Showing 36001 words to 39000 words out of 150519 words

Chapter 13 - Mannubiya Complete

ta ce

‘’Yauwa Abbakar, dan Allah zo mu je ka yi min shaida, ka cewa Sir Najeeb tun muna Yara haka Idanuna suke, ba har

ara ce na yi masa ba’’.

Kallon ta sosai Abbakar ya yi kafin ya ce

‘’Cewa ya yi ki bi shi?’’

Da sauri ta ce

‘’Eh, saboda ya kama ni Ina hararar sa’’.

Wata nannauyar ajiyar zuciya Abbakar ya sauk’e kafin ya ce

‘’Inaa! Ba saboda harara ya ce ki je ba, M

anu! yau ni da ke kashin mu ya bushe, ni ma ya ce min in biyo sa’’.

Za ta yi magana ya ce

‘’Mu je, mu je da sauri ke dai ki yi ta addu’a kawai’’.

..Da hanzari suka ƙarasa block

ɗ

in da office

ɗ

in Sir Najeeb yake, ba tare da b’ata lokaci ba suka kutsa kai

cikin building d’in…

Manubiya ba ta san hanyar office d’in ba Abbakar ne ya yi musu jagora.

A corridorn

office d’insa ne na farko-farko dan haka suka k’arasa da hanzari, duk saurin da su ke yi sai da suka tsaya suka yi addu’a tukunna Abbakar ya d’aga Han

nu da kyar ya fara knocking a hankali kamar wanda baya son yi…

Sun fi 5 minutes a bakin k’ofar office d’in idan Abbakar ya d’an buga sai ya tsaya ya ji ko za’a basu izinin shiga,

amma shiru.

Badaban sun ga motarsa ba

Kuma yanzu haka ma da su ke knocking

ɗ

in kamar suna d’an jin murya k’asa-k’asa, to da sai su ce ba ya nan.

Sai da suka cire rai knuckles

ɗ

in Abbakar har sun fara ciwo,

Tukunna suka ji ya ce

‘’Come in’’.

Abbakar ne ya

ɗ

an murza handle d’in ya fara shiga da sallama, dan Manubiya sai da ta t

saya ta karanto addu’o’in da za su saka Zuciyarta ta yi sanyi tukunna ta bi bayansa ta shiga da sallama itama,

kanta a k’asa.

A hankali ta lumshe kyawawan Idanuwanta tana me shak’ar kamshin AC, room freshner da na zafafan designer turarurrukan su waenda

su ka had’e waje guda suka bada wani zazzafan ƙamshi mai tsayawa a rai!.

Dama tunda suka shigo ta fahimci kamar ba shi kad’ai bane ba,

yanzun kuwa da suka sake bawa iska ajiyar su suka ci gaba da hirar su ya sanya ta tabbatar da

ba shi kad’ai d’in baneba



duk da kuwa har yanzu bata yarda ta kalli direction

ɗ

in da table da kujerun da su ke zaune a kai yake ba…

sam ta rasa dalilin

da ya sanya ta tsinci kanta da samun fa

ɗ

uwar gaba tun farkon shigowar ta cikin office

ɗ

in.

Abbakar kuwa ganin computer har uku

a kan table

ɗ

in nasu

gashi daga gani da shi da Abokin nasa abu mai mahimmanci su ke tattaunawa, hakan ne

ya sanya ya ja Bakinsa ya yi shiru gudun kar ya katse su ya je ya yi laifi

Dan tun

ɗ

azu a rikice ya ke!!!

Jiya dama tunda Mamansa ta ji ‘ya yi wa

Manubiya test’

shikenan take ta faman surutai kuma ta tabbatar masa “muddin ya janyowa kansa kora daga makaranta to wallahi sai dai ya koma ƙauye ya yi noma ko kuma ya yi aure!!

Dan ba zai yiu ace ta yi ta kashe kud’i akan karatunsa tun yana k’ank’ani amma

yanzu ya b’arar a banza ba, saboda wata Manubiya.

