Showing 3001 words to 6000 words out of 150519 words
dalilin da zai sa
nya ya yarda da auren Khadjansa da
Imam tun farko, tunda ya san ba sonta ya ke yi ba.
Yana ta fatan su samu su
ɗ
an sasanta, ya so ta wata rana
to kuma yanzu gashi zai auri wadda ya ke so!
Fatanshi
ɗ
aya ‘Allah ya sa Khadijan ta yi hankali ta kwantar da
hankalinta ta yi biyayya ta zauna lafiya…
Wataƙila ta samu matsugunni a zuciyar Mijinta…
In ba haka ba kuwa
Ba ya jin tana da rabo a Zuciyar Imam
……
An
ɗ
an kai ruwa rana kafin
Daddy ya yarda aka
ɗ
aura auren Khadija(Mai tallar nono) da Imam a cikin sati
ɗ
aya.
Wanda a tsakankanin kwanaki bakwai
ɗ
inna babu kalar haukar da Khadija (uwar gida) ba ta yi ba!
Har kalanzir ta zuzzuba a gidan koina lokacin yana bacci
ana i gobe
ɗ
aurin auren!
Allah ya taimaka,
ya ji warin kalanzir
ɗ
in cikin barci dan haka ya f
arka da wuri….
Yana zuwa ya tarar da ita ta na ta ƙoƙarin kyasta ashana….
Da kyar ya samu ya kar
ɓ
e ashanar
ya jefar, ai kuwa ya na jefarwa ita kuma ta rarumo wuƙa.
Fahimtar da ya yi da gaske kishi ya haukatata kuma idan ya barta kashe shi za ta yi, hakan
ya sanya ya fincikota zuwa parlour sannan da kyar ya fitar da ita tsakar gidan ya saka ta a mota…..
Iyayenta tamkar iyayenshi su ke,
dan zai iya cewa shi da
ɗ
an uwansa especially ma shi
ɗ
in kusan a hannun Mahaifiyarta ma ya girma!
To amma kuma ya kama
ta a takawa haukar tata burki!
Tun kafin ta yi
ɓ
arna, shiyasa ba dan ya so ba ya kaita gidansu ya fa
ɗ
awa su Abba duk abubuwan da ta ke yi masa har ƙoƙarin kashe shi
ɗ
in da ta soma yi.
..
Sallamar Imam kawai Abba ya yi
bayan ya bashi haƙuri.. ya ce a bar
ta a nan kar ya koma da ita.
A tunanin ta fa
ɗ
a kawai
za a yi mata, daga nan a maida ita
a ranar amma sai ta ji Abba ya hana! Sannan ya hana a barta ta
fita ko da ƙofar gida ne…
Tana ji ta na gani haka nan aka
ɗ
aura auren Imam da Amarya Khadijah…
Ba ab
unda ya fi
ɗ
aga mata hankali kamar yadda ta ji Abba yace
‘’ba za ta koma gidan Imam ba kwata-kwata‘’
Gashi auren da ta yi haukar a kai an riga an
ɗ
aura
dan haka a take ta fara da ta sani..
Hankalinta ya sake tashi sosai dan sai ta ga kamar ma ta bawa Ima
m damar cin amarcin shi hankali kwance kenan!.
Ko sati
ɗ
aya ba a yi ba ta ƙara gigicewa ta fita a haiyyacinta,
kamar mahaukaciya haka ta koma.
Ba dan Baabaa Larai wadda ta zo musu ta ke bata Baki da kuma Mahaifiyarta wadda itama ta ke tausar ta tabbas da
ba tuni ta zauce!!
….
Sai da ta sha wahala ta ƙara fita a haiyyacinta tukunna
da kyar su Maama Mommy da Daddy su ka takurawa
Abba ya kira Imam ya ce masa “ya zo ya
ɗ
auki Matarsa”
A Lokacin Amaryarsa watan ta
ɗ
aya a gidan har da
ɗ
an cikinta.
