Showing 93001 words to 96000 words out of 150519 words

Chapter 32 - Mannubiya Complete

bata samu ta je gidan ba saboda bata gama yanke shawara da farko ba da kuma ta

gama yanke shawarar lokaci ya riga ya shige mata, dan haka in dai ta gama da nan da wuri tana so ta biya gidan Ammi su gama da ita tukunna ta wuce exams saboda kar matar ta ga ko dan ta bar aiki shine yau zata yi mata wulak’anci ta bar ta da aiki ya kai r

ana……

..

Tana zuwa bakin gate security ya gaisheta ya bud’e mata k’aramar k’ofa ta wuce ciki.

Yau ma Racheal ce ta yi mata rakiya har chan sama office d’in nasa amma yau ba ta shiga ba suna zuwa ta ce mata ta shiga ita kuma ta juya ta koma.

Tana hango

shi fad’uwar da gaban ta yake yi ya tsananta…

yau black suite yake sanye da

amman ya cire babban suite d’in ya sak’ale ya bar k’aramar ta ciki armless (marar Hannu) da white long sleeve (farar riga ta ciki mai dogon Hannu) din da suka yi masa asalin kyau

,

ba ta san ya aka yi ba kawai sai ta shagala da kallon sa tana mamakin tsananin kyawu da kwarjinin da Allah ya ba shi.

Tana tsayawa a wajen jikinsa ya ba shi da Mutum a gurin dan haka ya d’ago da niyyar tabbatarwa

yana d’agowa kuwa suka had’a ido da i

ta.

Da sauri ta sunkuyar da kanta dan tashi d’aya duk sai ta diririce…..kafin da kyar ta samu ta d’an d’aga hannunta ta yi knocking a hankali tukunna ta tura k’ofar ta shiga a hankali bakinta d’auke da sallama…….

*MANNUBIYA*

*31*

A han

kali ya amsa..yau ma kamar ranar farko haka ya kafe ta da idanu tun lokacin da ta shigo har ta k’araso ta zo ta zauna a hankali ta ce

‘’Good morning Sir.

(Ina kwana, sir).”

A hankali ya samu ya

ɗ

an motsa

ɗ

an mitsitsin bakinsa ya ce

‘’Morning’’

ya fad’i

hakan still idanunsa na a kanta….

yana son blue a rayuwar sa gashi yau Manubiya ta sako royal blue d’in hijab wanda colour d’in ya fito sosai, har da kwalli da man leb’e yau ta saka

wanda hakan ya sake rikita Yashjub dan lokaci d’aya ya ji komai ya tsaya

masa chak!..tashi d’aya ta tafi da imanin sa.

Ganin da Manubiya ta yi Yashjub ba shi da niyyar daina kallon ta ne ya sanya ta d’auko wayarta ta shiga yi masa bayanin k’orafin da aka bata…

baiwar Allah har printing ta yi ta taho da shi dan ita har gobe ga

nin sauk’in aikin ta ke yi sosai!

duba da yadda za’a dinga biyan ta har 3Ok a wata…

sai da ta karanta masa ta d’ora da bayani tukunna ta hada da certificate d’in nata da takardar ta tura masa gaban shi.

Shi dai Yash ya ga ta ajjiye takardu kuma ya san t

anata magana tun d’azu amma

wallahi shi bai fahimci komai ba..duk bayanin da ta yi sam bai fahimci ‘Alif’ daga ciki ba.

kallon ta kawai ya ke yi yana jin wani sanyi da nutsuwa sannan yana lissafin mallakar ta a matsayin Mata…....yana mai addu’ar Allah ya

sa idan an fara maganar auren su kar a d’auki lokaci mai tsayi...shi kad’ai ya san me yake ji game da baiwar Allah n nan,a hankali ya fesar da numfashi ya lumshe idanunsa…

lokacin da yake ganin Abokansa a makaranta suna hauka a kan y’an matan su haushi su

ke ba sa,yanzu kuwa ya daina ganin laifin su dan a halin da yake ciki baya jin akwai abunda ba zai iya aikatawa akan baiwar Allah n nan ba muddin bai sab’ama addinin musulunci ba, ko ihu ne idan Manubiya tace tana so ya yi ta kurmawa tou tabbas a shirye

ya ke, zai kurma!!!!

