Showing 348001 words to 351000 words out of 407268 words

Chapter 117 - Raina Kama COMPLETE



wani aiki, nakai watanni 6 inason ganinsa akan matsalar Abie amma ban samu damaba, saboda matuk'ar Busy dayake, sai a daren jiya nasamu magana dashi, bakaji farin cikin dana samu kaina a cikiba, dan mun tattauna sosai akan matsalar Abie, yanzu haka yabamu

date d'in dazamu sameshi can Kashmir a asibitinsa”.

Alhmdllh Galadima yaketa ambata a zuciyarsa tunda Dr Ajay yafara bayaninsa, cikeda farin ciki yace, “Doctor lallai nayi farin ciki da wannan albiahir naka sosai, ka wuce matsayin likita kawai a ga

remu saidai d'an uwa”.

Murmushi Dr Ajay yayi, suka rungume juna shida Galadima kowa yanajin dad'i a ransa.

Galadima ya fito d'auke da wannan farin ciki sukaci karo da Akash a hanya.

Akash yace daddyn Triplets kenan, kwana

biyu ka 6uya?.

Hannu Galadima ya bashi yana fad'ad'a murmushinsa, yace, “Sorry my friend ka ganni dai yawo kamar ruwan sama, idan bani anan aganni acan, ya aikin?”.

“Gashi munata fama, ya naka?”.

Galadima yace, “Alhmdllh”.

“Wai

sai yaushe zaka dawo mana da Mummyn triplets ne? ga bikina yanata matsowa, bafa zan muku alfarma ba”.

Murmushi Galadima yayi, ya dafa kafad'arsa yana fad'in “kwantar da hankalinka, ai babu yanda za'ai bikinka babu mu a wajen”.

Aksha ya

ce, “Ato kun wanke kanku, daga ina ka fito haka cikin farin ciki?”.

Bayanin komai Galadima yayma Akash, dan baya 6oye masa komai gameda ciwon Abie.

Shima ya nuna tsantsar farin cikinsa kuwa, kafin suyi sallama kowa ya nufi inda zaije.

W

aya yaciro yana lalubo number Munaya................



🏻

*_Zan iya cewa yanzu zaku dinga rashin ganina, wlhy ammana haihuwar da tilas saina kasance a wajen a kullum, amma inhar Na samu time zaku dinga ganin posting, dan yauma banyi tunanin zanyib

a, amma saigashi ALLAH yabani iko bayan dawowata daga asibiti, nima kaina Na k'agara nagama Na huta kuma Ku huta

🤦🏻

‍♀

, I love you all

😘😘😘😘



🤝🏻

_*

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*

😭👏🏻

[8/15, 6:54 PM] 0mmer Farouk: *_Typing

📲

_*

*_

💡

HASKE WRITERS ASSO...._*

*_



RAINA KAMA...!!



_*

_(Kaga gayya)_

*_Bilyn Abdull ce

🤙🏻

_*

_____________________

*_ASSALAMU ALAIKUM_*

_Tabbas da nayi niyyar ajiye RAINA KAMA saboda sakkayar da w

asunku sukaimin, bazanyi ALLAH ya isa ga Wanda yafara fidda hotuna da nufin niceba, amma lallai koda ace aunty Ruk'ayya ce ko Ummi da muka fito ciki d'aya Na barsu da ALLAH, kai koda ace nina haifeta, ai kowacece ita ba dabba bace, kusan abinda ya dace da

Wanda bai daceba, ba hotona nazo talla a social media ba,

😭

kukuma masu gani da yad'awa jikinku Na rawa wlhy kushirya fidda hak'ina dake kanku a kotinda bakuda abin biyana sai ayyukanku, kunyi domin Ku tozartani saidai baku rageni da komaiba sai kanku, wa

nnan abun yay matuk'ar 6atan rai fiye da zatonku, har yanzu idan Na tura raina Na 6aci, wlhy bazan zubar da hawayena a banzaba akan wannan abun, sai ALLAH ya fiddamin hak'ina akan kowacece ta fara turawa da masu cigaba da yad'awa

