Showing 72001 words to 75000 words out of 150519 words

Chapter 25 - Mannubiya Complete

jagora basu ga kowa a wajen ba, a k’asa ma kwata-kwata mutum shida suka gani

daga receptionists sai wani a cikin suite sai masu gadi da cleaner, da alama dai company d’in bayan kasancewar sa private to mai company d’in ma baya buk’atar mutane da hayaniya tunda gashi itama ce mata aka yi dama ’sau d’aya za ta dinga zuwa a sati’.

S

una tafe ita da Ya Musbah suna bin bayan wannan baturiyar kowa da abunda yake aiyyanawa a ransa…

wani dogon corridor suka bi kafin su k’arasa wani babban guri tsakiyarsa na

ɗ

auke da wani abu kamar round about cikinsa duk flowers masu asalin kyau da ƙamshi

..

A ta chan gefen hagu suka hango wani waje kamar d’an k’aramin parlour mai d’auke da wasu d’urma d’urman sofa, 3seaters guda uku, masu tsananin kyau da d’aukar hankali sai center table a tsakiyar su da fridge da dispenser a gefe da gefen su.

Yayin da tsa

kiyar wajen ke d’auke da wani makeken roundabout wanda aka cika sa da shuke shuken flowers masu tsananin kyau da kamshi, sai kuma wuta kamar na pop yana ratsowa ta k’asan flowers d’in yana k’arawa shuke-shuken asalin kyau da d’aukar hankali…

Manubiya bat

a gama tunanin ta ya ake bawa flowers d’in ruwa ba ta ji baturiyar ta ce

mata “this way miss(nan za mu yi’’

Kafin ta kalli Ya Musbah ta ce masa

‘’U can wait,right there(ka

ɗ

an jira ta, a chan).’’

Ta fad’i hakan tana mai nuna masa wannan d’an mini parlour

d’in da yake ata chan gefen hagu.

Kwata-Kwata k’ofofi uku ne a wajen na glass,biyu suna kallon juna d’aya kuma yana opposite wannan mini parlourn da aka ce ya Musbah ya zauna

duk da roundabout d’in flowers d’in da yake a tsakiyar su tsaf kake iya hang

o komai da ya ke a ciikin dukkan wajajen.

Biyun da suke facing juna, a d’ayan kana iya hango tebura

da chairs d’insu da computer a kan ko wanne tebur, yayinda wanda yake kallon sa kuma yake d’auke da k’atoton tebur (dogo) da kujeru wajen sama da arba’

in zagaye da shi, sai doguwar micro a gaban ko wacce kujera a ajjiye kan tebur d’in sai projector d’insu da suka bari a kunne.

Sai last one d’in wanda yake kallon mini parlourn, a saman shi an rubuta C.E.O, kana iya hango normal tebur sai kujeru biyu a gab

an tebur d’in da kuma d’aya tana kallon biyun

sai parlour mai kyau a gefe da kuma wani mutum sanye cikin white suite dogo k’ak’k’arfa giant ya juya baya yana kallon waje da waya a kare a kunnensa….



Da farko Ya Musbah ya so ya yi musu da aka ce kar ya sh

iga, sai kuma yaga ai yana iya hango komai na cikin inda aka ce Manubiyan ta shiga dan haka ya je ya nemi waje ya zauna, yana kallon su har wannan baturiyar ta shiga Manubiya ta bi bayanta suka mayar da k’ofar suka rufe ….

BULAMA ✍



0

903 441 3252

*MANNUBIYA*

*25*

Tun lokacin da suka shigo cikin company d’in ya gan su ta cctv, kuma ya fahimci ita ce dan ba shi da appointment da kowa yau sai ita…

Babban abunda ya d’aga masa hankali shine Ya Musbah, ba ya ganin fuskokin

su sosai shiyasa bai fahimci fusgen kamannin da suke yi ba dan shi a tunanin sa ma Abbakar ne tunda tare ya gansu the other day(a wachchar ranar).

a ran sa ya ce ‘’to ko dai saurayin ta ne da gaske’’

A take wata zuciyar tace masa’’to idan ma saurayin nata

ne ina ruwan ka, kai naka ba kawai ka san more about her ba(santa bane ba)..’’

