Showing 27001 words to 30000 words out of 150519 words
so banajin za’a samu matsala wannan karon, InshaaAllah.
Na bar komai a Hannunki, ku shirya tarbar sa da kyau ranar juma’ar nan zai zo.’’
A hankali mommy ta ce
‘’InshaaAlla
h Daddy.
sannan da yardar Allah ba za a samu matsala ba.’’
Ta yi maganar tana mai yi wa Yahanasu addu’ar dacewa a wannan karon, ko ba komai hankalin kowa zai kwanta.
A hankali yahanasu wadda gaba d’aya hankalinta ya tashi lokaci guda ta ce
‘’Daddy, Dan A
llah…’’
Cikin rashin son ya saurare ta ya ce
‘’Sai magana ta ta biyu.’’
A take duk suka tattara hankulan su suka maida akan sa! Ganin yadda lokaci guda ya sake tamke fuskar sa ne
yasanya
duk suka sha jinin jikinsu.
‘’Yashjub ya sanar da ni
Irin ta
ɓ
a
rgazar da Yaran nan su ke shukawa’’
Daddy yayi maganar yana nuna Yasir da Kausar.
Kafin cikin b’acin rai ya kalli Mommy ya ce
‘’I’m really disappointed in you,
da ke da su bansan wa ya fi wani ba.
Anyways, na riga na gama yanke shawarar d’aura musu Aure
gobe da safe in sha Allahu!!!
dan ban shirya d’aukar shege a karo na biyu a cikin gidana ba’’…
Tun kafin ya kai k’arshen aya Kausar ta fashe da wani irin kuka, cikin sheshshek’ar kuka ta ce
‘’Allah ba zan aur……’’
Ai kuwa a take Daddy ya mik’e da shirin
isa inda take,
ganin haka ya sanya ta kwasa a guje ta yi sama.
Ya so ya bita, ya ci k’aniyar ta dan dama a mugun k’ule yake da ita, bayajin haushin Yasir kamar yadda yake jin haushin ta, sannan a ganin sa ita ta b’ata Yasir tun asalin farko shi kuma bai f
arga da wuri ba, shikenan garin tausayi gashi Yarinya tana neman tarwatsa masa tarbiyyar Yaro ko ma ace ta riga ta tarwatsa d’in…
Muryar Mommy ce ta katse shi
jin tana cewa
‘’Daddy u need to reconsider(ka sake tunani),
wannan abun da kake shirin yi ba
dai-dai bane ba!
kuma lokacin da ka d’auka a gaskiya ya yi kad’an,
dan Allah ka sake tunani.’’
Cikin tsananin
ɓ
acin rai ya ce
‘’Bar ganin a gaban ƴaƴanki kike, wallahi yanzun nan zan kifar da ke.
kin bar Yara suna shashanci sannan yanzu ana k’ok’arin gy
ara abu amma kina k’ok’arin kawo tangard’a akai ??
karfa ki bari rai na ya k’arasa b’aci da ke!
wallahi ba za ki ji dad’i na ba’’.
Yana gama fad’in haka ya juya fuuu ya wuce saman shima ya nufi side d’insa.
A zuciye Mommy itama ta mik’e ta k’arasa inda Y
ashjub ya ke tsabar fushi bata san lokacin da ta rufe sa da fad’a ba!
Baki da kumfa ta shiga cewa
‘’Mai yasa kake da muguwar zuciya ne? Yanzu kukan da take yi dad’i yayi maka ko mai?
ka fini sanin ciwon kaina ne?
ko kuwa ka fini sanin abun da ya fi dace
wa a yi?
Tunda har ka ga na yi shiru ai ka san akwai dalili dai ko?’’
A hankali ya d’ago lumsassun idanuwansa ya zuba mata ba tare da yace uffan ba…..
Ganin yanayin kallon da ya ke yi mata ne ya sanya ta yin shiru a take ta kauda kanta daga gareshi ta had
’iye ragowar maganganun nata.
Ya jima yana kallonta kafin ya d’auke idanuwansa daga gareta ya fesar da iska ya mik’e tsaye! daganan ya fara k’ok’arin barin wajen.
