Showing 60001 words to 63000 words out of 150519 words

Chapter 21 - Mannubiya Complete

ta amsa tukunna ta sa kai ta fice.

Har Yahanasu ta k’arasa d’akin Munira d’in tana

d’an jin ba dad’i musamman da ta tarar da Munirat d’in ta yi wanka ta shirya…

fuskarta babu kwalliya amma yarintarta da kyawunta sun fito matuk’a, dan haka atake sai ta ji d’an guntun kishi yana taso mata, amma kawai sai ta saka kyakkyawan zato a kyakkyaw

ar zuciyarta ta tura masa Munirat d’in ita kuma ta wuce wajen Daddy domin ta sanar masa da sak’on Senator Bashir d’in.

Tana fita itama Munira ta d’auki hijabinta ta zura ta nufi k’asa d’akin bak’in, ba dan ranta yana so ba.

A hankali ta k’arasa bakin gl

ass door d’in ta yi knocking tukunna ta shiga kanta a k’asa da sallama

‘’Ashe rai kanga rai’’

Muryarsa ta daki dodon kunnuwanta.

Da sauri ta d’ago, ai kuwa suna yin ido biyu ta juya da sauri zata fita.

Amman sai aka yi rashin sa’a ya riga ta zagayawa ya

tare hanyar, dama tun da ya ga ta shigo ya mik’e daga wajen zaman shi ya Isa kusa da ita.

Da sauri ya ce

‘’Haba Munira, after long time no see (bayan lokaci mai tsayi ba a ha

ɗ

u ba) shine kuma za ki yi min haka kamar kin ga wani Aljani?

Kin sa yadda na di

nga neman ki kuwa?‘’

Already Munira har ta fara kuka, dan haka ta d’ago a gigice ta ce ’’Dan girman Allah ka rufa mun asiri, mamana zata iya ganin ka, a gidan nan take aure mijinta kuma shine Mahaifin Adda Yahanasu wadda za ka aure’’

Cikin katseta ya ce

‘’Munirat ai yanzu maganar aure kuma ta tashi tsakanina da Yahanasu sai dai a yi maganar auren mu ni da ke,dan ni ke zan aura yanzu kam.’’

‘’Cin fuskar da zaka yi min kenan ??’’ su ka ji muryar Daddy a kansu.

Wani irin kuka Munirat ta fashe da shi, daman

abunda take jin tsoro kenan..

Yahanasu ta riga Daddy k’arasawa bakin parlourn, yadda ya ga tana hawaye

ya san ba k’aramin abu ta ji ba tunda gashi shima iyakar maganganun senator na karshe ya ji amma gaba d’aya hankalinsa har ya tashi.

Idonshi a kan s

enator ya k’arasa cikin parlourn,

ba tare da ya kalli Munirat ba

cikin fushi ya ce ‘’bamu guri’’

Da sauri ta juya ta fita har da tuntub’e.

A bakin k’ofar suka yi karo da Yahansu tana hawaye, tana ganin ta ta juya da sauri ta nufi main parlour yayinda

Munirat d’in ta bi ta da gudu, sai da suka kusa shiga parlourn tukunna ta samu nasarar cafko Hannun Yahanasun tana kuka ta shiga bata hak’uri sannan ta shiga ƙoƙarin fahimtar da ita ‘wallahi bata da niyyar cin amanarta, kuma ko Maza sun k’are bata ga dali

lin da zai sanya ta saurari senator Bashir ba ma ballantana a zo ga batun aure’’

Wani kalar murmushin takaici

Yahanasu ta yi kafin ta ce ’’kar ki damu, sam ba laifin ki bane ba Munirat,

Idan ba ki sani ba yau ina so ki sani ‘wannan shine aure na 8 da a

ka so a kulla min yana warwarewa’!

sam ban ji haushin ki dan ya ce ke yake so ba, kawai dai ina kuka ne sabo da…..”

Salatin da Kausar ta rafka ne ya katse su, tashi d’aya ta figo Hannun Munirat sai da ta kai ta tsakiyar parlourn tukunna

ta ce

‘’oya oya!

2

0 minutes kawai zan iya baki!

