Showing 57001 words to 60000 words out of 150519 words

Chapter 20 - Mannubiya Complete

fad’a maka amma sai ka yi min alk’awarin ba za ka yi min mummunar fahimta ba’’.

Murmushi ya yi kafin ya ce ’’inshaaAllah,ina jinki’’.

Sai da ta had’

iye wani abu da kyar wanda ya tokare mak’oshinta tukunna ta ce

‘’Wannan Mutumin na office d’in Sir Najeeb na ranar nan, to shine nake ganin wata Mata mai kama da shi anan gidan kuma in dai na ganta to sai in yi ta tunanin sa har mafarki fa…

Ni kuma bana

so ina yawan tunanin sa, bana buk’atar abun da zai had’ani da shi sam, shi yasa nake tunanin barin aikin nan..’’

Ta k’arashe maganar cikin tsananin sanyin murya da rashin jin dad’i.

Shiruu Abbakar ya yi yana tunani, har sai da ta sake cewa

‘’Ka fahimce n

i?’’

Tukunnan ya d’an yi firgigit

Ya ce

‘’Yeah, yeah na fahimceki’’.

Daganan ya yi shiruuu ya sake dulmiyawa duniyar tunani.

‘‘Shikenan tou tunda ba ka ma da abun da zaka ce, yanzu gaya min abun da yake tafe da kai’’

Ta fad’i hakan cikin d’an had’e gi

ra alamun ta ji haushin kanta na fad’a masa ta kuma ji haushin shirun da ya yi dan in ba dakyar ba to tasan tunanin abun da bata so

ɗ

in shi kwakwalwarsa ta bashi yake yi.

BULAMA ✍



0903 441 3252

*MANNUBIYA*

*20*

Murm

ushi Abbakar ya yi kafin ya ce

‘’Yi hak’uri, ban san me zan ce ba ne shiyasa kika ga na yi shiru….

abun ne ni kaina ya sakani a tunani da damuwa ballantana kuma ke, shawara d’aya

itace

‘kawai kiyi ta addu’a..Allah ya sa mu dace.’.”

A hankali ta ce ’’

Ameen’’

Sai da Abbakar ya d’an sake yin nazari tukunna ya ce

‘’Am..kiran da Sir Najeeb ya yi mini

ɗ

azu akan ki ne fa.’’

Da sauri ta zaro idanu waje, sai kuma ta ce

‘’A kan me wai???’’

Ta yi masa tambayar a d’an tsorace.

Murmushi ya yi tukunna ya ce ‘

’kwantar da hankalinki, abun alkhairi ne.

Aiki kika samu, a wata a yadda ya ce min 30k, kuma sau d’aya kawai za ki dinga zuwa a sati

ragowar kwanakin duk ta waya za ki dinga bada rahoto.’’

Da sauri ta ce

‘’Da gaske? Tayaya? a ina kuma?’’

Ta yi masa t

ambayar cikin zumud’i da d’aurewar Kai.

Yana murmushi ya ce

‘’Kina cewa sir Najeeb bashi da kirki ko?

To ba haka abun yake ba, sannan kuma wataƙila ina tunanin yana da wani rauni a duk lamarin da ya shafi mahaifiya…

Dan Ce mini ya yi yana yawan ganin ki

a damuwa

‘dayake kin san ranar ai kin ce

masa Inna bata da lafiya to inaga yana tunanin ko akwai wani problem d’in da ba za ki iya fad’awa kowa ba,

shiyasa ya ga ya dace ya taimaka miki ke kuma ki taimaki Inna’.’’

Abbakar ya zaiyyane mata hakan cikin

son rufe duk wata k’ofar da zata sa ta fahimci wani abun.

A hankali ta ce

‘’Allah sarki Sir Najeeb,

Allah ya saka masa da gidan Aljannah.

Amma aikin nasa ne? I mean (ina nufin) a Ina ne?company ne?’’.

‘’Eh to nima ban sani ba gaskiya amma inaga kamar n

a Uncle d’insa ne or something like that(ko kuma wani makamancin hakan), ga dai katin wanda aka ce ki kira nan, shi zai yi miki bayanin komai’’.