Cikin tsananin sanyin jiki ta ce
‘’Yash’’
Juyowa kawai ya yi ya tsaya yana kallon ta.
Gaba d’aya kuma sai ta diririce ta gagara cewa komai
Ta hau kame-kame
‘’am dama a ganina bai kamata ka gayawa Daddy…..”
A hankali ya ce ‘’Mommy ..’’sannan ya
ɗ
an girgiza mata kai yana mai lumshe idanunsa ya bud’e
daga haka ya juya ga Yahanasu ya ce
‘’Allah ya tabbatar da alkhairi.’’
Yana gama fa
ɗ
in haka ya sa Kai ya fice daga parlourn ko sai da safen su Yadira bai tsaya amsawa ba.
Mommy ji ta yi kamar ta d’aura Hannu a ka! Ta yi ta kurma ihu!!!
Tabbas idan akwai Yaron da bai San darajar mahaifiyar
sa ba tou Yashjub ne….kalli fa bashi ma da lokacin yi mata magana ballantana a je ga sauraronta ko bata haƙuru.
Tana tsananin k’aunar Yasir amman ya zama dole ya hak’ura da Kausar Yashjub ya aura dan bata hango shak’uwar da take kwad’ayin samu daga gare s
a ba muddin ya yi aure ya tare chan da wata ba Kausar
ɗ
in ta ba!
Musamman ma idan ya samo wadda yake so!
Shikenan ta zama ƴar kallo a gefe..
Tana wannan tunanin ta dake ta cire tsoro ta nufi sashen Daddy
da niyyar tana gamawa da shi kuma zata lek’a d’aki
n Baba Larai saboda tabbas a yau take so a yi ta, ta k’are!!.
Ɗ
aya bayan
ɗ
aya aka dinga watsewa daga dining table
ɗ
in,
ya rage saura Yasir shi ka
ɗ
ai.
Ya yi mamaki ha
ɗ
e da jin zafin yadda k’iri-k’iri ya hango rashin amincewar auren nasu a kwayar idan
un Mommy!
shiyasa tun lokacin ya fad’a duniyar tunani ya gagara cewa komai har izuwa yanzu da kowa ya watse ya bar sa a wajen.
A hankali ya mik’e ya nufi sama sashen Kausar
amman ko da ya je
ɗ
in sai ya tarar da k’ofarta a rufe ruff!!
Babu kalar bugu da k
iran wayar da bai yi mata ba amma sam ta ƙi yarda ta bud’e, ta ma ƙi kula shi.
Haka nan ya gaji ya kama hanya ya sauk’a ya fita daga sashen gaba d’aya ya nufi nasu, wanda yake a jikin mansion d’in amma k’ofar su ta baya take da wani makeken compound a wa
jen wanda ya ma fi na gaban gidan dan tsaf za a iya gina irin mansion d’in guda a wajen!
Da har da gate d’insu daban
a wajen amma saboda yawan yawon dare da Yasir ya tsira yakeyi ne
ya sanya aka rufe gate d’in Daddy ya hana fita ta nan gabad’aya.
…. Par
lour ne babba sosai
sai kitchen, dining area da 2 bedrooms a k’asan
sama kuma 2 bedrooms ne ko wanne da parlourn sa sai saperate d’aki guda d’aya,
Side d’in nasu ta b’angaren mansion d’in mai hawa
ɗ
aya ne
sab’anin na su Daddy wanda ya had’a hawa biyu….
A nan main parlourn ya tarar da Yash yana zaune yana sipping tea yana waya a hankali.
Mommy ta gaya masa yana nemansa! Sannan So yake ya tambaye sa abu dan haka ya nema waje ya zauna shima akan d’aya daga cikin kujerun parlourn.
sai da ya zauna tukunna
ya fahimci ashe da Abokinsa ‘Najeeb’ yake wayar
Wani dan guntun Murmushi Yasir ya yi a ransa ya ce
‘’Haba, dama ni dai na san ba da Mace yake wayar nan ba
Mutum sai kace waliyyi …..’’