Sannan a yanzun da ya kamata ace ta ji dad’in karatun nasa shine yake so ya sake zame mata liability duk saboda wata Manubiya. To ba zai yiu ba.”

Gaba d’aya ta d’aga masa hankali ta dagawa kanta, dan tun j

iya take fad’a masa tana sake nanatawa akan muddin aka gano su tou kamar ya gama shiga masifa ne a cikin makarantar……

Abbakar yana tsananin son karatu gashi ba k’aramar wahala ya sha ba kafin finally ya samu gurbi ya ci gaba da karatun nasa, shiyasa ta y

i nasara wajen rikita sa da kalaman ta..

A hanakali Manubiya ta shiga bin office

ɗ

in da kallo a ranta ta ce

‘’Aljannar duniya, ina ma za a bani aron nan in kawo Inna ko shekara d’aya ne ta yi ta huta sosai, a ha

ɗ

a mata tare da abinci mai kyau sannan ba

hayaniya,

Na san tabbas za ta rage wata damuwar.”

Ba abunda ya fi burge ta da office d’in irin yadda aka ware wajen Hutu daban wajen aiki daban…

Inda su ke zaune shi da Abokinsa ya yi kamar office, sai kuma chan gefe wasu lumtsuma-lumtsuman sofa ga fridg

e, dispenser, tv da center table, kamar dai wani parlourn amarya….

‘’You Guys Are Very Stupid,

GET OUT !!!!!’’

Suka ji muryar Sir Najeeb ya daka musu tsawa..

BULAMA ✍



0903 441 3252

*MANNUBIYA*

*11*

Tsananin rik

ici da tsoro ne suka sanya Abbakar durƙushewa a wajen, ya shiga ba shi haƙuri.

Manubiya kuwa takaici da baƙin ciki ne suka sanyata fashewa da kuka….

Tun farkon zuwan su dama da ya shanyasu a waje takaici ya isheta, daurewa kawai take yi!

Yanzu kuwa abun

na shi ya kaita bango gaskiya.

….Haƙuri sosai Abbakar yake badawa amma sam ya ƙi ma ya tsaya ya saurare shi, tijara kawai ya ke zuba masa da ihu kamar wani ubansa, ba abun da ya fi sake

ɓ

atawa Manubiya rai irin yadda ya sako iyayensu a lamarin

Ta inda y

a ke cewa

‘’..in da mom d’insu ko Dad d’insu suka zo suka gani a wajen ai da za su gaishe su!

amma da yake shi sun raina shi shine suka zo suka tsaya musu kyam!! A Ka, ko shirin gaida su ma basu da shi, da yake ga sa’annin su sun tarar, ko ?.

To idan basu

sani ba yau su sani

Malamanka suma kamar parents su ke a wajenka, in kuma suna da ja akan maganar tashi to su kama hanya su fita, shi kuma

ya basu c.o in fact har spill ma sai sun yi wallahi!!!!

Idan sun isa su je Iyayen su uwa ko uba wani a cikin su ya

basu A a course d’in sa……..’’

Kukan da Manubiya ta sake fashewa da shi sai da ya sanya Hatta Sir Najeeb d’in yin shiru.

Idan wani ya zo wucewa ta bakin office

ɗ

in ba abun da zai hana yayi tunanin dukan ta ake yi a cikin office d’in…

Duk tsura mata idanu

suka yi suna kallon ta!

Banda Yashjub wanda tun lokacin da ta fara kukan in fact

tun farkon shigowar su ma haka nan ya daina fahimtar Najeeb, yanzun kuwa kukan nata gaba d’aya ya sake dagula masa lissafi,

bai ganta ba dan bai juya ba

sai dai kuma wani ab

un mamaki

Iya muryarta kad’ai da ya ji lokacin da ta yi sallama da kuma sautin kukan ta wanda a wannan lokacin yake ji har cikin ransa

ne ya sanya shi jin kamr ya tashi ya je kawai ya rarrashe ta.