Yadda yake jin zuciyarsa tana tafarfasa ne ya sanya ya kasa jurewa, ya rufe computer, ya mik’e ya bar gaban tebur d’in nasa ya isa jikin glass ya juya baya yana mai kallon w

aje.

A haka secretary d’in tasa ta shigo ta same shi ta ce masa ‘Ga Manubiya ta zo’.

Yana bata izinin ta je ta shigo da ita ya zaro waya ya hau kiran Najeeb dan ji yake yi kamar ya sanya security su fitar da wanda yake tunanin Abbakar ne….

yana so ya san

alak’ar ta da shi kafin ma su shigo masa office..

‘’You are suppose to be busy by this time(kamata ya yi a ce kana busy a dai dai wannan lokacin), ko ba da safe ka ce mata ta zo ba?’’

muryar Najeeb ta katse masa tunanin da yake yi.

‘’Yeah, gata nan ta zo

amma basu shigo ba.

amm..Najeeb, wanann yaron da na gansu tare ranar a office d’inka waye ne shi d’in saboda yau ma gasu nan ta taho min da shi.’’

D’an guntun murmushi Najeeb ya yi yana mai jiyo kishi k’arara a muryar Yashjub d’in,kafin ya ce ’’inaga kam

ar d’an uwanta ne..

Maybe ko cousin dan surname d’in su ba d’aya bane, amma wani lokacin ma tare suke shigowa aji, so ina ga kamar a gida d’aya suke zaune.

are u jealous?’’

Najeeb ya k’arashe bayanin nasa da tambaya, yana mai dariya k’asa-k’asa.

Tsaki

Yashjub d’in ya yi, dai dai nan Racheal ta d’an yi knocking tukunna ta yi sliding k’ofar ta shigo Manubiya na biye da ita a baya.

Sama-sama ya fara jin Najeeb

saboda lokaci d’aya jikinsa ya yi sanyi sannan yanayin bugun zuciyarsa ya k’aru.

A hankali ya

cewa Najeeb “I’ll call you back’’

bai jira jin mai Najeeb d’in zai ce ba ya katse kiran, yana jin yadda yanayinsa ya sauya tashi d’aya.

Cikin nutsuwa Racheal ta ce ’’Sir she’s here(ga ta nan)”

A hankali ba tare da ya juyo ba ya ce ’’Thankyou,you can leave

(za ki iya tafiya, na gode)”

Racheal d’in ce ta nunawa Manubiya inda zata zauna kafin ta juya ta fita bayan Manubiyan ta zauna da kyar, tunda suka shigo company d’in jikinta yayi sanyi..tunda ta hango shi a tsaye ya juya baya ta nemi kuzarinta ta rasa!!!

gashi yanzu kuma tunda ta shigo office d’in k’irjinta ya hanata sukuni…

Gashi ƙamshin turarensa wanda ya karad’e ilahirin office d’in ya yi mata kamar na mutumin da ta had’u da shi a office d’in Sir Najeeb,

dan tabbas hancinta ya shak’i ƙamshin sosai a

wachchar ranar a lokacin da ya matso kusa da ita zai fita…

sannan babu abunda ya fi d’aga mata hankali irin muryar da ta ji a yanzu a lokacin da ya yi wa wadda ta rakota( Racheal) magana, kar dai fa ace wannan mutumin ne, dan in dai ba gizo muryarsa ta yi

mata ba to kuwa tabbas wannan Mutumin shine wanda suka had’u da shi a office d’in Sir Najeeb kwanakin baya.

Da kyar Yashjub ya d’an nemo nutsuwa ya sakawa gangar jikinsa tukunna ya juyo, cikin takun shi na k’asaita ya nufo tebur d’in, ba tare da ya kalle

ta ba.

