Showing 258001 words to 261000 words out of 407268 words
Nuren ya murmusa yana tahowa cikin falon, hannu yabama Galadima sukayi m
usabaha, yana tambayarsa yaya jiki?.
Akan la66a ya amsa da “Alhmdllh”.
Nuren yace, “ina yarana?”.
Da hannu yamasa nuni da lfy.
Kular da Nuren yayi yau k'asaitar a kusa take saiya barsa ya mik'e, Coffee ya had'o yadawo ya zauna y
ana kallon abinda su Muftahu sukeji.
Shikam Galadima yayi shiru yana tunano yanayinsu da Munaya na d'azun, yana da buk'ata mai tsanani, saidai yakan danne saboda jarumta, musamman idan ya tuna matsayin auren nasu, ko a baya saboda yanayin data shiga
ne ya sakashi yin yadda yaso da ita, Dan hak'k'insa ne ya taimaketa a lokacin kodan buk'atar tazame mata lalurar cikinsa, yanzu kam dolene yanemo mafita ko matar aur..........
Tunaninsa ya katse lokacin da Shazali ke fad'in “itace wannan yalla6ai”.
Daga Muftahu har Nuren kallon picture d'in suka tsaya yi, sannan duk suka kalli Galadima da shima idonsa ke Kansu.
Nuren ya d'auki laptop d'in ya mik'a masa, shiru Galadima yay yana kallon hoton, Matar Abie ce ta biyu, wadda yata6a gani a way
ar Harun, yay wani miskilin murmushi yana yana kallon Shazali, saikuma ya janye idonsa batare da yace uffanba.
Shazali ya gyara zama yana fad'in “bayan ita kuma sai aka had'amu da wannan matan daga masarauta, sukuma sunce Uwar gidan sarkice ta sakasu
”.
Nuren yace, “uwargidan Sarki kuma? to tayaya tasan kud'in ga abinda zakuyi?”.
“wlhy ban saniba nima ranka ya dad'e, abinda na Sani kawai a ranar wlimar kafin mu shigo hall d'in aka taremu a hanya, shine wani dogari ya shigo motarmu, da
farko mun taso masa harda fiddo wuk'ak'e, saishi kuma ya nuna mana bindiga, hakanne ya sakamu nutsuwa, yace, yasan abinda zamujeyi ai, dan haka idan munason mu tsira da ranmu mu sauraresa da k'yau, shima aiki zai bamu. Zai had'amu da bayi biyu mata dazasu
taimakemu mu sace yaran, bayan mun gama akwai kaso mai tsoka, sannan zai fad'a mana wani sirri, mahaifin yaran yayi shirin canjasu da y'ay'an babyn roba dan haka karmu sake mu d'auki yaran da za'a bama wasu yara, mu d'auki na cikin gado daza'a sakasu a wa
jen taron, sune zasu zamo na gaskiya, mak'udan kud'in daya bamune suka samu amincewa da gaggawa, Yakuma sanar mana aikin uwargidan sarkine, idan har mukayi kuskuren wani yasani dagamu har ahalinmu sai sun shafe labarinmu a doron k'asa”.
Daga Muft
ahu har Nuren kallon Galadima suke da mamakin Brain nashi, hakan suka shirya, amma daga baya sai sukaga ya canja yabada yaran da gaske, sunyi mamaki sosai, amma bai basu fuskar tambayarsa ba a time d'in.
Yay musu alamar miye suke wani kallonsa.
Salute d'insa sukayi su duka, ya kauda kansa kawai yana ta6e baki.
Sun kuma tabbatar da akwai sirrika da yawa da Galadima ya Sani, akwai yana basarwane saboda jiran lokaci.
Da hannu yamasu Nunin Shazali yatashi yaje.