Ya fi 1 hour yana waya kafin finally ya ajjiye wayar ya d’ago ya na
kallon Yasir ya ce
“Ka je kawai, maganan da za mu yi an gama ta tun
ɗ
azu a wajen dinner, an rufe komai ai”
Murmushi Yassir ya yi ya
ɗ
an sunkuyar da kanshi ƙasa ya ce “eh”sai kuma ya ƙi tafiya, dan haka Yashjub
ɗ
in ya ce masa
‘’Lafiya?’’
Sai da Yassir ya
ɗ
’an sosa kansa tukunna ya ce
‘’Um, dama ina d’an son…’’
Tun kafin ya k’arasa Yash ya ce
‘’Kud’i,ko?’’
Murmushi ya yi kafin yace ‘’yess,a lot (masu yawa)”
A hankali Yash ya mik’e tsaye
sannan ya ce
‘’Yadda Daddy ya Zuciya da ku
ɗ
innan Yassir idan ka y
i
dinner ko wani shirme a auren nan ka san ranka ne zai yi mummunan b’aci,therefore ba za ka samu kud’i daga gareni ba, gaskiya’’.
Yana gama fad’in haka ya wuce sama.
Yasir ji yayi kamar ya bi shi a baya ya make shi! a ransa ya ce
‘’Munafuki!!! Ai kaine
ka janyo Daddyn ya ke fushin da mu, duk da dai munafurcin naka yau ya yi mini rana tunda gashi gobe za a aura min farin ciki na .’’
Mutsutstsuka idanunsa ya yi, ya fesar da iska kafin ya mik’e shima ya wuce saman yana tunanin ta yadda zai yi raising kud’
i!!
dan ba zai yiu ace bikin su shi da Kausar amma wai babu dinner ba wani shagali ba……
…….
A bakin gado Mommy ta samu Daddy, a tsaye yana shirin shiga wanka.
Ya ji shigowar ta, dan haka ba tare da ya kalle ta ba ya ce
‘’Don’t try anything stupid (kar ki
gwada yin shirme a lamarinnan) Khadijah
daga nan har gobe. Ban san wasan da kike son bugawa wannan karon ba amma ina shawartar ki da
kar ma ki fara shirin yin komai, idan kuma
ba haka ba to zan baki mamaki.’’
Ba tare da fargaba ko tantama ba ta ce
‘’Ba
wai shirin wani abu sabo zan yi ba, dan na riga na gama shiri na, kawai dama naga kamatar in sanar maka abunda ya kamata ka yi ne domin ya tafi dai-dai da shirin nawa!
Dan haka ka saurara ka ji
‘Inaso ka janye maganar auren Yasir da Kausar, dan
ba mai y
iuwa bane ba’.’’
Sai yanzu Daddy wanda ya gama d’aura igiyar bathrub
ɗ
in da ke Jikinsa ya juyo gareta, ya d’an taka inda take ya tsaya
tukunna ya ce
‘’Dole, a gobe Kausar za ta fitar mini daga gida Khadijah,
It’s either ta wuce gidan Yasir ko kuma ta sa
n inda zata je,
na yi iya yina!!.’’
Wani kalar murmushin takaici Mommy ta yi
kafin tace
‘’Ai dama na sani, na san ka gaji da rik’e ta ne shiyasa za ka yi mata auren dole.’’
Cikin fushi Daddy yace
‘’A kul d’inki Khadijah!.
Idan ke dak’ik’iya ce baki sa
n ciwon kanki ba baki san kishin d’an da kika haifa a cikinki ba tou ni na sani.
Ki godewa Allah ma da har na yarda Yasir zai auri Kausar d’in…
Allah na tuba Maraici ai ba hauka bane ba!
Yarinyar nan fa har haihuwa ta yi sannan bata da uba!
Amma duk da hak
a na amince na yarda zan aurawa Yasir ita..
Shine amma har kike da bakin cewa za a yi mata auren dole?’’
Daddy bai tsaya jin amsarta ba ya d’aura da cewa ‘’Bari kiji, ba don na san Yasir yana da ikon
k’ara aure ba to da ba zan bar shi ya auri shegiya ya
rayu da ita ba wallahi.’’