…..
Tare
da Larai suka koma gidan nata
saboda itama Laran a lokacin an
ɗ
an samu matsala da ita a ƙauyensu, ta ƙi komawa.
Sosai Imam ya yi mamakin yadda Uwargidan tasa ta chanza lokaci guda….
Ba kishi ba hauka sannan ta ja Abokiyar zaman ta a jiki kamar za ta cin
ye ta domin so…
Cikin jikinta kuwa ko ita uwar iyaka yadda za ta kula da shi kenan.
Sai wani nan-nan ta ke da ita ko abu mai nauyi bata ta
ɓ
a bari ta
ɗ
auka…gashi sun hanata girki shima sun ce ta huta kawai ita Uwargidan da Larai ne su ke yin komai!
Ko ruwa
in ta je tafasawa haka Uwargidan za ta amshe
Ita ko Larai a samu wani ya tafasa mata a kai mata har
ɗ
aki.
Wani Abu da Imam ya yi noticing
shine kullum fuskar Uwar gidansa
da idanunta a kumbure su ke,
ya yi tambayar duniya ta ce mishi kawai ciwon ido n
e ya ke damunta….
A yadda su ka ha
ɗ
e kansu gidanshi kullum cikin zaman lafiya da lumana ya sanya kawai ya kauda duk wasu shakku ya kwantar da hankalinsa ya guji tsawwala bincike sannan ya rungumi matanshi Hannu bibbiyu. Dan sosai a ta
ɓ
angarensa ya ke iyak
a bakin ƙoƙarinsa wajen kwatanta adalci,
shi kan sa ya san yana Namijin ƙoƙari tabbas wajen ganin ya yi adalci a tsakanin Matan nasa
duba da yadda ya ke ji game da ko wacce a cikin zuciyarsa……
A yadda uwar gidan tasa ta ke kula masa da Amaryar ya kamata
ko Albarkacin haka ne a ce ta ci itama
ta samu guri a zuciyarsa
Amman har gobe ya kasa bata
ko da kaso
ɗ
aya ne a cikin
ɗ
ari na zuciyar sa saboda
Amaryar ta riga ta ha
ɗ
e ta mamaye gaba
ɗ
aya kaso
ɗ
ari
ɗ
in
Itace zuciyar tashi ma gaba
ɗ
ayanta.
Amman ku
ma dukda haka
Yana iyakar bakin ƙoƙarinsa sosai wajen boye hakan.
Abu
ɗ
aya ya ke yi wasu lokutan ya ke tonawa kan sa asiri….
Kasancewar sa mutum mai masifaffen kishi ya sanya kishinsa ba ya
ɓ
oyuwa akan Amaryarsa amma Uwargidan sam ba ya nunawa sosai.
Ts
ananin kishin sa a Amaryar ya janyo ko Abokan shi ba ya bari su gaisa da ita. Idan za a fita ya dinga gyara mata zaman hijabinta ya na rufe koina, ko gaisuwar mai gadi in ta amsa su ka
ɗ
an gaisa sai ta ha
ɗ
u da mita na ƴan kwanaki
Sa
ɓ
anin yadda ya ke nunawa
uwar gidan sa halin ko in kula.
Shiyasa ko ba a fa
ɗ
a ba ko ya
ɓ
oye su sun riga sun sani.
Ba tare da shi kanshi ya san sun gama ganewa
ɗ
in ba.
Cikin Amaryar ya na watansa na biyar Imam ya tattara gaba
ɗ
aya dukiyarshi ya damƙawa babyn da za ta haifa!
Mac
e ko Namiji ya ce shi bai damu ba, kawai dai shi ya san ya da
ɗ
e da gama yanke shawarar idan aka Haifa mishi baby na farko a rayuwarshi to ya bada komai nashi a babyn kenan…
Amaryar har kuka ta dinga yi akan ya janye wannan ƙudiri nashi
dan a ganinta zai
janyo mata baƙin jini ne amma furr ya ƙi ji ya ƙi gani.
