Showing 84001 words to 87000 words out of 150519 words

Chapter 29 - Mannubiya Complete

sak’ala key d’in ta waje tana k’arasowa jikin k’ofar ta ji ya rufe su ya zare makullin….

….

Ko da Dr ya zo, ce musu yayi “ba wani abun tashin hankali bane ya samu Yassir d’in,

kawai azaba ce ta saka shi ya suma sannan kurjewa

ne kawai kan nasa ya yi ba wai dukan ne ya fasa masa kai har yasa yayi jini ba…

Dan haka su kwantar da hankalin su”

Daga nan, ya basa allurai da duk abunda ya kamata, ya tabbatar musu da “inshaaAllah he’ll be fine..”

Yashjub ne ya raka shi har mota yana d

awowa ya tarar da Daddy har yanzu a tsaye a kan Yassir wanda

ɗ

azu ya farka Dr ya yi masa allurar bacci kafin ya tafi.

K'arasawa ya yi ya tsaya shima yana kallon Yassir d'in….

tabbas

yana son d'an uwansa amma kuma halayen Yassir kullum sake tab'arb'arewa

suke yi sannan shi kuma ga yanayin zuciyarsa wadda yake sake tunzura sa ga aikata wasu abubuwan….saboda Allah bayaga girman shirmen da Yassir

ɗ

in ya yi wa Munira ai ko ba komai bai kamata ya yi mata hakan iyayensu suna cikin gidan ba!!!

Da sauri ya dakat

ar da tunanin gudun kar ransa ya sake

ɓ

aci,

a hankali ya sunkuyar da kansa a ransa ya ce

''bai kamata ace na dake sa ba, inda ace Yassir ya yi aure da wuri to da yanzu maybe yana da ƴaƴa biyu ma..''

Cikin dakakkiyar murya ya ji Daddy ya ce “abun da ka yi

yau was incredibly stupid(gagarumin shashanci ne), ko da wasa kar ka sake yin wannan shirmen,

Ranar da case d'in Yahanasu da Munirat ya faru cewa ka yi saboda ka ga muna wajen ne shiyasa baka hukunta su Yassira ba!

It would be nice of u(za ka fi burgeni)

idan ka ci gaba da bar mini komai a Hannuna…

ban haifi ya’yana

dan wani ya ci kashi a kanku ba kuma

na san ka fi kowa sanin wannan.”

Sai da ya juyo ya kalleshi ido da ido tukunna ya ce

“Next time idan Yassir yayi laifi

U

report

To me!

(Nan gaba idan

Yassir ya yi laifi, ka kawo min ƙararsa kawai)”

Yana gama fad'in haka ya juya ya fita….

Daddy yana fita daga wajen Yassir fannin Ummi ya biya…..ya je ya murza ya ji a rufe kuma bai tarar da akwatunanta ba, dan haka ya yi tunanin ta tafi ne…

a take ya ji

wani irin sanyi yana ratsa shi, yayinda a chan wani b'angare na zuciyarsa kuma yana takaici da jin haushin tafiyar tata da kuma abunda ya yi mata….

Gaba d’aya Yashjub a hargitse yake, mari da maganganun Mommy sun yi mugun b’ata mishi rai!!

Ga kuma abund

a Daddy ya yi masa, sannan ga yadda ya ga Yassir and yana kyautata zaton su Yasmeen ne suka shiga tsakanin Daddy da Ummi….

Ba zai yiu fa ya zuba ido ya tsaya

tarbiyyan k’annensa ya zama haka ba!!!

amma matsalar shine ta Ina zai fara tunda gashi k’iri-k’

iri Daddy ya ja masa barrier(ya shata masa layi)….

ganin da yayi gaba d’aya yana neman sake b’atawa kansa rai ne yasanya kawai ya fice ya nufi side d’insa ransa a mugun b’ace.

Yana shiga parlourn shi ya tarar da Najeeb a zaune….

ajiyar zuciya ya sauk’e

kafin ya ce ‘’zuwa babu sanarwa?’’

Murmushi Najeeb ya yi sanann ya ce ’’inata kiran wayarka baka d’auka, driver d’inka na kira ya ce min kana nan, shine na zo,’’



‘’anything important?