Tun a lokacin da ta fara kukan

Abbakar ya fahimci takaic

i da kuma tuno Inna ne suka saka ta kuka.

Sir Najeeb kuwa takaicin ta ne ya sake lullub’e sa, ya lura da yadda bata ma yi attempting ta ba shi hak’uri ba tun farko, yanzu kuma ta cika masa office da koke-koke, abun da yace ta daina yi masa a aji shine yau

ta kwaso ta kawo masa har office, dan haka a fusace ya zagaye tebur d’in da ke a gaban sa ya wuce Yashjub da niyyar nufar inda take kamar wanda zai dake ta.

Cikin hanzari Yashjub ya tashi tsaye, ba tare da ya juyo ba ya ruk’o Hannun Najeeb da sauri dan a

lready har ya gota sa

‘’Wait pls!’’

Kawai ya iya cewa.

Daga haka ya cika masa Hannu tukunna ya juyo ya nufi inda Abbakar ya ke a durk’ushe ya ce masa

‘’Stand up!.’’

Sai da ya lumshe idanuwansa ya bud’e tukunna ya ce ‘’ki yi shiru ko ki fita’’ yayi mata m

aganar ba tare da ya kalle ta ba.

Da kyar Manubiya ta samu ta ha

ɗ

iye sannan ta share hawayenta ta shiga sauk’e ajiyar zuciya a jejjere itama har yanzu bata bari sun yi ido biyu ba.

Da sauri Abbakar ya mik’e ya na cewa

‘’Wallahi , I don’t want to i

nterrupt you ne, thats y (wallahi bana so in katse ku ne, shiyasa) muka yi shiru, dan Allah ku yi hak’uri’’.

Kamar ba zai ce komai ba sai kuma kawai ya juya ya ce

‘’Sir Najeeb a yi musu afuwa mana’’

Shiruu kawai Najeeb ya yi ya ƙurawa Yashjub ido yana

mamakin shi, tun da ya san shi

bai tab’a gani yayi irin hakan ba…

lamari wanda ya shafe sa ma

barin wajen yake yi ballantana wannan da bai shafe sa ba.

Shi har gq Allah da ya ji ya ce masa ‘wait pls’ yayi tunanin so yake ya mik’e ya fita inyaso daga nan

sa cigaba da hayaniyar tasu …..

Sai da Najeeb d’in yaga Yashjub ya d’an yi masa murmushi tukunna ya kawar da nazarin da ya soma ya d’aga masa kai kawai ya juya ya koma wajen zaman sa ya zauna,

Ya zubawa Abbakar Idanu.

Chan kan sofa Yashjub ya koma ya zau

na ya tsurawa tV

ɗ

in da ba a jone take ba ido.

Da sauri Abbakar gudun kar su sake yin wani laifin ya ce

‘’Morning !

Sir,ka ce mu biyo ka shine..’’

Cikin katse shi Najeeb ya kalli Manubiya ya ce

‘’Discuss on Email and Linguistics’’

Dibi-dibi ta hau yi

kafin kawai ta yi bismillah ta rufe idanunta

tukunna a hankali ta ce

‘’Ban iya ba’’.

Cikin fushi ya ce

‘’Ko kuma dai kin manta,ko?

Saboda a takardarki in da ace ban gano yi miki akayi ba!

Da tsaf zan baki A.’’

A hankali gaban ta yana fad’uwa ga b’aci

n rai ta ce

‘’Ka yi hak’uri Sir, Mahaifiyata ce bata da lafiya, tana kwance a asibiti ma yanzu haka!

Shiyasa ya yi mini, ka yi punishing d’ina amman dan Allah ka kyale Abbakar,

tausaya min yayi, bashi da laifi.

dan Allah.’’

Tabbas ya tausaya mata, dan

ko ba a bashi tabbaci ba ya yarda da gaske take duba da yadda yanayin kalar idanunta suka chanza da kuma zafafan hawayen da ya ga sun zubo mata, ka

ɗ

ai, sun isa tabbatar masa gaskiya take fad’a.

