Showing 318001 words to 321000 words out of 407268 words

Chapter 107 - Raina Kama COMPLETE

kawai bayada rai sai mahaifan Badi, dakuma wasu daga cikinsu da sukabar

duniya, Dan haka ina rok'on wannan kotu data nemo dukkan Wanda Na ambata domin jin ta bakinsa”.

Alk'ali ai yama kasa magana, sai kad'a kai kawai yake mamaki da al'ajabi Na cinsa, yayinda kotu tayi tsit kowa yana k'ullawa da kwancewa da tausayin

Galadima, irinsu Alhaji Halluru kam ai cikine ya d'uri ruwa, sunsan dai tasu tagama k'arewa kam, Dan yau ranar bankad'a Ce da walle-walle.

Alk'ali yad'anyi rubuce-rubucensa sannan ya buk'aci ganin Badi da Alhaji Rabilu, Galadima kuma yaje ya zauna.

Alhaji Rabilu da Badi sun bayyana a gaban kotu, hakan ya kuma hargitsa hanjin cikin Waziri, yana mamakin dama Badi bai mutuba? Amma su hak'ilu sukazo sukace ya mutu a wancan lokacin, dan agabansu mai besfa ya kad'eshi, innalillahi ya shiga ambata

a zuciyarsa, sai zufa ke jik'eshi, sauk'insa ma akwai malun-malun da rawani a jikinsa, Abba Hayatudden kallonsa kawai yake da tsantsar tsana da mamakinsa.

Duk yanda Badi da Alhaji Rabilu sukaima Galadima bayani haka suka maimaita a gaban kotu, wasu ha

rda hawayen tausayinsu suke matsewa, Alk'ali yace, a kawo Alhaji Auwal Fharuk Dan Badi yaga idan shine yabama camera.

An kawo Abba, Wanda Alhmdllh jikinsa yayi sauk'i sosai, saidai abinda ba'a rasaba Na k'arfi, kallo d'aya Badi yayma Abba ya ganeshi

Dan bai canja masaba sai canjin girma irinnan shekaru, hakama Abba ya gane Badi sarai Dan shima d'in bai canja masanba, aiko suka rungume juna kowa yana hawaye, Abba yana fad'in “Bawan ALLAH Dama baka mutuba a waccan ranar?”.

Shima Badi cikin kuka y

ace, “ban mutuba, sai daga baya ne Na farfad'o a wajen”.

Alk'ali ya ankarar dasu cewa a kotu suke, kotu kuma Na buk'ar jin bayani daga bakin Abba, ta Yaya Camera ta dawo hannunsa?.

Abba ya dai-daita tsayuwarsa sannan ya gabatar da kansa ga

kotu, ya d'ora da fad'in “shekaru 22 kenan da suka shud'e wannan camera take a hannuna ranka ya dad'e, nakuma sametane ta hanyar kad'e wannan bawan ALLAH danayi da abin hawana a wancan lokacin, saboda ya shigo hanya yana matsanancin gudun dabansan mafariba

sai yanzu danaji a ya fad'a a gaban kotu. bayan na bigeshi numfashinsa Na Nuna alamar bankwana da gangar jikinsa ya d'auki wannan camera yabani acikin akwati da sunan amana, yakuma ambatamin sunan wad'anda zanba kamar yanda yafad'a, daganan numfashinsa ya

tsaya cak da aiki, ina cikin k'ok'arin taimakonsa saiga wasu mutane da gudu da makamai sun dosoni, tsoro naji, Dan inada tabbacin shima sune suka biyoshi, saboda son isar da amanar daya bani inaji ina gani badan nasoba Na tsallakesa Na gudu, Dan nasandai

zasu iya kwatar abinda yabani d'in. tunda camera d'in nan ta dawo hannuna ban sake barci mai dad'iba, kullum burina da tunanina tayaya zan Isar da amanarta Na huta, tsawon shekaru ban ta6a fuskantar wani k'alubale akanta ba, Dan ko iyalina babu Wanda yasan

