Showing 72001 words to 75000 words out of 407268 words

Chapter 25 - Raina Kama COMPLETE

danginsu na tayasu.

Innarmu dai tana daga cikin d'aki abinta, sai zuba murmushi take tana sharar hawayen dad'i, yau kokad'an rashin mutuncin 'yan gidanmu bai 6ata rantaba, saima wani farin ciki dasuke sakata.



🤣🤣

Maganar sisters and brothers event

kam ai bai yuwuba yau, dan gidanmu gaba d'aya a harmutse yake, ga 'yan anguwa sunata turuwar zuwa ganin kaya harda mota.

Nikam ma zazza6ine yagama rufeni tunda nagama kukan, duk wannan kacaniya da akeyi ina cikin bargo k'udundune, su munubiya kam sun

acan tsakar gida sun kasa sun tsare akan kayan gudun masu suruf bahana

😜🤣

.

Da k'yar aka tartare kayan aka kaisu falon baba k'arami kasancewar magriba ta gabato, sai bayan isha'i su Abba da Dady suka gani, ranar Abbanmu shima saida yayi kukan dad'i

, ALLAH Sarki Ai'sha, nagodema ALLAH da wannan babban al'amari yashigomin ta 6angaren tsatsonki, kema yanzu k'ya samu 'yancin kanki agidan mijinki, 'ya'yanki zasu samu 'yanci a gidan mahaifinsu, dama akance ka yarda da k'addara kakuma godema ALLAH a yayin

da ya jarabceka, Ashe sharrin da akama d'iyarsa zai zame mata alkairine, sun had'ata da babban mutum domin 6atanci agareta dashi kansa Ashe zai zama sanadin alkairi a rayuwar yaranne, dan yasan inba dan wannan abin yafaruba ina Galadima zai ga munaya har i

yayensa sunema masa aurrenta? hikimar ubangiji yawane da ita, yakan jarabeka

domin kankare zunibinka, kokuma danya d'aga darajarka ta inda bakayi zato ko tsammaniba.

★★★★★★

Labarin tarbar mutunci dasuka samu tuni ya karad'e masarautar, was

u kam dariyama abin yabasu, ina wata tarba dazasu samu ga talakawa fak'irai. suna dai fad'ane dan kar amusu dariya.

Mama Fulani koda labarin yaje kunnenta saita ta6e baki tana murmushi k'asaita, Wanda ita kad'ai tasan fassarar kayanta.

Tsaf

yagama shiryawa zaije sashen da aka sauke abokansa a cikin masarautar, dan babu damar saukesu a 6angarensa, saboda angama masa gyara tsaf amarya kawai ake jira, su aunty Mimi ma dasuka kai lefe sun Sanar da amaryarsu kawai suke buk'ata, basai su Abba sun

wahalar da kansuba wajen kaita da komai. Wannan dalilin yasaka aka yanke shawarar k'arama munubiya kayan munayar kawai, da safe za'aje a kuma jera mata su a gidanta

😄

.

Cikin takunsa na kasancewar cikakken namiji mai tashen k'uruciya ga jinin mulki d

ake yawo ajikinsa yafito, waya ce manne a kunnensa, yayinda d'ayan hannunsa ke cikin aljihun jeans d'insa, bayi da hadiman gidan sai zubewa sukeyi suna kwasar gaisuwa, kansa kawai yake d'aga musu yayinda yake cigaba da wayarsa da Momma wadda tana India ita

batazoba.

Samha tak'araso gareshi a hanzarce, “Uncle ka tsaya mana please ”. ‘tayi maganar a shagwa6e saboda ganin ya basar da ita tamkar baima gantaba’.

d'an juyowa yayi ya kalleta sannan ya d'auke idonsa yana cigaba da Murmushin sa na k'asa

ita saboda addu'ar da Momma ke jero musu ta zaman lafiya da samun albarka ta har abada acikin auren daza'a d'aura a gobe. jiyake tamkar yace Momma ta dainama auren shekara d'ayannan addu'a irin haka, shifa harma tausayi suke bashi yanda suke nuna farin cik

i da zumud'insu akan auren, musamman idan ya kalli yanda masarautar tagama cika tab da dangi takowanne 6angare, ga tawagar wasu masarautu dasukayo gaba tun yau, hakama 'yan siyasa ba'a magana, dan ba k'aramar gayya papi da Sarki sukaima wannan aurenba, kas

ancewar shine jika namiji na farko dazaiyi aure a masarautar, Wanda kuma kowa ke saka ran shine magajin sarautar masarautar.

