Showing 273001 words to 276000 words out of 407268 words

Chapter 92 - Raina Kama COMPLETE

basu damuba, dan sunsan halinsa Na rashin son hayaniya tuni, ayanzuma suna d'

an ganin canji fiye da shekarun baya, shiyyasa suka fara zargin ko (Hikimar matace take aiki?) Dan kad'an daga aikin mace ta tada gari, kuma kad'an daga aikin ta ta gyarashi.

Sund'an tattauna har baba Rabilu shima ya shigo, wayar dayay recoding d'in

dukkan musayar yawunsa da SD yabasu, babu Wanda baimasa jinjina ba, Galadima ya d'ora da musu godiyar hidimar da sukeyi a kansa tsawon lokaci.

Suka amsa da cewar lallai mahaifinsa ya cancanci sumasa fiyema da hakan, dan yataka rawar gani shima a t

asu rayuwar.



Lokacin da suka fito abinda yabani mamaki shine su Ameer duk salute nasu sukayi suna k'amewa.

Galadima basarwa yay, sai Sir Isa ne yay musu inkiyar su sauke hannayensu, baffi yay murmushi yana kallon Galadima dayak'i kallon

kowa ta gefen ido.

Sarkin mota dai yasha jinin jikinsa, musamman Basarwar da yaga Galadima yayi.

SD dake zaune ya zuba tagumi yana kallonsu kawai ya janye hannunsa, cikin jinjina kai yace, “lallai duniya tana cike da abin tsoro, wai Isa kana n

ufin kaima wani abune a k'asarnan? Kai kuma babban munafuki Brr Usman Audu Tsanyawa! Ba kaine da kanka kaje kasamemu da albishir d'in ajiye aikiba? Ashe wannan k'aramin kwaron d'an cikinku kukema aiki?........”

A tsawace Ameer ya katseshi, tareda

d'aga hannu zai makeshi amma sai Galadima ya d'aga masa hannu.

Sir Isa ne yay wata y'ar dariya yana matsawa ga Darma, yace, “Idan banda abunga Alhaji shehu kowama irin kune mai tsukakken tunani? Ai abin kallo bai k'are makaba saima nan gaba kad'an, k

asan ita mota hanyarta kwaltace, birji ma idan tasamu bitake, balle dagwalon ruwa mai kayan datti, shikam jirgi miye gamisa da wannan? ko d'aga a tashi hanyar babu duk wad'annan, kaga kenan aikwai matuk'ar tazarar banbanci a tsakaninsu, kallon idoma tattan

cewa yake basai an shiga gasar tabbatarwa ba, kaikuma ai taka ta k'are, sauran shekaru sai a prison d'in dajin SAMBISA zaka idasu”.

Dariya SD yayi, ya mik'e tsaye yana fad'in “iyaka dai Ku kaini police station, ina mai muku alwashin kwana d'aya ba

zanyiba a can, daga can a mik'amu Court, alk'alinma namune masu k'ananun basira, yanzu haka nasan sak'ona ya Isa ga y'an uwana, kafinma Ku kaini station d'in reshe ya juye da mujiya, dan dolene a kamaku da alhakin kamani kunga martabar wasu saita zube, mul

kin da akema mutane homa da buri babushi kenan”.

Murmushi Galadima yayi, dan yasan dashi yake, yad'an ta6e bakinsa yana cigaba da latsa waya hankalinsa kwance, Sir Isa da baffi da baba Rabilu, su Ameer duk kallon Galadima sukayi, don suji amsar dazai

bada, amma saiya basar tamkarma baijiba.

Saida ya kammala abinda yakeyi yay kiran Nuren suka kammala magana sannan ya kalli SD yana murmushi, “Wannan lissafin naka fa ya birgeni Alhaji shehu, saidai albishir d'in dazan maka nima shine, duk wani kira

dazakayi ko ayi maka to zai shigo wayatane, yanzu haka driver d'inka yayi had'ari, rashin ganinka a motar kuma zantuka sun baje kowacce kafar yad'a labarai, Na tabbata dukkan labaran rana kaine shafin farko, hakama jaridun gobe masu fita, labarin nemanka

da ta Yaya ka 6ata? Shine babban labari, sukuma abokan naka hakan zai tada hankalinsu, saisu fara zargin ko dai d'an tsohon Sarkine Galadima Sameer da wannan aiki?, dole kuma sufara bincike, bayan sun haukata y'an sanda wajen nemanka, daga haka kaga nikum

a saina cigaba da samun hujjoji........