Ashe haka so yake?….

Yahanasu ta yi gaskiya,dan yana bata labarin Manubiya ta ce masa

“in bai yi sauri ya gaya mata yana son ta ba to nan da y’an kwanaki kad’an sai ya ji kamar ya yi hauka.”

“Sir I’m done(sir, na kammala bayanin)”

Mur

yar Manubiya ta katsewa Yashjub tunani wadda ta fad’i hakan ba tare da ta kalle sa ba.

‘’You look cute today!

(Kin yi kyau yau!)’’

Muryar Yashjub ta dira a cikin dodon kunnuwan Manubiya.

Wani irin fad’uwa gabanta ya yi wanda har sai da ya sanya ta d’an s

ake sunkuyar da kanta k’asa.

Kamar ta fashe da kuka haka ta ji…

Tabbas Yashjub so yake ya karya juriyarta dan in aka ci gaba a haka ba zata iya ci gaba da tsayawa kai da fata a kan abunda ta yi wa kanta alƙawari dan ta ga alamar ya dage sai ya ga bayan d’a

n guntun kwarin guiwar tata, bai san a ta ya take iya yin aikin nan da shi ba! bai san me take ji ba! bai san yadda take kokawa da zuciyarta bane ba…..

Tana buk’atar aikin nan

saboda ta samu ta kula da ahalinta amma muddin zai dinga torturing d’inta(wah

alar da ita) irin haka gaskiya ba zata iya jura ba gara ta nemi wani hanyar taimakawa ahalin nata, dan ba za ta yadda ya juyar mata da tunani ba.

Tana sane da shi akan kiran da ya yi mata jiya akan maganar certificate….bayan tuni a zuwanta na farko ya ri

ga ya ce mata ta taho da certificate d’in nata

photocopy, amma shine ya kama ya wani kira ta jiya cikin dare.

Ba ta san takun da yake ha

ɗ

awa akanta ba amma tabbas ba za ta ba shi k’ofa ba, tunda ta san ba auren ta zai yi ba dan wannan ba sa’an auren ta

bane ba, dan ko da ace ya yi niyya ma ta san yana zuwa idan ya ga yanayin gidan su zai fasa, bayaga haka ma ta ma san yana da matar shi tuni dan wannan a shekarunsa ga kud’i ga kyau ya ci a ce yana da mata da Yaro ko Yara….

Sosai Yashjub ya yi mamakin ya

dda Manubiya ta had’e rai ta tamke fuskarta tamau!!!

Ta k’i cewa komai.

Yadda ta chuno d’an mitsitsin bakinta ne ya bashi dariya kuma ya burge sa.

A hankali ya d’an yi murmushi mai sauti wanda har sai da ta ji sa, ba tare da shakku ba ya sake cewa”

You l

ook cute today!

breathtaking,to be precise

( kin yi kyau yau, a taƙaice irin mai tafiya da numfashin nan)”

Saboda yana so ya tabbatar da ‘shin maganar tasa ce ta

ɓ

ata mata rai har haka

kuma yana so ta sake cuno bakin dan ba kad’an ba kara mata kyau yake

yi sannan har ga Allah daga cikin zuciyarsa direct maganar take fitowa.’

Shiyasa tashi d’aya Manubiya ta rikice dan har cikin gangar jiki da tsoka maganganunsa suke shigar ta..jin tana shirin bada Kai ne ya sanya ta ta mike tsaye da sauri…

ba ta yarda ta

kalle sa ba kawai ta fara magana

“Sir! with all due respect, our relationship is strictly professional

(Sir! Cikin girmamawa, dangantakarmu ni da kai ta aiki ce kawai!)

ka ba ni aiki saboda Sir Najeeb yana jin tausayi na amma hakan ba wai yana nufin zan ba

rka ka ci min fuska ta ko wacce siga ba!