da zamanta a hannuna, matata tasha tambayata idan taganni cikin damuwa amma banta6a fad'a mataba, kwatsam cikin laluben Wanda zan bamawa sai Marigayi Alhaji Abdul-hakeem Uba tsohon Governor d'inmu ya fad'omin, Dan ganin yana auren d'iyar tsohon Sarki wadd

a tana d'aya daga cikin wad'anda akace nabamawa, to lallai anan Alhaji shehu SD yasan Camera Na hannuna, Dan tabbas yaji zancen da mukayi da Alhaji Abdul-hakeem d'in ta hanyar la6ewa, aranar da mukayi zan bama Alhaji Abdul-hakeem camera ya damk'ata ga mata

rsa sai aka samu akasi wani aiki ya tasomin Na manta ban fito da camera ba, amma mun had'u da shi marigayi Alhaji Abdul-hakeem Na bashi hak'uri da sanar masa uzirina, shikuma SD a tunaninsu nabama Alhaji Abdul-Hakeem wannan camera, shine suka hari rayuwars

a da nufin kar6a kafin ya kaima matarsa, inaga daga baya da suka fahimci babu Camera d'in a hannunsa shine suka juyo kaina. Sunta matsama rayuwata da barazana iri-iri, kiran waya da sauransu, duk number da suka kirani da ita gobe bada ita zasu kirani ba, h

akkane ya sakani ware sim card guda kawai dansu, babu Wanda ya sanni dashi, sai matata Dana saka number cikin wayarta batare da itama tasan hakanba, nayi hakanne saboda watarana koda ALLAH yabasu nasarar kasheni d'in. A lokacin da akaima yarana 6atanci da

Galadima lallai hankalina ya tashi matuk'a, amma daga baya danayi nazari saina gano maybe su SD ne suka aikata hakan domin 6atamin suna, hukuncin ALLAH kuma saigashi mai martaba Sarki jalaludden da mai martaba Sarki Abdul-fatah sunzo nemawa d'ansu Galadima

auren yarinyata da abin yafaru akanta, dukda a 6adda kama sukazomin ni sarai Na ganesu, amma ko y'an uwana ban sanarmawaba, abinda yabani k'arfin gwiwar aurar musu da yarinyata shine Isar da amanar hannuna cikin sauk'i, saikuma aminin mahaifina Baba mai k

anwa yace nabasu, Dan shine kawai yasan da zaman Camera a hannuna, shima bani Na sanar masaba, bankuma San a ina yajiba. A randa za'akai y'ata gidan mijinta a ranar Na saka wannan camera da takarda cikin wani kwali Na sakashi a kayanta batare da tasaniba,

bansaniba kota gani? Dan cikin gifts d'inta data samu a hannun abokan mijinta ranar dinner d'in auranta Na sakashi, nabama d'an uwantane Abdul-Hameed babban d'ana yabata batare da shima ya san minene a ciki ba. Hikimata anan idan tagani tabama mijinta bata

re da kace Na ceba. SD bashikad'ai ke bibiyar rayuwata ba, Dan akwai masu sakashi yazomin da farashin kud'i masu tsoka akan camera d'in amma nayi kunnen uwar shegu dasu, hakanne yasakasu k'ok'arin salwantar da rayuwata wai tunda Na hanasu camera, nasan sun

ajin tsorone saboda Na kusantu da Galadima a lokacin, zan kuma iya bashi camera d'in, saidai abinda basu ma saniba tuni Camera d'in tabar hannuna. Alhaji Halluru abokinane Dan school mate d'inane, ada babu wata alak'a mai k'arfin tsakanina dashi, amma daga

baya sai yayta Jana a jikinsa, ban fahimci manufarsaba dagashi har Alhaji Mamman, Dan da zuciya d'aya ni nake zaune dasu. Sai wannan karon da suka tabbatarmin da zulwa jahainin fuskarsu, sannan suka tursasa y'ay'ana biyu Dana d'auka nabama y'ay'ana Alhaj