Bayan tafiyar
Shazali ya kallesu yana sauke ajiyar zuciya da gyara zamansa, ya d'auki kwalin hollandia yazuba a cup, Muftahu da Nuren dai na kallonsa, saida yafara sha da kallon agogon hannunsa sannan yace, “Zanje India gobe idan ALLAH ya kaimu, akwai ayyukan dazan tat
tara na kwanaki uku, sannan na d'auki Hutu a wajen aiki, dukda muna shirye-shiryen fidda kaya na shekara mai zuwa, a Daren yau Harun zaisan matsayinsa, Dan tuni nagama da matsalarsa dama, wannan ranar nake jira, so Nuren ka bincikamin inda matarnan take za
une a yanzu, Dan ina dawowa zan shiga aikine sosai, matsalar Harun da ita da Sarauniya kowanne akwai manufa, su nasu wasan yarane a wajena. Erfan shine yajema Munaya a matsayin Fu'aad, yanzu na fahimci sune suka saka aka buga waccan jaridar, amma da saka h
annun wasu a gefe........”
Muftahu yay saurin cewa “yi hak'uri ranka ya dad'e zan katseka, sai yanzu wani Abu yazomin a rai, wato ranar salla a filin idi, kasan Erfaan yana tare damu, anya kuwa ba a wannan time d'in ya ganku kaida gimbiya ba, lok
acin da kukayi karo, wata k'il shikuma yayi tunanin alak'a Ce a tsakaninku?”.
Murmushi Galadima yayi yana lumshe ido, “ni kaina ina tunanin haka, saidai akwai wani Abu bayan wanna, dan haka sarakuna uku sun shigo cikin aikina”.
Da mamaki M
uftahu da Nuren sukace sarakuna kuma?.
K'ala baice da suba ya mik'e tsaye, ya kalli agogon dake tsintsiyar hannunsa sannan ya kallesu, “gobe da safe Alhaji Shehu Darma zaije taron k'arama juna sani a jihar Katsina, lallai bana buk'atar yama k'arasa”
.
Kusan a tare sukace Alhaji Shehu Darma kuma?.
Ficewarsa yayi batareda yabasu amsaba balle su sami k'arin bayani. baki bud'e Nuren da Muftahu suka kalli juna, Muftahu yace, “shikuma miye nasa to?”.
Cikin jimami Nuren yace, “nima a
binda nake son Sani kenan, mutumin da tunda mijin aunty Mimi ya rasu yake fad'i tashi a kanta da yaranta, danma tak'i amincewa ne da aurenta zaiyi, anya kuwa shi yake nufi kodai wanine mai irin sunansa?”.
Jiki a sanyaye Muftahu ya yarfar da hannu a
lamar bai saniba shima. danshi lamarin Galadima yafara bashi tsoro, mutum kamar wani tsohon aljani.
Shikam koda yabar wajensu wani office yace Sarkin mota ya kaisa, yakai tsawon lokacin a wajen tareda wani mutum dabazai gaza shekaru 56 ba a duniya,
bansan mi suka tattauna ba, dan ba'a bani damar jinba.
A wajen yay sallar azhur har la'asar sannan yayo masa rakkiya wajen Motocinsa, saida yaga fitarsu sannan yakoma Office d'in.
Daga nan masarauta suka nufa, dan Galadima a matuk'ar ga
jiye yake,
Ya iske sashensa fes an gyara, ko ina yana tashin k'amshi tamkar yadda yake buk'ata, kayansa yacire ya watso ruwa, bai nemi kowa baya ya zauna a falo yana aiki a System, dukda yaga abincin da aka ajiye masa baiko bud'eba balle tunanin ci
nsa, Yakuma san Aunty Mimi ce zata saka a kawo.
Yana tsaka da aikin Sauban ya shigo, bai kallesaba koda ya gaidashi, yadai Amsa.
Sauban yace, “yaa Sam tafiyar safe zamuyine goben?”..
Ido Galadima yad'an d'ago ya kallesa, ya maida
kansa ga laptop d'in yana fad'in, “Kwana 3 zamuyi ni da kai mu dawo, komanka na gameda bautar k'asa yagama kammaluwa”.
Kamar Sauban zai sanya kuka yace, “Amma Yaa Sam su Momma sai abarsu babu kowa?”.