Ita dai Samha tana tsaye tana kallonsa harya kammala wayar da Momma ya kashe.

Had'e fuskarsa yayi yana hararta, “to m

aganatu miya faru kuma? kike kwalan kira tundaga wata uwa duniya?, wai sai yaushene zakiyi hankali Samha?”.

Baki ta tunziro gaba, idonta harya cika da gwalla “amma dai Uncle aina fara yin hankalin ko, kumafa wani Abu Nazo na nuna maka, naje Sashenka

wannan sarkin k'ofar yawanice kana wajen mai martaba”.

Kansa kawai ya girgiza yana kallonta, saida takai aya sannan yace “to aini inada abunyi, yanzuma ba wai sauraren naki zan zauna yiba, dan nan ba India bane, ba'a ganina available ko yaushe OK?”

.

Harya juya zai tafi tarik'o hannunsa tana daddaga k'afafu idonta na zubar da hawaye.

Kansa ya dafe domin sanin fitinar Samha, tace,

“please Uncle Sam 2munutes to”.

Juyowa yayi tamkar zai maketa, saikuma komi ya tuna ya fasa

, d'an cije lips d'insa yayi yana hararta, “ke wai wace irin fitinanniyace ne?, Uwarmi to zaki fad'amin?”.

Dariya tayi tana share hawayenta dan ganin tasami nasara, wayarta ta daddana sannan ta mik'a masa.

Nanma Harar tata yayi kafin ya kar6a,

itace yagani a photo da 'yammata biyu masu kama d'aya, kamarma yarinyar dasuke shirin auren contract, harya yatsina fusaka zaice suwaye? saikuma yatuna. d'an murmushi basarwa ya saki kafin ya kalli Samha da ta tsaresa da idanu. “Uncle ina aunty Munaya an

an? ”.

Wayar yamik'a mata yay gaba abinsa yana fad'in titsiye zakimin ma kenan? an fad'a miki bazan ganeta baneba?”.

Baki ta turo tana k'unk'uni, “waikai Uncle Sam bazaka ta6a canjawa baneba? kai kenan kullum sai jan ajin tsiya, shiyya sam

a ALLAH yayoka jinin sarauta wlhy, Aunty Munaya kin bani da wannan mijin naki mai k'asaitar tsiya, aiko wlhy tunda kace haka saina had'a maka mugunta gobe a wajen dinner ”.

Ta tuntsire da dariya saboda tuno mizata shirya masa.



★★★★★

*

Rana bata k'arya........*



🏻

‍♀



Yau mun wayi gari safiyar d'aurin aure, gida yakuma d'inkewa da jama'ar dukda d'aurin Auren na Azhar ne bayan sakkowa masallacin juma'a.

Tun jiya banida lafiya, amma na hana su Ayusher fad'ama kowa, sai M

agani suka samo min nasha, itama dai Munubiya duk sukuku take, babu abinda ke damummu sai jimamin rabuwa da juna, dan itama kusan zazza6inne ma ta kwana dashi, sai dai dayake nawa ya had'a da damuwa saina fita nuna jin jiki.

Jama'ar gidanmu dai a h

armutse suka kwana, wasuma ko barcin basu sami damar yiba saboda ciwon hasada dake cin zukatansu, gashi gida d'inke da jama'ar babu damar matsawa koda nan da canne sai an gane, bare sufita neman mafitar tarwatsa Auren, waddama suke d'an samin tallafinta kw

ad'ayinta yasaka canja shek'a (innaro

🤣

), dan jiya da suke zuba tijara shigowa tayi tamisu tas, harma tana Neman tone musu asiri gaban tawagar 'yan biki, badan gwaggo Safiyya ta lalla6a taba ba'asan inda jarabar innaro zata tsayaba kam.