🤦🏻

kai zaka samin ciwon kai wlhy”. Galadima ya karashe maganar da bud'e mota ya shige abinsa.

Su Ameer duk suka shiga k'yark'yala dariya, saboda yanda Darma ya mugun shiga rud'ani da sakin baki yana bin Ga

ladima da kallo harya shige mota.

basu tsagaitaba saida Sir Isa ya tsaidasu ta hanyar d'aga musu hannu, yace, “Alahaji Shehu yadai? Kaji irin aikin masu basira ko? Kai! Kai! Harna tausaya muku lallai. Ameer! Kubi yalla6ai Galadima dashi, shikeda masa

ukinsa”.

Angama ranka ya dad'e. Suka fad'a suna salute nashi.



🤦🏻

‍♀

lallai nimafa yau nashiga ciwonkan Galadima, shin wane laujene cikin nad'i kuma dabamu saniba haka? Nadai fahimci Su Ameer ba y'an iskan matasa bane, kamarma jami'an tsar

one?

🙆🏽

. To Aunty Salama fa? Data kawosu a cakwakiyar. Masu karatu, kumuje zuwa dai, nasan komai yana gab da bayyana lallai kam.

☹⛹

🏻

‍♀⛹

🏻

‍♀

.

__________________________

Galadima dai kam plaza suka koma, yayinda Nuren ya tari su Ameer a han

ya suka bashi SD.



Acikin Plaza Galadima yad'anyi zagaye-zagaye, saida ya tabbatar da komai dai-dai a wajen ma'aikatan sannan ya fito suka d'auki hanyar masarauta.

*****************

Bayan fitar Galadima Aunty Mimi sashen su M

unaya ta nufa, ta isketa har yanzu tana juya kalaman Galadima dabata fahimtaba.

Bayan sun gaisa tabata Umarnin ta shirya dan za'a kaita sashen manyan gidan ta gaishesu da bangajiya sannan suga yara, inhar zaki tafi wanka bayan kwana d'aya da suna ha

ka akeyi a masarautar, to amma su nasu Munaya yazo da Matsala, tunda gashi sai bayan kwanaki hud'u da suna zasu tafi, matan Sarkine kawai basa zuwa gida wanka.

Kuyangi biyu sukaima Munaya shiri, itadai wannan lamari Na d'aure kanta, haka kawai da

girmanka ace komai sai anmaka, dolene mai mulki yake kallon talaka ba komaiba, sauk'inta ma bakomaine Galadima ke bada fuskar ayi mataba, yama hana hadiman masarautar sakewa a sashensa gaba d'aya, sai iya wad'anda ya aminta dasu kawai.

Yaukam tasha

kallon kanta a mirror, hakan yakuma tabbatar mata da tuna mata agidanfa SARAUTA take, a kuma matsayin matar mutum mai girman rawani da matsayi a Masarautan.

(Kusan dai mutuniyar taku da jan aji

😉

, ai saita kuma tsumewa tana basarwa

🤣

).

S

uma yaran an musu shirin dake nuna lallai Ubansu waninine a wannan masarauta, sannan suma ababen tattaline ga wannan kujera kwara 1 tal dakowa ke mutuwa da rayuwa a kanta a masarautar gagara badau



.

Sun sami rakkiyar kuyangi da Aunty Mimi, kowane sa

she saida suka zagayashi amma a mota, an farane da fada.

Yau itace ranar farko da Munaya ta shiga Fadar sarkin ta, yaukam taga abin mamaki, musalta yanda wannan fada ta k'awatu ai 6ata lokacine kawai, ammafa lallai komai yaji, ga Sarki hakimce bisa

garagarsa cikin kwarjini irinna mutuntakar mulki, sarkinmu kenan kuma sirikinna ta wani fannini, daga ni sai aunty Mimi da kuyangi ukune muka shiga, kowanne d'auke da yaro d'aya a hannu.

Fada cike take mak'il anata fadanci, Su Wanbai da talba duk

ana ciki, hakimai da masu manyan muk'amai Na masarauta da wajen masarauta duk an hallara, kasancewar shine zaman farko Na wannan makon, kuma ana saka ran zuwan Governor ne da zaizoma mai martaba jajen abinda ya faru Na 6atan y'an uku, dan labarine daya zag

aye kowacce kafa ta yad'a labarai da socia media Na k'asar nan, (kunsan dai abin manya duk k'ank'antarsa saiya fita, balle wannan da yazamo mai girma).