“kafin ka girma dawa suke zaune?, Sauban
ka kiyayeni, karka bari na fusata akanka, tashi bani waje”.
Sauban ya mik'e zuciyarsa na zafi, harzai fita Galadima yace, “zonan”.
Dawowa yay yana mirgina kai, batareda Galadima ya kallesa ba yace, kar6a wannan, kaje ka sakashi jikin rigar Ab
durrahman ko Amaturrahman ka d'auki Wanda ka samawa d'in kaje sashen Ummu Amaan (gimbiya Zulfa) dashi”.
Sauban baice komaiba ya kar6a abinda yabashi mai kama da ma6alli ya fita, ya iske Munaya na barci, yaran kuma na tare da Khaleel dake ta fama jag
walgwalasu, Abdurrahman ya d'auka ya sakamawa ya nad'eshi a showal ya fita......
Nikam wannan gangancin na Galadima ya isheni
😨🙆🏽
.
Bansake jin miya faruba dan banbi Sauban ba nikam, ina tsoron ganin abinda zai hanani barci
😌
.
__
________________________
Misalin 8:30 na dare Galadima ke shiri bayan ya dawo daga sallar isha'i, yagama tsaf cikin k'ananun kaya da jacket d'insa wadda takai masa har gwiwa, ya saka safa har a hannunsa, cikin takunnan nasa na gwarzantaka ya fi
to, sashen Munaya ya nufa, sukaci karo a k'ofar d'aki zata fito a rikice, sauri tareta yayi ta fad'o jikinsa saboda kad'an yarage ta fad'i, k'amshin turarensa ya sakata shaida shine, ta share hawayenta tana kallonsa a rikice, shima kallonta yakeyi, Muryart
a na rawa saboda kuka tace, “yalla6ai Abdurrahman sai kuka yakeyi, jikinsa ya d'auki zafi”.
Baice komaiba ya kama hannunta suka koma cikin d'akin, laraba da aunty Mimi na zaune, aunty Mimi tana zarema Abdurrahman kayan jikinsa za'a watsa masa ruwan d'
umi kozaiyi shiru.
Zama yayi ya kar6e sa daga hannun Aunty mimi, ya fiddo wani kwali k'arami daga aljihun jacket d'insa ya bud'e, k'aramar kwalbar dake cikeda magani ya fiddo, ya d'iba maganin cikin tsinken da ake bama yara magani ya zubama yaran a b
ak'i, dak'yar ya shanyeshi.
Sudai sunyi jugum-jugum suna kallonsa.
Yunk'urin amai da yaron keyi yasaka Galadima d'agashi daga jikinsa dan kar yay masa, baimayi amanba, hakanne yasaka Galadima sauke ajiyar zuciya ya mannashi da k'irjinsa yana hur
a cikin kunnen yaron a hankali.
Tun yana kukan kad'an-kad'an ya koma ajiyar zuciya, sai gashi yayi barci. Kwantar dashi yayi kusada y'an uwansa ya lullu6esa.
Ya kalli aunty Mimi yana mik'ewa, “insha ALLAH zai sauka zaza6in”..
Yanda
Aunty Mimi kebinsa da kallon tuhuma saiya janye idonsa yakama hanyar fita, da sauri tamik'e tabi bayansa a fusace. Dan Sauban ya sanar mata Galadima ya sashi kai yaron sashen mai martaba d'azun.
“Dakata Sameer”.
Cak ya tsaya yanajan hular ri
gar bisa kansa, amma bai juyoba.
“Sameer wai mike damun kankane haka? da zaka ringa wasa da rayuwar yaranka da kanka?”.
Lips d'insa ya ciza, ya juyo yana kallonta, amma ita bata ganin idanunsa saboda hular ta rufe, murmushin takaici yayi, y
ace, “Ni ba wasa da rayuwarsu nakeba aunty Mimi, komai kikaga nayi nasan abinda nakeyi, zuwa nangaba kad'an kuma zaku fahimci komai”.
