Showing 12001 words to 15000 words out of 150519 words
adaidaita sahun ya shige ya yi gaba……
Anguwar su
ɗ
aya da Abbakar shine best frnd
ɗ
inta…tun daga sakandire Abotar tasu ta yi ƙarfi, amma tun su na Yara su ke shiri dama.
Abokanayen sa Maza har dariya su ke yi masa, dan
tun yana
ɗ
an mitsitsi ya ke
wanke ƙafa ya tafi gidan su Manubiya wasa, tun Inna ta na hanawa har ta zo ta daina.
Har k
awo yanzu kuwa shi ka
ɗ
ai ne Abokin ta tun da ita
ɗ
in
Ba kula ƴan unguwar su ta ke yi sosai ba saboda munafurce munafurcen su…..
a makarantar ma
ta ƙi yarda ta yi ƙawaye, dukda yadda ake son yin ƙawance da ita amma ita ta ƙi yarda, duba da yadda yaran su
ke ƴan gayu
a ganin ta idan ta biye su za a iya zuwa ga
ɓ
ar da za ta kasa godewa Ubangiji na na’imomin da ya yi mata.
gashi kullum idan aka je wajen cin abinci sai dai su yi ta biya mata
ku
ɗ
in
Ba wai suna complain bane kawai dai itace ba ta feeling comfo
rtable (ta kasa sakewa da hakan) kuma ta san
yau da gobe sai Allah
shiyasa ta ke ta zizzillewa.
Tun suna yi mata naci tana zillewa har suka haƙura suka rabu da ita. Su suna ganin girman kai gare ta, yayinda Ita kuma a nata ganin bai kamata ta
ɗ
aurawa ka
nta abunda ya fi ƙarfin ta ba,
Matsalar ta ma ita kam ta isheta.
Tana wannan tunanin mai Adaidaita sahun ya ƙaraso cikin layin nasu wanda ke a Anguwar ‘Gadon ƙaya’,.
Ita ta nuna masa ƙofar gidan ya yi parking daga haka ta fito ta nufi gidan bayan ta c
e masa ta gode .
Tun a kallo
ɗ
aya, in aka yi wa gidan ya ke faiyyace da
ɗ
ewarsa a doron ƙasa, sannan bai ma san me ake nufi da renovation (sabunta gini) ba.
Katangar gidan both side sun tsatstsage, yayin da fentin ya goge gaba
ɗ
ayan shi!
Ba’a ganin komai
sai jar ƙasar ginin gidan wanda ya baiyyana daga tsakiya zuwa ƙasa, ta saman katangar kuma ragowar farar ƙasar fentin da bata gama gogewa ba ce itama duk ta yi dishi-dishi, sai zanen Yara na shirme wanda akayi da baƙin gawayi, duk a jikin katangar.
Normal
ƙaure ne a gidan sai dai shima ya ji jiki matuƙa……
Tana ƙarasawa jikin kyauren ta kama ta tura ƙofar ta kutsa kanta cikin gidan…
Dama tun daga waje yanayin gidan ya ke nuna Babban gida ne, saboda yanayin fa
ɗ
in tsayin katangar…
Ta wani dogon soro ta bi
kafin ta ƙarasa ainihin cikin farfajiyar gidan!
A ta farko-farko gefen dama babban kitchen
ɗ
in gidan ya ke wanda murhu da kurfeti suka cika shi taf ta inda hakan ya ke nuni da kowa girkin shi ya ke yi a daban.
Farfajiyar asalin cikin gidan kuwa
ɗ
auke ta
ke da fanni-fanni wajen guda takwas!
Wasu sabbi ƙal ginin zamani
wasu tsofaffi tukuf ginin ƙasa
Wasu manya ne domin tun daga kallo
ɗ
aya in an musu an san za su ƙunshi wajen
ɗ
akuna uku sannan a ciki har a samu parlour ma sai kuma masu ciki da parlour, yay
inda wasu kuma
ɗ
aki
ɗ
aya ne kawai sai ban
ɗ
aki…..