Ko karyawa ba

n iya tashi nayiba bare aje maganar wanka, ina kwance cikin bargo sai shar6ar kuka nakeyi babu wanda yasani.

Ahaka gwaggo Safiyya tashigo kiranmu nida Munubiya, da k'yar su Ameera suka samu natashi zaune ina tangad'i, gaba d'aya nayi wujiga-wujiga

dani, da taimakon Munubiya dake rik'e da hannuna muka iso gidan innaro inda su Abba suke jiranmu.

Gaba d'ayanmu ne amaren aka had'a, abin mamaki saiga innaro ta kamani ta zaunar tanamin sannu, harda lallashina wai na kwantar da hankalina.

Kowa

zuba mana idanu kuwa yayi, su Fiddausi sai jan tsaki suke a zukatansu sunajin wata tsanar innaro aransu.

Itakam bama tasan sunayiba, sai nannan takeyi damu nida Munubiya.

Nasiha mai ratsa jiki da 6argo sukai mana sosai, muhimmancin aure da hak'

uri, biyya da tsoron ALLAH, kare hak'in miji da k'yautatama danginsa da iyayensa, k'arfafa zaman lafiya a tsakani da rik'e sirrin miji, banda biyema k'awayen banza sukaika su baroka, musamman ma da dukanmu zamu cigaba da zuwa makaranta.

Gaba d'ayanm

u kowa hawaye yakeyi, musamman mani danakejin tausayin kaina dana iyayena dabasu San auren shekara d'aya nake shirin yiba nadawo garesu.

Munci kuka sannan aka sallamomu, tunda muka dawo sai aunty salamah ta saka mu agaba dole mukayi wanka, da k'y

ar muka amince aka mana simple kwalliya, muka saka dakakken leshin da mama Rabi'a tasa aka d'inka mana cikin kayan biki dasuka mana itada innarmu, less d'in blue ne da fararen bet ajikinsa, sai aka nad'a mana d'an kwalima blue, munyi k'yau harma bansan yaz

an musalta ba, nan su Ayusher suka hau zuba mana pictures. lokacin 12 tama wuce, masallacin anguwarmu daza'a d'aura auren yagama cika dank'am da jama'a, dayake bashida nisa da k'ofar gidanmu.

Cikin gidanmu kam ai ba'a magana, dan babu masaka tsinke,

sai hayaniya kakeji wani bayajin zancen wani, rabin hirar jama'a kuwa duk akan zancen lefe nane da Wanda zan aura, wad'anda suka gani suna bama wad'anda basu ganiba labari.

Su siyama dai koma ganinsu ba ayi, dan suna taya iyayensu kishi da hassada, a

unty Ramla da aunty Raihana sai aunty Hauwa'u ne kawai suka shigo sukaima innarmu murna har d'akinmu, amma aunty khaleesa ko k'eyarta bamu ganiba, kuma tunda safe tazo gidan daga ita har zarah, matar yaa hameed ma mama hanata zuwa tayi, dukda tanaso tazo t

ama innarmu murna amma surukarta takasa ta tsare, gashi bama dad'in zaman 6angaren takejiba, saboda 'yan ubanci na dangin miji da aketa nuna mata, itama matar yaa Naseer tashigo, dan har picture mukayi da ita, amma matar yaa Shafi'u ma bata shigoba.



Hakan duk bai dameniba, dan ni yanzu basune agabana ba, damuwata tarkon dana saka kaina na auren contract shike cazan tunani a halin yanzun, Wanda ko munubiya nakasa sanarma gaskiya lamarin.

