Showing 48001 words to 51000 words out of 150519 words

Chapter 17 - Mannubiya Complete

farko ka k’i yi,shi za tayi.

Ita da take y’a mace wadda ya ci ace yanzu ta yi Yara biyu ko uku ma, amma ka ja mata har ta yi kwantai…

tunda ni dai rabon da in ji sallamar zance da sunan ta har na manta,

ta d’auki shegen girman kai ta azawa kanta bata

kula waenda suke zuwa mata ai gashi duk sun gudu, ba fata nake miki ba Amman da wuya ki auru sai ki je ki rungumi littafi.’’

Shiruu kowa ya yi baka jin maganar kowa sai ta Kaka Mallan ta inda ya d’aura da cewa

‘’Duk da ka nuna ban Isa da kai ba dole zan s

aka baki a maganar Jidda wanda dalilina na biyu kuma shine

ba zai yiu ka tara Yara da kai kanka ku na ta kurmutsa a d’aki a takure kuma kak’i d’aukar shawara sannan ka yi tunanin za mu yi shiru ba.

Ba zan zuba ido Yaranka mata har biyu su tagaiyyara ba.!

Ita Manu yanzu ta riga ta zama sai an had’a da addu’a, shiyasa tun kafin Jidda itama ta yi kwantai na riga na gama yanke shawara kowa ya saurara ya ji..

Nan da sati biyu dama za’a kawo kayan sa ranar Siyama dan haka a tare a kuma rana d’aya Yusuf shima za

i bada na Jidda, in Allah ya kaimu nan da wata uku za ‘a had’a a d’aura auren tare da nasu Siyama a mik’a ta d’akinta, in kuma anan cikin gidan ma zai zauna shima sai a ware ma sa nashi fannin.

Sai maganar kud’in Matar senator, Ummaa da Uncle sun bada du

bu bibbiyu Habu ya bada uku nima zan bada uku a had’a a bata kai kuma sai ka nemi cikon ka cikata mata, Allah ya rufa asiri.

Akwai mai magana?’’.

Ahankali Anty Umma ta ce

‘’A’a Kaka’’.

Tana mai jin takaici a ranta, ita da take Mace kuma za’ayi auren y’a

rta, babu wanda a cikin su ya bata ko sisin kwabo, Yayar Siyaman sai ita ne kawai suketa fafutukar komai, hatta lemukan da za’a tarbi bak’i ita ce zata siya, an sakar mata komai an zuba mata ido kuma ta sab ba bayarwar za su yi ba daga nan har akai siyama

d’akinta,amma yanzu ita an hura mata wuta sai da ta bada dubu biyu…

A hankali Baba ya ce

‘’Kaka Mallan,Ina da magana’’

Sai da Kaka Mallan ya d’an k’ura masa ido tukunna ya ce ‘’Muna jin ka’’.

Sai da ya fara yin godiyar karo karon kud’ad’en da suka yi ma

sa tukunnna.

Cikin rashin jin dad’in maganar da zai fad’a ya ce

‘’Ka yi hak’uri Kaka, ba wai jayayya zan yi da kai ba amma Ina ganin maganar auren Jidda da Yusuf

gara kawai a barta’’

Ba tare da Baba Habu ya ce komai ba kawai ya mik’e ya fice daga parlou

rn gaba d’aya.

Cikin fushi Uncle ya kalli Baba ya ce

‘’To ai shikenan, gata nan sai ka kwad’ata ka cinye, amma wallahi idan ta sake janyo magana kar a kuskura a sake involving d’ina a ciki’’.

Daga haka ya juya ga Ya Yusuf wanda ya sunkuyar da kansa yay

i shiruuu

ya ce

‘Yusuf dan Allah dan Annabi ka hak’ura da Yarinyar nan, kana da degree d’inka da sana’arka babu gurin Yarinyar da zaka je ta k’i ka’’.

Anty Umma dai bata tanka musu ba hakanan ta jaa Bakinta kawai ta yi gum, tana kallon kowa.