Ginin daya fi ko wanne tsufa kuma
ɗ
aya daga cikin jerin ƙananun buildings
ɗ
in Manubiya
ta nufa, tana zuwa dai-dai bakin ƙofar
ɗ
akin ta sa Hannu ta
ɗ
aga labulen ta shiga ciki da sallama.
Babban
ɗ
aki ne sosa
i da manya manyan taga guda biyu suna kallon juna
sai ƙofar ban
ɗ
akin da ta ke a chan kusurwar
ɗ
akin.
Ƙ
atuwar katifa ce kawai a yashe a gefe cikin
ɗ
akin.
Sai babban wardrobe na katako..
Laidar
ɗ
akin bata wani yayyage ba ammanfa ta ji jiki dan ta yi laush
i matuƙa…kallo
ɗ
aya za a yi mata a fahimci takatsantsan da kula ne kawai su ka kawota war haka ba ta fatattake ba.
Wata farar budurwa, fara ƙal, ce, zaune a kan katifar ƙafafunta su na ƙasa. dududu budurwar ba za ta wuce shekaru sha bakwai a duniya ba, s
ai gefen ta kuma wata dattijuwar mata ce kwance a kan katifar, budurwar na yi mata fifita.
Tun a kallo
ɗ
aya yanayin Matar ya ke nuni da abun tausayi dan sosai ta ke jin jiki, a zahirance da ba
ɗ
ini.
Saitin su kuma wani dattijon tsoho ne zaune da wani Yaro
a gefen shi, Yaron ba zai wuce shekaru sha
ɗ
aya a duniya ba, dattijon kuma ba wani mai shekaru bane a ba
ɗ
ini a zahirance ne kawai tsufanshi ya fito ya baiyyana muraran saboda yanayin rayuwa.
Fuskokin su gaba
ɗ
ayasu, babu walwala! Kowa ya yi jigum, ana ta
tunani, Ba ma su san Manubiyan ta
ɗ
aga labulen ba har sai da su ka ji sautin muryarta, sanda ta shigo da sallama.
Jidda, wadda ke zaune a kusa da Inna ce ta
ɗ
ago ta kalle ta a hankali ta ce
‘’har kin dawo?
Sannu da zuwa.’’
Jinjina kai kawai Manu ta iya
yi kafin ta juya ta kalli Muhsin
wanda ya ke yi mata sannu da zuwa shima, ta yi masa wani guntun murmushi tukunna cikin nutsuwa ta ƙarasa ta durƙusa a gaban Baba ta ce
‘’Baba Ina wuni.’’
Kamar ba zai yi mata magana ba sai kuma ya ce
‘’Mai yasa baki
ɗ
au
ki ku
ɗ
in motar da na ajjiye miki ba?
Bana ce miki munada ku
ɗ
in abun karyawa ba?.
Mai yasa kike da taurin kai ne?’’
ya jero mata tambayoyin a jere kafin ya
ɗ
aura da cewa
‘’Ce miki akayi nan da b.u.k
ɗ
in tafiyar wasa ce?”
Ya ƙarashe tambayar ta sa ta ƙarshe
cike da rashin jin da
ɗ
i da takaici.
A hankali ta sunkuyar da kanta ƙasa tukunna
ta ce
‘’ka yi haƙuri Baba ba zan ƙara ba.’’
Sai da ya
ɗ
an fesar da iska tukunna ya kauda kai gefe ya ci gaba da tunanin da ya ke yi kafin ta shigo.
Su Jidda ta juya ta ka
lla kafin ta ce
‘’Ya jikin nata?”
Da kyar dan sai da ta ha
ɗ
iye wani abu wanda ya tokare mata maƙoshi tukunna Jidda ta ce
‘’Da sauƙi. Alhamdulillah .’’
A hankali Manu ta ce
‘’Allah ya ƙara sauƙi.’’
Kamar Muhsin zai fashe da kuka haka nan ya
ɗ
ago ya ka
lli Manubiyan kafin ya ce
‘’Adda Manu, sai da fa ta kuma suma da ki ka tafi makaranta
ɗ
azu’’.