Abbakar d’in ya bata amsa, yana mai mik’o mata card d’in Yashjub wanda Najeeb ya ba sa.

A hankali ta sa Hannu

ta karb’i katin tana mai jin yanayinta yana chanjawa, haka kurum….

Cikin nutsuwa take kallon had’ad’d’en business card d’in mai d’auke da sunan ‘Yashjub Imam Kura’.

Shiruu ta yi tana sake kallon sunan tana sake maimaitawa…

kamar wadda ta tuna wani abun ku

ma sai ta d’ago da sauri ta kalli Abbakar sannan ta ce

‘’Abbakar ko dai wannan Mutumin ne wanda muka had’u da shi a office d’in Sir Najeeb

ɗ

in wanda na gama maka maganar shi yanzu?’’

Cikin katseta ya ce

‘’A’a ba shi bane ba, in da ace shine da zai gaya m

ini…

wannan d’in Sir Najeeb ce min ya yi kamar Uncle d’insa ne fa, Kinga wanchan kuma ai bashi da shekarun da za’a ce masa Uncle ko?’.

sannan duba katin da kyau wannan fa landlord ne

Estates gareshi har a su Abuja da nan garin, yaushe aka haifi wanchan Mu

tumin wanda bana jin ya kai 30yrs da har zai gina estates haka??’’.

‘’Eh kam.’’

Manubiya ta ce. Tana mai k’ok’arin son yarda da maganar Abbakar d’in, daga nan ta saka a ranta

maybe kawai ta ji fad’uwar gaban da ta saba ji in ta yi tunanin shi ko ta had’u

da Mama

By mistake ne,

Amman wannan ba wanchan Mutumin bane ba.

A hankali ta ci gaba da karanta sunan tana sake maimaitawa

dan ya yi mata dad’i sosai

A fili ta ce

‘’Yashjub’’

A hankali,sai kuma ta d’an yi murmushi.

Ba tare da ta kalli Abbakar ba

Still

idanunta na akan katin

ta ce

‘’Nagode kwarai Abbakar,

Allah ya sa mu dace’’.

Sai kuma ta d’ago kyawawan idanuwanta tana kallon sa tukunna ta ce

‘’Amman ka san sai na yi shawara da su Ya Musbah da Baba, mu yi adduar Allah ya sa su yarda dan ka san halin

su ba sa so su ga ni ko Jidda wani a cikin mu yana contributing (kawo gudummawa) wajen ciyar da gidan.

Ya Musbah ya dage yana k’ok’arin d’aurawa kan sa abun da ba zai iya ba, wuni yake yi yana guga da wanki A shagon Mati kullum in ka gan shi a gajiye ya

ke abun tausayi.’’

Ta k’arashe maganar tata idanuwanta suna ciccikowa da kwallah.

Murmushi Abbakar ya yi kafin ya ce

‘’Ai har aiki yake yi a wajen masu ginin chan na bayan layi

ya tura suminti ya tura bulo duk dai wani aikin k’arfi yi yake,

ni fa yana

burgeni Manu, Namiji da neman na kanshi aka san shi.’’

Cikin karyewar zuciya ta ce

‘’eh, hakane Abbakar,

amma shi abun nasa ya yi yawa kuma kar aje ayi biyu babu, ka duba fa ka gani saboda d’aurawa kai aikin wahala Baba ya rasa k’afarsa guda d’ayar kuma

ta ji rauni,

Inna ma saboda yawan tunani kalli halin da take ciki!

Kar mu je shima Ya Musbah

abu ya yi mishi yawa shima

ɗ

in aje ya samu wata matsalar, in hakan ta faru( Allah ya rufa asiri )

da ni da Jiddan da basa so mu wahala mu zamu zama a wahale ai g

a Muhsin shima.

A rayuwa in dai ana so a ga abu ya yi perfect (dai-dai) to fa sai an had’a Hannu da Hannu k’arfi da ƙarfe tukunna.’’