*_1:30pm_*



Masallacin yagama cika taban mamaki, tun

i tawagar gidan Sarki sun iso tun bayan gama sallar juma'a, d'aurin aurene daya tara manyan mutane ta dalilin gidan sarauta, manyan sarakunan k'asarnan da 'yan siyasa, governors senators attajirai na gida dana k'etare, talakawan gari da tawagar iyaye da da

ngin sauran angunan, abokan su abbanmu danasu yayunmu, abokan anguna da abokan arzik'i, dangin iyayenmu mata danasu abbanmu, kowa ya hallara, bakajin komai sai kad'e-kad'e da bushe bushe irinna gidan sarauta. president da Kansa ya iso wannan waje bisa gayy

atar papi, bansan yanda zan musalta muku irin cikarda anguwarmu tayiba aranar, bama zaka iya gane taka maimai inane ake d'aurin aurenba. Su Kansu masarautar su Galadima sunsha mamaki, basuyi zaton auren Na Galad

ima zai tara jama'a manyan mutane hakaba, dub

i da yanda ba d'iyar wata hamshak'iyar masarautar zai auraba. basu San abin ba anan yakeba wai *d'uwawu yafi fuska k'yawun gani*

🙊🤥😜😂

inji masu iya magana......................



🏼

Amin afuwa, mu had'u tomorrow danjin yanda d'aurin aurenba zai kay

a



🏻

‍♀⛹

🏻

‍♀⛹

🏻

‍♀

.

Barkanmu da dawowa

😄



🏻🤝🏻

*_ya ALLAH ma gafartama iyayenmu_*

😭👏🏻

*_Typing

📲

_*

*_HASKE WRITERS ASSO...

💡

_*

_(Home of expert and perfect writer's)_

*_



RAINA KAMA......!!



_*



_{Kaga gayya}_

*_Bilyn Abdull ce

🤙🏻

_*

👉🏻

2



0



.........A cikinmu Fauziyya ce babba, dan haka aka fara d'aura auren ta, daga nan sai ni da Munubiya, an fara d'aura na Hassana Auwal fharuk (munubiya) da yaa mar

wan Ibraheem, sannan ni Hussaina Auwal fharuk (Munaya) da Muhammad Sameer Saifudden Abubakar (Galadima), saikuma Safara'u, sai Haleematu, Fiddausice k'arshe.

Ana gama d'aurin auren busar algaitu suka fara tashi, sarkin marok'a yafara zuba kirari w

a Ango Galadima sarkin gobe a masarautar gagara badau.

Maganar k'yawun da Anguna sukayi ma 6ata lokacine, kowanne yafito angonsa sak abin kallo da birgewar kowa, duk miskilancin yaa Marwan saigashi yana washe hakwara tamkar gonar audiga

😁

.



🤥

ance anguna basa kuka ranar aurensu, to kuwa yau saiga Galadima na share hawaye, dukda auren contract yayi nakuma shekara 1 kacal, saiyajisa wani iri daban, ya kuma zama babban mutum, tuno Abie dayayi yasaka hawaye fitowa daga idanunsa, bazai iya tuna tsaw

on lokacin dayayi kuka na k'arsheba, amma saigashi yau yanayi acikin d'umbin jama'a, akuma ranar d'aurin auren da ya rad'ama suna na (wucin gadi).

Papi ne yad'an bugi kafad'arsa yana murmushin jin dad'i shima, dajin wata k'aunar jikan nasa ta musam

man.

Aikam masu videos da photuna ansamu abinyi, hakama masu d'auka awaya ba'a magana.

Kafin kace mi social media ta d'auka, lungu da sak'o hotunan d'auren aurenne suketa yawo, musamman da jama'a ketajin wai wadda aka bugasu a jarida yana kiss

ing ce ya aura, wayyo ALLAH abin magana yasamu a yanar gizo, kowane polder na charts ka shiga zancen kenan dai.

Daga wajen d'aurin aure tawagar gidan su Galadima k'aton hall d'in da aka tanada domin cin abincin bak'i suka nufa, duk wani maiji da

kansa zaka sameshi awajenne, Galadima har kansa yafara ciwo saboda yawan magana ta amsa gaisuwar jama'a da murna da yakeyi.