(Akwai wani abu mai mahimmanci ne)’’

Kawai Yashjub ya iya cewa.

Murm

ushi Najeeb ya yi kafin ya ce “ko in tafi ne ?’’

Dai-dai nan Yashjub ya k’araso ya zauna kusa da shi, sai a lokacin Najeeb ya lura da yadda idanuwansa suke

wanda hakan ya basa tabbbacin ransa ne a b’ace.

‘’Me kuma ya faru ??’’

Najeeb ya yi masa tambayar

.

Numfashi Yashjub ya fesar kafin ya ce ‘’ba komai’’.

Tunda ya ce hakan Najeeb ya fahimci maybe family issue ne

ko kuma ba shi da niyyar gaya masa ne, dan haka ya kawar da zancen ta hanyar cewa “tun jiya Ya’isha ta k’i d’aukar wayata, ban san me ya faru

ba. Yash sai ka saka baki a lamarin nan fa dan Yarinyar nan tana wahalar da ni da yawa.’’

Tsaki Yashjub ya yi tukunna ya ce ’’k’aton banza kawai.’’

Dariya Najeeb ya yo kafin ya ce “ai gara ni, I’m not living in denial sannan bana fakewa da

employing

mutum..k’arara nake fitowa, speaking of which..how is she.

(Ai gara ni kai tsaye ƙarara nake fitowa in yi abuna, kuma bana fakewa da

ɗ

aukar Mutum aiki..

Ni ka ma tuna min,

Ya take.??)”

Kamar Yashjub ba zai yi magana ba sai kuma ya ce ’’she’s ok(tana dai d

ai)’’

Ya yi maganar yana mai jin wani sanyi yana maye gurbin b’acin ransa.

‘’Gaya min yadda kuka yi da ita, lokacin da ta je.’’

Najeeb ya fad’i hakan ya na mai gyara zamansa ya fuskanci Yash d’in sosai .

Tiryan-tiryan haka Yashjub ya bashi labarin komai,

wanda kafin ya gama gaba d’aya b’acin ran da yake a ciki ya b’ace b’at!.

Shi kansa Najeeb sai da yayi mamakin yadda Yashjub ya zage ya yi doguwar magana haka.

Dan haka yana dasa aya Najeeb ya ce

‘’Yashjub Yarinyar nan ba na jin iyayenta za su barta ta

k’ara shekara d’aya ma ba tare sun yi mata aure ba,

kar ka tsaya b’atawa kanka lokaci ka je garin hakan miskilanci ya cuce ka, ka san dai kana son ta ko?’’

Shiruu Yashjub ya yi a ranshi yana lissafin ‘ko dai ya cire kunya da taurin Kai ya gayawa Najeeb n

e, dan yana buk’atar shawara! Saboda har ga Allah bai san ta Ina zai fara ba, kuma kamar yadda Najeeb ya fad’a

tabbas tsaf iyayenta za su iya aurar da ita anytime..ya zama dole ya ajjiye komai a gefe dan Manubiya ce peace of mind d’insa(kwanciyar hankalins

a)

Strength (kuzarinsa)

Happiness (farin cikinsa)

da komai na shi’’

‘’Yash….’’

Muryar Najeeb ta katse masa tunani ta hanyar kiran sunansa da ya yi cikin k’ura masa idanu.

A hankali Yash ya gyara zama yana kallon Najeeb d’in tukunna ya ce ‘’menene abun

yi yanzu?’’

D’an fiki-fiki Najeeb ya yi da idanuwanshi tukunna ya ce ‘’kana son nata kenan?’’

Murmushi Yashjub ya yi tukunna ya d’an d’aga masa Kai alamun “yes” kafin a hankali ya ce “a lot(irin sosai

ɗ

innan)”

sai kuma da sauri ya nuna Najeeb d’in da yat

sa alamun warning sannan ya ce ‘’don’t laugh, kuma wallahi kar in ji maganar nan a Bakin kowa.’’