“ALLAH yasa to, amma ni yanzu na zone muyi maganar komawar Munaya gida kafin mu wuce goben, tunda jirgin rana zamu
bi”.
Agogon hannunsa ya kalla, yace, “yanzu kam inada uzirin fita?”.
“fita? Inakuma zakaje a wannan daren?”.
Batareda ya tanka mataba yajuya yakama hanyar fita, saida yaje bakin k'ofa sannan yace, “Farauta”. yay ficewarsa.
Ka
sa motsi aunty Mimi tayi a wajen, sai maimaita Sunan Galadima kawai takeyi akan la66anta.
******
Tacan baya yabi shikam, hanyar akwai k'arancin mutane sosai, yana zuwa ta wani waje yagamu da wani Wanda ke sanye da irin kayan hadiman masarauta
r, rissinawa yay yabashi keys d'in mota. ya kar6a batareda sunma juna maganaba ya wuce.
Can sashen su Harun naga ya nufa, dukda tazarar dake tsakaninsu baiji tafiyarba, motar dake fake a wajen ya bud'e ya shiga ya zauna, zamansa da mintuna uku Harun
yafito ad'an hanzarce, motar yabud'e seat d'in baya ya shiga ya zauna, cikin bada Umarni yace, lawandi muje, kasan d'an bala'innan yanada securitys dake kaimasa rahoto”.
Murmuahin gefen baki Galadima yayi yatada motar yafice daga masarautar..........
......
✍
🏻
“Hummmm! Reader's harna sauke numfashi, babbar magana, yau dai ga Galadima ga Harun, sauran abinda zai faru kuma sai a buk 3 na raina kama”.
Miya faru da Abdurrahman lokacin da Sauban ya kaisa sashen gimbiya zulfah ne
🤔
? Yaya batun
kama SD?, wad'anne sarakuna ne Galadima yake zargi? Kodai dama can Galadima yasan wanene Harun yabashi damane kawai?
🤔
, Yaya batun warkewar Abie da Auren Contract tsakanin Galadima da Munaya?, mi suke shiryawa itada Momma da suka damu da zuwanta wankan gi
da? Ko Galadima zai amince?”.
Yaya batun gano asalin innarsu Munaya? Da ita Munayar ta d'auki alwashi?.
Tofa wannan amsar dai duk zatazo a littafi na 3 kuma na k'arshe da izinin ubangiji, dukkan wasu tambayoyinku amsarku na cikinsa, zan had'a
muku da albishirin zan dingayi a weekend rana 1, kodai asabar ko lahadi, kowacce rana nasamu dama aciki, dan buk 3 inason kammalashi ne a gaggauce saboda uzirin danake dashi insha ALLAH.
Ngd sosai da had'in kan da kuke bani, muje zuwa my guys
⛹
🏻
♀⛹
🏻
♀⛹
🏻
♀⛹
🏻
♀
🥰🥰🥰🥰🥰🥰
😍😍😍😍😍😍
❤❤❤
.
Barkanku da juma'a
🙋🏻
.
Musha weekend lafiya
⛹
🏻
♀⛹
🏻
♀⛹
🏻
♀⛹
🏻
♀
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*
😭🙏🏼
*_typing
📲
_*
💡
*_HASKE WRITERS ASSO....._*
*_
♦
RAINA KAMA.....!!