Daga ƙarshe dai ya tilasta ta ba yadda ta iya ta haƙura ta bi tsarin nasa sannan su ka tsayar akan ‘Maganar za ta tsaya iyaka su biyu’
Idan Allah ya sa ta haihu shi zai ci gaba da kula da dukiyar ha
r sai Yaron ko Yarinyar ta/ya kai munzalin aure tukunna za a damƙa mishi komai…
A cewarshi sannan a yadda ya faiyyace mata wai kyauta ce kawai ya ga damar bayarwa
sabooda farin cikin samun haihuwa ne shiyasa ya shirya hakan a
ɗ
an da zai haifa na farko k
uma ko da ace uwar gidansa ce ta haifa tou hakan zai yi…
Amman a chan cikin zuciyarshi
har ga Allah ya yi hakan ne saboda tsananin so da ƙaunar da ya ke yi wa Amaryar tashi!
Dan yadda ya ke sonta ya kuma kwallafa rai a kanta haka ya ke ji da cikin jikinta
shima, kamar ranshi. Ba ya fatan wani abun ya sameshi ta wulaƙanta.
Ya san su Abba ba za su bar Yaron ya wulaƙanta ba amma ita fa! Dan ta Uwargidansa ta na da nata gatan Amaryar ce abun ji…
Wani sabon abu da ya fara lokacin da cikin ya kai wata bakwai
shine
rashin godewa abunda su Larai su ke yi!
Duk kalar ƙoƙarin da su ke yi waAmaryar sai ya daina gani..
Ko maganinta ne idan ba ta sha a kan lokaciba to ranar sai an ga abun mamaki! Dan rashin kara ya
dinga masifa kenan har washegari.
Kuma in dai Ama
ryar ta yi missing magani tou ko dai ita Uwargidan su na girka mata abinci ne sun sha’afa ko kuma wani abu makamancin haka…amma sam Imam ba ya fahimta.
Ganin rigima ta na shirin fara kunno kai hakan ya sanya ita da kanta Amaryar ta kar
ɓ
i magungunan nata
daga Hannun Abokiyar zaman tata ta ce za ta dinga sha da kanta.
Dan ita kanta abubuwan da Imam
ɗ
in ya ke yi sam ba ta jin da
ɗ
insu…
Ko dan yadda su Laran su ke sonta da gwada Namijin ƙoƙari wajen bata kulawa ita da abunda ya ke cikinta ya kamata ace ya y
aba amma kamar ma ba ya gani. Shi komai kawai ita da cikin Jikinta.
Abunda Imam ya ke yi a kan cikin nan za ka
ɗ
auka a kan shi aka fara haihuwa a duniya!
Abu
ɗ
aya da uwar gidanshi ta yi shine kau da Kai!
Sosai ta yi ƙoƙari wajen
ɗ
auke kanta ta rufe Idanu
nta, sam ta ƙi
yarda ta biye mishi, kuma
sarai ta san da maganar ‘bawa
ɗ
an da Amaryar za ta haifa kakaf dukiyarshi da ya yi amman shima ba ta ce masa ƙala ba!
Dan ita a wannan lokacin babbar damuwarta
Ita ce yadda ta gagara
ɗ
aukar ciki!
Dan haka ta duƙufa
addu’a
sannan ta bar Imam ya na ta kinibibin shi shi
ɗ
aya.
Ƙ
arƙari idan ya ce ba ta yi wa Amaryarsa abu ba
ta bashi haƙuri kawai
a wuce wajen, ko yana mita bata biyeshi.
A kwana a tashi….
edd
ɗ
in Amarya ya cika har ya wuce
amman sam ba ta ji motsi ko
alamun labour ba, dan haka su ka
nufi asibiti.
Su na zuwa tun a gwajin farko
aka fahimci
Babyn babu rai ya ma da
ɗ
e da mutuwa dan har kamar ya fara dagargajewa ma.
