Showing 108001 words to 111000 words out of 407268 words

Chapter 37 - Raina Kama COMPLETE

damuba saboda nema

n gindin zama take ajikina.

Bamu baro gidanmu ba sai gab daza'a shiga sallar juma'a, an taho da motata da lefena, duk kayan daza'a bana mutane kuma na barsu a can, harna Munubiya.

Su Abba sunsha alkairi awajen Galadima Ashe, hakama matan gida

nmu d'akin kowacce daya shiga saida ya ajiye alkairi, sunata kukan zuci da fad'in inama-inama 'ya'yansu ne a wannan daular

🤣

🥴

.

Zamu shiga motane ina sharar kwalla baba k'arami yace namusu godiya wajen Galadima, kaina kawai na iya d'aga masa.



Innarmu bayan tafiyarmu har 'yan kwalla tayi, matan gidanmu kam duk haushinta sukeji, idan kacire maman fauziyya.

Daga nan gidan Munubiya muka nufa, amma anan bai shigaba, yace naje zuwa anjima zai dawo mutafi, dan yanzu zaije sallar juma'a.



Kai na kawai na d'aga masa, nafita bayan dogari d'aya yabud'emin k'ofa, basu bar gate d'inba saida sukaga na shige ciki, ya maida kansa jikin kujera ya kwantar tareda lumshe ido, abinda yafaru a gidanmu kawai yake tariyowa, yakula family nawama sai a hank

ali dai. Sunada shigen irin halallayyar family d'insa.

Nikam da gudu nashiga ina kwala kiran sunan Munubiya, itama yafito aguje muka rungume juna, sai muka fashe da kuka kawai, ALLAH ma ya somu yaa Marwan yarigada yafita masallaci.................



🏼

*_Masoya bansan yanda zan nuna muku tsantsar farin cikinaba, amma tabbas inajin dad'in Comments naku, kuyi hak'uri da rashin amsawata d'ai-d'ai, kunmin yawane wlhy, ga massages na PC, idan kuma nagama typing d'inan kaina d'aukar zafi yake, ko so

n ta6a waya banayi wlhy, naga wasu suna d'auka kamar wulak'ancine rashin amsawar, wlhy ba haka bane, kumin afuwa da uzuri please & please, duk da nasan bazan iya k'yautatama kowa acikinku yanda yakamata ba, dole wani yaga gazawata koyayane tawani fannin

😄

.

_*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu

😭🙏🏻

_*

*_Typing

📲

_*

*_HASKE WRITERS ASSO...

💡

_*

_(Home of expert and perfect writer's)_

*_



RAINA KAMA......!!



_*

_{Kaga gayya}_

*_Bilyn Abdu

ll ce

🤙🏻

_*

👉🏻

2



8



...........Bansan yanda zan musalta muku farin cikin damuka tsinci kanmuba nida 'yar uwata Munubiya, abin kawai ba'a magana.

Duk da bata yarda zan zo d'inba amma bata fasa tanadar min duk abinda tasan inasoba, ta

rasa inda zata sakani dan dad'i, gaskiya gidan munu yayi k'yau sosai, gashi an cika ko ina da kaya, kasancewar harda nawa aka had'a mata, muna yin salla muka 6arke da hirar yaushe gamo, a haka yaa marwan yazo ya samemu, yaukam abin mamaki naga fara'a a fus

karsa, nace lallai aure yayi citta kenan, yanda yake bama Munubiya kulawa sai abin ya birgeni, kamar Na lashesu kuwa Dan dad'i. Haka muka yini muna tad'i har lokacin sallar la'asar yafita salla.

A lokacinne aunty Salamah tazo gidan, Ashe Munubiya ce

takirata ta fad'a mata zamu tafi India yau da daddare, mun tarbeta da murna sosai, yayinda ita kuma taketa yaba wai munyi k'yau. mukaita rufe fuska alamar kunya.

Shawarwari taita bamu akan rayuwar aure da yanda zamu tattali mazanmu, babu ko kunya

take 6aro mana komai, sai mune muketa sunkuy da kai, itakam ko a jikinta, ta rarraba mana wasu buks da ke d'auke da abubuwa masu amfani dazasu bada gudunmawa a zaman takewar aure, nidai bawai na d'auki nawa da muhimmanci baneba.

Wajen 5 tatafi, tafi

yarta babu dad'ewa saiga Galadima da yaa marwan sun shigo, Ashe wai ya dad'e a k'ofar gida zaune, ya kira yaa marwan yace baya gida amma gashinan zuwa.