Shiruu ta yi chan kuma sai ta sunkuyar da kanta ƙasa,
wanda hakan ya bawa hawaye damar fara gangaro mata…
Haka ita ma Jidda ta sunkuyar da kanta ƙasa
ta fara
nata kukan…
Ganin hakan ne ya sanya shima Muhsin ya fara nashi kukan….
Haka nan suka tusa Baba a gaba kowa ya na hawaye.
A hankali Baba ya zaro wayarsa daga aljihu ya danna kiran Ya Musbah…
Kamar
ɗ
azu yanzun ma wayar a kashe!
dan haka ya
ɗ
ago ya kalla J
idda bayan ya maida wayar cikin aljihun malun malun
ɗ
in da ke a Jikinsa ya ce
‘’Maijidda kikace
ɗ
azu ya ce miki
Mu jira shi zai zo ko?’’
Sai da ta
ɗ
an yi shiru tukunna a hankali ta gyada masa kai sannan ta ce
‘’Eh, Baba.’’
Tsaki ya yi daga haka ya miƙe
tsaye ya ce
‘’Muhsin taso mu je .’’
Da sauri Jiddan ta ce
‘’Baba ka bari ni in sake komawa, in dubo shi, ba sai ka je ba.’’
Kallon ta ya yi kamar ba zai ce wani abun ba
Sai kuma ya ce
‘’kar ki damu!
yanzu za mu je mu dawo
InshaaAllah…
Ina son ganaw
a da shi.’’
Daga haka ya kalli Manubiya ya nuna mata gurasarta wadda suka ajjiye mata a cikin kwano ya ce “ki tabbatar kin
ɗ
auka kin ci.”
Sannan ya sa kai ya fice cikin tafiyarsa da ke baiyyana nakasar da ke tare da shi, dan ƙafa
ɗ
aya gareshi yayinda
ɗ
ayar
ta kasance ta roba.
Ya na fita Muhsin ya mara masa baya da hanzari, dan shi ma Yaron
hankalinsa a mugun tashe yake, Allah Allah kawai yake a san yadda za a yi a kai innar tasu asibiti, dan jikin nata ya tsorata kowa!
Babba da Yaro.
Suna fita Manubiya t
a miƙe ta cire hijabin Jikinta.
Daga haka ta ƙarasa inda su Innar su ke, (ita da jidda).
Sai da ta tabbatar innar bacci ta ke yi tukunna ta kalli Jiddan ta ce
‘’Mai ya faru
ɗ
azu da kika je gidan?
kin gan shi?’’.
A hankali Jidda ta share hawayen da su ka
zubo mata.
Kafin ta shiga koro mata bayanin
yadda su ka yi….
Da yadda Ya Musbah ya ce kawai ta zo gida, su jira shi.
Gashi kuma har yanzun bai zo ba.
Shiruuuuu, duk su biyun su ka yi!
Ko wacce zuciyarta babu da
ɗ
i.
Suna kuma tunanin a ina za su je su
samo ku
ɗ
i!
Dan sun san tunda Ya Musbah ya fara wasar ƴar
ɓ
uya da su
tou shima bashi da yadda zai yi ne.
A take zuciyar Manubiya ta fara bata shawarar ta cire kunya kawai ta gayawa Abbakar gaskiya, ta san zai taimake su.
………
A ƙofar gidansa su Baba su ka
hango shi.
Kamar wani saurayi haka yanayi da jikinsa ya ke, sam bai yi kama da magidanci ba.
Fari ne sol kyakkyawan gaske, bai cika tsayi ba amman yana da fa
ɗ
in ƙashi.
Cikin sanyin jiki Baba da Muhsin su ka ƙarasa inda Ya Musbahn ya ke
alwallar sallar M
aghrib
ɗ
in da ta gabato, shi da wani maƙwafci kuma Abokinsa mai suna ‘Nafi’u’.
Cike da girmamawa
shi da Abokin nasa
su ka gaida Baba.
Kafin Abokin ya cewa Ya Musbah
‘’Bara in wuce.
In fara karatu kafin ku kammala.’’