Ki tartare garbage d’in (sharar) tsummokaranki ki bar gidan nan tun kafin in yi miki abun da za ki yi regretting (da na sanin) haihuwar ki da aka yi a duniya’’

Cikin tsananin b’acin rai takaici da kuma tausayin Yahanasu

waen

da suka had’e waje d’aya

suka tunzura Munirat ta kalli Kausar da idanuwanta da suka jik’e da hawaye ta ce

‘’Ai ba ke kika kawo ni gidan ba,

ballantana ki ce za ki koreni’’

Kamar jira Kausar d’in take yi tashi d’aya ta d’aga Hannu ta

d’auke Munirat da

mari!!!

dai-dai nan Mommy Ummi

da su Yasira suka faara firfitowa sakamokon hayaniyar da su

ke ji sama-sama tana d’an k’ara yawa.

Kallon ƙasƙanci da tsana Kausar ta yi mata kafin ta matso daff da ita

ta ce

‘’Ko Yasira kin tab’a jin ta gaya mini magana

anyhow a cikin gidan nan?’’

Da sauri Ummi ta k’araso ta ce

‘’Kausar, mai ya had’aki da k’anwar taki haka?’’

Cikin rashin kunya da tantiranci

ta kalli Ummi sama da k’asa ta watsar sannan ta juya ga Mommy wadda ta k’araso garesu yanzun ta ce

‘’Mommy, sen

ator ya ce ya fasa auren Yahanasu, Munirat zai aura!!!

All thanks to abun da ta zuba masa a cikin abinci ya ci yau’’

Kusan duk a tare Ya‘isha,

Yasira, Yusra da Yasmeen su ka ce ‘’watt!’’

Suna zaro ido

‘’Dama tun da na ga tanata faman kai kawo a kitche

n da sunan tayata girki wallahi na san za a rina!!!

Idan ba haka ba tayaya tashi d’aya zai ce wani ita yake so? Kaff y’an Matan gidan nan bai ce yana son kowa ba, sai ita’’

Cewar Kausar.

‘’Ya Isa haka Kausar’’

Ummi ta fad’a cikin d’an tsare gida

‘’Ke Sa

ddik’a bai Isa ba!!!

ko kowa ba zai yi magana ba ni zan yi magana kuma sai in da k’arfina ya k’are wallahi, sai kun warware abun da kuka yi kafin ta bar gidan nan, dan ba za mu iya ci gaba da ganin Yahanasu a wannan situation d’in ba’’.

Kausar ta ce tana k

allon cikin Idanun Ummi…

Da sauri Yasira ta matso ta ce ‘’Tabbas nima zan yi magana, kuma bayaga haka ma yau in ta yi mata aka yi shiru gobe d’aya a cikin mu zata sake yi wa dan haka dole a d’auki mataki’’

Kamar yadda Kausar da Yasira suka ce ‘sai Munira

ta bar gidan

After ta warware asirin da ta yi wa senator yau ba sai gobe ba’ haka ma su Ya’isha da Yasmeen da su Yusra suka yi wa Ummi da Munirat chaa!! A ka!

chin kashi Kala-kala babu kalar wanda ba su yi musu ba a wannan ranar…

Ganin rashin kunyar ta

su ta yi yawa ne yasanya Ummi ta kalli Mommy da Baabaa Larai ta ce

‘’Yanzu sai na ce ku hana su tukunna za ku yi magana??’’

Dai-dai nan Daddy ya shigo cikin parlourn ransa a b’ace da alamun ya sallami Senator ya fita ta k’ofar baya sannan daga gani basu

k’ark’are k’alau ba..

A hankali Mommy ta ce

‘’Saddik’a, situation d’in nan is out of my hand(al’amarin ne ya fi ƙarfina), Yaran nan sun fi ku gaskiya…

Yahanasu has sufferd a lot (Yahanasu ta sha wahala sosai) a kan irin wannan issue d’in.

a ko da yaushe

idan irin hakan ta faru mu kan ji inama ace munada ikon gyarawa, yanzu kuwa muna da iko kinga kuwa ai bamu da abun yi wanda ya wuce mu gyara d’in ko?.