Shine yajirashi amota harya iso suka shigo tare. Sun gaisa da Munubiya a mutunce, ta shirya musu

abinci, da yace yagode sauri yakeyi, amma munu ta marairaice wai yaza'ayi mijin 'Yar uwarta yak'i cin abincin gidanta, in baimasa baneba ta sake masa.

Murmushi yayi ya zauna yaci kad'an, yayinda mukuma muka shiga d'aki dan mu basu waje suci abincin

, d'an kuskus d'inmu mukayi muma, takuma kwantar min da hankali akan auren nawa da wasu 'yan shawarwari, da nunamin fushinta akan abinda nace nama Galadima d'in, ta nunamin wannan ba tarbiyyar da iyayenmu suka bamu baneba, gaskiya karna sake irin haka, kum

a nabashi hak'uri akan hakan, nace “to amma tayaya zan basa hakurin?”.

'Yar takarda ta d'auka tayi rubutun tabani wai nabashi.

Na kar6ane kawai badan ina tunanin zan bayar d'inba, duk da nasiharta ta shigine gaskiya, kuma nima tun a ranar n

ayi nadamar ce masa azzalumin gaskiya, Duk da nasan a cikin fushine Nima Na fad'a, Dan nashiga rud'ani sosai akan abinda yayimin daban zataba.

tabani kayan da aunty salamah takawo a Leda, batareda na dubaba na amsa.

Itama k'yauta ma

i tsoka yamata sannan muka fito, nida ita kowa yana sharar kwalla, bamason rabuwa da juna, amma yazamuyi? aure ya rabamu.

Daga nan gz yaa marwan muka nufa gaida mama rabi'a, namayi mamakin yanda yasanta, nankam tare muka shiga, su Ayusher suka ruk

unkumeni cikin tsantsar farinciki da kewa.

Bamu dad'e sosaiba itama ya ajiye mata alkairi muka fito, su Feena ma yabasu kud'i wai su sai kayan kwalliya, hakama Ahmad, yaa Fadeel dai mun tarar baya nan, yakoma inda yake bautar k'asa.

Nanma sa

ida nayi kuka dazamu taho.

Saida muka shiga mota ina sharar hawaye sannan ya kalleni cikeda k'asaita yana ta6e baki, “ke wai bak'ya tsoron hawayenki su k'are ne?”.

Bance masa komaiba nacigaba da kukana, shima saiya shareni.

★★★

***

★★★

Koda muka isa Masarauta bamu wuce sashenmu kai tsaye ba, wasu 6angarorin gidan mukaje mukai musu sallama, harda sashen mama Fulani, yauma dai babu magana mai dad'i tsakaninta da Galadima, nifa lamarin nasu na d'aure kaina gaskiya.

Mai ma

rtaba kam munsha addu'a a wajensa, sannan muka fito.

Mun shiga sashenmu ana kiran sallar magriba, zan shige yace “kiyi azamar shirya kayanki trolley d'aya, karki wani kwashi kaya dayawa”.

Da to kawai na amsa nayi shigewata ciki.

*_7:30

pm_* Muka bar masarautar, nida shi da Samha motarmu d'aya, muna baya tana gaba.

d'ayar motar kuma Sauban da aunty Mimi da khaleel ne aciki.

Mun sami rakkiyar Harun da Muftahu sai wasu k'alilan daga masarautar.

Tom nidai ba k'auyace a airp

ort, dan banta6a shiga jirgiba, amma kunsan mutuniyar taku da Jan aji,

🤨

saina Fiske abina nima inajan citta tamkar wadda ta saba.

Duk abinda yadace ayi anyi mana, musamman ma ni danake sabuwar fita k'asar, harun yad'an sha cukuniya a kaina tunda r

ana.

9pm dai-dai jirginmu ya shilla a gajimare

😆😜🛫

.

Lokacin da akace asaka belt ban sakaba, sai shine ya jawo yasakamin batareda yace uffanba, yana jikin window nikuma ina gefensa, sai bayan mu khaleel da Samha, can baya kuma aunty Mimi

da Sauban.

Ina lafe jikin kujera, yayinda shima yake kwance ya jingina bayansa, wani English novel ne a hannunsa yana karantawa, dama tun amota yake rik'e da kayansa.

Da akazo tambayarmu mi muke buk'ata Coffee kawai yace yacigaba da karatu

nsa, nima ta tambayeni saina girgiza mata kai alamar bana buk'atar komai.

Janye book d'in yayi yana kallona, saikuma ya janye ya maida kanta, harta bar wajen ya kirata, yace takawo min abinda su Samha sukace sunaso.

Bance komaiba nidai, sh

ima saiya cigaba da karatunsa.



(*************)

Alhmdllh mun sauka kasar India, k'asar da nake gani a films, abin mamaki sainaga dogarawa ne sukazo tarbarmu, saikuma Akash dawani danaji Galadima yakira da beejay.