Da dakakki

yar murya Kaka Mallan ya ce

‘’Musa, inaso ka gaya min laifin Yusuf kwara d’aya tak’’.

Ba tare da shakkah ba Baba ya ce

‘’Yusuf bashi da laifi Kaka kawai dai na ga a halin da Jidda take ciki na damuwa da rashin lafiyar Mahaifiyarta bai kamata a yi mata au

ren dole ba, kuma ni ban shirya aurar da Jidda ba har sai mahaifiyar su ta samu lafiya, InshaaAllah.’’

Sai yanzu Anty Umma ta ce

‘’Ita Jiddan ta ce maka bata son Yusuf d’in?’’

Tun kafin Baba yayi magana Jidda ta yi k’arfin hali da sauri ta ce ’’Eh,Umma

’’ a hankali.

‘’Uhm, to ai shikenan’’

Anty Umma ta ce, daganan ta ja bakinta ta sake yin shiru.

Tabbas ran Kaka Mallan ya b’aci dan haka kawai ya ce “kowa ya tashi ya tafi’’

Yanayinsa kad’ai ya sanya kowa ya fahimci tabbas in ba da kyar ba to kuwa sun d’

aura gaba kenan da shi da Baba har abada..

Hakanan taro ya watse zuciyar kowa da k’unci, dan shi kansa Baba saboda yaga ba yadda zai yi ne shiyasa yayi magana bayaso ya sako karatu su yi masa chaa amma yanaso Jidda ta fara ko da level one ne ta d’an saka

k’afarta a jami’ar tukunna a yi auren, ga kuma damuwar da suke ciki ga rashin lafiyar Inna, abubuwan da yawa!! Ya san dama ba lalle su fahimce sa ba.

Shiyasa washegari ya bi Kaka Mallan anty Umma Baba Habu da Uncle,

dan yana so su sasanta a tsakaninsu su m

anyan sannan ya fahimtar da su.

Amman sai abun bai yi masa dad’i ba sam dan Anty Umma ce kawai ya samu ta d’an saurare sa ya gama bayanin sa, ta ce

‘Ba komai’ kawai.

Dama ita ƴar i don’t care ce.

Uncle kuwa tun a masallaci ya ce masa yana son ganin su s

hi da Baba Habu in an fito amma suna fitowa ya shiga gidan da yake parking motarsa ya zari mota yayi gaba gashi ranar lahadi ne bare ace aiki ya je.

Baba Habu kuma ya ce masa bacci zai yi, lokacin siesta d’insa yayi.

Kaka kuwa tun kafin ya k’arasa shiga wa

jen nashi ma ya kore sa.

Tun daga ranar kuwa kan y’an gidan ya sake tarwatsewa, da farko lamarin nasu rashin had’in kai ne kawai yanzun kuwa abun ya had’a har da jin haushin juna da fushi.

….

Satin Manubiya d’aya da fara zuwa aiki gidan Ammi.

most atimes (

mafi yawanci) exams

ɗ

in nata da safe suke yi shiyasa take zuwa gidan tun kafin gari ya fara haske saboda ta samu ta yi ta gama ta tafi on time,ranar na Sir Najeeb ne kawai ta rok’i Ammi,

tun ana i washegari exams

ɗ

in ta ce mata ’Dan Allah ta yi mata hak’ur

i

10 za ta taso InshaaAllah zuwa 11 za ta iso gidan ta yi aikin nata.’

Allah ya taimake ta a lokacin da ta je ta na neman alfarmar

Mama tana d’akin Ammin

tana shirya mata wardrobe d’inta,ai kuwa tashi d’aya Maman ta saka Baki…

Dan haka ba dan Ammin ta so b

a sai dan girman Maman a idanunta ya sanya ta hak’ura ta yardar ta amince…..

Itafa so take ta maidawa su Manubiya rayuwar su living hell (mafi ƙololuwar azaba) amma ta lura Yarinyar ita da k’aninta (Muhsin) kamar waenda ake jona musu charji, duk kalar uba

n aikin da ta tula musu kafin ace kwabo sun kammala shi tsaf.