Duk yadda Najeeb ya so hana kan sa yin dariya sai da ya yi, kafin daga baya ya yi shiru sannan ya ce ’’sorry Man, na ji dad’in abun ne sosai shiyasa…

congrat

ulations Allah ya baka Manubiya.’’

A hankali Yash ya ce ‘’Ameen’’ yana wani irin blushing.

Kafin Najeeb d’in ya yi serious face sannan ya maida gaba d’aya hankalinsa a kan Yashjub tukunna ya ce ’’yanzu abunda ya kamata ka yi shine……’’



BULA

MA ✍



0903 441 3252

*MANNUBIYA*

*29*

A hankali Yash ya ce ‘’Ameen’’ yana wani irin blushing.

Kafin Najeeb d’in ya yi serious da fuska, sannan ya maida gaba d’aya hankalinsa a kan Yashjub tukunna ya ce ’’yanzu abunda ya kamata ka

yi shine, ka yi k’ok’ari shaƙuwa ta shiga tsakaninku ta hanyar friendship…

In ya so idan Allah ya kaimu kamar nan da one week (sati

ɗ

aya) to kana iya tunkarar ta da maganar, in ya so mu kuma sai mu je mu samu uncle, brother ko Mahaifinta a san da zaman ka

’’

Wani irin kallo Yash ya yi masa wanda ya sa Najeeb

ɗ

in yin wata y’ar siririyar dariya kafin ya ce ’’a tunanin ka yanzu idan ka ce mata kana son ta direct za ta amince ne?ai ya yi wuri sosai Yash..

Gara ka fara neman friendship d’inta first.

kuma ba fa

nan da wata d’aya ko biyu na ce ba, iyaka sati d’aya na ce maka, sarkin zalama.”

Numfashi Yashjub ya fesar kafin ya ce

’’Najeeb, Manubiya fa ba zata saki jiki da ni har ta yarda mu zama friends ba, that too in one week time that’s impossible(da

ɗ

in da

ɗ

awa

a cikin iyaka sati

ɗ

aya, gaskiya abu ne wanda ba zai yiu ba)

Saboda tanada kamun kai da nutsuwa sosai..she is not the type (ba irin ƴan Matan nan bace) da zata zama friends da duk wani baƙon da ya shigo cikin rayuwarta bane tunda a yanzu dai hakan nake a

wajenta(baƙo/stranger).

Amma tabbas maganarka ma gaskiya ce tunda ko da ace ban tab’a soyayya ba na san kafin mutum ya samu guri a cikin zuciyar Mace ana buk’atar shak’uwa da kuma yarda da sauran su amma ni yanzu a hanlinda nake ciki yanzu haka Najeeb Ina

so ka fahimceni ka fahimci yadda nake jin ta a cikin

zuciyata..dan haka Ina ganin gara kawai in nemi su yardar tata daga baya amma for now abu na farko shine ta san Ina son ta…

kar fa ka manta bayan na gaya mata ta amince da ni

akwai fa su tambaya saka r

ana da buki a gaba kafin

ɗ

aurin aure wnda na san Daddy da Mommy sai sun d’an d’auki lokaci dole su na shirye shirye kafin ayi auren,

Ni kuma gaskiya a matse nake ta zamto matata, ba wai lust(sha’awa) ko wani abun ba a’a abunda kawai na fi buk’ata a yanzu s

hine ta yarda da ni ta aminta da ni in mallake ta ta zama tawa ni kad’ai, ka fahimceni??’’.

Numfashi Najeeb ya fesar kafin ya ce ’’Yash na fahimce ka amman kuma kaima ka fahimce ni,

gaggawa fa aikin shed’an ne..

Gara mu bi komai a hankali.’’

Najeeb d’in y

a fad’i hakan saboda shi yana so su d’an fara shaƙuwa kafin komai dan ba zai yiu ace ya bata aiki Monday kuma Friday tashi d’aya ya ce mata yana son ta ba, ba lalle ta fahimce sa ba zata ga kamar yaudarar ta ya zo yi…



A hankali, bayan zurfin tunani shima

Yash d’in sai ya ce ‘’ok, bara in jira one week d’in.”

……..

