu ta yi kafin ta ce

‘’Siyama ai iyayenmu ne basu gane haka

n ba tun wuri,

zaman tare dole akwai sab’ani wasu lokutan ma har da rashin fahimtar juna amma muddin aka ce akwai had’in kai a tsakani to sai ki ga an dace’’

Da sauri Siyama ta ce

‘’Wallahi Manu rashin had’in kan y’an gidan nan namu nima yana damuna, har

gwara ma ku ku biyu ne

Ni fa?

Wani zubin fa idan aka k’unsa mana sai dai mu zauna Umma tana kuka nima ina taya ta, babu mai rarrashinmu’’.

Murmushi Jidda ta yi daga haka ta kamo Hannun Siyama tukunna ta ce ’’rashin had’in Kai wannan zab’in iyaye da yay

yen mu ne. amman mu za mu iya gyarawa, ko da a tsakanin mu ne, wanchan tsarin su ne dan haka inaga muma za mu iya shimfid’a namu tsarin!

watak’il idan suka ga ribar had’in kan a tsakanin mu suma su gyara….

kasancewarsu manya ba shine zai sanya ace

duk ab

unda suka yi shine daidai kuma muma sai mun bi ba’’

Murmushi Siyama ta yi kafin ta ce “tabbas Jidda maganarki hakan take.

Tun tasowata bani da burin da ya wuce inga mun had’a kai ni da y’an uwana, amma kash!

Ɓ

angaren Mahaifina sun fi nan gwanancewa a fa

nnin rashin ha

ɗ

in dan su kam zan iya cewa da su gara babu ma, tou nan d’in ma dande kawai muna zaune a waje d’aya ne Ina ganin ku Ina jin sauk’i amma ta fannnin had’in kai kam duk sammakal….

Na cire rai da gyaruwar al’amura a tsakanina da

ɓ

angaren Babana a

mman nan kam dama Ina saka ran dacewa.

Na ji dad’in wannan goyon bayan dana samu daga gareku y’an uwana, Ina rokon Allah Ubangiji ya dafa mana ya bamu ikon gyara zumuncin mu.’’

Ta k’arashe maganar tata tana mai rungumo su gaba d’aya…..



Siyama ta yi waec,

takardarta ce dai batayi wani kyau ba, ta ji kwad’ayin inama ace itama itace zata zana post utme jibi

kamar Jidda, dan haka suka k’ara k’arfafa mata guiwa akan ‘ta sake yin waec, ta yi jamb ta koma makaranta…’

Idan Allah ya kawo aure ta yi in kuma bai zo

ba ta maida hankali akan karatu da gina rayuwarta, kar ta bari wani chan Suraj dashi ya saka mata damuwa.’

Sun tab’a hira, tare da shawarwari a tsakanin su sosai. kafin suka yi mata sallama suka wuce d’akinsu itama ta koma fanninsu.

•••

K’arar zuge gate

tare da parking d’in motar Yashjub ne ya katsewa kowa tunani.

A kurkusa ya yi parking d’in shiyasa har ya samu damar shigowa kafin Daddy wanda ya nufi k’ofa kamar wani zararre ya Ida fita.

A bakin k’ofar suka yi karo da shi da Daddyn wanda ya sauk’e wata

nannuyar ajiyar zuciya sakamokon ganin Yashjub d’in da yayi a kan ƙafafunsa lafiya lau.

Cikin kwantar da murya Yashjub ya d’an yi kalar tausayi ya ce

‘’Daddy I’m so sorry, dan Allah ka yi hak’uri…

Tun 5 lokacin da ka kira Najeeb muka fito, to muna fito

wan ne sai motar Najeeb ta lalace, shine na tsaya na ara masa battery

ɗ

ina wai dan a samu a tashi nasa ashe wata waya ce ta lalace dan haka nima sai nawa battery d’in ya samu matsala….

Da waya d’aya na fita, to da yake tun rana muke yawo ni da shi munata

waya kuma akayi rashin sa’a duk ba wasu isashshen charge ne a wayoyin namu ba shiyasa duk sai suka d’auke, bamu samu mun kira kowa ba.

D’azun kuma da na fita daga meeting wani abune mai matuƙar muhimmanci ya taso, zan yi maka bayani akai anjima amma yanzu

n dai ka yi hak’uri akan fitar da na yi da komai ma, ka yi hak’uri pls Daddy.’’

Ya k’arashe mganar tasa yana me had’e hannuwansa guri guda alamun roƙo.

Juyawa Daddy yayi, ya kalli yadda gaba d’ayansu har Ummi da Munirat suka zuba musu idanu sannan suka y

i musu cirko cirko.

A hankali ya juyo ya kalli Yashjub d’in ya ce

‘’ka je ka

ɗ

an huta, ka ci abinci, sai ka same ni a sama.’’

Daga haka ya juya ya wuce.

Yana wucewa Yahanasu da Mommy suka taho a tare.

Fuskar Mommy kamar wadda za ta fashe da kuka har d

a hawaye yaga ya taru a idanunta.

Dasauri ta

ɗ

an ture Yahanasu ita ta k’arasa, ta na zuwa ta rungume Yashjub d’in kafin ta cikashi ta shiga tattab’a fuskarshi tana dudduba jikinshi, sai da ta tabbatarwa idanunta da lafiyarsa k’alau tukunna ta ce ’’Gaba d’a

ya hankalin mu a tashe yake Son…’’

Wani guntun murmushi Yashjub ya yi wa Mommy, da kyar, kamar irin an saka shi dole d’innan. tukunna ya kamo hannunta wanda yake rik’e da kumatunsa a hankali ya sauk’ar mata da hannun nata daga haka ya matsa kusa da Yahana

su wadda

ta ja ta tsaya tun lokacin da aka ture ta gefe.

Murmushi yayi mata kafin ya ce ’’sorry, na d’aga muku hankali….

Am anjima inaso za mu yi magana dake,kar ki yi bacci da wuri pls’’

Murmushi ta yi ta d’an shafa fuskarsa da alamun kulawa tukunna ta c

e ‘’tam,

I’m just glad you are okay

(Na ji da

ɗ

in da ya kasance ba abunda ya same ka).”

Ahankali ya ce ’’na gode’’ kafin ya juya ya kalli Yassira wadda ta turo baki ta ce ’’you owe me an apology…(gaskiya ina binka bashin ban haƙuri)…..

Ka saka na bada spee

ch d’in da ban shirya ma ba.’’

Murmushi ya yi kafin ya ce ’’Ina buƙatar hutu yanzu, sai da safenku.’’

Har ya juya zai fita sai kuma ya sake juyowa ya kalli Yahanasu ya ce ’’kar fa ki yi bacci!’’

daga haka ya sa kai ya fice.

Tun lokacin da Yash ya ture h

annun Mommy, ta k’ame a wajen, ta gagara motsi. Gaba d’aya kanta ya d’aure ya d’au zafi dan kwata-kwata

ta ma kasa fahimtar yanayin Yash d’in.

Chaan kuma sai tashi d’aya kwakwalwarta ta d’au chargi gumi ya shiga keto mata dan in dai abubuwan da ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login