Ta k’arashe maganar tata wasu siraran hawaye suna zubo mata, da sauri ta yi ƙasa da kanta.

A hankali Abbakar ya sauk’e aji

yar Zuciya kafin ya ce

‘’Manubiya k’addara kowa da irin tasa, ki daina kuka dan Allah, ki yi addu’a, ki kwantar da hankalinki.

wata rana sai labari.’’

A hankali kanta a ƙasa har yanzun ta ce

‘’Astaghfirullah! amman Abbakar k’addara ta mai zafi c…’’

Ciki

n katse ta ya ce ‘’shiii‘’ Sai kuma ya sauk’e wata nannuyar ajiyar zuciya kafin ya ce ’’Taki kawai kika sani.’’

Kamar zai ce wani abun sai kuma ya mik’e ya ce

‘’Bara in wuce,duk yadda kukayi kya gaya min gobe’’.

A hankali ta ce

‘’To’’.

Daganan suka yi

sallama ta sake masa godiya sannan ta koma gidan Ammi shi kuma ya wuce yana tunanin Allah yasa Manubiya kar ta ji haushin sa sosai idan ta fahimci ya san Yashjub za ta yi wa aiki amma ya b’oye mata..dama bai yi niyyar gaya mata ba, ya fi so ta je ta fara a

ikin tukunna ta fahimci Yashjub d’in ne, ya san kafin nan ba lalle ta iya bari ba.

To kuma yanzu a yadda ya ji tana ik’irarin zata bar gidan Ammi saboda mai kama dashi ya san babu dalilin da zai sanya ta aminta da aikin in ta san shi d’in ne…

wannan dalili

n ya sanya shi ninke ta ta bai-bai..

Sai dare tukunna ta samu gayawa family d’inta har Inna, duk da sun san ba iya magana zata yi ba amma za ta ji su kuma ance in ta amince ta lumshe idanuwanta za su fahimta.

Kamar yadda suka yi zato tashi d’aya Baba

da Ya Musbah suka ce “A’a”, shi Ya Musbah ma cewa yayi ‘’mutumin d’an kidnapping ne ko kuma dai yanada wani mummunan nufi akanta, dan in ba hakan ba tayaya za a yi Mutumin da kullum shine yake bata tsoro a cikin Malamanta ace tashi d’aya ya bata aiki

kuma

aikin ma ba zuwa zata dinga yi kullum ba iyaka sau d’aya a sati kawai, sannan a wata ya d’auki dubu talatin zuwait!! Ya bata.”

cike da bin bayan ya Musbah Baba yace ‘’Tabbas maganar ka haƙƙun Musbahu, ke Manubiya ina so ki..’’

Cikin katse su su ka ji Jidd

ah ta ce

‘’Inna ta amince’’.

Da mamaki duk suka maida duban su gare ta, ai kuwa ta sake lumshe idanuwanta kamar yadda ta yi da farko.

Cikin rashin jin dadi Ya Musbah ya ce

‘’Inna,Manu Mace ce, nauyin

family d’in nan akaina ya ke

Pls karki…’’

Ahankal

i ya ji Baba ya dafa kafad’arsa,Kafin da sanyin murya ya ji ya ce

‘Shikenan’’

Sai kuma ya juya ya kalli Manubiya ya ce

‘’Ki kira Mutumin.

Duk Ranar da ya baki ya ce ki je sai ku tafi tare

Ke da Musbahu’’.

Yana gama fad’in haka ya mik’e ya fice daga d’a

kin.

Ko bayan fitar Baba sai da Ya

Musbah ya kuma yi wa Inna bud’ad’d’an bayani akan illolin da shi yake hangowa game da aikin Manu da kuma yadda ya kamata ace shi ne ya ke d’awainiya da family d’in ba wai ita Mace ba.

Amman yana gamawa da ya sake ce

mata

‘’Kin yarda Manubiya ta je ta yi aikin da aka nemeta ta yi?’’

Sai ya ga ta lumshe masa idanuwanta ta bud’e.