Tunda Daddy ya koma d’akinshi yake ta faman kai kawo, gaba d’aya ranshi a dagule ya ke hankalinsa a tashe yake, sam ya rasa gane me yake damun sa ma!

dan shi kansa zuwa wannan lokacin ya fahimci

a mugun birkice ya ke.

Tun kafin aje ko’ina har ya fara tunanin bai kamata ya kori Ummi ba!

ta chanchanci hukunci tabbas dan bai kamata ta tab’a masa y’a ba amma kuma shima bai kamata ya ce ta bar gidan ba,

ko ba komai ya san tana son shi tun ba yau ba so

na tsakani da Allah dan itama ba matsiyaciya bace balle ya ce kud’i ta bi, tana business tana aiki kuma ya san mijinta ya bar musu mak’udan kud’ad’e..

saboda shi (Daddyn) ta yi resigning aiki sam bata damu ba ta ce itama tafi so dama ta kula da shi da y’

ay’an su…

A hankali ya dafe kansa yana jin yana wani irin sarawa ….

Da sallama Mommy ta turo k’ofar d’akin ta shigo a hankali ta k’arasa kusa da shi tana d’ar-d’ar tace

‘’Daddy Yassir fa har yanzu bai farka ba, lafiya kuwa?’’

Ba tare da ya cika kan na

sa ko ya d’ago ya kalle ta ba ya ce ’’lafiya,allurar tana da nauyi ne.’’

Ahankali ta matso ta d’an riƙe Hannun shi ta ce ’’am..i’m sorry about umm..’’

Hannunsa rik’e da Kai har yanzu ya d’ago ya kalle ta tukunna ya ce ’’Get,out!’’

Ta bud’e Baki za ta yi

magana ya yunƙura ya kamo kafad’unta da Hannu biyu ya ce ’’in kin san kina da Hannu a koma meye ne to tun wuri tun kafin mu dena sheda juna ki janye ki fita a idanuwana Khadijah!’’

Wasu hawaye ne suka zuba mata wanda hakan ya sa Daddy ya ji ina ma bai y

i maganar ba.

A hankali ta ce ‘’daddy i…’’

Wuce ta kawai shi yayi ya fita da sauri yana da na sanin yi mata hakan dan bai kamata ya d’aurawa kowa laifin abunda ya aikata ba.

Yana fita aka fara kirana sallar azahar dan haka ya wuce zuwa masallaci.

A masa

llacin suka had’u da su Yashjub,

bayan an fito…

cikin girmamawa Najeeb ya gaida shi Daddyn kuma ya amsa da kulawa daganan Najeeb ya wuce side d’in Yash ya barsu a wajen dan ya ga kamar suna buk’atar space.

Najeeb na wucewa Yashjub ya bawa Daddy hak’uri ka

fin ya fad’a masa abunda ya yi wa su Ummi.

Bai yi murna ba kuma bai yi bak’in ciki ba, makullin kawai ya karb’a a hannun Yash ya wuce sama.

A zaune ya same su, su biyu, a kan gado. Kowacce ta yi tagumi amma fa sun had’a kayayyakinsu tsaf gaba d’aya sun

juye a cikin akwatunan da jakankuna

sun jere su a gaban su.

Tun kafin ya ce wani abu suka mik’e, ba tare da ta kalle sa ba ta ce ‘’Yashjub ne ya kulle mu,

ka yi hak’uri, yanzu za mu tafi’’

Ta fad’i hakan tana k’ok’arin jan akwatuna biyu waenda suke ciki

n jerin akwatunan gaban su.

A hankali Munirat itama ta mik’e ta fara k’ok’arin jan wasu akwatunan…

cikin sanyin jiki Daddy ya matso kusa da ita(ummi) ya ce

‘’Ki tsaya mu fahimci juna …..’m”

Munirat ji ta yi kamar ta kwala k’ara dan takaici,

ya gama ci m

usu mutunci sannan yanzu ta ga da alama so yake ya hana su tafiya…

har ta bud’e Baki za ta yi magana sai kuma ta ajjiye akwatin Hannunta ta fita dan already Daddy har ya kamo hannun Ummi ya hanata fara jan akwatin.

