Showing 42001 words to 45000 words out of 150519 words
kaita ma sabon gidanshi wanda ya ke a nndc quarters.”
Tsit!! Haka parlourn yayi daga jin hakan, dan hatta Yashjub sai da ya ji ba dad’i…
Har d’aurin auren sai da ya je, j
iya. Amman Daddy bai ce masa ba tare da su zata zauna ba!
Kuma shi ya ce masa kar ya gayawa kowa ya yi shiru amman gashi shi ya b’oye masa abu, bayan haka sabon gidan ai Mommy ya kamata ya kai tun da shima mansion ne kamar girman nan
‘’Okay ba damuwa,zamu
zo inshaaAllah,’’
Muryar Mommy ta dawo da gaba d’ayan su daga duniyar tunanin da suka dulmiya.
Ba yadda Ummi bata yi da
Ya’isha akan ta biyota su tafi tare ba
Saboda y’arta Munira age mate d’in Ya’ishan ce kuma jibi zata baro gidan Yayarta ta komo wajen
ta da zama a chan nndc d’in!
Amman Ya’ishan tak’i yarda…
Ta bata excuse
ɗ
in ‘tanada shirye-shirye na masters d’in da ta fara recently,
so tana buk’atar time domin ta nutsu ita kad’ai ta shirya abubuwa.’
Ba dan Ummi ta so ba ta tafi bayan sun yi mata alk’a
warin za su je, inshaaAllah.
Har mota suka rakasu saida suka ga fitar su, tukunna suka koma ciki.
Yadira ce ta ce
‘’Yanzu dan Allah Daddy ya ..’’
Da sauri Mommy ta kalle ta,
dan haka ta ja Bakinta ta yi tsit.
Har suka yi dinner aka tashi
babu wanda ya
yi zancen
Ummi ko Daddy!
Yashjub ya yi musu sai da safe
ya wuce,
Kowa ta nufi side d’inta.
Ba abunda ya fi yiwa Kausar dad’i irin yadda ta ga babu Yassir babu dalilin sa.
Dan ita sam case d’in sabuwar kishiyar Mommy bai wani d’aga mata hankali ba!
sab
oda ta riga ta san k’aramar alhaki ce…….
Tunda Yashjub ya koma Ɗaki, sam sai ya kasa
tab’uka komai!
zuwa wannan lokacin tabbas ya fahimci yana buk’atar sanin more about Manubiya.
Ya riga ya tsaya akan cewa ba son ta yake yi ba saboda to tayaya ma za ayi
ya so ta!? in fact idanuwanta kawai ya gani dan haka if there is anything ma (idan akwai ma abun) da yake drawing nasa towards her maybe it’s the eyes, dan ya tabbatar bai tab’a ganin kwatankwacin masu kyawun su ba, ko kuma maybe akwai wata k’addarar da t
ake jan sa zuwa gare ta wataƙila shi ya taimake ta a wani abun ko kuma ita ta taimaka masa……
A mazaunin haka ya bar lamarin, daga nan ya d’auki wayarsa ya kira Najeeb…
Ya san zai sha tsokana
amman gwara tsokanar Najeeb akan wannan rashin kwanciyar hanka
lin da yake fuskanta daga zuciyarsa dan in banda azalzalar sa ba abun da takeyi….
‘’Kawai ina buƙatar sanin fiye da sunanta ne,
daganan na san shikenan!
Ba wani abun da zai sake biyo baya kuma’’
Ya fad’a hakan a fili cike da son gasgatawa kansa iyakar
abu
nda yake buk’ata kenan.
Sai da Najeeb ya yi murmushi yana mamakin taurin kai irin na Yash,
dan ya san yau
ɗ
in ma in ba da kyar ba akan Manubiya ne ya sake kiran sa….
Sai da ya girgiza kai, ya ce ‘’hmm’’
tukunna ya d’au wayar ya kara a kunnensa ya ce ’’He
llo Yash,how far’’
‘’Kar ka ce komai kuma kar ka tambaye ni meyasa, kawai Ina da buk’atar sanin ƙarin bayanai akan wannan Yarinyar’’
Yashjub d’in ya fad’a yana mai runtse idanu, sannan ya yamutse fuskarsa kamar irin
‘Meyasa ma na tambaye sa’
d’innan.