Idan ba ki duba komai ba to ina so ki duba maraicin Yahanasu dan Allah ki yi wa Munirat magana, a samu a

daidaita komai, wallahi

Yarinyar nan tausayi ta ke bani, ba zan iya ci gana da ganinta cikin wannan pain

ɗ

in ba.”

Wani sanyi Daddy ya ji a zuciyarsa, in akwai abunda zai iya rantsuwa akai to shine

‘tsaftatacciyar zallar ƙaunar da Mommy take yi wa Yahan

asu!..’

dukda ta kasance y’ar kishiyarta kishiyar da ya fifita nesa ba kusa ba a sama da ita amma sam Mommy bata kishi ko jin takaicin Yahanasu.

Cikin kaiwa iya wuya

Ummi ta ce

‘’Haba Mommy..

Ita kuma Munirat d’in ba marainiyar bace?.

kamar yadda Yahana

su ta ke marainiya haka Munirat itama,

Hasali ma maraicin Munirat ya ma fi na Yahanasu tunda ita uba ta rasa’’.

Cikin tsananin fushi Daddy ya ce

Saddik’a……….

……..

Sai da Yashjub ya yi sallah, ya yi wanka ya d’an huta tukunna ya d’au makulli ya nufi gida

n da Yasir yake.

Shi Yasir a tunaninsa ya b’oyewa kowa ne bai san tun lokacin da ya saka Ƙafa ya bar gidan idanun Yashjub yake a kansa ba..

da farko Abuja ya wuce sai last week tukunna ya dawo shi da tawagar y’an Mata da Abokansa suka

tare a guest house d

’insu d’aya daga cikin Abokanayen nasa su ke cin karen su babu babbaka.

Wallahi,ba daban yana jin tausayin Mommy da halin da take ciki kwana biyu ba

sannan shi kan shi yana jin Yasir d’in a ransa tunda duk lalacewa dai d’an uwansa ne shi

ɗ

in ciki d’aya su

ka fito, to da tuni ya turawa su Yasir y’an Hisbah!!!

Kuma ya cikawa y’an Hisbahn aljihu ya had’asu da manyan sojoji sun nad’e kaff d’in su ta yadda ba uban wanda ya Isa ya amsosu….

..

Yana zuwa bakin gate d’in tun kafin ya gama mik’a hancin motarsa ga gat

e d’in wani mutum k’ak’k’arfa sanye da gajeran wando da vest ya taho daga majalisar chan gefe da gudu yana cewa ‘’kai! Kaii!! Kaii!!’’

Sai da ya zo

Jikin glass d’in motar ta dai-dai inda yake ya d’an buga tukunna Yashjub d’in ya ma lura da shi.

Glass d’i

n motar tasa bullet proof ne sannan hankalinsa ya tafi ga lissafin ta yadda zai shiga gidan saboda ya san Yasir da shegen wayo da taka tsantsan ba zai tab’a zama babu security ba..

Sai da ya gama k’arewa

mutumin kallo tukunna ya zuge glass d’in motar tas

a,ya zuba masa dogayen idanuwansa kawai ba tare da ya ce komai ba.

Cikin girmamawa mutumin ya ce

‘’Oga ai masu gidan basa nan,

sun yi tafiya,sannan ni ban ma sheda ka ba …’’

Dai-dai nan wasu samari guda biyu suka k’araso suka saka mutumin a tsakiya fusk

arsu babu alamar wasa.

Sai da Yashjub ya d’an lumshe idanuwansa ya bud’e tukunna

ya d’an matso mutumin

yana kallon cikin idonsa ya ce

‘’Ni yayan Yassir ne, na san ka san shi..

Yasir wanda ke a cikin wannan gidan yanzu haka’’

ya yi maganar yana nuni da

gidan kafin ya d’aura da cewa ‘’Ban zo ba sai da aka tabbatar min da yana nan yanzu haka.

Ka bud’e min ko in kira maka sojoji da y’an Hisbah,

dan in baka barni na shiga ba hankalina ba zai kwanta ba sai na tabbatar na yi maka d’aurin goro.

Amman in ka barn

i na shiga

zan baka kud’i yanzu ka kama gaban ka dan kar ma su hukuntaka kuma zan hana Yasir nemo ka ya hukuntaka shi kuma Yasir na san zai yi maka tsakani da Abokansa.