Ana tsaka da cin abincin Momma ta kirashi, dama shi ba ma abincin yakeciba, zaune kawai yake yana juya spoon a plate, wayarsa

yaciro daga aljuhun gaban rigar milk d'in shaddarsa, dan tuni yacire malum-malun d'in tana hannun Harun.

Ganin Momma yasashi mik'ewa yafice daga hall d'in gaba d'aya, can waje yasamu wasu kujeru ya zauna sannan yakirata ta video call, tana d'agawa s

ai kawai ya fashe mata da kuka ganinta zaune kusada Abie.

daga Momma har Abie d'in sagade sukayi suna kallonsa, saida yayi mai isarsa yasaka handkerchief d'insa ya goge fuska sannan Momma tace “ho d'an nema duk murnar aurence kokuwa shagwa6a ce ta mo

tsa?”.

Tur6une fusaka yayi zai sake wani kukan Momma ta kwashe da dariya irin wadda yadad'e baiga tayiba, Abie ma murmushin sane ya fad'ad'a sosai. saida Momma tayi dariyar mai isarta sannan tace, “Muh'd kafa girma, kai yanzu babban mutumne, nan kum

a da wata shekarar kazama baba, amma katasamu gaba kana kuka?”.

Handkerchief yasaka yakuma goge hawayen dasuka taho masa, sannan yace “momma na barka da rana”.

“Barkan ka dai angon d'iyata Munaya, ALLAH ya sanya alkairi yabada zaman lafiya

yasa bad'i iyanzu munan muna shagalin sunan jikan mai martaba”. tayi maganar tana kallon Abie daketa zuba murmushi, gira d'aya ta d'aga masa, shikuma ya k'yafta mata idanu.

Dariya Galadima yasaka musu, irin wannan soyayya haka summa manta dashi.

Gyaran murya yayi sannan Momma ta d'ago tana kallonsa, suka saki dariya lokaci d'aya. yayinda Abie ke tayasu da Murmushi.

Galadima ya tsagaita dariyar yana fad'in “my Abie ya jiki?”.

Da idanu Abie ya amsa masa da Alhmdllh, sannan yamasa

nuni da ALLAH ya Santa alkairi.

Hannu yasa yarufe fuskarsa alamar jin kunya.

Har aka kammala liyafar cin abincin yana a waje suna hira da parent d'insa, saida papi ya aiko akirasa saboda yanason nunashi wa jama'arsa da basu sanshiba, hakan y

abama wasu daga cikin 'yan masarautar su haushi, sai dai basuda yanda zasuyi da wannan tsohon mai k'arfa-k'arfar tsiya da Nuna Isa.

Bayan ya Yanke call d'in yamik'e yabi bayan d'an Aiken, ya iske a hall d'in kuma papi ya had'a wani video call d'in d

asu Momma, domin Abie yaga d'umbin jama'ar dasuka halarci d'aurin auren gudan jininsa.

Aiko yaji dad'i sosai harma Momma, harda hawayen farin ciki Abie yayi.

Nandai a kaita zuba masa addu'ar Neman lafiya ga mummunar addu'a ga dukkan masu hannu

na shigarsa wannan halin tsawon shekaru, da idanu yake fad'ama Momma magana itakuma tana fad'a musu. Daga nan Galadima yayi jawabin daya ta6a zukatan jama'ar wajen, wasu harda share hawaye, wasu daga cikinsu dasuka San wasu abubuwan daya faru wa tsohon sa

rki Saifudeen kam duk sai zukatansu suka karye, musamman masu hannu aciki dasuka bada gusunmawa, jin addu'a da alwashin d'ansa Muhammad Sameer dake tabbatar da bazai bar duk mai hannu acikiba, sai dai shima amasa irin na mahaifinsa, hakanne kawai zai iya

dakatar dashi.

Abie da Momma Kansu kuka sukeyi daga can suma.

Taron yatashi zukatan wasu cikeda tausayin Galadima da k'udirin taimakonsa, yayinda yasamu k'yaututtuka daga manyan k'asar.

Masu hannu aciki kuwa suntafi da nufin sake shiri

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login