Sumewa Imam ya yi a wajen da jin wannan mummunan batu!
Dan tabbas bai ta
ɓ
a shiga tashin
hankali kwatankwacin na wannan lokacin ba.
Har aka yi aikin aka gama aka cire babyn aka mata wankin ciki bai farfa
ɗ
o ba.
A tare su ka yi jinya a asibiti ita da shi dan ba ka
ɗ
an ba jinin shi ya hau !
A bangaren Amaryar itama abun babu sauƙi sam!
Dan ba
yan kwana biyu da yi mata wankin ciki
Yayarta itama ta rasu!
Ta sanadiyyar haihuwa da ta zo yi
duk su biyun ita da Yaron ba wanda ya rayu.
Shiyasa abun sai ya ha
ɗ
e mata biyu, gaba
ɗ
aya ta burkice…
Ba dan ƙarfin Imani ba da tuni ta zauce tsabar yadda abu
buwan su ka daketa.
Imam ma sosai ya yi fama dan kamar wani ƙaramin Yaro haka ya ke kwana ya na wuni kuka, ga rashin lafiya, sai da Mahaifiyarsa(Yahanasu)
ta tsawatar masa ta yi
masa nuni da muhimmancin kar
ɓ
a da yarda da ƙaddara tukunna da kyar da taima
kon Allah da addu’o’i ya
ɗ
an dawo dai-dai.
Ko a gidan nashi ma sai da aka kwashe duk wasu kayayyaki na babyn da ya kashe uban ku
ɗ
a
ɗ
e ya yi ta siya ya na jibgewa a
ɗ
akin da aka ware guda domin babyn tukunna
aka samu sa’ida!
Dan kafin a kwashe
ɗ
in haka nan
zai shiga
ɗ
akin ya rungume kayan Yaron ya yi ta uban kuka kamar wani ƙaramin Yaro abun tausayi!
Dama shi tun ya na Yaro yana da masifar son ƴaƴa
Shiyasa ya kwallafa rai akan cikin jikin Amaryar tashi masoyiyar shi, sai dai kuma
Ƙ
addara ta riga fata………..
*Bayan Watanni Uku*
Kamar ha
ɗ
in Baki, a lokaci guda duk su biyun su ka samu ciki.
Sai dai edd na uwar gidan ya fi na amaryar
A yadda ya nuna Ita uwargidan ce za ta fara haihuwa da sati biyu daga nan amaryar itama ta haihu …
Murna wajen Imam ba a magan
a
amman a wannan lokacin ma duk yadda ya so ya
ɓ
oye kowa sai da ya fahimci ya fi farin ciki da cikin jikin Amarya.
Kasancewar Uwar gidan itama ciki gareta wannan karon shiyasa aka ƙaro mai aiki, wadda ta ke zuwa da tafiya su ka ha
ɗ
u ita da
Larai su k
a yi ta kula da su.
Kamar yadda Imam ya yi wanchan karon haka ya yi wannan ma
Ya kwashe komai ya damƙawa
ɗ
an cikin Amarya.
A nan ne kuwa ya ga
ɓ
acin ranta kalar wanda bai ta
ɓ
a gani ba dan burkice masa ta yi, ta ce ba zai yiu ba, in har gaskiya za a b
i ai itama yayar tata ciki gareta….
Har kuka ta dinga yi masa sannan ta ha
ɗ
a da nasihar kar ya yarda ya zamto cikin Maza masu zalinci babu kyau sam.
Ita Amaryar babban abunda ya sake
ɗ
aga mata hankali ma shine tunda ta ke da Uwargidan ba ta ta
ɓ
a cutar da
ita ba!
Abunda ta ke yi mata ko Ƴar uwarta wadda ta rasu ba ta yi mata shi ba…dan haka ta yaya zai dinga yi mata haka saboda Allah ita kuma ta na
ɗ
e Hannu ta zauna ai ba zai ma yiu ba.