😭

, Ku miyasa Baku tura bak

u hotunanba? Da kunga Abu jikinku narawa kuhau yad'awa, saikace social media gidankune, ai cikinku babu Wanda baya banbance dai-dai da akasinsa, saboda kawai ina son nayi suna a gareku saina turo hotona nace kuyad'a, kwana nawama bana online d'in, inacan d

a damuwar son Na k'arasa muku abinda Na fara Ku kunan kuna cutar dani

😭🤦🏻

‍♀

._

*Kosuwaye suje suda ALLAH, ALLAH kuma zai tozartasu suma fiye da Wanda suka aikata a gareni, Dan Na tabbata wlhy su ba masoyana bane, duk masoyina bazai aikata haka a

gareniba,

😭

kai ALLAH dai ya gaggauta sakamin kawai, bikin sallar da kowanne bawan ALLAH yake tsintar kansa a farinciki ammani kuka 6ata nawa da 6acin ran da bansan mafariba

😭

.*

__________________________

*_BOOK 3_*

👉🏻

2



2



.................Bata

d'agaba dan haka ya maida wayarsa a aljihu yanufi d'akin da Abie yake jinya.

★★★★★★★★★

Zazza6in da innarmu ta tashi dashi yasaka mama Rabi'a zuwa dubata da iyalanta duka, kasantuwarmu waje d'aya a yau saiya bamu damar tuntu6ar sauran y'an

uwanmu mizai hana mu tunkari iyayenmu da batin sanin asalinsu?.

Damacan ya Marwan ne matsalarmu, danshi muke shakka, amma Alhmdllh Munubiya ta lalla6a manashi ya amince. Hasalima shine ya tunkaresu kai tsaye da maganar.

Da farko shiru duk suk

ayi basu amsashiba.

Saida ya Fadeel yace, “please iyayanmu Ku taimakemu Ku fiddamu daga wannan duhun, muma cike muke da shauk'in son sanin ina danginku suke, maybe hakan zai rage mana rad'ad'i da kewarsu, amma kuyi hak'uri idan mun Shiga hurumin da

ba namuba”.



Innarmu ta sauke ajiyar zuya daga kwancen datake, ta kalli Mama Rabi'a datai k'asa dakai idonta cike da kwalla, tashi innarmu tayi zaune tana kallonmu d'aya bayan d'aya, ganin duk mun zuba musu idanu saita murmusa, cikin dakiya tace,

“Nasan wannan tambayar ta dad'e tana cinku tsawon shekaru, dukda nuna mana da kuke Na buk'atar sanin su wanene mu amma muna sharewa, ina mai muku albishir da lallai wannan karon zaku samu dukkan amsoshinku daga garemu, amma ta hanya guda d'aya tak”.



Kallon juna muka shigayi, kowa yana mamakin wace hanyace wannan?.

Murmushi innarmu ta sakeyi, tana fad'in “karku zurfafa tunani, hanyar dai bata wuce shirya tafiya gaba d'ayanmu domin waiwayar ahalinmu ba, duk da kuwa su basa buk'atarmu a cikins

u, saboda kasantuwarmu jinsin da basa baraba dashi a tsarinsu, jinsin da basu shirya kar6aba saboda wani al'adar banza mara amfani da amfanarwa, sun mata dukkan saurinsu sai sunjira ALLAH. Munaya yanzu kece kad'ai matsalarmu, saboda bamusan ko mijinki zai

aminceba, amma ki tambayesa, inhar ya amince to lallai k'arshen satin sama zamu tafi”.

Gaba d'ayanmu farincikine ya baibayemu, kowa fuskarsa a washe, ya Marwan sarkin miskilanci ne kawai yay d'an murmushi, amma fuskarsa shima ta nuna alamar jin d

ad'in hakan.