♦
_*
_(Kaga gayya)_
*_Bilyn Abdull ce
🤙🏻
_*
__________________________
*_Kai jama'a yau dai kun Sani typing dole saboda munafurcin y'an bani Na iya, wannan karon kuma kurasa k'ullin da zakuyi sai akan Uwa da '
Diya?, nikam yau koda mamana (mamu gee) kwaikwayar RAINA KAMA tayi to wlhy birgeni zatayi, ai baiwace ma wani yayi Abu kabishi daki-daki kana kwaikwayo. Irin wannan shirmen naku baya cikin kan Bily, ba mamu gee ba koda watace aka jingina da hakan bazanji k
omaiba wlhy, sannanma nifa abinda yabani mamaki a writeup d'in da mamana tayi bata ambaci sunan RAINA KAMA ba aciki ko wani littafi daban, to tayaya y'an bani Na iya da tsugunne-tsugunne su anasu writeup d'in suka saka sunan RAINA KAMA? (Wlhy halin wasu da
ga cikin writers namu ko kad'an bashida k'yau, neman sunane kokuwa son asanine niban saniba
🤦🏻
♀
)._*
_Reader's kuma da naku, sometimes bakunanku basuda linzami, irin wannan abubuwan kune ke fara tsirarsu saisuzo kuma su buwayeku, Ku ke karanta RAINA
KAMA DA TARAYYA Ku kusan banbancin abinda ke cikin kowanne, amma dayake Ku irin wannan dama shine farin cikinku saikuyita k'irk'irar abinda dolene daga k'arshe saiya zama rikici, to nikam zan sanar muku, awanan karon sai had'in naku baiyiba, Dan MAMU GEE
DA BILYN ABDUL duk Abu d'ayane, daga tarayya har Raina kama buks d'inmu ne, mu muke rubuta abunmu, babu wata munafukar writer ko reader da mukayi shawara da ita kafin mu d'aura alk'alaminmu a takarda, masu had'a husuma kuma sai kusha fetur Ku had'iyi ashan
a kuyi bombing d'in kanku, ina dai shikenan ko?
🙅🏻
_.
*Daga k'arshe inamai muku nasiha da kuji tsoron ALLAH, wlhy bashin naira 10 kacal yana hana bawa kwanciyar kabari, karo tsakanin rago da rago kawai akwai hisabi tsakaninsu, aranar kiyama bayan an
tsaya hisabi duk Wanda kasani koya sanka saika Ganshi kakuma ganeshi, bawai kaitsaye za tantanceka akaika wuta ko aljanna ba, wlhy sai an tsidaka, ancire hak'in mutane a kanka, ka zagi wane babu hak'k'insa, ka harari wane, kama wane zind'e, ka cinye kud'i
n wane, ka had'a fad'a tsakanin wane, ka 6ata sunan wane, ka cuci makwafcin, ka...ka...ka...da yawan gaske, duk wani cin amana ko zalunci dakama wani inhar bai yafe makaba a wannan ranar sai an cire masa hak'insa a cikin ayyukanka, (Dan sune kad'ai guzirin
ka) komai tarin aikin alkairin daka tara inhar kanada irin wad'annan bashishshikan d'aya bayan d'aya sai an zaresu daga gareka, koda dabba da kafiri ka zalunta kuwa, idan dama bakada komai, sai ayita kwashe nasu zunubai ana lafta maka, sai angama tas, kabi
ya an biyaka saikuma a gwada ayyukanka a kan mizani, miyarage kuma? Saika koma gefe jiran sakamako. Wlhy y'an uwa babu babban tashin hankali irin kar6ar sakamako, a wannan lokacin uba baya gane d'ansa, y'a bata gane uwarta, miji baya gane matarsa saboda ts
antsar tashin hankalin da ake ciki, da wane hannu xaka amsa, ina ne zaizama mazauni Na dindindin, duk baka saniba, haba y'ar uwata, kinada wannan babban aiki a gabanki amma kika shagala wajen had'a husuma irin ta social media wadda bansanki ba, baki sannib
a, maybe ma har Abadan bazamu ta6a sanin junanmu ba, muji tsoron ALLAH wlhy, yakamata irin wannan abubuwan su tsaya hakanan, daga ni har mamana badan Neman suna mukeba, domin Isar da sak'o mukeyi a cikin tarayya da raina kama, burinmu kuma ko mutum d'aya y
a amfanu da manufarmu ya wadatar, bawai tarin masu karantawa ba, ni miyasa babu Wanda yata6a tarata yacemin tarayya copy d'in raina kama ne? to Ku kama kanku please, kodan tsoron ALLAH.*
_My Sweet mah-mah mamu gee wannan page d'in sadaukarwane a ga
reki, kiyi yadda kikeso dashi nabaki, ALLAH yabarmu tare, I love you