Showing 54001 words to 57000 words out of 150519 words

Chapter 19 - Mannubiya Complete

ya ji ko zan huta,’’

dan haka t

a yi saurin kau da kai kamar ba ta gan shi ba, ta bud’e baki za ta yi magana kenan shi kuma ya ce ’’Mommy’’ da d’an k’arfi.

Da sauri Mommy ta saka Hannu ta toshewa Kausar Baki dan har ta cigaba da cewa’’wallahi…’’.

Ba tare da ya kalli Kausar d’in ba ya

k’araso wajen ya na kallon Mommy

Fuskarshi a murtuke kamar bai tab’a dariya ba ya ce

‘’Barka da gida Mommy’’

bai jira jin me zata ce ba ya d’aura da cewa

‘’Mommy dan girman Allah kar ki sake aiko min Yarinyar nan side d’inmu, tun da kin san bata da hankali

kuma bata san ciwon kanta ba to

da baki turomin ita ba….

ko mayafi fa babu a jikinta

ɗ

azun, a haka ta je min.’’

Cikin rarrashi Mommy ta ce

‘’Yash wayoyinta fa da atms har ma da passport duk ka had’a ka kwace yau kusan wata ko in ce fiye da wata d’aya

ma, kaga kuwa ai kai ka kira ta side d’inka ba niba’’.

Cikin fushi yace

‘’Au dama ba ke kika turo ta ba

zuwan kanta ta yi?’’

Ya fad’i hakan yana nufar Kausar d’in a zuciye kamar zai make ta.

Da sauri Mommy ta sake shiga tsakanin su cikin rarrashi tace

‘’A’a ni na turota mana

Hausa ce nayi maka..

Anyways tunda baka gane ba shikenan

yanzu ka yi hak’uri ka bata wayarta muna son ta kira Yasir dan ya kamata ace yayi hak’uri haka ya dawo gida, naga alama Daddyn ku yana k’ok’arin mantawa dashi a cikin ya’y

an sa’’.

Tunda Mommy ta fara magana idon Yashjub yana kan Kausar

wadda ta sunkuyar da kanta k’asa,wata kalar hararar tsana yake jifan ta da shi.

Ahankali Mommy ta d’an kamo hannunshi ta ce

‘’Ka ji Yash, d’an uwanka ne kar

mahaifinku ya yi zuciya ta

har abada da shi ata dalilin shirmen nan nasa, ka bata wayoyinta ita za ta san yadda za ta yi ta yi contacting

ɗ

insa,in ta yi masa magaa zai dawo.’’

Sai yanzu ya d’auke idonshi daga kan Kausar ya maida kan Mommy tukunna yace

‘’Na san inda yake,anjima za

n je in taho dashi

Dan naga alama absence d’insa yana k’ok’arin janyo min bala’i’’.

Shiruu duk su biyun sukayi

Mommy tana adduar Allah yasa ba maganar su ta yanzu itada Kausar ya ji ba,

Kausar kuma tana adduar Allah yasa ya ji d’in.

Muryarshi ce ta ka

tsewa duk su biyun tunani

Jin yana cewa

‘’Mommy dan Allah dan annabi kar ki sake turomin Yarinyar nan, zan kawo miki phones d’in nata da komai anjima,

Ina shikenan?’’

Yayi maganar yana mai d’aga hannunshi duka biyu da gira d’aya.

Murmushi Mommy ta yi

sannan ta sa hannu ta shafa kumatun shi a hankali tana murmushin ta ce

‘’Shikenan son,shikenan na gode’’.

Kama Hannun Mommy wanda yake a fuskar tasa yayi kawai yana kallon ta,

Itanma shi take kallo tana nazartar shi

So take ta gano ‘ya ji zancen nasu ko

a ‘a.’

Bai bata dama ba kuwa dan k’asa yayi da kansa ya furzar da iska ba tare da ya ce uffan ba ya cika Hannun nata ya juya ya fita ya nufi side d’insu bayan ya tsaya ya d’auki belongings d’insa daga motarsa…

Ko shiga side d’in nasu dama bai yi ba ya nu

fi wajen Mommyn dan ba kad’an ba ya ji haushin zuwan da Kausar ta yi masa

ɗ

azu da safe bagatatan…..