Ita kam babu ruwanta kuma idan ya matsa sai ta je ta samu su Daddy ta fa
ɗ
a musu dan ba da ita za a yi wannan zalincin ba
……
Yanayin yadda cikin Amaryar ya yi tsini kamar wanchan karon na farko
hakan ya saka masa yaƙinin Namiji za ta haifa in sha Allahu sa
ɓ
anin
na uwar gidan wanda ya bi jikinta sosai yasanyata ta yi ƙiba.
Shiyasa ya zauna ya yi ƴan lissafe lissafensa tukunna ya yanke shawara, ya zo ya sanarwa Amaryar cewa tunda ta
ɗ
aga hankalinta kuma ta ce ya yi adalci shikenan zai yi…
Na farko ya fasa bada duka dukiyar
maimakon hakan zai rabata gida biyu ne ya bayar da
rabi ya riƙe rabi
Sannan zai bayar a duk wadda ta haifa masa
ɗ
a Namiji
Idan kuma duk su ka haifi maza tou sai a rabata gida biyu a bawa kowa kashi
ɗ
aya, kuma kamar tsarin farko shi zai ci gaba da kula da ita har sai
Yaron ya kai munzalin aure ko shekaru g
oma sha takwas tukunna zai damƙa masa abunshi.
A wannan karon ma ya kawo mata wani dalilinsa na yin hakan, inda ya ce Yaro Namiji na farko ya kamata a bashi support tunda duk ƙannensa a ƙarƙashinsa su ke sannan kuma dama ya na so ya bada kyautar saboda f
arin ciki dan haka gara kawai a barshi ya yi…
Sai dai ita Amaryar sam ba ta fahimci fa’idar yin hakan ba.
Tun ba ma yadda ya ware ta ita ka
ɗ
ai ya gayawa ba bayan itace ma ƙarama….
A ganinta kamata ya yi ya ha
ɗ
e su duk su biyun ya yi shawara da su,
Idan ma
hakan ne decision
ɗ
insa tou ya gaya musu a tare.
Ganin da ta yi ranshi ya na sake
ɓ
aci game da tirjiyar da ta ke ta yi ne ya sanya kawai ta haƙura ta rabu da shi…
Amman har ga Allah a chan ƙasan ranta addua ta ke yi Allah Ubangiji ya sa Uwargidan ta haif
i
ɗ
a Namijin.
Sarai ta san Matar tana fahimtar wasu abubuwa na bambanci da Imam
ɗ
in ya ke nunawa a tsakanin su amman dukda haka ta ke kauda Kai kamar ba ta san me ke faruwa ba, but fa ta san ko zuciyar gwal gareta muddin akace yau sun haihu tare ita ta hai
fi
ɗ
a Namiji an
ɗ
auki rabin dukiya an bata tou fa ta san zaman lafiyar ta da Abokiyar zaman na ta tsaf sai ya ta
ɓ
u!
Ita kuma bata son abunda zai ha
ɗ
ata da Abokiyar zaman nata
dan ta yi mata abunda ba za ta ta
ɓ
a mantawa da ita ba..yadda ta
kula da ita da
ɗ
an cikin ta na fari ba ko wacce kishiya ce za ta iya ba, ko
ɗ
anuwa na jini iyakar abunda zai yi maka kenan.
…………
A kwana a tashi…..
Watan haihuwa ya kama, cikin hukuncin Ubangiji ko wacce ta sauƙa lafiya, sai dai fa abubuwa ba su tafi yadda Imam ya tsara
ya kuma yi zato ba domin Amarya Mace ta Haifa!
Uwar gidan shi kuma ta haifi
ɗ
a Namiji…
Sam-sam Imam bai yi zaton hakan ba.
A ranar da suka haihun ma ba ya nan….
Ya yi tafiya zuwa Abuja,
A ranar da zai tafi
ɗ
in Uwargida ta fara labour da sassafe dan haka
ya bar musu duk abunda ya san za su buƙata sannan ya ce shi da Amarya