Tab
bas sai da Najeeb ya yi da gaske
tukunna ya samu ya danne dariyarsa sannan ya ce
‘’To a gaskiya Yash ni dai bana tara bayanai akan
ɗ
alibaina..
Iyakar abunda na gaya maka jiya shi kad’ai na sani a game da ita.
Amma y not (mai zai hana) in karb’a maka numb
erta in yaso kaga sai ka binciketa ka ji komai da daga Bakinta?”
Tun kafin ya rufe Bakinsa Yashjub ya ce
‘’Kana hauka ne?
Ka ga bafa
wani abun bane ba, i just saw her jiya jiya(jiya jiya na ganta) so kar ka yi mini tunanin wani shirme’’.
Yana gama fad
’in haka
ya yi sauri ya kashe wayar, dan tabbas idan ya ci gaba da magana ba iyakar Najeeb ba shi kansa zai iya gano abun da yake ta k’ok’arin k’aryatawa tun a jiya.
“Innalillahi wa innailaihirrajiun”
Ya shiga maimaitawa a ransa
dan yana ajjiye wayar s
ai kuma ya fara jin haushin kansa na
Kashe wayar da ya yi ba tare da ya nacewa Najeeb d’in
ya
nemo masa information (bayanai) game da iya ba.
BULAMA ✍
️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*14*
••••••
Lokacin tafiyar da Al
’ameen ya ce zai yi,ya cika!
Dan haka ya je ya samu Dr da nurses d’in, duk wasu abun buk’ata sai da ya biya kuma ya bada numbersa ta k’asar da zai je ya ce a kira sa in wani abun ya taso.
Da kyar ya samu Jidda ta yarda ta k’arba waya daga Hannunsa.
A ra
nar da zai tafi kuwa kamar kar su rabu, haka nan suka dunga yi wa juna rakiyar kura kafin ya samu ya rakata bakin k’ofar d’akin da Inna take jinyar ya bud’e mata ya ce “ta shiga”
tana shiga ya jaa ya rufe ya juya ya wuce da sauri yana murmushi….
Sai da In
nah ta k’ara sati biyu a asibitin tukunna aka sallamo ta.
Ba laifi jikin nata da d’an sauk’i.
A cikin sati biyun nan
kuwa Manubiya bata je ba dan k’iri-k’iri Baba ya hana ta zuwa, dole haka nan ta hak’ura ta ci gaba da karatunta dan exams za su fara yau s
aura kwana d’aya.
Y’an gidansu ma tun zuwan da Siyama ta yi har yau ba wanda ya koma sai Ya Yusuf da ya je sau uku.
Baraka itama bata sake komawa ba dan cewa ta yi
‘’Ba zata je inda za a dinga wulak’antata ba, zata dinga yi wa Innar fatan samun sauk’i
t
ana daga Gida.”
Matar Nafi’u kuwa kusan kullum sai ta je, dama ita tun fil’azal basa shiri da Baraka!
Amma dukda haka da ta lura bata zuwa sai da ta je har gida ta bata shawara, ai kuwa basu k’ark’are k’alau ba dan k’arshe ma Baraka k’ofar fita ta nuna m
ata ta ce
‘’Ta fice mata a gida’’
Rufe-rufen files ne da wasu ƴan gwaje-gwaje suka d’an tsaida su Baba daga dawowa da wuri.
Tun safe da Jidda tacewa Manubiya an sallame su, Manubiyan ta gyara d’akin tass ta share ta yi girki ta kunna turaren wuta ta wa
nke band’aki!
Sai zumud’i suke yi itada Muhsin dan shima ba kasafai aka cika zuwa da shi ba, basu samu sun k’araso ba kuwa sai wajajen k’arfe uku.
Suna zaune a d’aki lokacin, kaar daga sama suka ji Baba yana gaisawa da Anty Umma.