Yes,

I know I’m poor (eh, na san ba ni da shi) amma hakan ba shi zai sanya in barku ku ci zarafin talaucina ba,

dan haka ko ma wanne irin tunani ne a ranka game da ni ka daina,

Banaso!..

Sau biyu kawai ka ganni t

a ya har ka samu ƙarfin halin iya gaya mini kalar kyawun da na yi?.

Mu ba komai ba ne face baƙi ga juna. A gaskiya, kirana da ka ke yi cikin dare da kuma yadda kake mu’amala da ni suna sa ni jin rashin kwanciyar hankali.

Aiki ne kawai ya had’a ni da kai,

babu wata alaƙa ta ƙashin Kai da ke a tsakaninmu…

Ka je gida ga Matarka! Na tabbatar tana chan ta yi maka kwalliya..ita ya kamata ka cewa she looks cute (ta yi kyau) ba wai ni ba.’’

Tana gama fad’in haka ta juya da sauri ta nufi k’ofa, ji take yi kamar t

a kurma ihu a ranta ta ce ‘’ku yi hak’uri Inna, na san na yi muku bak’in cikin albashi na duk wata amman ba zan yarda yayi wasa da tunani ba’’….

Dama tun farko yanayin yadda aka bata aikin ya

ɗ

an so ya d’aure mata kai amma kamar yadda Abbakar ya ce

‘taus

ayin ta Sir Najeeb ya ke ji’ ne ya sanya kawai ta kawar da duk wani tunani na rashin kyakkyawan fata,

In ba haka ba a ganin ta tsaf secretary d’insa za ta iya dan aikin sam ita ba ta ga wani dalilin hiring d’in ta (

ɗ

aukarta) da aka yi ba.

Tun lokacin da

ta mik’e ta fara zazzaga masa bala’i ya kasa cewa komai, kuma ya kasa d’auke idanunsa a kanta..dama tun ranar farko da ya fara ganinta a office d’in Najeeb! Yadda ta ƙi yin magana da kuma yadda ta saka kuka ya sanya ya fahimci tana da temper but she’s als

o very weak (tana da zafin rai amma kuma tanada raunin Zuciya)

tunda ga shi yanzu ma sam ta gagara jure tasirin da kallon sa gareta da maganarsa ta yau suka yi mata!!!

Sai da ya fesar da numfashi tukunna ya aiyyana a ransa

‘Kawai ni fatana, Allah ya sa ta



ɗ

an ji wani abun da ya shafi so da ƙauna a kaina, ko da

ɗ

an ka

ɗ

an ne!

Ba wai iya

ɓ

acin rai maganganu da kallona suka janyo mata ba’……..

Ba abunda ya fi ba sa mamaki

irin yadda sam ko sau d’aya bai ji zafin maganganunta ba!

In banda burge sa ma shi kam

ba abunda ta yi kuma ta sake samun mazauni ta zauna daram a cikin zuciyarsa, tabbas Manubiya ta san darajar kanta.

Babu kuma abunda ya fi bashi dariya irin yadda ta balbale shi da masifa kamar ta samu d’an cikinta amman kuma sam ta gagara kallon idanunsa

ko da sau d’aya ne.

Tana kama hanyar k’ofar, Yashjub ya danna wani abu a kan tebur d’in nashi, ya koma ya jingina da jikin kujerar yana kallon yadda take tafe tana sassarfa kamar wadda aka ce mata zai biyo ta ya kama ta ne.

Tana zuwa jikin k’ofar ta far

a k’ok’arin jan glass d’in amman sai ta rasa ta ya ma za ta ja!