Wani irin bugawa zuciyar Manubiya ta shiga yi

dan yana juyowa ta shaida shi

‘’amma Abbakar bai kyauta min ba’’

ta fad’i hakan a chan k’asan zuciyarta, kafin a hankali ta sunkuyar da kanta k’asa tana jin kamar ta tashi ta fita da mugun gudu.

Idan

uwanta da zuciyarta sam

sun gagara daina zuzuta mata

tsananin kyawun da yayi ga wani haiba da kwarjinin da yayi mata wanda suka taimaka wajen sake hautsina mata lissafi…

A ranta ta shiga aiyyana cewa “ashe wanchan karon ban gansa sosai ba.’’

Tana wannan

tunanin Yashjub ya nemi waje ya zauna a kujerar da take facing d’in ta, yana mai jin k’irjinsa yana bugawa, kafin a hankali ya d’ago lumsassun idanuwansa ya zuba su a kanta…..

Wani irin sanyi ya ke ji yana ratsa shi tun daga saman kansa har izuwa kan babb

an d’an yatsan k’afarsa….a take wata nutsuwa da kasala suka sak’e rufar masa yana mai jin wani irin nishad’in da bai tab’a jin kwatankwacin irin shi ba.

Duk da yadda ta sunkuyar da kanta hakan bai hana shi k’arewa kyakkyawar fuskarta wadda ke zagaye a ciki

n hijabi kallo ba, a hankali a chan k’asan zuciyarsa ya ce

‘’Subahanallah, MashaaAllah,

Allahu akbar!..’’

Tun lokacin da ya zauna ya fara kallon ta ta diririce…

da kyar da mugun kyar ta samu ta iya d’ago fuskarta da niyyar gaida shi amma sai ta ga ya kaf

eta da kyawawan idanuwansa, cikin sauri ta kauda kanta gefe saboda girma da nauyin da ta ga kwayar idanun nasa sun yi mata…a hankali ta ce

‘’Good morning,Sir,’’

da kyar.

Lumshe idanunsa yayi ya bud’e yana kallon yadda take kallon gefe kad’an ita ala dole

ba za ta had’a ido da shi ba bayan kwanakin baya da kyar ta iya zare idanunta a nashi..bai san lokacin da wani murmushi ya kufce masa ba

wanda har sai da ta d’an jiyo sautin kad’an, kafin cikin kamala da dad’in sauraro ta ji ya ce ’’’Morning, you called

me day before yesterday(kin kira ni shekaran jiya)’’

ya fad’i hakan har zuwa wannan lokacin idanuwansa na a kanta yana yi mata wani irin kallo kamar wanda yake so ya k’irga duk wata b’ular gashin da ke a fuskarta ne. Shi kan sa yana so ya d’an d’auke idanu

n nasa daga kanta amma sam ya gagara, babu abun da ya fi d’aure masa kai kamar yadda tashi d’aya ya shiga nutsuwa walwala da farin ciki da annashuwar da bai tab’a shiga ba.

A hankali ya ji ta ce

“Sir Najeeb said you have a job for me, that’s why I called

.(sir Najeeb ne ya ce kana da aikin da za ka bani, shiyasa na kira).”

Ta k’arashe maganar a hankali

kamar tana jin tsoro.

Shiruu ya yi, yana kallon ta kafin chan yace’’Yeah,i do,can i see your credentials.(eh, ina da aikin da zan baki, zan iya ganin taka

rdunki?.)”

A hankali ta lumshe idanuwanta dan sai a wannan lokacin ne ta tuna bata d’auko na secondary school ba wanda ya ke shi a chan sama yake a cikin akwati, dama tana ta zuci zucin za ta d’auko ta had’a da ragowar sai dai kuma har ta fito Allah bai b

ata iko ba, haka nan ta mik’a masa na primary da diplomar ta tukunna ta ce masa’’ ta manta na secondary school d’in’’

dan haka ya ce ‘’ba damuwa, next zuwan da za ta yi, ta zo da shi’’.