Da zumud’i suka mik’e s
ukayi waje, anan tsakar gidan suka tadda rabin y’an gidan kowa ya fito yana duba jikin Innar.
Ta
ɓ
e Baki Manubiya ta yi a ranta ta ce
‘’daga baya kenan’’
daganan suka nufe su ita da Muhsin, a tare suka rungume Innar wadda take zaune akan wheelchair, Manubi
ya har da hawayenta kafin daga bisani
suka wuce ciki y’an gidan suma kowa ya wuce Fanninsa.
Suna shiga Manubiya ta shiga gabatar musu da abinci.
ita da Jidda ne suka bawa Inna, ta ci kuwa ba laifi duk da rabi duk ya zube saboda har yanzu gefen Bakin nat
a ba aiki yake yi sosai ba.
Haka suka zauna suna y’ar hira ana cin abinci gwanin ban sha’awa ba wanda zai kalle su ya ce sunada wata matsalar, dan hankalin Baba a mugun tashe yake saboda bai san yadda zaiyi ya biya ƴan basusssukan da ya ci waenda suka zama
dole ba, sannan bai san yadda zai yi ya ci gaba da kula da iyalin nasa ba, amma sam bai bari sun gano halin da yake ciki ba haka nan ya biye su akayi ta raha.
To haka a b’angaren Ya Musbah shima yayi k’ok’ari ya danne tashi matsalar aka ci gaba da hirar
suna ta yak’e daga shi har Baba.
Kiran sallar la’asar ne ya tashi zaman nasu, Maza suka tafi masallaci Matan kuma suka yi a gida.
Sai a lokacin Jidda ta samu damar zama da Manubiya
dan Inna har ta samu bacci.
..
A hankali suna ida addu’a
Jidda ta kamo
Hannuta ta ce
‘’Adda Manu ina ta so mu yi magana amma ban samu right time ba sai yanzu’’.
Da kulawa
Manubiya ta juyo tana kallonta
tare da bata dukkannin attention d’in ta.
Tun daga ranar da ta hana Al’ameen zuwa ta kuma hanata kula shi ita kuma ta c
igaba
Ba abunda Jidda ta b’oyewa Manubiya sannan ta mik’e ta je jakarta ta kawo wayar da ya bata ta nuna mata.
Cikin son fahimtar da ita Manubiya ta ce
‘’Jidda ban hanaki kula Al’ameen ba, saida na duba
na ga abun da hakan kan iya janyowa.
Jidda Mahai
fiyarsa bata k’aunarki…ki duba ki ga halin da muke ciki, kar ki je ki sake janyo mana wata matsalar.
Tunda ya ce miki Ammin nasa zata zo kin ji ko waya ne ta yi??’’
A hankali Jidda ta ce
‘’Ya ce min ta yi tafiya ne, Adda Manu ki fahimce ni dan Allah,
In
a son Ya Al’ameen nima, kawai ki tayani da addu’a dan shine farin cikina. banajin zan iya rabuwa da shi, a matsayin ki na y’ar uwata ina tunanin ke zaki fara fahimtata..”
Cikin katse ta Manubiya ta ce
‘‘Jidda,ba wai inaso inyi going against farin cikinki
na yanzu bane ba, Inaso ki samu dauwamammen farin ciki na har abada ne shiyasa kika ga Ina haka.
Idan ya ce Mahaifiyarsa ta yi tafiya ai ya kamata ace ko waya ne kun yi ke da ita considering (idan aka yi la’akari da) abunda ya faru a baya, saboda a samu
a tabbatar da yess tana son ki yanzun..”
Sallamar Siyama ce ta katse su dan haka duk suka d’ago a tare suna kallonta da murmushi.
Itama murmushin ta mayar musu
kafin ta ce
‘’Tare nake da bak’uwa, ta shigo?’’
Ba tare da sun san wacece ba
suka ce mata
‘’eh.’’
Tana shigowa gaban Manubiya ya yanke ya fad’i amma sai ta dake tace mata ‘’Ina wuni’’
daganan ta miƙe ta je ta d’auko darduma ta shimfid’a mata.