A b’angaren Manubiya kuwa sam aiyyukan da Ammi take tula mata basa damun ta, ita babban tashin hankalin ta a gidan ita ce’Mama’, kamanninta da wannan Mutumin sun yi yawa sannan in dai ta kalli

fuskar Mama tou sai ta tuno shi kuma indai ta koma gida ta kwanta barci tabbas sai ta yi mafarkin shi maimakon ta yi mafarkin Mama tunda ita ta ke gani,

A’a

Mafarkin Mutumin take yi

kuma kullum kamar sake ingiza mata tunanin sa ake yi.

Hakan ya sanya a

ko da yaushe take k’ok’arin ganin ta yi nesa da Mama. Wanda zuwa wannan lokacin Hatta ita kanta Maman ta fahimci Manubiya wasan y’ar b’uya take yi da ita, bata san dalilin Yarinyar na guje mata ba gashi ita kuma har ga Allah Yarinyar ta shiga ranta, sosai

………

•••••

Amaryar Daddy tana cika sati biyu da tarewa rana tsaka ya ce ’ta had’a kayanta za su koma main house d’insa,’.

*Ummi*

Mace ce mai sauk’in Kai da fahimta ga hak’uri, shiyasa tun kafin auren ma da ya ce mata ta ajjiye aikinta tashi d’aya ta ajj

iye, sam bata yarda ta yi jayayya da shi ba shiyasa yanzun ma da ya ce su koma main house

ɗ

in nasa tashi d’aya ta ce ’’to’’,

Kuma ita har ga Allah bata ji komai ba dan by then (zuwa wannan lokacin) sun saba da Mommy da Ƴaƴanta saboda bata yi k’asa a guiwa

ba sai da ta amshi numbers d’in su kaf su ke gaisawa,

sam

bata damu da yadda a ko da yaushe ita take kiran su ba.

Basu samu dawowa ba sai

washegari, dama gado da set d’in kujeru kawai ta yi amma hatta kayan kitchen a gidan ta je ta tarar dan haka aka kun

to mata iya gadonta da kujerun

aka zo nan mansion d’in aka kafa mata a side d’in da Daddy ya nuna mai d’auke da parlour mini kitchen dining area da two bedrooms, k’ofar side d’in nata yana kusa da na Kausar na Yasira kuma kusa da na Mommy.

Tare ta zo da

Ƴ

arta Munirat, mai kirki sosai da hankali ga nutsuwa

Ga ta kyakkyawa sosai

doguwa dirarriya black beauty, ga gashi tubarkallah.

Ummi ta so Munirat ta zauna

a d’ayan d’akin gefenta(na cikin fanninta)

amma sai Mommy ta yi insisting

akan itama a ware mat

a nata d’akin a gefen na su Yasmeen, hakan kuwa aka yi,

aka ware mata d’aki anan side d’in nasu su uku

Ita, Yasmeen sai Yadira

kowa da d’akinta amman suna sharing parlour….

Lamarin Yasir ya ishi Mommy

gashi gidan an dawo kamar komai bai faru ba dan h

atta Kausar ta ware sosai ta ci gaba da shiga mutane…

Daddy shima ya d’an sak’k’o yana d’an wasa da yaran

Shi da Mommyn ne dai har yanzu daga gaisuwa shikenan

shima sai in a gaban yaran ne ya ke amsawa amma

Idan iyaka su biyu ne ko kallonta baya yi.

Am

man shi Yasir har yanzu shiru Allah kad’ai ya san inda ya je ya zauna.

Dan haka ta yanke shawarar tunkarar Daddy da maganar yau duk da bata san ya za su kaya ba amma ta saka a ranta zata yi koma menene muddin za a nemo mata Yasir d’inta.

Dama yau

ɗ

in ita

ce da girki dan haka ana gama dinner bayan an d’an tab’a hira kowa ya watse itama ta je ta d’an kimtsa ta nufi chan sama hawa na biyu inda side d’in shi yake.