i Halluru aure saboda yarda wai su d'akko musu camera a d'akina kosu kashesu dani dakuma iyayensu mata, sun razanasu da cewar sun dasa bomb a gidana, agabana duk suka sanar musu a waya. Abinda yasa ban damuba nasan k'arya suke, sannan Camera d'inma bata gi

dan, duk k'ok'arin lalatama Galadima sirrika da sukayi agabana sukayishi, amma ALLAH baibasu nasaraba, jin asirinsu zai Toni ta hanyar Garkuwa da y'ay'ansu da Galadima yayi shine suka shak'amin abinda ban saniba, daganan ban kuma Sanin ina kaina yakeba sai

a asibiti yamai shari'a”.

Wannan bayanima Na Abba ya girgiza zukata sosai. Dan har alk'ali kasa motsawa yayi, saidai yaja kusan mintuna biyu sannan ya sauke ajiyar zuciya mai k'arfi. Ya buk'aci a kawo masa camera nanda awa 2 kacal. Anbar lokacin a m

atsayin hutun kotu.

Babu Wanda yaso matsawa konan da can, kowa burinsa dai camera ta iso aga mita k'unsa.



Galadima ya kira Munaya, yace ta shirya ga Sarkin motanan zasuzo da Nuren su kaita masarauta ta duba cikin gifts d'inta Na

Aure data samu Abba yace camera Na ciki.

Dayake a labarai an nuna takuma gani, sai kuka dama takeyi da mamakin miyasama bata duba gifts d'in auren nataba tun wancan lokacin? Koda yake bata dad'eba a Nigeria suka wuce India, itakam a dukkan zaman

da suka d'an tayi idan sun dawo bata sake bi takan gifts d'inba, to kawai tace masa ya yanke wayar, Dan yanzu babban burinsa kawai a tabbatar camera d'in tana wajen nata.

Tana gama shiryawa sarkin mota yazo da Nuren dakuma police, bata d'auka yaro k

o d'ayaba tafito suka tafi masarauta.



Sun iske masarautar tsit, tamkar anyi sharar mutane, kowa Na sashensa abinda ke faruwa yama zukatansu murus, hannu kawai take iya d'agama hadiman sashen nasu dake gaisheta, basu damuba, dansunsan tana

cikin wani yanayine.

Sashen nasu yayi y'ar k'ura, saboda kwana uku babu kowa a ciki, Munaya kanta tsaye bedroom d'inta ta shige kawai, ta bud'e wardrobe nata tashiga fiddo gifts d'in aurenta data tara gefe, tareda Na haihuwar su Abdurraheem. d'ai-d'a

i taita farkesu, idan taga bashi bane ko bud'awa batayi take jefawa saman gado, tasha wahala matuk'a kafin ta gano akwatin da idonta ya ta6a tozali dashi a d'akin Abba itada Munubiya, rungume akwatin tayi ta fashe da kuka maiban tausayi, ana haka kiran Gal

adima ya shigo wayarta, share hawayenta tayi ta d'aga.

A d'arare yace, “kin hanshi?”.

Cikin dariya da kuka ta amsa masa da eh ta gansa, shima murmusawa yayi, yace, “maza Ku tahoto, mintuna 46 suka rage a lokacin da alk'ali ya bada, sonake kawa

i a kammala shari'arnan a yau”.

Munaya ta amsa da “to gamunan.................



🏻

*_“insha ALLAH gobe idan ALLAH ya kaimu, koma mike cikin camera d'in dai zamu gani, nima Na k'osa nagani a wuce wajen

😬🤦🏻

‍♀

”_*.

*_ALLAH ya gafartam

a iyayenmu_*

😭👏🏻

a zuwa, saidai a dad'e ba'a zoba

😏🐢

.

*_ALLAH ya gafartama mahaifanmu_*

😭👏🏻

[8/3, 3:35 PM] +234 810 341 4063: *_Typing

📲

_*

*_

💡

HASKE WRITERS ASSO...._*

*_



RAINA KAMA...!!