Bamu 6ata l

okaciba mukabar airport d'in, a nawa tunanin sainaga rayuwar tasu kamar dai tamuce gaskiya, saidai banbancin sutura zuwa wasu mu'amullat haka, mutane sunata hidimarsu da kai kawo hankali kwance.

Masha ALLAH na fad'a yayinda muka isa gidan danake k'

yautata zaton nasu Galadima ne. gidan kam yamin k'yau gaskiya, su beejay basu shigaba suna saukemu suka juya, mune muka Shiga hannuna aunty Mimi tarik'e, yayinda su Samha suke agaba.

Galadima kam mun barsa a harabar gidan yana waya.

Ai kaina b

ai gama kwancewa ba saida muka shiga falon gidan, hummm manyan k'asarmu sunajin dad'insu gaskiya, yo kanada irin wannan gidan a k'asar daba takaba to k'asarka kumafa?.

A falo muka zube bayi suka Shiga hidima damu, muna zaune a wajen Galadima yashi

go, shima zaman yayi ya aza k'afa d'aya bisa d'aya, Sauban yazuba ruwa a cup yabashi, kar6a yay yana fad'in “thanks”.

Ya kalli baiwar datake shirya abinci daga can gefenmu, “k zonan”.

Da sairi ta ajiye spoons d'in hannunta tanufo inda mu

ke, agabansa ta zube tace “gani ranka ya dad'e”.

“kisamu wata ta tayaki Ku gyara d'akin can nakusada Samha yanzun nan”.

“angama ranka ya dad'e”. tayi maganar cikeda tdantsar ladabi.

Aunty Mimi Na najinsa batace uffanba. Shigowar momma

tasaka khaleel tashi da gudu yaje ya tarbota, itama Samha zuwata ta kwakwameta, tunkan ma

afad'amin nagane mahaifiyarsu Galadima ce, koda yanda fuskar kowannensu ta washe da farincikin ganin juna.

Hankalinta Na kaina tana murmushi da fad'in “oyoyo

d'iyata”.

Zamowa nayi daga kujerar na durk'usa har k'asa ina gaisheta, ta k'araso inda nake ta kama hannuna ta tadani nakoma saman kujerar, “zauna kinji, sannunku da zuwa, kinsha hanya ko?”.

Murmushi nayi ina duk'ar da kaina.

Galadima ya

ce “wai Momma dan ALLAH duk baki ganmu baneba?”.

Kallonsa tayi cikin Hararar wasa, tace, “yo naganku bata taku nakeba”.

Su aunty Mimi dariya suka Sanya, yayinda Galadima yad'an 6ata rai yana fad'in “da tsohuwar Zuma dai ake Magani Momma”

.

“a fad'arka ba, amma sabuwa ma aitafi aiki da dad'i”.

Nidai murmushi nakeyi, Dan wasan nasu ya burgeni, inason ganin family haka cikin farinciki, gaskiya sai sunfi jin dad'in zaman nan fiyema da masarautar sun can.

Gaishe-gaishe a

ka shigayi, kowa yana k'ok'arin bama Momma labarin yanda biki ya kasance, sai dad'i takeji da sanya albarka, nidai nida Galadima babu mai cewa komai.

Mik'ewa Galadima yayi, “bara nad'an watsa ruwa Momma”.

“to afito lafiya Muh'd”. ta kalleni

nima, “d'iyata tashi kibi mijinki kiyi wanka kuzo ga abinci”.

Harya fara tafiya saiya tsaya, juyiwa yayi yana mata magana a yaren daban saniba.

Ta galla masa harara da masa dak'uwa, itama bansan mitace masaba. naga dai ya tura baki yaci gaba

da tafiyarsa. ita kuma tace natashi naje.

(Wai ashe cayay mata ai yasa a gyaramin d'akin da zan zauna, shine tamasa dak'uwa tana cewa d'akin safa?, shi idan ance Araba mana d'aki saiya amince?, to tare zamu zauna, shine yakuma cewa ammafa d'akins

a ai ba kowa ke shigaba, tace tasani aii, muje nima sirrinsace ai, shinefa ya tura baki gaba).

Kamar an maken k'afafu haka nabisa abaya muna taka steps d'in benen, har muka isa k'aramin falo mai k'yau, komai farine a wajen, TV ce kawai takasance

bak'a.

Falon yad'anyi k'ura alamun ba'a gyaraba (babu mai aikin dake hawa samansa, gashi kuma sunyi tafiya suduka, Momma kuma batada time d'in gyara masa d'aki).