A parlournsa ta same shi yana waya dan haka ta koma gefe ta samu guri ta zauna.



BULAMA ✍



0903 441 3252

*MANNUBIYA*

*17*

Ya fi 1 hour yana wayar kafin finally ya katse kiran ya ci gaba da danna computer dake a gaban sa.

Ta ji zafin yadda ya yi mata, dama a wuya take dashi yau ko kunya babu haka ya dinga

zolayar Ummi

ɗ

azu a wajen dinner a gaban kowa ita kuwa ko kallo ba ta ishe sa ba.

Da kyar ta samu ta danne abunda takeji yana taso mata, ahankali ta ce’’barka da dare,Daddy’’.

Ba tare da ya kalle ta ba

Ya ce ‘’za ki iya tafiya, na gode.’’

Yana gama f

ad’in haka ya mik’e ya tartare kayayyakinsa waenda ke zube a gabansa kan centre table

ɗ

in, daga nan ya nufi hanyar d’akinsa.

Da sauri itama ta mik’e ta ce ’’a kan Yasir na zo mu yi magana’’.

Kamar ba zai kula ta ba sai kuma ya ce ’’what about him?( me y

a faru akanshi?).

Ba tare da ya kalle ta ba.

Sai da ta sauk’e ajiyar zuciya tukunna ta ce

‘’Ba ka lura baya gidan nan ba?

Ya fi 4 weeks fa ba ya nan’’.

Sun fi 2 minutes a tsaye dan sam Daddy bai so ya kula ta. Ya so ya danne fushin sa ya manna mata kaw

ai ya yi wucewar sa amma sai hakan ya gagara..

A hankali ya juyo ya ajjiye computersa da wayoyin

a kan kujerar dake kusa da shi

sannan ya taka ya k’arasa inda take ya ce

‘’Khadijah, kar ki yarda ki kai ni bango a cikin gidan nan, ba ki san ya nake ji ba

idan na kalli fuskarki, ina zaune da ke ne kawai saboda Ƴaƴan da ke a tsakaninmu da kuma alk’awarin da na yiwa su Abba kafin su rasu sannan na dawo gidan nan ne domin na lura in dai na zauna a daban daban ni da Ƴaƴana tou tabbas za ki iya raba ni da su.

B

anason yawan magana ta da ke! saboda na lura baƙin ciki, da tashin hankalina kike son gani, a ko da yaushe kin fi so ki ganni cikin tashin hankali….

Dan haka na zab’a yin nesa da ke!.

Ina samu lumana da kwanciyar hankali daga wajen Saddik’a, abun da kika

gagara ki bani.’’

Bakin Mommy har rawa ya ke yi, ganin tana shirin fara magana ya sanya yayi saurin d’aga mata Hannu alamun ‘wait(jira)’

ya ce

‘’Ba na buk’atar komai daga gareki, kin yi kuma kin ce me isarki…..

Kin san bani da lafiya amma a wannan shekaru

n ki ka zab’i ki tuna mini da case d’in ‘Khadijah’.

Ban san mai zan ce miki ba.

Amma kamar yadda na yi miki sutura na bar ki a cikin Ƴaƴanki sannan bayan na zab’i raba gida da ke na hak’ura na dawo na ci gaba da zama da ke a k’ark’ashin inuwa d’aya tou nim

a inaso ki yi mini alfarma d’aya tak,ina so ‘ki fita a harka ta’!!!!

Iyaka wannan kawai nake da buk’ata daga gare ki.

Case d’in Yasir na ce a gaya miki ki yi solving tun kafin mu zo ni da Saddiƙa, yanzu kuma da ya ƙi dawowa wannan ma matsalarki ce, ke kik

a san yadda za ki yi ki je ki nemo sa, amma Yasir ba jariri bane ba da zaki fake da case d’in sa ki k’ulla wata alak’a a tsakanin mu,

duk inda ya je idan ya gaji zai dawo in bai gaji ba kuma

Ubangiji ya sada fuskokinmu

A aljannah….

abu na k’arshe da zan

ce da ke shine ki tabbata wannan ita ce maganata mai tsayi ta k’arshe da ke, in ba haka ba wallahi zan baki mamaki.’’