Jinjina kai kawai Ya Musbah ya y
i, dan gaba
ɗ
aya hankalinsa a mugun tashe ya ke, ga shi ya ga Baban sai wani irin kallo ya ke ta yi ma sa
wanda ya kasa gane ma’anarsa.
Rashin sanin abun yi da kame-kame ne su ka sanya shi cewa
‘’Bismillah Baba
Mu shiga daga ciki ko?’’
Sai da Baban
ya sauƙe ajiyar zuciya tukunna ya ce
‘’Naa shiga kuwa?’”
A hankali Ya Musbah ya ce
‘’to ko soro ne ka shiga dan Allah.
Akwai bayanin da na ke so in yi maka ne.”
Ba dan Baba ya so ba!
Ya Kama Hannun Muhsin su ka bi bayan Ya Musbah.
Anan soron kuwa ya
shimfi
ɗ
e musu tabarma…..
Dan a wannan lokacin bai isa shigar da su cikin gidan ba!
Daff da zuwan su Baban
Nafi’u ya gama yi musu shari’ah shi da Baraka!
Saboda kawai Jidda ta zo
ɗ
azu, shikenan tunda Yarinyar ta zo ta tafi Baraka ta ke ta bambami
‘Wai ta z
o har gida ta yi mata rashin kunya!!!!’
Kuma sarai ya san ƙarya ta ke yi!
Kawai ta na neman hanyar da za ta bi ta datse zuwan ƴan uwan nasa gidansa ne!
Gaba
ɗ
aya.
Bayan a yanzu kamata ya yi ma ace shi ya ke riƙe da Jidda ko Manubiya…..
‘’Tunanin mai ka k
e yi???’’
Muryar Baba ta Katse ma sa tunani.
A hankali ya sauƙe ajiyar zuciya!
Ya na shirin yin magana Baban ya sake katseshi ta hanyar cewa
‘’Innar ku har yanzu ta na kwance,
babu ku
ɗ
in magani, babu na zuwa asibiti.
Musbahu!
Kai ne ka hanani aikin ƙarfi,
Sannan kai ne ka ce ƙannen ka Mata ba za su yi Aikatau ba wanda ba daban hakan ba na san da yanzu mun san yadda mu ka yi
aka kai ta asibiti.
Tun shekaran jiya mu ke ta tsammanin ka!
Ka kashe wayarka kuma
ka ƙi ka yarda ka zo inda muke.
Wanda in m ku
ɗ
a
ɗ
en ne ba su samu ba a gani na dai a ya kamata ace ka zo ka duba Mahaifiyar ka dai ko?’’
Cikin yin ƙasa da murya sannan a hankali Ya Musbah ya ce
‘’Baba, kalli fa ƙafar ka. Ba za ka iya aikin ƙarfi da ita ba!
Ina tsoron ka saka mata nauyi da yawa haka n
an mu je Itama ƙwaya
ɗ
ayar wadda ta rage maka ya zamana itama ta samu matsala.
Su Manubiya kuma
ba wai girman kai bane ya sanya na ce ba za su yi aikatau ba!
Kawai a ganina bai kamata ace ina raye muna zaune a unguwa
ɗ
aya
amman ace ƙanne na Mata su ne za
su na kula da iyayena, ba.
Dan Allah Baba ka yi haƙuri,
ka bar maganar dakon da ka ke so ka yi, da duk ma wani aikin ƙarfi.
In sha Allahu zan yi ƙoƙari in san yadda za a yi.
InshaaAllah zan iya kula da kowa.
Ku
ɗ
in asibitin ma na nemo, ba wai ban nemo ba!
Amman sai jikin Baba ƙarami ya
ɗ
an mot……’’
Shiru ya yi kafin ya ci gaba da cewa
‘’Amman karka damu
Nafi’u ya yi wa
ɗ
an uwansa magana kuma
ɗ
an uwan ya ce
za’a san yadda za ayi…
Mu jira shi zai kawo ku
ɗ
in. Shiyasa ma ka ga ban zo ba saboda
bana so in
zo muku ba tare da ku
ɗ
in ba. Shi nake ta jira na fi so in ya zo ya bani ni kuma sai in zo
a kaita asibitin‘’.