BULAMA ✍



0903 441 3252

*MANNUBIYA*

*19*

Kamar kullum yau ma tare Abbakar da Manubiya su ka fito

daga

ɗ

akin jarab

awa.

Suna tafe yana bata labarin Baraka a jiya da ta je gidan su….

Adashe ta ke yi ashe, ta kwashi nata har naira dubu d’ari uku a jiyan!

Yana d’akinsa na soro ya ji ita da maman shi da mamanta suna hirar ‘wai fili zata cika ta siya ta yi gini’.

A hankali

Manubiya ta sauk’e wata nannauyar ajiyar Zuciya a fili ta ce ’’Allah ya sa ta fi haka!

Allah ya bata ikon siyan wasu filayen dayawa nan gaba..’’

‘’Abbakar!’’

Suka ji an kira sunan shi.

Cikin yanayin maganarsa ta masu sanyin jiki ya juya ya kalli mai kir

an nasa ya ce

‘’Na’am’’.

Dariya saurayin ya yi kafin ya ce ‘’ka bi ka dagewa k’awance da Mace dama kai ga ka ga yanayin ka yanzu kam ba marabar muryarka da ta Macen….

ka je Sir Najeeb yana neman ka’’

Ya k’arashe maganar tasa yana me tapping shoulder d’i

n Abbakar d’in daga nan ya yi gaba ya wuce ya bar su nan tsaye.

Yana wucewa Manubiya ta ce

‘’Allah yasa lafiya’’

Murmushi ya yi ya ce ‘’InshaaAllah ma lafiya, mu je sai mu ji menene’’

Dasauri ta ce

‘’Wa?Ni?tab!inaaaa..’’.

wata kalar harara ya yi mata



kafin ya ce

‘’Ban gane ba, ba za ki raka ni ba?’’.

Cikin nemo mafita da sauri ta ce

“Abbakar na fa gaya maka na bar aiki burjik a gidan Ammi, gashi yanzu 4har ya wuce, dan Allah ka yi hak’uri kar mu je yau ma mu tarar yana da bak’o mu yi ta zaman jiran

sa in yi letti wajen Ammi, sannan kaga ga karatun exams d’in jibi, ta yau ma ta bani wahala wallahi.’’

Cikin sigar tsokana ya ce

‘’Ko dai ba kya so yau ma ki sake yin gamo da crush d’in ki ba.’’

Da sauri ta zaro ido sai kuma ta buga masa littafin Hannu

nta tana mai cewa

‘’To k’arya dak’ik’in tunaninka ya baka, wallahi ba wani crush’’.

Dariya ya yi yace

‘’Auch’’.yana sosa inda ta buga masa littafin sannan still yana dariyar ya ce

‘’Shikenan, ki je sai mun had’u gobe inshaaAllah.’’

Hararar sa ta yi da

ga nan ta juya ta wuce.

A hankali ya sunkuyar da kansa yana murmushi kafin ya d’aga kai ya bi bayanta da kallo…..

sai da ta b’acewa ganin sa tukunna ya sauƙe ajiyar zuciya sannan ya juya ya nufi office d’in Sir Najeeb…

Yana zuwa wajen ana shiga sallah,

sanin halin Sir Najeeb d’in ne ya sanya sai da ya je office d’in nasa ya tabbatar da baya nan tukunna ya nufi masallacin shima.

Yana shiga ya tarar da shi a sahun gaban sa.

Cikin nutsuwa aka gabatar da sallar la’asar ana idarwa shi da wasu a cikin masall

acin da suka rasa raka’a suka tashi domin ramawa masu addu’a kuma suna yi.

Yana idarwa shima yayi addu’a ya shafa daganan ya zauna zaman jiran Sir Najeeb

yana mai ha’dawa da adduar ‘Allah dai yasa ba wani laifi ya kuma yi ba’

dan bayan class rep in dai

ka ganka a office d’in Sir Najeeb to ba k’aramin abu bane ba.