Tun yana k’ank’ani mahaifiyarsa ta rasu bayan doguwar jinya

amma sam bai manta zafi da ra

ɗ

a

ɗ

in rashin lafiyar mahifiya da kuma rasuwar ta ba!

Hakan ya sanya ya d’an sauk’o, zuciyarsa ta d’an yi sanyi.

Tsit office d’in ya yi, baka a jin k’arar komai sai na Ac yayin da Manubiya take ta faman sauk’e ajiyar Zuciya a

jejjere, ahankali.

Yashjub yana nan a yadda ya ke tun

ɗ

azu ya k’urawa waje d’aya ido, k’arar wayarsa ce ta katsewa kowa tunani….

A hankali ya zaro wayar daga cikin aljihu ganin sunan Daddy ne ya sanya shi mik’ewa ya amsa wayar ya kara a kunnensa kafin ya

nufi k’ofa da

ɗ

an hanzari cike da k’asaita.

Tun lokacin da Manubiya ta shigo dama take tsaye a bakin k’ofar har kawo wannan lokacin, ganin da tayi ya mik’e kuma ya nufo ta ne ya sanya gaba d’aya ta diririce….

d’azu ta ji k’arar waya amma a zaton ta bai am

sa ba ko kuma ma maybe ta Sir Najeeb ce ya bari akan in sun fita ya amsa, sam

Bata lura da wayar da ke kare a kunnensa ba dan ba shi take kallo ba directly kawai dai tana iya ganin Motsin sa ne.

Ganin da ta yi dai da gaske itan ya nufo hakan ya sanya ta

yi sauri a k’ok’arin kaucewa dai-dai shima ya kauce da niyyar zagaye ta ya bi ta bayanta ya fice!

A tare suka sauk’e ajiyar zuciya sakamakon d’an kusancin da suka sake samu wanda ya sake dilmiya su a wani yanayi na daban.

Sai da Yashjub ya lumshe idanuwan

sa ya bud’e tukunna ya sake k’ok’arin kaucewa domin ya samu ya wuce ta inda take da farko, ba tare da ya kalle ta ba yanzun ma,

amman sai akai rashin sa a dan a dai-dai wannan lokacin ne itama ta kauce da niyyar ta bashi hanya a karo na biyu!.

Ɗ

an taku

ɗ

ay

an da ya yi da niyyar kaucewa kuma sai ya sanya suka matso daff da juna kamar za su yi gware.

Zuwa wannan lokacin Manubiya ta tabbatar fad’uwar gaban da take samu da yadda bugun zuciyarta ya sauya tun farkon shigowar ta office d’in a

ta dalilin wannan bawa

n Allahn ne

Saboda

The more yana kusanto ta

The more bugun zuciyarta yake k’aruwa…..

Haka kurum sai ta tsinci kanta da son kallon fuskarsa dan haka ta d’ago kyawawan idanuwanta waenda ruwan hawaye,takaici, bak’in ciki, damuwa da k’unci

Suka cikasu taff.

.

Ganin sun kusan yin gware a karo na biyu ne ya sanya Yashjub saita kwayar idanunsa a fuskarta da niyyar ce mata

‘Ta tsaya shi zai matsa, ya wuce,ya fita’…

Karaff!idanuwansu suka sark’e a cikin na juna.

Sai da numfashin Manubiya ya d’auke na y’an sakan

nni

tukunna da kyar ta samu ta nemo shi ta daidaita shi ya dawo mata dai-dai,

A Chan ƙasan zuciyarta ta ce

‘’Ma shaa Allah!!!!’’

Duk yadda Yashjub ya so ya d’auke idanuwansa daga kanta kasawa yayi, a lokacin in da za a tambaye shi yanayin Bakinta ko han

ci hatta ma da kalar fatar ta to ba lalle ya iya fad’a ba! Saboda

tsabar yadda zuciyarsa da ruhinsa suka karkata sannan suka dulmiya a cikin kwayar idanunta……

…….