Wasu zafafan hawaye ne suka zubowa Mommy, a hankali yana shirin wucewa ta ce

‘‘Ubangiji ma muna yi masa laifi mu rok’i gafara kuma ya y

afe mana, na ce ka yi hak’uri Daddy!

Ka bani last chance!

I love u, kar ka yi mini haka…..’’

Cikin fushi ya ce

‘’Ba kya so na ba kya k’aunata sam, shiyasa kike turturing d’ina(azabtar da ni). ko kin san cewa akan maganar da kika yi mini kad’an ya rage in

mik’a kaina ga hukuma?kuma na san kin san menene hukunci na ko?’’

Cikin zubar hawaye Mommy ta ce

‘’Ka yi hak’uri mu bar wannan maganar ta wuce…..’’

‘’Get out!’’

Daddy ya fad’a cikin katse ta.

Za ta yi magana ya sake cewa

‘’ki fita ,na ce.’’

Da d’an k’

arfi.

A hankali ta sa Hannu ta share hawayenta ta toshe Bakinta saboda kar sautin kuka ya sake fitowa, sai da ya

ɗ

an lafa tukunna cikin tsananin mutuwar jiki ta ce’’ka yi hak’uri’’

daga nan ta juya ta fita tana mai sake toshe Bakinta.

Ya dad’e a wajen

kafiin da k’yar ya samu ya juya ya wuce d’akinsa.

….

A d’akinta ta tarar da Kausar da Yasira…

Ta so ta b’oye musu damuwar ta amma suna had’a idanu da su sai ta karaya bata san lokacin da ta fashe da wani irin kuka ba.

Sai da suka yi da gaske tukunna suka

samu suka rarrashe ta, ta yi shiru, Yasira ta d’au waya ta kira Baaba Larai, tana zuwa suka shiga tattaunawa.

Ba su suka bar d’akin nata ba sai wajajen k’arfe d’ayan dare bayan sun saka Kausar ta yi musu alk’awarin kiran Yasir washegari,

Idan Allah ya kaim

u…..



Washegari da sassafe

Kausar ta tashi ta shirya cikin wata dress mai kyau wadda bata k’arasa rufe mata k’afafunta ba.

Jan jambaki da kwalliya ta rambad’a sosai wanda hakan ya sake fito da ainihin kalar farar fatarta…

Hula kawai ta saka a kanta daga

nan ta kama hanya ta fice ta nufi side d’in su Yashjub tana adduar Allah yasa bai fita ba, dan dukda yau ba aiki ta ji Yasira tana cewa sunada important meeting.

A parlourn ta same shi shirye tsaf cikin suite ga briefcase d’insa a gefe yana zaune yana sip

ping tea.

A hankali ta saki wani lallausan murmushi kafin ta k’arasa ciki, cikin takun ta mai tsananin d’aukar hankali.

sai da ta je kusa da shi tukunna ta ce

‘’Salam alaika’’.

Tun lokacin da ta turo k’ofar ta shigo ya lura da ita dan haka ya sake tam

ke fuska tamau kamar bai tab’a murmushi ba.

A hankali ta nema waje ta zauna a gefen sa, sannan ta ce

‘’Ya Yash, Ina kwana’’.

Ci gaba kawai yayi da sipping tea d’in sa yana kallon tv still bai ce mata uffan ba.

Badaban Kausar A ce a fagen tsaurin ido ba

to da

a yadda ya tamke fuska ka

ɗ

ai ya Isa yasanya ta tsorata, ta fita.

Duk da tana d’an fargaba haka ta daure a karo na uku ta ce ’’Ya Yash’’.

Lumshe kyawawan idanuwansa yayi a hankali ya juyo gare ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login