Ko wani abun ne ma kake da buk’atar yi ko gaya masa to daman an san ka’idarshi’ka gayawa class rep shi kuma ya fad’a masa’….

Ganin fitar sa ne ya sanya

Abbakar d’in mi’kewa da sauri ya bi

bayan sa.

A bakin office d’in nasa suka had’u yana k’ok’arin bud’ewa dan haka yana bud’ewa suka shiga tare Abbakar ya shiga da sallama sannan ya shiga gaida shi da ladabi.

Cikin nutsuwa ya amsa masa

yana mai neman guri ya zauna akan d’aya daga cikin

sof

a d’in dake a office d’in kafin ya d’ago ya kalle sa

ya ce ‘’d’an zauna.’’

Cikin d’an d’ari-d’ari Abbakar ya nemi waje ya d’an d’osana mazaunansa ya yi shiruu,

zuciyarsa tana masa sak’e-sak’e kala-kala.

Shiruu shima Najeeb ya yi yana tunanin ta ina ma

zai fara ne,

Wallahi ba dan Yashjub bane Allah da babu abunda zai sa ya yi wannan abun

haba!student d’insa fa abun ya yi wani iri da yawa, amma ya ya iya dole ya daure ko ba komai shima yana so ya ga Yashjub ya yi aure, kuma tunda har ya ga Yashjub ya zo

ya same sa a kan maganarta tou kuwa ya san abun na gaske ne, wanda hakanne ya sa shima ba zai yarda ya

ɗ

auki batun da wasa ba.

Ahankali ya sauk’e ajiyar zuciya ya d’an yi gyaran murya

wanda hakan ya sanya Abbakar ya mik’a masa

dukkannin hankalinsa.

Ci

kin nutsuwa Najeeb ya ce

‘‘Akan wannan ƙawar taka na kira ka, Manubiya”

Shiruuu Abbakar d’in ya yi da farko

kafin a hankali ya ce ’’Ok,Sir.’’

Dan zuwa wannan lokacin

Kwakwalwarsa ta gama bashi

amsar dalilin kiran da aka yi masa.

‘’Tana da wata matsal

a ne?,as in family issue besides rashin lafiyar Mahaifiyarta?’’

..

Manubiya ƙawarsa ce da yake yi mata kallon kamar ma ta zama ƴar uwa, a ganin sa bai kamata ya kunce mata zani a kasuwa ba.

Dan haka ya ce

‘’A’a rashin lafiyar Maman nata ne kawai issue d’

in ta’’.

‘’Shiyasa take kuka kusan kullum a class?’’

Sir Najeeb ya sake jeho masa wata tambayar cikin katse sa.

Shiruu ne ya d’an biyo baya kafin Sir Najeeb d’in ya ce

‘’Kamar yadda na fad’a muku the other day

Malamai kamar iyaye su ke,

a yadda na k

e ganin ta so disturbed (a dame) kullum na yi tunanin tana da financial issue ne.

Am na san ba hurumin mu bane

but Aboki na wanda ka ganmu tare ne yake da offer na aiki very simple wanda Mace ko tsoho za su iya yi…”

A Ta’kaice Sir Najeeb ya yi wa Abbakar

bayanin aikin da ya ga damar had’awa a kansa a take a wannan lokacin kafin ya d’aura da cewa

‘’Na yi tunanin tana da financial problem shiyasa na ce mishi akwai wadda zan nemo ta yi mishi aikin but tunda ka ce ba haka bane ba shikenan zan ce mishi ya nemi

wata kawai’’.

Shiruuu Abbakar ya yi, ya hau tunani…...

‘Tabbas ya san Manubiya za ta yi farin ciki da offer d’in nan, to amma kuma….’

Cikin katse masa tunanin Sir Najeeb ya ce ’’Shikenan, u can leave, dama reason d’in kiran naka kenan’’.

Duk da b’oye-b

’oye da kwana-kwanar da Sir Najeeb yayi tashi d’aya Abbakar ya fahimci inda suka dosa daga shi har Abokin nasa, hakan ya sanya ya shiga tsaka mai wuya dan on the other hand, no matter how (a ta wani fannin, duk rintsi)…ko ma menene yake ji yake kuma tunani

to fa bai kamata ya yi wa Manubiya bak’in ciki ba!