Saboda

ɗ

azu k’ofar a d’an bud’e take kad’an amma yanzu kuma kamar an yi sealing (ha

ɗ

e) glass d’in an manne su duka a waje d’aya dan sam babu alamar ta inda zaka ce zaka zuge ko kuma ka tura ka

bud’e…

“innalillahi wa inna ilaihirrajiun” Manubiya ta furta hakan a fili sai kuma wani irin tsoro ya lullub’e ta!

Tabbas Yashjub ne ya rufe k’ofar nan, ko shakka babu.

A yadda ta zuba masa rashin kunya sannan ta wuce za ta barshi a nan wurin.. to fa in d

ai babu mummunar nufi a cikin zuciyarsa game da ita kai tsaye yana zuwa ta san zai koreta ne bayan ya dake ta ko kuma shima ya rama bak’aken maganganun da ta zuzzuba masa!!

Waenda ita kanta sai yanzun ne take tariyo wasu maganganun da ta faffad’a masa masu

zafi waenda bai kamata ace ta gayawa Babban Mutum kamar shi ba, a ranta ta ce ‘’shikenan yanzu na tonawa kaina da kaina asiri, dan shi dai ba cewa yayi yana sona ba amman na bi na tak’arkare ina ta faman cewa ‘dangantakarmu ta aiki ce kawai’.”

In dai k

uma mummunan nufi ne a zuciyarsa game da ita to kuwa yadda ya rufe k’ofar nan

Yana zuwa raping d’inta zai yi shikenan tata ta k’are yau.

Ta aiyyana hakan a ranta Jikinta yana soma karkarwa.

Juyawa ta yi da niyyar ganin me ya ke yi..

ta ganshi zaune ya h

ard’e hannuwansa biyu a k’asan k’irjinsa ya jingina da jikin kujera ya zuba mata ido sai kuma ta ga ya taso ya nufo inda take…

Ai kuwa da sauri sannan a rikice ta juya ta fara kiciniya tana shashshafa k’ofar tana addu’ar Allah ya sauk’o da mu’ujizar da ida

nuwanta za su nuna mata wata tsaga ko alama a jikin glass d’in domin ta samu ta bud’e ta fice.

..

A rikice take dudduba glass d’in tana yi tana waigen sa a gigice.

ganin dai da gaske itan ya nufo ya sanya ta fara dukan glass d’in tana kwala k’arar

‘‘Help’’

Murmushi kawai Yashjub yayi,

dai-dai nan ya k’arasa inda take.

Tsoro da rikici ne suka sanya Manubiya ta juyo ta runtse idanunta ta d’aga hannuwanta sama kamar irin mutun yayi laifi ƴan sanda sun zo za su kama sa d’in nan, kafin a rikice ta ce’’Dan Alla

h ka yi hak’uri’’...

*MANNUBIYA*

*32*

Murmushi kawai Yashjub yayi,

dai-dai nan ya k’arasa inda take.

Tsoro da rikici ne suka sanya Manubiya ta juyo ta runtse idanunta ta d’aga hannuwanta sama kamar irin mutun yayi laifi ƴan sanda sun zo

za su kama sa d’in nan, kafin a rikice ta ce’’Dan Allah ka yi hak’uri’’

Yashjub bai san lokacin da dariya ta kufce masa ba, aikuwa ya shiga yi kalar wadda ya dad’e bai yi ba.

Ba k’aramin k’ulewa Manubiya ta yi ba kuwa, sannan ga tsoron da ya bi ya dabai

baye ta dan haka ta yi k’asa da kanta a take hawaye suka shiga wanke mata fuska.

A rikice ya ce

‘’Ooo’O!sorry,i’m so sorry’’

dan tashi d’aya sai hawayen nata suka d’aga masa hankali.

Bata kalle sa ba kuma bata daina kukan ba sai ma yawa da yaga hawayen

nata sun k’ara, sannan ya lura da yadda hatta jikinta ya ke karkarwa……

A hankali ta d’aga hannunta, ta juya ta shiga k’ok’arin bud’e k’ofar a karo na biyu, wanda hakan ya ke nuni da

alamar so

take kawai ya bud’e mata ta samu ta fice.