Shiruu Mutumin ya yi yana

kallon Yashjub….

Suturar jikinsa, motarsa da kuma yanayins

a kad’ai sun isa su sanya a fahimci tabbas kud’i sun zauna sannan ya jik’u a naira, yana lura da yadda Abokan Yasir d’in suke yi masa fadanci saboda duk ya fi su kud’i to Ina kuma ga yayansa,kar ya je garin gadin y’an tsaki ya janyowa kan sa fad’a da giwa.

.

‘’Ina da abun yi ka tsaida ni’’.

Yashjub ya fad’a yana d’an kallon tsadadden agogon da ke

ɗ

aure a tsintsiyar Hannunsa.

Sai da mutumin ya kalli Mazan dake a gefe da gefen sa su ka yi masa sign da ido tukunna ya kalli Yashjub ya d’an jinjina kansa alamu

n amincewa.

‘’Hmmm’’kawai Yashjub ya ce

yana mai d’an girgiza kansa daga nan ya d’auko bandir biyu na kud’i ya mik’a masa.

Wani kalar murmushi Mutumin ya yi shi da samarin biyu daga nan ya sa Hannu ya amshe ya yi godiya..



A tare su duka ukun suka shiga

gidan ta k’aramar k’ofa suka wangale masa gate ya shige su kuma suka d’auki ghana most go d’insu dake a d’akin mai gadi suka yi gaba abun su..

Gida ne mai kyau flat babba sosai dan compound d’in zai d’auki motoci kamar 15 haka,sai pool da pool house d’i

n shi a ta baya.

Flat din kuma daga gani d’akunan ba zasu wuce 5 ba da maybe 2 two parlours da kitchen haka.

Yana yin parking ba tare da b’ata lokaci ba ya bud’e motar ya d’au wayarsa ya fito ya nufi main door d’in gidan.

Tsaki yayi ganin ta a rufe dan

haka ya d’an danna bell ya koma gefe ya tsaya.

Budurwar da take parlourn zaune tana kallo ce ta mik’e a ranta tana cewa’’i wonder who that could be

(Waye kuma ya zo mana?’’.

Tana zuwa bakin k’ofar ta d’an tsaya ta lek’a…

duk da ta y’ar b’ular k’ofar ta

gan shi hakan bai hanata ganin tsananin kyawaun sa ba, jikinta da hannunta har rawa suke yi haka ta sa Hannu ta bud’e k’ofar cike da zumud’i.

Tana bud’ewa ta d’an saita kanta kana ta d’an karkace tana wani irin shu’umin murmushi.

“Innnalillahi wa inna ila

ihirrajiun”

Ya ambata a ransa a zahiri kuma ya sake tamke fuska yana mai jin kansa yana tsananin sarawa, sanann yana da ya sanin zuwa gidan.

Da kyar ya samu ya iya bangaje ta

ya wuce ciki dan har ta nufo shi tana shirin yin magana.

..

Ransa a mugun b’ac

e haka ya nufi cikin parlourn, ya nemi guri ya zauna yana mamakin yadda take yawo a cikin gidan daga ita sai wannan guntuwa sannan shara sharar bathrobe d’in wadda ko pant d’inta bata gama rufewa ba sannan in dai idanuwansa ba gizo suka yi masa ba to tabba

s ko bra babu a jikinta.

Sam ba ta damu da yadda ya yi mata da farko ba dan ta riga ta gama rikicewa da ganin sa.

Haka nan ta wuce kitchen ta had’o masa juice da cake.

ta fito tana rangwad’a ta zo gaban sa ta ajjiye sanann ta koma gefen sa ta zauna daff

da shi.

Ba tare da ya kalle ta ba ya ce

‘’Ina Yasir??’’

Cikin sake matsowa kusa da shi ta ce

‘’Ooh,he’s a little busy at the moment (akwai aikin da ya ke yi yanzu) sai dai ka d’an jira shi kad’an, but don’t worry I’ll keep

you company(amma kar ka dam

u zan tayaka cinye lokacin)’’.