Farin cikin damuke ciki yasani bamma San Galadima ya kiraniba, saida Na d'auki wayar da nufin kiransa na fad'a masan zancen tafiyarmu ne sannan naga kiran, idanu Na waro waje, Na mik'e ina barin cikinsu Ayusher danma karsu isheni da

hayaniya.

Harta tsinke bai d'agaminba, nakuma kira nanma baiyi picking ba, sainaji duk babu dad'i, kardai fushi yayi?, k'ok'arin rubuta masa massege Na fara saiga kiransa ya shigo.

'Dagawa nayi da sauke ajiyar zuciya, Galadima dake zaune b

akin gado sanye da bathrobe Dan yana wanka taita kira. Murmushi yayi mai sauti har tana jiyoshi, cikin sanyin Murya yace, “wannan ajiyar zuciyarfa?”.

Tsayuwa Munaya ta gyara, da y'ar shagwa6a tace, “Ba kaineba”.

“Tofa, ni jikan Abubakar

da Abdul-fatah, ni minayi kuma?”.

“Shine naketa kira kak'i d'agawa”.

“O, Na ramane nima. d'azun ban kiraki ba? Amma baki d'agaba, bakuma ki biyoniba, awa nawa kenan?”.

“Kayi hak'uri My king, wlhy ban kulaba sai yanzu, hirace ta d'au

ke hankalina, Su Ayusher duk sunzo duba Innarmu”.

“Humm, toya jikin inna?”.

“Alhmdllh ai tama warware, yasu Momma da jikin Abie”.

“Everything Alhmddllh, ina maganarmu ta tsaya?”.

Dafe kai Munaya tayi, ta zauna saman katif

ar su Aryaan, tawani narke murya da shagwa6eta, “Haba yalla6ai miyasa kakeda son maida zance bayane? Ba mungama da wannaba?”.

'Dan kausasa muryarsa yayi. Yace, “Munaaya! Nagaji da wannan yawo da hankalin, shin wai k kam bakida tausayine? Nifa ba d

utse bane, ko har yanzu baki yafemin kuskurena bane ba?”.

“Kayi hak'uri to, dama yanzu wata mafita Na samo, dan wlhy kunya nakeji, bazan iya tunkarar inna nace mata zan komo ba”.

Kamar bazaiyi maganaba, harma Munaya ta fidda tsammani saikum

a taji muryarsa a sanyaye yace, “Miye mafitar?”.

Kwanciya munaya ta gyara jin tafara samo Kansa, Dan burinta kawai ya amince suyi tafiyar, sauran zance saita dawo sayi.

tace, “Yauwa Autan Momma bud'e kunnenka da k'yau kasha labari”.



Murmusawa yay kawai yana zamewa ya kwanta shima, wayonta Na birgeshi, inhar zai 6ata rai akan Abu tasan hanyar da zatabi ta bashi nutsuwa. yace, “ina jinki”.

A nutse tabashi labarin zuwansu Niger domin ganin danginsu inna, a salon data fahimtar

da shid'in lallai ya fahimta, saidai amsa zai barta zuwane yad'anso yin gardama, saida ta kalallameshi da dad'in baki da magiya sannan ya amince akan shima zai biyo bayansu, daga nan zai d'akkota su taho. Kai tsaye tace ta amince. Yayi farin cikin da hakan

, yabata labarin shima yanda sukayi da Dr Ajay.

Yanda ta nuna tsantsar farin cikinta da murna akan lamarinne Yakuma saka masa nutsuwa akanta, soyayyar da takema mahaifansa da dukkan ahalinsa shine makamin farko data fara amfani dashi wajen bige dukk

an yak'ininsa akan shirin Auren contract, takuma k'ara kima da daraja a idonsa.

Daganan suka cigaba da hirarsu ta soyayya anutse, abin akwai birgewa. Yace saita sakashi yayi barci sannan zata kashe, wannan ne punishment d'inta.