Cikin sunkuyar da kai Jidda ma ta gaida Mahaifiyar Al’ameen (Ammi).
Duk jimla Ammin ta yi musu ta am
sa gaisuwar tasu, kafin ta juya ga Siyama ta ce ‘’ta je ta kira mata Uncle, dan ta ga shigowar sa yanzun’’.
Kana ganin yanayin fuskarta ka san ba dubiya ta zo yi ba.
Dan haka duk suka zauna shiruu kowa da abun da yake tunani.
A tare Uncle,Ya Musbah,Baba
da Muhsin suka shigo d’akin.
da sallama.
Tunda Baba ya ganta a gidan dama ya san ba lafiya ba!
amman sanin da ya yi ya riga ya raba y’arsa da d’anta hakan ya sanya ya d’an ji sauƙi…
Duk da ya san ba lalle Al’ameen d’in ya gaya mata ya basu kud’i ba
amm
a dama a shirye yake
yana ta k’ok’arin neman bashi ya samu ya had’a kan kud’ad’en da Al’ameen d’in ya basu ya biya saboda ya san fitinar Mahaifiyar tasa,
kuma a lokacin da Al’ameen d’in yace zai taimake su
Inda ya k’i amincewa ya san Yaron ba zai ji dad’
i ba, bayaga haka ma basu da yadda za su yi a wannan lokacin.
Da Uncle suka fara gaisawa
sai Ya Musbah da Muhsin
kafin Baba Musa ya kalle ta ya ce
“Barka da yamma,Ammi.”
‘’Barka dai,Musa’’
Kawai Ammin ta ce ba tare da ta kalli inda yake ba.
Daganan
kowa yayi shiru a d’akin kafin
Uncle ya kalli Manubiya ya ce
‘’Manu ke da su Muhsin ku d’an bamu guri ko?’’
Da sauri Ammi ta ce
‘’A’a,ai zuwan nasu ne,ma’’.
Bata jira jin mai za’a ce ba ta juya ta kalli Baba ta fara magana
‘’Kwanakin baya, mun samu ma
tsala da ku akan wannan Yarinyar Maijidda da take mak’alewa Yarona, ta shiga tsakanina da shi har sai da ta kai ta kawo ya dena yi mini biyayya.
To an samu an gyara matsalar kwanaki da kyar!! Yanzu kuma an koma ruwa…
Da sauri Uncle ya ce
‘’A’a fa Misunde
rstanding (rashin fahimta) dai aka samu Ammi, dan rabon Jidda da Al’ameen ai tun kwanaki da muka yi musu tsakani ko ba haka ba? Maijidda’’
Yayi maganar yana mai kallon side d’in da Jiddah take nan Kai a durk’ushe.
Kafin ya juyo ya kalli Ammi ya ce
‘’Kuma
ina Al’ameen d’in baya nan ma? jiya na ji Yaran nan Maza suna cewa ya tafi England ko’’
‘’Eh ya tafi akwai course d’in da zai yi a chan shiyasa ma na samu na zo nan
ɗ
in, dan cewa ya yi muddin na yi wani yunk’urin sake raba shi da Jidda to babu ni babu sh
i’’
Cewar Ammi
Sannan ta d’aura da cewa
‘’Already Al’ameen yana da Matar da zai aura, an riga an gama magana. Shi kad’ai Allah ya bamu
da ni da Mahaifinsa!!
Muna da burin mu ga ya samu rayuwa da Abokiyar rayuwa wadda ta dace da shi!!.
Ba zan b’oye muk
u ba Jidda is the last person (ita ce Mace ta ƙarshe)a duniyar nan da zan so Yarona ya aura!!
A kwanakin baya ban fuskanci Jidda da lamarin nan ba na fuskance ku ‘Mahaifanta’ saboda na ga kune magabatanta kuma a tunani na Ita
ɗ
in Yarinya ce amma yanzu ta n
una mini cewa ta girma kuma ta fi k’arfin ku dan haka
Ki saurara ki ji!!’’