Besides (baya ga haka ma) shi a rayuwa da ko da yaushe yana saka farin cikin ta ne a saman nashi..

Dan haka ya

ɗ

an gyara zama!

Da kyar ya iya danne zuciyarsa ya d’ago manyan fararen idanuwansa waenda suka

d’an fara surkuwa da kalar ja ya ce ’’za ta yi, baku da matsala za ta yi cikin farin ciki ma, in sha Allah.’’

Yana gama fad’in haka ya maida kansa k’asa.

Har cikin zuciyarsa ya yi wa Manubiya farin ciki da samun wannan aiki dan daga gani mai tsoka ne, ya

san zata rage damuwa kwarai sannan za ta yi maganin matsalolinta, duk da kuwa ya riga ya san akwai wata

ɓ

oyayyiyar manufa a bayan aikin da aka bata, amma dama tun ba yau ba ya dad’e da yankewa ‘indai rana mai kama da ta yau ta zo, to ba zai bari zuciyarsa

ta rinjayi tunanin sa ba’.

Ya san ba wai Sir Najeeb d’in ne yake son ta ba amma shakka babu kamar yadda ya lura da itama ta tab’u da ganin wannan Abokin nasa haka zalika shima Abokin, tunda gashi ya fara fakewa da bata aiki…..

A hankali ya fesar da iska a

ransa yana sake jaddadawa kansa cewa ‘’inshaaAllah, ba zai tab’a bari shirme da mafarkinsa su shiga tsakanin Manubiya da auren wannan Mutumin ko aikin da ta samu ba..’’

A b’angaren Najeeb shima shiruu kawai ya yi yana nazartar Abbakar d’in kafin daga ba

ya ya ce ’’ok,ga katin friend d’in nawa, idan ta shirya sai ta kira shi ta ce masa itace Manubiya Musa wadda za ta yi masa aikin da Najeeb ya ce zai had’asa da wadda za ta yi’’.

Ya fad’i hakan yana mik’awa Abbakar katin.

A hankali kamar marar lakka a jik

i Abbakar ya mik’e ya k’arasa ya je ya amsa, sannan ya ce

‘’Mun gode kwarai Sir,Allah ya k’ara d’aukaka da arzik’i, Allah ya ji k’an magabata’’.

A hankali Najeeb yayi murmushi ya ce

‘‘Ameen Abbakar, ta kira soon’’

‘‘In sha Allah’’

Abbakar d’in ya ce da

murmushi kwance akan fuskarsa.

Daga nan Sir Najeeb ya sallame sa suka yi sallama ya tafi…

Tashi

ɗ

aya!! Najeeb ya gama fahimtar komai game da Abbakar amma ko hauka ya ke yi ko da wasa bai isa ya gayawa Yash ba! dan ya san zai kunno fad’an da ba lalle ya

iya kawo k’arshen sa ba ne, saboda a yadda ya ga kishi k’arara a Idanun Yashjub

ɗ

azu ya san tabbas in ya bari ya ji wannan batu to fa sai ya raba su ko da bala’i ne. Shiyasa ya bari akan ba zai fad’a mishi ba, shi ya san

ta yadda zai bi ya taya Abokin nas

a akan Abbakar da komai ma

In sha Allah komai zai tafi normal..

Abbakar kuwa abubuwa biyu ne suka had’e masa na farko damuwar sa wadda yake ta k’ok’arin b’intikewa wadda ya ji mamakin yadda ta ke shirin cin galaba akansa na biyu kuma farin cikin ta ya Ma

nubiya murnar samun riba biyu da ta yi na aiki da masoyi in sha Allah.

A hankali yayi murmushin da ya fi kuka ciwo a chan k’asan zuciyarsa yana adduar ‘Allah yasa yadda ya tsara yake kuma tunani ya tafi yadda ya ke zato, Allah yasa yadda yake tunanin zuciy

arsa zata huta zata samu nutsuwa idan Mannubiya ta yi auren ta, hakan ya kasance. sannan Allah kar yasa yayi da na sanin wannan ƙudirin nasa da ya yanke .’.