Cikin rashin jin dad’i ya kalli Manu, shima ya ce

‘’Ki kira sa, duk yadda kukayi kya gaya min gobe, sai da safen ku.’’

Ya fad’i haka yana

mai mik’ewa ya fita.

Haka kurum kuma itama Manu d’in sai ta ji duk bata son kira, sai da Jidda da Muhsin waenda suke ta murna da zumud’i suka tisa ta a gaba tukunna ta fita ta je ta aro wayar Siyama ta dawo d’akin.



Gani suka yi kawai Manubiyan tana ta

kallon wayar da katin tana juyawa dan haka Jidda ta sa Hannu ta karb’i wayar da katin ta kwafe nambobin farko a cikin jerin nambobin waya guda ukun da ta gani ata chan k’asan katin,ta dannna call ta saka a speaker..

Yadda wayar take ringing tana d’uu-d’uu

haka zuciyar Manubiya take bugawa kamar zata faso k’irjinta ta fito.

Jin har ta tsinke ba a d’aga ba

ya sanya ta sauk’e wani bahagon numfashi, dan haka kurum ta ji tana fargabar jin muryar wanda zai amsa kiran.

A hankali ta lumshe kyawawan idanuwanta ta

na mayar da numfashi a hankal a hankali…

Tana shirin bud’e idanunta ta yi magana ta ji Jidda ta sake danna kiran a karo na biyu

ta shiga ringing..

Da sauri ta bud’e idanuwanta ta wafce wayar ta ce

‘’Ke ya isa haka, ba ki ga dare ya yi ba, Mutum Babba da

matarsa kin dame sa da kira haka ki bari gobe ma sake gwadaw……’’

ta fad’i haka tana duban wayar dan ta ga ko ta kashe ne saboda ta ji ta daina ringin d’in…

Tsit!haka muryarta ta katse sakamokon ganin timer da ta yi tana tafiya akan fuskar wayar alamun wan

da aka kira ya riga da ya d’auka.

Ganin yadda Manubiyn ta yi tsit ta zubawa fuskar wayar ido ne

ya sanya Jidda da Muhsin su ka lek’a fuskar wayar suma,

cikin zumud’i k’asa-k’asa Muhsin ya ce

‘’Adda Manubiya an d’auka fa, ki yi magana mana.’’…..

A ha

nkali Yashjub ya lumshe idanuwansa ya rintse pillow d’in da ya d’aura akan k’irjinsa yana mai sake tabbatarwa da kanshi

Tabbas ita d’in ce…….

BULAMA ✍



0903 441 3252

*MANNUBIYA*

*21*

Earlier..

Zuwan Abokin Daddy,

senator Bashir biyu wajen Yahanasu, yau zai yi na uku.

Suna waya sosai da Yahansun sannan suna chatting, ta fahimci yana k’aunarta sosai dan yana nuna mata kuma yana yawan gaya mata.

Itama kuwa ta kamu ba kad’an ba dan hatta Daddy da Mommy da su Yashjub d

uk sun fahimci hakan dan har walwala yanzu suka ga tana yi shiyasa

Daddy Mommy da Yash suka duk’ufa da addu’ar ‘Allah ubangiji ya tabbatar da auren ta, yasa kar a samu matsala a wannan karon’.

Yau tun safe take shirye-shirye, k’arfe biyu tana yi ta shiga

kitchen ta fara girke-girke

dan ya ce mata yau yana son cin girkin matarsa, saboda already a jiya suka tsayar ita da shi a kan

Next week zai turo a saka rana kamar wata uku haka a yi aure,

so yau suka tsayar za su sanar da Daddy.

Tana cikin aikin Muni

ra ta shigo, tana son Yahanasu dan haka ta dage akan sai ta taya ta. Duk y’an gidan they are nice to her(ba sa yi mata rashin kirki) duk da basa zama su yi hira especially da Ya’isha wadda take ganin itace sa’ar ta amma kuma babu kyara ba kallon banza tsak

anin su iya gaisuwa ne da murmushi daganan kowa ta shige d’akinta, duk ranar da bata da makaranta ta kan je d’akin su Yasmeen domin su yi hira amma tana zuwa daga gaisuwa suke shareta ko kuma su fara waya tunda ta ga haka itama sai ta ke zama kawai a d’aki

nta wani lokacin kuma ta tafi wajen Mamanta ko Yahanasu su yi hira.