Ta yi maganar referring to Jidda wadda ta fara kuka k’asa-k’asa.
‘’Duk zuwan da yake yi da irin kud’ad’en da ya ke kashewa
na san komai
Dan haka …..’’
Da sauri Manubiya ta ce
“
Ammi Mahaifiyarmu bata da lafiya, at least idan baki yi considering d’in ta(la’akari da ita) ba..’’
Cikin d’aga murya Ammin ta ce
‘’Na tabbatar idan na bar Al’ameen tare da Jidda to nima condition d’ina sai ya dawo irin na Mahaifiyar taku saboda tsabar b
aƙin cikin da za ta dinga d’ura mini.’’
Ciki d’acin Zuciya ta juya ta kalli Uncle ta ce
‘’tunda na haifi Al’ameen
bai tab’a yi mini musu ba
sai da ya had’u da Yarinyar nan, Wallahi’’.
Cikin katse ta Manubiya ta ce
‘’Kar ki d’aura alhakin taurin kan d
’anki akan mu, tunda ba ke kad’ai yake yi wa ba…ki tambaye shi ki ji yadda muka dinga cewa kar ya zo inda muke amma sai da ya je!!!
bayaga haka a gani na ai ke kika haifi Al’ameen dan haka idan yayi taurin kai
ko ya ƙi yi miki biyayya hakan yana nufin ke
ce kika kasa sannan ke ce kika sangarta abunki …..’’
‘’Manu!!’’
Ya Musbah ya kira sunanta da kakkaurar murya yana kallonta
da idanuwansa waenda suka kad’a suka yi jaa.
Sai a sannan Ammi ta d’auke idanuwanta daga kan Manubiya ba tare da ta ce komai ba ta
mik’e ta kalli Uncle ta ce
‘’Shigowar da na yi cikin d’akin nan ya ishi k’ask’anci ba sai na tsaya wannan y’ar ta gaya mini maganganu ba!
Idan ka lura ko uban su bai isheni kallo ba shiyasa na kira ka akan ka yi mana alk’alanci ni da Jidda, amma tunda b
asu san sulhu ba sannan basu san
banbancin da yake tsakani na da su ba, inaso ka gaya musu nace ‘duk abunda Al’ameen ya kashe musu su dawo mini da shi!!
kafin nan da awanni ashirin da hud’u, idan kuma ba haka ba to wallahi kotu ce za ta raba ni dasu’.’’
Tana gama fad’in haka ta juya ta fita fuuuuu.
Cikin rashin jin dad’i Uncle ya kalli Baba ya ce
‘’Haba Musa, yanzu ina amfanin haka? wutsiyar rak’umi fa ta riga ta yi nesa da k’asa, bayan haka ma Ina ce ita Jiddan Yusuf za ta aura, mai ya sake had’ota kum
a da Al’ameen
ɗ
in da aka raba ku da
wannan Matar kwanakin baya da kyar????’’
Cikin tsananin
ɓ
acin rai Ya Musbah ya ce
‘’Ta je ta tafi kotun, idan bata da hankali, waye take tunanin zai kalle ta?
kud’i ai Al’ameen ne ya bayar ba ita ba’’.
Cikin katse shi
Uncle ya ce
‘’Kai Yaro ne har yanzu Musbahu, kamar yadda ta ce
akwai fa bambanci mai k’arfi a tsakanin ta da ku, Allah na tuba ko police station ta kai ku ta kulle wallahi sai kun ji a jikinku!!
dan babu d’an sandan da zata zubewa kud’i ya ƙi sakawa a
narkeku, barin ma idan ta ce kud’i take binku tsaf za a yi ta jibgarku, tunda an san baku da shi har sai kun biya, idan ma za a tsaya muku to fa kafin a yi wani abun kun ji jiki….
gashi yanzu kowa ta kansa yake yi ban san taya ma za a fara biyanta kud’in b
a, thats in ba a yi rashin saar kullenkun ba…
Kai yanzu instead of ka ji da rashin lafiyar Matarka mai yasa
ka je kana amshe kud’in Yaro?.’’
Uncle ya Ƙarashe