_*

_(Kaga gayya)_

*_Bilyn Abdull ce

🤙🏻

_*

*_BOOK 3_*

👉🏻

1



6



.................Jin tsayuwar motoci ya saka Ameer lek'awa ta window, juyowa yay ya kalli Galadima, “Ranka ya dad'e y'an sandane”.

Baki Galadima ya ta6e, ya share tamkarma baijiba,

yana cigaba da bud'e wasu file daya fiddo a briefcase. Saida yaja kusan 1 minute sannan ya mik'ama Nuren dake kusa dashi wasu files, ya zaro takarda kuma yay rubutun dabai Gaza layi biyarba ya mik'ama Ameer da wata k'amar waya a kwali.

Kar6a Ameer yaz

o yayi, batareda Galadima yayi magana ba ya nuna masa window.

Muftahu daya fahimta yace, “Ameer ka jefa musu takardan da wayan”.

Ameer ya amsa da to, yanufi window d'in, cikin dabara ya jefa kwalin da takardar.

Wani d'ansanda dayaga tahowa

rsu yay saurin zuwa kusada window d'in, ALLAH yabashi nasarar cafewa.

D.p.o dake tsaye tare da sauran police ana shawarar yanda za'a shiga gidan ya kaimawa.

Yay salute nasu kafin ya Isar da sak'on dukda yasan duk sunga daga ina kayan suka fito

, d.p.o ya gyara tsayuwarsa yana fad'in “bud'e kwalin mu gani”.

Bud'ewa yayi, yaciro wayar yana cewa, “wayace sir”.

Cikin ta6e baki d.p.o ya jinjina kansa, yace, “takardar fa?”.

Itama bud'ewa yayi, yafara karanto abinda ke jiki, wanda Gal

adima ya rubuta da harshen nasara.

*_Kamar yanda suka fad'a Muhammad Sameer ba d'an ta'adda baneba, inhar zakubi yanda nace lallai yarannan zasu fita lafiya, idan kuma har kuka nuna k'arfin iko, zanta jeho muku gawarsu d'aya bayan d'aya ta saman b

enenan, ga wayanan, idan kuna buk'atar magana koni ina buk'ata ta wadatar, Dan kar wani yay gigin cewa zai shigo. Idan nayi ba dai-daiba a gafarceni

👏🏻

_*

Daga d.p.o har jama'ar dake kusa dashi duk ajiyar zuciya suka sauke, ya jinjina kai yana cije

bakin mamaki, cikin sauke numfashi yace, “saimu bishi yanda yakeso mugani, idan munga zai mana wasa da hankali sai a d'auki mataki, C.. babangida a zagaye gidan”.

“Ok sir”. C babangida ya amsa yana salute nashi.

Dandanan suka warware wani blue

d'in zare suka zagaye gidan dashi, mutanen anguwa dasuka fara fahimta harsun fara taruwa kallo, harma wad'anda sukaji a labaran sunfara gangarowa anguwar damin ganema idonsu.

Duk abinda ke faruwa Galadima Na zaune k'afa d'aya kan d'aya yana kallo

ta CCTV, sai famar buga pen yake saman la66ansa a hankali, suma dai su Muftahu dasu Harun suna kallon komai.

Kujera aka kawoma d.p.o ya zauna, dayake da sauran safiya babu maganar neman runfa ko umbrella.

Wayar d.p.o ya kar6a da kansa, da

n case ne Na manya IG da kansa yakirashi, yakuma abbatar masa shima yana nan zuwa.

Shiru d.p.o yay yana bincikar wayar da Galadima ya aiko da ita, babu komai a cikinta sai Number guda d'aya, baice komaiba yaciro wayarsa yayma IG bayanin komai.

Daga can IG yafara fad'a, wai tayaya zasu saurareshi, bayan d'an ta addane, duk Wanda zai iya kidnapping aiko d'an ta'addane, kawai su nuna masa k'arfin iko wajen ku6tar da yaran.