Babu yanda ta i

ya dole ta bishi yanda yakeso, har saida taji tsitt alamar yay barcin da gaske sannan ta kashe tana dariyar wannan shagwa6a ta Galadima, a yanzu Idan yamata wani abun takanyi mamakin dama haka yake?.

Aiko data koma d'aki tasha tsiya wajensu Feen

a, sai banza tamusu sukayi mai isarsu.

************************

Kamar yanda shirye-shiryen tafiyarsu Munaya Niger ta kankama haka shirin kai Abie Kashmir wajen Doctor Erfan Fahad Sajaad ta kankama suma.

Y'an gidansu Munaya dai an

samu abinyi, sai gulmace-gulmace da gugar zana sukeyi akan wannan tafiya, harda masu fad'in talauci da wahalane ya koro su inna, yanzu anga ansamu arzik'i za'a koma k'auye amusu iyayi da farfaganda.

Duk abinda ke faruwa Inna naji kuma tana saurare,

amma baiwar ALLAH sai dai tayi Murmushi kawai, takuma hana su Munaya cewa komai, har Innaro saida ta yaddama Inna habaici akan wannan tafiya. Su Maman ya Hameed akaita dariyar gatsatsa.



Wannan abin da inna taga sunayi ya sakata rok'on Abba akan t

afiyarnan yakamata ace Innaro ma aje da ita.

Abba bai kawo komai a ransa ba ya amince, harma ya nuna mata farin cikinsa, yakuma shiga yima Innaro shiri itama

__________________________

Dukkan shirin da ake buk'ata nakai Abie Kashmir

ya mammala, Galadima da doctor Ajay da Dr Akash ne kawai zasuje, Anbar su Momma gida su huta, duk da taso binsu amma Galadima ya lalla6a ta dai ta zauna.

Ta jirgi suka tafi, dukda bawani insane mai yawaba, to amma jikin Abie bayason yawan matsala

da takurar zafi. Suna Isa Ambulance tazo ta d'aukesu.

Asibitin bawani k'ato baneba, hasalima Wanda Abba ke ciki a new Delhi yafi wannan girma da k'ayatuwa, dukda shima wannan d'in ya had'u bakin gwargwado, sunkai 3hours zaune basu sami ganin d

octor Erfan ba, dukda kuwa shine yabasu wannan date d'in domin ganinsa, andai shiga da Abie wani d'aki tun zuwansu.

Ran Galadima ya fara 6aci, abinka da ba sabawa yay da hakan ba, zai fara k'orafi saiga doctor Erfan Fahad ya fito daga wani d'aki, da

alama ma wani aikin yayi a ciki, su Galadima basuga fuskarsa ba harya shige Inda suke tunanin Office d'insane.

Wajen 30minute's da shigarsa sannan aka basu izinin shiga.

Sai wani cika da batsewa Galadima yakeyi Na haushi, shi dai Dr Ajay yanat

a lallashinsa akan inhar zasu sami biyan buk'ata ai hakan ba komai baneba.

K'ala dai Galadima bai ceba.

Doctor Erfan Fahad Sajaad, matashin likita dabazai wuce sa'ar Galadima ba, k'yak'yk'yawan ba indiye mai tashe da lokacinsa, Wanda duniyace

ke amfanuwa da fik'irarsa bawai India ko yankin Kashmir kawaiba.

Kallo d'aya Galadima yamasa ya d'auke kansa, Dr Erfan ya ajiye file d'in Abie dayake dubawa yana fad'in “Kuyi hak'uri dani Brother's, aikine babba ya dinkareni daga cika alk'awarin Dan

a muku, gashi kuma Na gaggawa”.

Galadima ya juyo da nufin juye masa abinda ke ransa sai kawai doctor Erfan Fahad yad'anyi baya cikin mamaki. Yace, “Waishi wama nake gani a gabana kamar Muhammad Sameer Saifuddin?”.

Galadima da mamaki ya kashe

shi yace, “lallai shine, amma a ina kaimin wannan sanin haka?”.