Ta fad’i haka tana mai d’aura hannunta akan cinyarsa ta fara shafawa tana masa tafiyar tsutsa tana yin sama da kad’an da kad’an.

Tsabar yadda ransa ya b’aci bai ma san ta ya aka yi ya mik’e tsaye ya zare belt d’in jikinsa ba

dan tsintar kan sa kawai

yayi yana kimarta da belt tana ihun ceton rai…

Kafin su Yasir su fito har ya farfasa mata jiki, sai da suka yi da gaske

tukunna Yasir Abokinsa da d’ayar Yarinyar da suka fito tare daga

ɗ

aki

ɗ

aya su uku! suka iya kwatar budurwar

nan a hannun Yashjub wadda zuwa lokacin har ta suma.

Cikin tsananin tashin hankali Yashjub ya ke yi wa Yassir wani irin kallo….daga shi sai boxers haka shima Abokin nasa sai d’ayar Yarinyar ita kuma da towel.

Wata mahaukaciyar shak’a ya kaiwa wuyan Yassi

r cikin hargagi da hargowa ya ce

‘’Dan ubanka gay ka zama?’’

Su kam wannan budurwa da saurayi sun ga tashin hankali, dan a still sai da suka kuma yin da gaske tukunna suka iya kwatar wuyan Yassir daga hannun Yashjub.

Dakyar Yasir ya iya cewa ‘’A’a, Wall

ahi ba abunda kake tunani bane ba, ka tsaya zan yi maka bayani.’’

Da kyar Yashjub ya iya danne zuciyar da take tunzura sa…

da yatsarsa manuniya ya nunawa Yasir k’ofa, kawai……

Duk hauka,iskanci da rashin kunyar Yassir yana tsananin jin tsoron Yashjub a iri

n wannan yanayin dan yadda ya tunzura d’in nan abun ba sauk’i ko last month da yayi irin haka a gida hatta Daddy sai da yayi shakkar sa da kyar da mugun kyar aka ci sa a Yahanasu ta samu ta iya lallab’a sa, amma duk da haka ya fi wata d’aya a kumbure.

Da

kyar yana jin maganar tana harhad’e masa yana ganin dishi-dishi ya sake cewa Yasir

ɗ

in

‘’Za ka wuce ko sai na baka mamaki?’’

A hankali Yassir yana d’an d’ari-d’ari ya ce

‘’Na san motarka babu tint, ka yi hak’uri in shiga in d’auki kayana, dan Allah’’



’In tsaya in jira ka kenan??’’

Yayi masa tanbayar yana sake tunkaro shi da idanuwansa waenda suka yi jajawur abun tsoro.

Da gudu wannan budurwar wadda gaba d’aya ta gama tsorata

ta wuce d’akin ta janyo akwatin Yasir ta fito da shi.

Tana fitowa Yashjub ku

ma ya juya ya fita dan ya fahimci in dai ya sake damƙar Yassir tou tabbas zai iya kai shi lahira, cikin fushi ya nufi gate d’in gidan ya na jin kamar ya fincike zuciyarsa ya jefar tsabar tafarfasa da azabar da take yi..

Da Sauri Yassir ya bud’e akwatin na

sa ya zaro jallabiya ya bi bayan Yashjub da mugun gudu yana zuwa ya bud’e motar dan Yashjub har ya kunna yana shirin bata wuta,

dan ma ya tsaya wangale gate ne shiyasa yaci sa’ar samun shi amma da tuni ya tafi.

Ko rufe motar Yassir bai yi ba

Yashjub ya fig

ee ta suka fice da guduu da kyar ya iya rufe motar ya zura jallabiyar shi dan mutane har sun d’an fara kallon su duk inda suka bi………

Hakanan suka k’arasa gidan da ikon Allah saboda tsananin gudun da Yashjub ya tsula Allah ne kawai ya kaisu gidan lafiya.

T

un kafin su k’arasa main door su ke jiyo hayaniya, dai-dai suna shiga suka ga Daddy ya dakawa Ummi wata mahaukaciyar tsawa sannan ya nufe ta gadon gadan kamar zai rufeta da duka……

..

Cikin fushi bayan ya isa gareta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login