Shidai d.p.o ya kwantar da murya cikin sigar lallashi yace,

“Nidai Sir da ace za'abi ta tawa daminbishi a hankali, maybe akwai sak'on da yakeson isarwa, karfa mu manta shima d'an manyan mutanene, shikansa akwai sarauta mai daraja a kansa, ai mai martaba bazai ta6a jin dad'iba shima, tunda ya buk'aci dama mu bashi,

idan munga batai manaba saimu d'auki mataki”.

IG yace, “shikenan, Ku kirashi muji miyake buk'ata, nima a had'a dukkan maganar da zakuyi dani naji komai, dukda munama hanyar isowa yanzunan”.

Cikeda farin ciki d.p.o yace, “ok sir”.



Duk kayan aikin dasuke buk'ata suma sun tanadesu, yayinda y'an jarida suka fara isowa wajen.

Shima C.P ma saigashi ya iso, duk suka k'ame wajen salute nashi har d.p.o.

Ya amsa musu cikin jinjina kai, sannan ya buk'aci jin mi'ake ciki?.



Bayani d.p.o d'in yamasa, shima ya gamsu da shawarar abi komai a sannu d'in.

Galadima ya murmusa yana lumshe idanunsa yana sauke ajiyar zuciya. Saboda dukkan wayar da d.p.o yay da IG a kunensa ne.

Sudai su Nuren sunyi jugum-jugum Dan son

ganin minene shirin Galadima waine?, da har yaza6i fiddo kansa wa duniya a matsayin mai laifi?.



Kiran da C.P yayi da kansane ya shigo wayar Galadima bud'e ido yayi yana kallon su ta CCTV, sannan yay picking call d'in, shiru yay yak'i maga

na, saida C.P ya fara masa sallama sannan ya amsa.

C.P yace, “Ranka ya dad'e barka da safiya”.

Baki Galadima ya ta6e, ya amsa da “Barka dai”.

Gyara zama C.P yay yana kallon saman gidan, duk su Galadima suna ganinsa, yace, “Ranka ya da

d'e muna saurarenka, ka fad'i buk'atar taka, inhar batafi k'arfinmu ba za'a biya maka insha ALLAH ”.

“Humm” Galadima ya fad'a yana mik'ewa tsaye, duka hannunsa Na zube cikin aljihu, dayake yana amsa call d'in ne da abin da ke kunnen sa.

Falon

ya shiga zagayewa cikin takunnan nasa na k'asaita da izza, saikace namijin tantabara yana gwada gasar tafiya a gaban matarsa

😜🤣

.

Suko sai binsa da kallo suke tamkar wani magiji.

A hankali yace, “Buk'atata ta farko shine iyayen yarannan s

u fiddo Alhaji Auwal fharuk, idan sunyi haka lallai zakuji manufata kai tsaye batare dana ja muku raiba, Dan nima ina buk'atar hutu”.

C.P ya shiga jinjina kansa kawai yana sauraren Galadima da dukkan sauran police d'in dasuma sukeda alhakin jin k

omai ta hanyar abinda suka saka a kunne.

Bai k'ara komaiba ya yanke wayar, Yakoma mazauninsa ya zauna yana kallon yaran dasuma dukshi suke kallo, d'an murmusawa yayi yana d'aukar ruwan daya ajiye, saida ya bud'e murfin ya mik'ama Wanda yake kusa dash

i.

Shima yay murmushi yana girgiza kai da fad'in “A'a ranka ya dad'e, Na gode”.

Galadima ya mik'ama sauran suma, amma duk sai sukace A'a, murmushi yayi yasaka kayansa a Baki yasha, yana kallon Harun daya zuba masa ido, rabi yasha ya mik'ama H

arun sauran, amma saiya kauda kansa gefe, Galadima ya ta6e baki yana d'aga kafad'a alamar kaika Sani.

Sauran ruwan ya ajiye yana kuma kallon yaran, da hannu yakuma yima Na farko alamar yaya sunansa?.

Bai fahimtaba Dan haka ya kalli Na kusa da

shi, sannan yakuma kallon Galadima yana nuna kansa da fad'in “Sunana wai?”.

Galadima ya jinjina kai yana lumshe idanu.

“Sunana Ahmad Bana bb gana".

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login