Hakanan ya na tafe yana tunani ya nufi gate dan ya san dama ta riga ta tafi gida tun

ɗ

azu, ya san

zai ga farin ciki a kan fuskarta in ta ji labarin aikin dan haka yake ta sauri domin ya je ya sanar mata saboda ba kad’an ba yake kwad’ayin ganin wannan farin cikin nata.

Duk da yadda yake fargaba amma hakan bai sanya ya ji zai fasa ba dan ya fi bid’ar ga

nin farin cikin ta da walwalar ta sama da komai…..

Adaidaita ya samu ta kai shi har k’ofar gidan su Manu

amma sai Jidda ta ce masa

‘’Da ta dawo jakarta kawai ta ajjiye ta yi alwallah ta nufi gidan Ammi.’’

A k’ofar makeken gate d’in ya tsaya

ya d’an bu

ga kad’an..

Dakyar, bayan mai gadin ya ji buk’atar shi ya yadda zai je ya kira masa ita dan a cewar sa k’a’ida ne sai an fad’a a day before (ana i gobe) tukunna visitors suke zuwarma masu aikin gidan.

Ba a yi 5minutes ba

Manubiya ta d’an lek’o da fuskart

a ta k’aramar k’ofar gate d’in, suna had’a ido ta sauk’e ajiyar zuciya kafin ta ce

‘’Ashe da gaske kai d’in ne’’.

Ta fad’i hakan tana mai fitowa daga gidan gaba d’aya..

…..

Ahankali cikin tsananin sanyin jiki ta fito ta tsaya tukunna tace “Na yi mantuwa n

e? ko handout aka bada?’’

Sai da Abbakar ya fesar da iska tukunna ya ce “yau dai na tabbatar da duk abun da yake sanya ki tunani kike ta faman b’oyemin for the past few weeks (kwanakin da su ka shu

ɗ

e) a gidan Ammi ya ke, meye ne Manu?

Akwai abun da take y

i miki na cutarwa ne?’’

Murmushin yak’e Manubiya ta yi kafin ta ce

‘’Kawai na gaji ne, shiyasa ka ga haka.

meyafaru ance kana nema na wai ka ce it’s important,ko?’’

Ta yi mishi tambayar cike da son kaucewa tambayar ta shi dan bata san amsar da zata bashi

ba.

‘’Manu yau fa ba zaki kaucemin ba wallahi sai kin fad’amin damuwar ki.’

Ya fad’i hakan yana mai zama akan tebur d’in dake anan ta gefen gate d’in Kad’an

Kafin ya sake cewa

‘’Sam ba haka mood d’in ki (yanayinki) yake ba lokacin da muka rabu da ke d’a

zu-

ɗ

azun nan a school,so definitely (dole) anan gidan ne kike da damuwa.

Talk

Ki gaya min mu nemo mafita kafin ya zamana lokaci ya ƙure.

Kinga ba inda ma fa zan je har sai kin fad’a min, kin dai sanni da naci ko?’’

A hankali Manubiya ta lumshe idanuwant

a ta bud’e, ta san halin Abbakar da shegen naci, a yadda ya kafe d’innan in bata gaya masa ba to ko ruwa ba zai barta ta sha ba, bayaga haka ma in ba shi ko Jiddah ba

bata san wa zata gayawa ta samu sauk’i ba, dukda bama ta san inda damuwar tata ta dosa b

a bata san ta yaya za ta fassara ko ta fasalta damuwar tata ba saboda ba lalle ta yi making sense to anyone ba(bada

ma’ana a kwakwalwar kowa ba) dan ita kad’ai ta fahimci sannan ta san me take ji take kuma fuskanta dan haka ba lalle a fahimce ta ba..

‘’Ma

nu ke nake saurare’’

Abbakar ya fad’a yana sake gyara zaman shi.

Cikin tsare gida Manubiya ta ce

‘’Ok.

zan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login