Ba zai tab’a iya j

urar ganin ta a hakan ba, dan yadda hawayen nata yake zuba akan kumatunta haka yake ji kamar ruwan zafi ne ake kora masa a cikin k’irjinsa..

So yake ya bud’e mata k’ofar, amma kuma ya san muddin ya bud’e ficewa za ta yi , ba tare da sun fahimci juna ba.

Jin kukan nata ya fara fita da sauti had’i da jan hanci ne ya sanya kawai ya d’aga hannunsa, a nan jikin glass d’in ya danna abunda ya bawa k’ofar damar bud’uwa wanda ba kowa ne ma zai fahimci za a iya bud’e k’ofar da shi ba.

Tana ganin glass d’in ya

ɗ

an

motsa ta saka hannu ta jaa ta bud’e ta yi waje da wani irin sauri…

Zai zama wani iri idan ya bita, kuma ya san ba za ma ta so hakan ba dan haka kawai sai ya juya a hankali ya koma ya zauna akan kujerarsa!

ya dafe kansa wanda har ya fara sara masa.

Sai

yanzun ya fara jin haushin kansa da ya kasa fahimtar ya kamu da kaunarta ne tun a ranar farko..tun asalin farko soyayyarta ta yi wa zuciyarsa sahihin kamu, amma ya gagara fahimta bayan ga gaskiya nan k’iri-k’iri amma bai iya ya fahimta ba ya dinga wahalar

da kansa da kuma ita kanta Manubiyan har da su bata aiki gashi ynzu ta tashi ta dank’ara masa matsayin boss d’inta a kwakwalwa da tunaninta… baya jin za ta yarda da shi cikin sauk’i..a yadda yaga ta

rikice ta kid’ima sannan ranta ya b’aci daga ya ce mata

ta yi kyau

ɗ

innan, ya san idan ba yayi da gaske ba to ba k’aramar wahala zai sha ba kuma sai ta d’auki lokacin da baya so a

ɗ

auka a lamarin nasu kafin ma ya samu matsayinsa na ‘sir’ya goge a idanunta na ‘masoyi’ ya shiga.

A hankali ya sake fesar da iska

, kafin tashi d’aya ya yanke shawarar zuwa gidansu!…

Ba zai sake d’aukar lokaci ko jira ba tunda ga abunda kwana kwana da jiran ya haifar.

Sai da ya jera mata misscalls sama da biyar amma bata d’auki ko d’aya ba.

A take gaba d’aya hankalinsa ya sake tash

i ya yi dan haka ya ga gara ya kira Najeeb..

ko gaisawar kirki bai bari sun yi da Najeeb d’in ba ya ce ‘’ya nema masa adress d’in Manubiya yanzu, gashin nan zuwa wajen sa, idan ya zo zai ji komai’’.

Yana gama fad’in haka ya katse kiran ya bar Najeeb kare d

a waya a kunne..

Wanda ya shiga lissafin

…ya kamata ace a dai-dai wannan lokacin ya fara yi wa Yash dariyar mugunta, duba da yadda a baya yake zaginsu idan yaga suna abu a kan soyayya dan gashi alhakin su ya kama shi, tunda gashi yana nema ya susuce tun k

afin a je ko’ina ma…..da kuma alhakin y’an matan da suka sha yin kuka a gaban sa saboda matsananciyar buƙatar samun kulawar Yash

ɗ

in, amman kuma gaba d’aya tausayin Abokin nasa sai ya hana shi, sakamokon rikici, fargaba hatta da tsoron da ya jiyo k’arara

a cikin muryar Yashjub d’in yanzunnan…

A hankali ya fesar da iska kafin ya furta kalmar ‘’so gamon jini’’ a fili. daga haka ya datse ya kira class rep ya ce “ya tura mass number Abbakar yanzunnan”

A ransa yana mai cewa “k’iri k’iri dai Yash sai ya janyo m

in raini a wajen

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login