Kamar an kunna fanfo haka fuskar Mommy ta jik’e sharkaf da hawaye,
Cikin kuka ta ce
‘’Na gode ‘Imam’ na gode sosai.
Alk’awarin kenan ko?
Allah ya ji ƙan Abba da Daddy…
A gaban su ka amince za ka rik’e Kausar, ruk’o na amana
amma
yau da kanka da Bakinka kake cewa ta fitar maka daga gida
da kanka kake kiran ta da sunan ‘shegiya’
D’an Adam butulu, walllahi Allah sai ya yi mana hisabi.’’
Cikin tsananin b’acin rai ya ce
‘’Dole in ce Kausar ta fitar mini daga gida, Khadija
‘Ƴaƴana
takwas a duniya amma babu wadda a kullum take d’aga mini hankali take janyo min abun kunya da magana sai y’ar ruk’o,
ko su Mazan ba sa yin fitinar da Kausar take yi!!!.
Kalli yanzu yadda ta lalata Yassir,
shikenan ni
kullum gidana cikin case saboda ita?.
Ki duba fa ki ga yau tafiya na yi na dawo amma ko isashshen sannu da zuwa da hutawawa ban samu ba ban yi ba na fara da case din y’ar ruk’o.’’
Cikin d’aga Hannu (alamun stop )
Mommy ta ce
‘’Dakata daganan Daddy.
Maganganun ka ga Kausar sun ishe ni, sannan
idan ba zaka kirata da Kausar ba to
ka yi shiru!
dan shegiya ko y’ar ruk’o ba sunanta bane ba, gorin ka da cin fuskar yayi yawa haka ya isa!!!.
kuma ta Ina kausar ta lalata Yasir?fyad’e ta yi masa?
da aka ce maka sun tafi Auckland d’in tare shi munafukin
naka camera ya mak’ala musu ya ga sun yi wani abun?
Baya ga haka ba fa su ka
ɗ
ai suka yi tafiyar ba??
har da Abokansu suka tafi.
Kawai kai dai ka tsani Kausar!
Na riga na sani tun ba yauba ka tsane ta shiyasa kullum burin ka ka ga ka k’untata mata.
Tayaya
ma za ka ce wai Kausar ta lalata maka
ɗ
a! haba Daddy,
ka dinga adalci mana,
ko kara babu?’’
Cikin takaici Daddy ya ce
“karar da na yi tun farko ita ta cutar da ni, gashi inaji Ina gani
Yasir zai auri Matar da sai addua kawai, kuma a matsayin uwar gida
,
Idan jikokina suka tashi a gagara nuna musu dangin uban Mahaifiyar su’’.
Cikin jin-jina kai Mommy ta ce
‘’shikenan tunda kai ba Mahaifinta bane ba!
ka fa
ɗ
a ka nuna kuma ka furta.
Tou nima daga yau
Inaso ka tsame Hannunka a duk lamari da rayuwar Yarin
yata.
Aure kuma da Yasir tunda har kana ganin kamar za a cuce shi ne to wallahi ba za a d’aura ba!
Idan kuma ka d’aura to za a sha mamaki na.
Tunda baka son had’in
ta fi nono fari
muma bama so.
Kuma inshaaAllah daga yau
Ni zan dinga kula da ƴata,
babu r
uwan ka da duk wani abun da ya shafe ta!
Zan nemo cook inn siyo kayan abinci a dinga yi mata girkinta a daban…
k’arshen wata kuma zamu dinga biyan ka kud’in haya,
ruwa da na wuta!!!
Iyakar abunda nake nema daga gareka shine ka daina takura mata, kuma ka d
aina yunk’urin yi mata dole.
Iyakar tsakaninka kai da ita gaisuwa.
Tunda a iya sani na babu inda Kausar za ta je muddin Ina cikin gidan nan, dan haka sai ka jira har sai ranar da Allah ya kawo mata wanda take so ta aura tukunna.’’