Wata dariya Dr Erfan Fahad yayi, yad'an bigi tebir d'in gabansa yana fad'in “Duniya labari, Muhammad Sameer Saifuddin kenan! Nikam kaga koda saida muka tsufa Na ganka saina ganeka wlhy,

shin zaka iya tuna wani Wanda kukai karatun Addini shekaru 19 da suka shige a wajen Sheaik Mu'azzam Abdul'aziz khan?”.

Shiru Galadima yay ya lula duniyar tunani, Dan a yanzu yad'an fara d'ago fuskar Dr Erfan Fahad d'in.

Dr Erfan Fahad ya d'an

daki kafad'arsa cikin dariya, “My friend mu ajiye wannan chapter d'in, tana buk'atar nata time d'in, amma lallai nayi farincikin ganinka bayan tsawon shekaru Dana d'auka wajen nemanka, kardai kacemin har yanzu Abie yana jinya?”.

Ajiyar Zuciya Galad

ima ya sauke yana jinjina kai, danshikam tunanine dank'are a ransa gameda Dr Erfan Fahad Sajaad d'in.

Dr Erfan Fahad yace, “Abie ne mutum Na farko daya fara fad'omin a rai bayan zamana cikakken likita kwararre ta fannin irin matsalarsa, sai dai duk

tunanina shi yasamu lafiya, Ashe yanata ibadar ALLAH har yanzu, insha ALLAH matsalarsa tazo k'arshe kuwa, Doctor Ajay nadawo gareka, ina buk'atar k'arin bayani gameda magunguna da Abie yakesha?”.

Dalla-dalla Dr Ajay ya shiga ma Dr Erfan Fahad bayani,

Galadima dai Na saurarensu, dukda Rabin hankalinsa naga son tunano wanene Dr Erfan Fahad?.

Bayan Dr Erfan Fahad yagama sauraren Dr Ajay, shima yaymusu bayani dalla-dalla akan alurai daza'a dungama Abie duk bayan wasu awanni. Allurarce zata zama m

akarin wannan ruwan guba daya gauraye dukkan jijiyoyinsa, ahankali zasu fara motsawa daga dakatar dasu aikin da akayi da wancan poison d'in, daga nan ga66an jikinsa saisu fara aiki insha ALLAH.

Dukda nauyin tsadar wannan Allurai haka Galadima ya amsa,

yasan tattalin arzik'insa ba k'aramar girgiza zaiyiba, Dan harma saiya had'a da saida wasu kadarori, bashida burin dayafi yaga Abie yasamu lafiya, koda ace dukkan dukiyarsa zata salwanta bazaiyi bak'in cikiba, fatanshima ALLAH yabashi ikon had'a dukkan ku

d'ad'en da ake buk'atar batareda ya dogara da taimakon kowaba.

Masauki Na musamman Dr Erfan Fahad yabama su Galadima, dukda Akash yashiga gari ya sama musu, amma Dr Erfan Fahad yace Sam bazai yuwuba, a gidansa zasu sauka tilas.

Bayan su

n sami nutsuwa, Galadima yayi wanka ya kira Momma yamata bayani akan komai, hankalinta ya tashi kwarai da gaske, Dan kud'ine masu yawa, wad'anda tana k'yautata zaton dawuya ace Galadima yanadasu gaba d'aya.

Amma jarumin naku saiya shiga kwantar mata

da hankali akan Neman nasara da addu'arta.

Fatan alkairi taita masa da fatan dacewa.

Yana yanke wayar ya kira Baffi suka tattauna shima akan kaddarorinsa daya kamata a saida, danshima dai shine lauyan nasa.

Sosai Baffi ya tausaya masa, Ind

a ace shid'in wanine tabbas daya taimakama Galadima da iya k'arfinsa, amma ina, a abinda ake buk'ata shiba komai baneba, Dan ko kud'in ruwan allura d'aya ba iya saya masa zaiyiba.

Haka ya shiga shigi da fici akan dukkan abinda

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login