Guntun tsaki yaja yana yamutsa fuska, d'an zaman danayi dashi na fuskanci bayaso

n k'azanta komin k'ank'antar datti yata yamutse fuka kenan, bamu tsaya ananba muka shiga bedroom d'in bayan yabud'e, mayataccen k'amshinsa yana manne da d'akin, sai dai nan d'inma yayi k'ura, waya yazaro yayi kira, ashe Samha yakira, yace “k zoki gyaramin

d'aki”.

Bai jira cewarta ba ya yanke wayar.

Bance masa uffanba nima nataka nawucesa, bina yayi da kallo dan yaga ina zanje?.

Zanin gadon na yaye duka, nacire rigar filaluwan tareda rumfar da akama gadon, shidai kallona kawai yakeyi, yan

a tsaye jingine da bango (baiyi tunanin zance zan gyaraba).

Knocking d'in da akayine yabada izinin shigowa, Samha ce d'auke da kayan tsintsiya, ta zubesu a k'asa tana fad'in “aunty kibarsa zan gyara”.

Kaina na girgiza nace “barshi Samha, nun

amin kawai yanda zanyi, kije kema ki huta”.

Nunamin komai tayi, har inda bedsheets suke, tafice a d'arare da zaton Galadima zai hanata yace takoma ta gyara.

Amma saitaji baice komaiba, yama kauda kansa gefe kamar baisan munayiba.



Bathroom nashiga, nazage sosai na tsaftaceshi, Dana k'urarce kawai, duk abinda zaisa toilet k'amshi da tsafta nasakashi, saida naganshi need sannan nafito, ban iskeshi a d'akinba, Dan haka hankali kwance Nagyara bedroom d'inma nagama, nasaka kamshi sosai.

falon nafito danufi gyarawa, sainaga Samha harta gama itama tana saka air fresheners masu dad'in k'amshi, da turaren wuta irin namu na gargajiya.

Sannu da aiki namata, itama tamin, Galadima yafito daga wata k'ofa yawucemu batareda ya tankaba, bedroom

d'in yakoma.

Kallon Samha nayi nace, “saura wannan d'akin daya fito cikin ko?”.

“ai Aunty wannan d'akin dakansa yake gyarawa, babu mai shigarsa duk gidannan inba Momma da Mummy na da shiba”.

Cikin mamaki nace “miya sa to?”.



“d'akin sirrinsa ne aunty”.

Ban fahimci maganarba, bankuma tambayeta ba, ta tattara kayan damukayi amfani dasu tafice tana fad'in “aunty bara naje nayi wanka, dama wankan zanyi yakirani”.

Kaina kawai na iya d'aga mata, saman kujerar na zauna

shiru ina nazarin maganarta, miye kuma ma'anar d'akin sirri? nashiga k'ololuwar nazari banyi zaton time yawuce hakaba, k'afata yad'an shura, nad'ago idona ad'an firgice na kallesa, haryayi wankan yana sanye cikin jajayen kaya na Adidas, sun masa k'yau sos

ai.

Juyawa yay zai sauka k'asa yana fad'in “kitashi kije kiyi wanka”.

Bai jira cewata ba ya sauka.

Nima saina tashi nayi yanda yace, d'akinsa sosai ya had'u gaskiya, harma bansan Yaya zan fasalta mukuba, nasan farin Abu namai tsaftane, l

allai yanada tsafta, daga bedroom parlour zuwa bathroom nashi komai farine, bedroom d'inne kawai keda d'an sirkin Golden kad'an-kad'an shima.

Nidai ina wanka da d'unbin tunani, haka kawai naji kwad'ayin son Shiga d'akin sirrin nasa.

Kod

a na fito saina saka zani da riga na atanfa, ban shafa komaiba na d'auki turarensa na saka saboda neman magana

😂

. ina tsaka da saka turaren Samha tashigo kirana.

Ajiyewa nayi na d'auki gyale nabi bayanta.



Falon k'asa muka sakko, inda ak

a shirya abincin saman wata lallausar darduma, duk suna a zaune har Momma, kusada Galadima daketa cin abincinsa ko kallon mutane bayayi Aunty Mimi ta nunamin wai na zauna.

Kamar nafasa kuka haka naji, Sauban dake gefen haggunsa yace, “auntynmu har y

anzu amarcin bai k'are bane? kin shige d'aki kinyi bulum”.

Murmushi kawai nayi na k'asa ce masa komai, dan yabani kunya gaskiya, nakula kuma yanada yawan tsokana, aunty Mimi kam dariya tayi, yayinda Samha tarufe baki tanayin tata.

Momma tama

sa dak'uwa, “o kai Sauban ALLAH ya shiryeka, kowama

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login