Sai a sannan
Baraka wadda ta la
ɓ
e musu tun
ɗ
azu ta shigo cikin soron.
A hankali ta ƙarasa inda su ke ta zauna!
Cikin ladabi ta gaida Baba. Inda
ya
amsa mata da Kulawa ya na mai tambayarta “Ina takwaran sa” ta ce
masa “yana ciki yana barci.”
Da ladabi Muhsin ya gaida ita
ta amsa daga nan soron ya
ɗ
auki shiruuuuu,
kafin a hankali sautin kukan Baraka ya soma tashi.
Da sauri Baba ya ce
‘’Subah
anallah,
Baraka lafiya?
Mai ya faru?”.
Cikin kukan da kyar ta
ɗ
an tsagaita sannan ta ce
‘’Ba komai Baba, ba komai. Ku yi haƙuri, su
ɓ
uce mini ya yi.’’
Tana gama fa
ɗ
in haka ta fara ƙoƙarin miƙewa.
Cikin
ɗ
an tsare gida Baba ya ce
‘’Koma, koma
Baraka.
Kom
a ki zauna’’.
Ya bata umarni
ransa duk babu da
ɗ
i.
A hankali ta koma ta zauna ta na
ɗ
an satar kallon Ya Musbah wanda ya ha
ɗ
e rai!
Yana ji kamar ya rufe ta da shegen duka.
Cikin kulawa Baba ya shiga rarrashin ta….
Har sai da ta yi shiru tukunna ya nemi ta
fa
ɗ
a masa me ke faruwa.
Cikin yin ƙasa da murya ta fara zaiyyane masa cewa
“dama kwanakin baya ne Ya Musbah ya kar
ɓ
i ku
ɗ
inta, kuma itama ku
ɗ
in ba nata bane ba
na wata ƙawar Mamanta ne
To a halin da ake ci
Maman tata ta biya rabi, amma ta kasa biya
n rabi shine ƙawar ita Mahaifiyar tata ta ce ‘za ta je da ƴan sanda ta tafi da Mahaifiyar tata’.
Tun jiya ta ke bin Ya Musbah akan ya bata ku
ɗ
in shi kuma ya ƙi ya bata,
yanzu gashi ƴan sandan sun je za’a tafi da Mahaifiyarta.….”
Shiruuu Baba ya yi,
da
jin batun Baraka.
Kafin ya miƙe tsaye ya kama Hannun Muhsin.
A hankali ya kalli Ya Musbah ya ce
‘’Musbahu, idan an kawo ku
ɗ
in da akayi maka alƙawari ka bata.’’
Da sauri Ya Musbah ya ce
‘’Amman fa Baba..’’
Cikin katse sa ya ce
‘’Bana son musu!
Sannan
bana son ja-in-ja!
Ka bata kawai.
Kar ka damu, zan san abun yi ‘’.
Tukunna ya kalli Baraka
wadda ta yi kalar tausayi ya ce
‘’Kar ki damu, ba za a tafi da Mahaifiyarki ki ba.
Inada mara lafiya a gida, shiyasa ba zan iya bin ki mu je in ga komai ya lafa
ba.
Yanzu ki yi sauri ki je wajen ta, Musbahu zai biyo ki da ku
ɗ
in
InshaaAllah.
In basu cika ba ma
In na san yadda nayi na ha
ɗ
a kan ƴan ku
ɗ
a
ɗ
e na kashe wutar gaba na…
Ki yi mini magana sai in cika miki ‘’.
Yana gama fa
ɗ
in haka ya jaa Hannun muhsin su
ka fice daga soron.
Cikin
ɓ
acin rai Ya Musbah ya kalle ta kamar zai ce wani abun
sai kuma kawai ya miƙe shima ya fice!
Ya bi bayan Baba ranshi a mugun
ɓ
ace!.
Yaso ya fahimtar da Baba
a samu
ya yi haƙuri ya kar
ɓ
a ku
ɗ
in ya bar batun Baraka!
Amman fur
r Baba ya ƙi sauraron sa,