A parlourn ta nemi waje ta zauna tana

addu’ar ‘Allah kar ya sa Ummi ta yarda su ci gaba da zama a cikin gidan nan.

Shigowar Mommy ce ta katse mata tunani..

Ahankali Mommy ta sauk’e nannauyar ajiyar zuciya kafin ta ce ’’Munirat na godewa Allah da baku tafi ba. na kira wayar mamanki bai shiga b

a.

kar ku d’au zafi kamar yadda shima ya d’auka kin ji ko?

bara in shiga

In yi mata magana itama’’.

Ahankali Munirat tace ‘’ita da Daddy ne.’’

Da sauri Mommy ta ce

‘’Yauwa perfect, bari in same su duk su biyun.’’

Har ta nufi k’ofar sai kuma tace

‘’A

m..Munirat dan Allah, d’an je ki kitchen akwai soup d’in da na d’aurawa Yassir, kar ya k’one kafin mu gama.

ki juye a bowl ki kai masa d’akinsa’’.

Kamar Munirat za ta yi mata musu,

sai kuma kawai ta mik’e ta wuce. ‘…..Tun ranar da ta fara ganin Yassir ya

d’an burge ta!

Kyakkyawa ne ajin farko,

halayyarsa ce da ta fahimci ba ta da kyau da kuma yadda gwaggwo ta ja mata kunne kawai ya sanya ta cire rai da shi, dan a tashi d’aya ma tun daga ranar ta ji ta tsane shi….

amma duk kalar tsanar da ta yi masa ta kasa

jin tausayinsa a yau

ɗ

in, dan ta tabbatar inda ita aka yi wa wannan mahaukacin dukan to da tuni ta mutu…..’

Tana wannan tunanin ta ƙarasa kitchen d’in, ta juyo soup d’in a bowl…

Ɗ

akin da ta ga su Daddy sun shiga da shi

ɗ

azu ta nufa, tana zuwa ta d’an yi

knocking….

jin shiru ya sanya ta tura k’ofar ta shiga bakinta d’auke da sallama.

Tana shiga ta ganshi a kwance a kan makeken gadon shi…

A hankali ta k’arasa ta d’an tsaya akan sa tana kallon yadda fuskarsa ta kumbura…

A take kuma sai ta fara da na sanin z

uwa dan sai da ta ganshi ta ga yanayin jikin nasa tukunna ta fara jin haushin kanta na kasa hak’ura da ta yi har sai da ta zo, dan haka ta ajjiye bowl d’in da niyyar juyawa ta ji ya kira sunanta!.

Da sauri ta juya da niyyar fita amma sai ta kasa sakomakon

magiya da hak’urin da ya shiga bata yana cewa ‘sharrin shaid’an ne! ta yi hak’uri ba zai sake ba, kawai he got carried away by her beauty ne (tsananin kyawunta ne ya ru

ɗ

e sa) ya biyewa feelings d’insa towards her(shi kuma ya bari feelings

ɗ

insa gareta su k

a yi galaba a kansa)..

Wallahi bai san me ya shiga kansa ya aikata mata hakan ba!

amma inshaaAllah ba zai sake ba.’’

Yadda jikinta yayi sanyi shi kanshi Yassir d’in ya lura da hakan, yana shirin ci gana da magana ta juya da sauri ta fita, dan tabbas in ta

ci gaba da zama a d’akin tou za’a samu matsala……

Munirat tana fita Yassir ya yi wani killer smile(shu’umin murmushi)….

‘…..Tun ranar farko da ya fara ganinta, dama ya fahimci Yarinyar za ta yi saurin shiga Hannu!!!!

Kum ya lura kamar tana d’an son shi.

Dole ya san yadda zai yi ya samu abunda ya ke so daga gareta, ta ko wacce hanya!!!!

Sannan ya yi amfani da ita wajen hukunta Ummi! Dan ya lura lamarin Mommy da Daddy ya sake tab’arb’arewa kuma yana da tabbacin Ummi ce sila.

Sannan Yarinyar ta tafi da iman

insa, ya san baya sonta,

amma fa tabbas a cikin Mata idan za a tara a raba su kashi d’ari tou kashi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login