Kamar irin idan Mutum yana bacci

ɗ

innan ya dinga jiyo muryar Mutum daga chan nesa ana tashin

sa, haka Yashjub ya fara jiyo muryar Daddy a chan nesa yana cewa

‘’Hello,Yash!Yash!!Yashh!!!!are u with me, kana jina kuwa?’’

Wani bagwaren numfashi ya fesar sannan ya yi saurin lumshe idanunsa, a hankali ya sake runtse idanuwan nasa waenda bai riga da

ya bud’e su ba har kawo wannan lokacin…

da kyar ya had’iye wani abu wanda ya tokare masa mak’oshi!!!

Kafin ya sauk’e ajiyar zuciya tukunna ya ce

‘’Yes!,Daddy’’

Daga nan ya zagaye ta tukunna ya bud’e idanunsa ya kama handle d’in ƙofar da sauri ya murza ya

fita..

Sai da Abbakar ya ce ’’Manu!’’

tukunna Manubiya ta dawo office d’in, a take kunya da takaici suka lullub’e ta dan ta san tabbas sun lura da irin kallon da ta yiwa wannan bawan Allah da kuma yanda ta k’ame k’am! Ko bayan fitar sa.

‘’Hmm’’

Kawai

Sir Najeeb ya ce, kafin ya fara magana

‘’Dole zan yi cancelling test d’in ku both of you, sai ku dage a exams. Bai kamata a ce na d’aga muku k’afa har haka ba bayan gashi na kama ku dumu-dumu!!!

Amman uzurin ki shi ya taimake ku, ku dage a exams sannan k

o da wasa karku k’ara yi mini wannan shirmen a test ko assignment, idan mom d’inki bata da lafiya ki zo ki yi reporting’’.

Da sauri suka had’a Baki suka ce

‘‘In sha Allah, mun gode Sir,

Sosai.’’

A hankali ya jawo computersa ya fara latsawa

kafin ya ce



‘’U can leave’’

Ba tare da ya kalle su ba.

………………………

BULAMA ✍



0903 441 3252

*MANNUBIYA*

*12*

Tun lokacin da Yashjub ya baro office d’in Najeeb, gaba

ɗ

aya ya rasa nutsuwar sa. Har ya k’arasa gida ya yi wanka ya yi

sallah ya nufi side d’in Mommy domin ya Isar mata da sak’on Daddy gaba d’aya hankalinsa yana kan Yarinyar da ya gani

ɗ

azu a office d’in Najeeb.

Sai da ya yi addu’a sosai tukunna ya samu tunanin ta ya bar shi ya yi sallah a nutse.

Bai samu Mommy a parlou

r

ɗ

inta ba dan haka ya wuce d’aki sai dai nan

ɗ

in ma bata nan….

Har ga Allah Kansa har ya fara ciwo shiyasa ya bi gadonta ya kwanta shi kad’ai ya yi shiruu.

So yake ya lumshe idanuwansa ya d’an huta amma ba ya son yin hakan saboda ya san yana lumshe su id

anuwan wannan Yarinyar zai ke gani.

Abun takaicin shine ko sunanta bai sani ba sannan ya san idan za’a jere masa mata blindfolded(a rufe musu Idanuwa da kyalle) ace masa ya nuna ta a cikin su sam ba zai iya gano ta ba.

Ya san

bashi da wata alak’a da ita a

mman kuma sam muryarta da idanuwanta sun addabi zaman lafiyar sa ya rasa nutsuwa ya kasa yakiceta sam ya rasa sukuni, tun

ɗ

azu da ya ganta har kawo yanzu babu daƙiƙar da ta wuce wadda bai yi tunaninta ba.

Sai da ya yi da gaske ya had’a da addu’o’i tukunna



ɗ

azu ta

ɗ

an lafa a ransa ya samu ya yi sallah cikin nutsuwa…..

Wani bahagon tsaki ya jaa ya miƙe ya zauna a kan gadon,

kafin ya zaro

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login