Ya d’an jima yana nazari kafin

ya fara yi mata bayanin aikin

nata y

adda zata fahimta…….

‘’Akwai estate a Kano, Lagos da Abuja.

Bana so idan abu ya b’aci a dinga kira na direct almost everyday (kusan kullum) sannan secretary d’ina is very busy (aiyyuka sun yi

mata yawa) itama, dan haka zan tura musu number d’inki ta yadda

duk wani complain idan za su yi kawai za su gaya miki ki tara ki ajjiye, sai ki dinga reporting to me ranar Friday, duk Friday…

Kinga yau Monday to in four days time(to nan da kwanaki hu

ɗ

u) za ki zo nan kenan,

Amman idan akwai abu urgent(abunda ya ke buƙa

tar a duba cikin gaggawa), za ki iya kirana ko kuma ki gaya min ta online, ba sai kin jira friday ba…

k’arshen wata zan dinga baki 30k.

Mun fahimci juna?’’.

A hankali ta jinjina kai kafin ta ce ‘’Yes,Sir

Thankyou so much.’’



Jinjina kai kawai yayi yana

mai sauk’e wata b’oyayyiyar ajiyar zuciya kafin ya mik’a mata wata takarda mai d’auke da wajen saka;

Full name

Address

Personal sickness

Email

Phone number,da sauran su……

ya ce’’ki yi filling wannan.(ki cike wannan).”

Cikin nutsuwa ta zaro biro a ja

karta, ta hau cikewa…

wajen phone number ne ta bari blank dan bata san ya za ta yi ba, da farko ta yi tunanin ta saka number Siyama tunda ita bata da waya sai kuma taga ai aiki ne bai kamata ta d’aura mata komai a wayarta ta takura mata ba sannan anytime z

a ‘a iya kiran ta kar aji wata ta d’auka ya zamana kamar bata d’auki aikin ma da mahimman ci ba, shiyasa ta ga gara a yi

k’ok’ari a san yadda za ayi inshaaAllah ko mai torchlight ce su nemo sai ta taho da number tare da certificate d’in nata, dan haka ta

bar wajen blank

ta cike ragowar.

tana gamawa ta mik’a masa, tana addu’ar Allah ya sa daga wannan ya sallame ta.

D’auka ya yi, ya kalla yaga ta bar wajen phone number blank

dan haka ya ce ta k’arba ta k’arasa cikewa.

Sai da ta d’an yi shiruu tukunna tace

masa ‘’a yanzun ba ta da waya,amma inshaaAllah zata taho da phone number d’in a next zuwanta tare da secondary school certificate d’in nata.’’

Shiruu yayi kawai ya zuba mata ido yana mamakin ‘ta ya kamar ta ace bata da waya’

Wanda hakan ya sanya Manubiy

a ta ji kamar ta kurma ihu!..dan

gaba d’aya ya d’aure ta da idanuwansa, ta koina jin kwayar idanunsa take yi suna yi mata yawo a jiki.

Ya jima yana k’are mata kallo kafin ya d’an sunkuya ya janyo d’aya a cikin drawer da ke jikin tebur d’in ya zaro wata fa

rar leda, jiya ya sayi A1 d’in zai bawa mai wankin su da ya ce masa wayarsa ta fad’a a ruwa…

A hankali ya mik’a mata ya ce ‘’ga shi,idan kin yi charji sai ki turomin messge da number ki meanwhile zan basu email d’in ki idan number ya zama ready sai ki turo

min in tura musu ta yadda za ki fara aikin asap.’’

ya fad’i hakan yana mai mik’a mata wayar.

sai da ya sake cewa ‘’ki karb’a mana,consider it as an allowance’’

tukunna a hankali kamar mara lakka a jiki ta sa hannu ta karb’a ta ce ’’Nagode,sosai,’’

dan d

ama har ga Allah bata san ta ina zata fara neman waya ba su da suke fama da abinci.