Ba laifi suna shiri da Baaba Larai itama da kuma Mommy ma, ba wai za’a zauna a yi hira ayi wasa da dariya ba amman dai ana gaisawa cikin mutunta juna da kulawa.

Mutum d’aya ce ta fahimci t

a tsane ta a gidan ‘Kausar’ sai ko ‘Yashjub’ wanda shima in ta gaida shi da kyar yake amsawa ciki-ciki!

Kausar d’in kuwa ko ta gaishe ta bata amsawa, bata san mai ta yi mata ba

amman tabbas ta fahimci ta tsane ta gashi kuma ta lura kamar kaff gidan su Ya

sira da su Mommy sun fi son ta da k’aunarta.



Ba yadda Yahanasu bata yi da Munira ba amma ta dage akan sai ta tayata, a cewar ta dama zaman shiru ya isheta kuma ta riga ta gama exams(finals d’in ta)tun last week so bata da abun yi…

4 tana yi ta je ta yi S

allah ta dawo daga nan itama Yahanasu ta tafi domin ta yi Sallah sannan ta shirya bayan ta cewa Munirat d’in idan yayi kafin ta dawo ta juye a cooler dan already komai ya kusan kammaluwa.

Sai da Munira ta had’a komai tukunna ta saka masu aikin suka tayat

a ta kai parlourn bak’i!

Ta kunna burner ta saka turare ta gyaggyara komai sannan ta wuce d’akin Yahanasu.

A gaban madubi ta sameta

sanye cikin wata Turkish gown mai tsananin kyau da tsada,

kwalli kawai ta sanya wa idanuwanta sai powder da lipgloss amma

ta yi tsananin kyau!! asalin kyawun siririya kuma kyakkyawar fuskarta ya fito sosai.

Murmushi Munira ta yi kafin tace

‘’Adda Yaha, yau in senator ya ganki sai ya hantsila’’

ta fad’i hakan ta na mai k’arasawa cikin d’akin.

Dariya duk sukayi kafin

Yahana

su tana dariya ta ce ‘’Ba ki da dama wallahi’’.

Suna tsaye Munira tana taya ta rolling wayar Yahanasu ta fara k’ara.

Tun kafin ta d’auki wayar dama ta fahimci shine dan ringing tone d’in da ta saka masa daban ne.

Tana d’auka kuwa ya ce mata “ya k’araso

, yana ma parlourn bak’i, Kausar ta shigo da shi.”



Da sauri suka kammala,

Yahanasu ta nufi parlourn bak’i,

Munira kuma ta yi sama dan itama zafi take ji tana buk’atar ta d’an watsa ruwa..

Ya yaba kwalliyarta da girkin kuwa, sosai haka ya yi ta zuba san

ti.

Sai da ya kammala tukunna ya zaro kud’i ya bata ya ce ga tukuicin girkin ta sannan ya sake zaro wani ya ce

wannan kuma na masu aikin da suka d’an taya ta da y’an yanke-yanke ne .

Tashi d’aya ta ce masa “Masu aiki wanke-wanke kawai suka yi, girkin kuma

tare suka yi da sister d’inta Munira y’ar amaryar Daddy.’’

Ya san lokacin da Daddy ya k’ara aure amman basu tab’a had’uwa da Amaryar ba, balle y’arta sannan haka kurum tun da ta ce Munirat yanayinsa sai ya chanja.

Haka de suka d’an tab’a hira,

Sai da ta

zo fita domin ta je ta kira masa Daddy dan yana so su yi maganar akan zai turo

tukunna ya ce “ta turo mishi Munirat d’in, ya bata tukuicin ta sannan su gaisa’’

Da ‘’to’’

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login