Tana gama fad’in haka ta
juya zata fita sai kuma ta juyo ta dawo inda yake nan tsaye ranshi a mugun b’ace ta ce
‘’Allah dai ya so ba y’ar uwata kad’ai bace ta fara haifar shege!
kafin ta yi kafin Kausar ta yi sai da aka yi!!!
Ko in je in kawo maka Yahanasu?
Na san wataƙila idan
ka kalli fuskarta zaka iya tuno da wadda nake nufi da kuma abubuwa da dama,
saboda kalamanka da k’iyayyar ka ga shege sun sanya na fara tunanin maybe ko dai ka yi loosing memory ne.
A yadda ka tsani Kausar kake kyamar ta inada tabbacin ta fi dubu! saboda
na tabbata in dai Kausar ta auri wanda take so kuma yake son ta to ba za
ta tab’a cutar sa ba baza kuma a kamata da waninsa ba!
saboda ƴata tanada ruƙon amana kuma na san ta san darajar soyayya………..
Cikin tsananin fushi Daddy ya yunƙura da dukkannin ƙ
arfinsa ya
ɗ
auke ta da wani gigitaccen mari.
Dagowa ta yi da niyyar ci gaba da tsiwa amma sai yanayinsa da idanuwansa suka sanya ta had’iye maganganunta da tsiwar tata
domin a yadda ta ga yana kallon ta da jajayen idanuwansa tsaf zai iya illatata.
Da ky
ar ya iya cewa
‘’Fita kar in sake ganin fuskarki idan ba ni na neme ki ba.’’
Babu musu, haka nan
ta juya ta fice daga d’akin dan ta tsorata da yanayinsa.
Tana fita kuma sai ta ji wani sanyi ya lullu
ɓ
e ta, a haka ta fita daga side
ɗ
in nasa gaba
ɗ
aya ta s
auƙo tana mai jin zuciyar ta fess!!!
Tabbas ta san dama idan ba da gaske ta yi ba to ba lalle ta iya hana auren nan ba!
Amman a yadda ta tsokalo Daddy ta tuna masa da baya to fa
ba lalle ya iya shan ruwa ba ma daga nan har Jibi, ballanta har a zo ga magana
r
ɗ
aurin aure!!
Yayinda a chan k’asan zuciyarta kuma sai ta ji kishi yana taso mata!
Sakamokon k’unci, damuwa da tsananin kishin data gani a Idanuwan Daddy kamar
jiya jiya abun ya faru…………
••••••
Kamar yadda Al’ameen ya ce,
Da yamma kusan magrib sai ga sh
i ya dawo da laidoji nik’i-nik’i.
Ya kuwa ci sa‘a dan Jiddah ce a wajen,
Manubiya an tafi yi mata test
saboda tunda Baba ya lura ba ta da lafiya duk sai ya damu da kyar ma
ya wuce gida shi da Muhsin ya barsu tare da Ya Musbah akan idan komai yayi settling
shi sai ya dawo ya bar Jidda da Manu su kwana
washegari kuma ya koma su dawo su yi girki, idan Allah ya kaimu.
Tunda ya shigo ta diririce
gashi Inna ma bata jima da komawa bacci ba.
Dariya ta so ta ba shi dan kamar irin zai sace ta d’in nan haka yaga
tana yi….
Cikin sanyin murya da sanyin jiki ta gaida shi, shi kuma
ya amsa mata da kulawa yana mai tambayar ta “ya jikin Inna?”
A hankali ta ce ‘’da sauk’i’’
Har zai zauna sai kuma ya ƙarasa gaban gadon ya ajjiye ledojin ya ce mata ‘’gashi’’
tukunna ya
dawo ya zauna.
Da kyar ta ce ‘’mun gode’’
Sai kuma ta
ɗ
an yi shiru kafin ta ce
‘’Ya Al’ameen ka daina, dan Allah’’
Wani d’an guntun Murmushi ya yi kafin ya ce ‘’in daina me?’’
Ya fa
ɗ
i hakan yana mai kafeta da idanuwa.
Sai da ta
ɗ
an
ɗ
auki lokaci