Ganin ya yi shiruu ya koma ya jingina kawai yana k’are mata kallo ne ya sa ahankali ta sake cewa’’na gode’’

daga nan ta yi masa sallama ta mik’e ta nufi k’ofa tana adduar

Allah ya sa kar ya sake tsayar da ita, a haka har ta fice daga office d’in.

..

Tana fita ya lumshe kyawawan idanuwansa, ya kwantar da kansa a jikin kujerar da yake kai a zaune,

a hankali a fili ya ce

‘’It’s official,I’m in love

(Ta tabbata son Yarinyar na

n na ke yi.)”

Sai da ta fita daga office d’in, ta tabbatar ta zugo k’ofar tukunna ta bud’e hancita ta shaƙi iska sosai sannan ta sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya….

Da kyar ta samu ta ja k’afafuwanta ta nufi inda Ya Musbah ya ke wanda ya riga ya mik’e

tsaye tun lokacin da ya hango fitowar ta.

Kallon sa take yi tana jin k’auna da tausayin d’an uwan nata suna ratsa ta..

‘dole haka nan za ta hak’ura ta yi aiki da Yashjub ko dan y’an uwanta….domin ta samu ta bawa Ya Musbah jari sannan ta kula da ahalinta. d

ukda kuwa bata san ta yaya zata iya rayuwa da wannan mutumin wanda yake k’ok’arin tarwatsa mata zuciya ba amma dole ta dage ta taimaki ahalinta under any circumstances(duk rintsi), zata tsaya tsayin daka InshaaAllah ta yaƙi tunaninta sannan ta taimaki kant

a ta hanyar tirsasawa zuciyarta da tunaninta akan su daina yaba mata kyau,kwarjini,jarumta da nutsuwar Yashjub….

inshaaAllah daga yau duk wani abu mai kyau nasa ita kuma zata yi k’ok’ari wajen ganin ta maidashi mara kyau a idanu da tunanin ta…

Opportunity

comes at ones (Dama ta kan zuwarma wani lokaci

ɗ

aya kawai) hakan ya sanya ba za ta zubar da wannan damar ba, inshaaAllah za ta yi k’ok’ari ta daure ta dage ta yak’i zuciyarta,ta samu ta taimaki ahalinta..’

Da wannan tunanin ta k’arasa inda ya Musbah yake t

saye.

Jarumta ta aro ta yafawa gangar jikinta ta k’ak’alo murmushi sannan tace “Na samu aikin, ya bani har da allowance na waya ma..

Aikin dole yawanci ta waya ne..”

nan ta d’an yi briefing masa (masa taƙaitaccen bayani) akan yadda suka yi da Yashjub.’’

Cikin tsananin murna ya Musbah yace mata ‘’congratulations Manu.

kin ga rabo ko? lecturer d’in da kika tsana ga shi yau yayi miki gata.

na miki murna gaskiya…

gashi aikin ba wahala kwata-kwata, kuma na yarda da company d’in a yadda yake d’innan nasan an

sanshi kuma ya na bin k’a’idoji, kinga kuwa ba za’a cutar da ke anan ba..mu je’’

Ya fad’i hakan yana wucewa gaba,

a hankali Manubiya tace

‘’Tam’’ daga haka ta bi sa suka kama hanya suka fita……

‘Tana jin tsoron kasancewar ta tare da Yashjub amma ya zame

mata dole ta taimaki ahalinta’

Ta sake aiyyana hakan a ranta,

ahankali ta sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya..

‘tabbas gaskiya Abbakar ya fad’a ranar chan da ya ce mata Yashjub ne ‘crush d’in ta,’

Ta aiyyana hakan a ranta, da sauri kuma sai ta kawar da t

unanin, a ranta ta ce

‘’Manubiya wake up(farka!!)…

mutumin nan ba sa’an ki bane ba,

ki duba ki ga ko shekaru talatin ba lalle ya rufa ba amma ya mallaki estates nashi na kan sa…

matsalolin rayuwarki ma kad’ai sun ishe ki, kar ki je ki jefa kanki ga halak

a…”

BULAMA ✍



0903 441 3252

*MANNUBIYA*

*26*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login