Bayan Munaya da aunty Mimi sun zauna a k'asan lallausar darduma can gefe suka kwashi gaisuwa, d

ogarai suka amsa da yawun Sarki, sannan suka kuma gaisheda fadawa.

Daga nanan aka amshi su Abdurrahman, y'an majalissar Sarki sukaita d'auka d'ai-d'ai suna saka musu albarka, da addu'ar fatan alkairi.

Bayan fitowarsu sai sashin iyalan mai marta

ba, yau ma dai gimbiya zulfa bata fasa nunama Munaya da yaranta soyayyaba, daga Munaya har aunty Mimi basu San komaiba, dan haka sukaji dad'i da sakin jikinsu fiye da sauran matan sarki.

Daga nanan sai sashen Mama Fulani, (kaga manya, Sarautar gagara

badau a hannunku take, mama fulaninmu ta mutunci

🤸🏻

‍♀

😂

, ga irin naku manyan mata

👍🏻

)

To kunsan dai mutuniyar taku, yauma dai cikin izzar mulkinta suka isketa, ita dama Aunty Mimi babu ruwanta, tana mata yanda takeso, shiyyasa babu y'ar habaici

ko bak'ar magana tsakaninsu kamar Galadima, hakanne yasaka munaya samun tsira daga samun nata rabon, amma mama Fulani bata d'auki yaro ko d'aya ba, a hannun kuyangin ta gansu tana ta6e baki.

Daga Munaya dai har aunty Mimi babu Wanda yay ko tari, to ba

lle kuyangi dasuka zama takalmin takawarta, basu jimaba suka fito, haka sukaita zuwa sashe-sashe, basu sami Kansu ba saida suka Shiga ko ina .

Sun dawo kusanda awanni biyu aka gama loda kayansu a mota Samha da Sauban suka shige gaba aka kai gidansu Mu

naya. Ita kuma sai zuwa yamma za'a mata rakiya.

************

Gidansu Munaya dai tunda kaya suka isa aka tsaya kallon-kallo, daga Sauban kam har Samha babu Wanda yamusu kallon arzik'i, yo sunaji da hayak'in girma dana mulki, innarsu Munaya da Mun

ubiya da tuni tana gida kawai suka kula, harda sakin jiki dasu sukaita hira, sunmayi zamansu anan sai ankawo Munaya zasu koma.

Nanfa matan gidan suka fara k'ananun magana, saidai babu mai yunk'urin d'aga murya saboda tsaro

🤣

.

Oho innarsu Mun

u ma batasan sunayiba, balle Munubiya da yanzu saita ma gadama suke ganinta, ko yaushe tana d'akinsu, da anyi magana tace jego, dukda gasu Fiddausi a gidan duk suna wankan suma, Fauziyyace kan shigo susha hirarsu ta zuminci, amma sauran saidai idan an had'

u a gaisa, kowa uwarsa Na kitsa masa munafurci a d'aki (

🤦🏻

‍♀

gaskiya iyaye mata munada gyara babba ta wannan fannin, inhar zaka rayu gidan yawa sai kayi gamo da irin wad'annan matsalolin kuwa, ALLAH ya ganar damu baki d'aya dai).



****************

**

Su gadima Na shigowa masarauta ana kiran salla, hakanne ya sakasu yada zango a massalaci, saida aka idar sannan suka k'arasa sashensa, Duk agajiye yake, d'akinsa daret ya nufa, yashiga zame kayansa tun a falonsa, yana shiga ciki k'arasawa kawai y

ayi yashige bayi.

Ya dad'e aciki kafin ya fito, baiko cire rigar wankanba yasha wani Magani ya kwanta, dan kansa ciwo yake masa. Cikin mintuna k'alilan barci yay gaba dashi.

Munaya batasan ya dawoba, d'okin zuwa gida ya hanata barcin ranarma it

a, sai yawan duba lokaci takeyi

😂👍🏻

.

*_3:35pm_* Galadima ya tashi, saboda kiran wayarsa da akayi, idonsa a lumahe ya d'aga, a haka suka gaisa da Momma, ya tambayi Abie tace barci yakeyi, sunyi wayar kusan mintuna 15 haryaso makara fita sallar la'asa

r.

Bayan yadawoma papi ya kira suka tattauna, sannan yakuma sabon shiri cikin Orange d'in yadi anmasa kwalliyar bak'i kad'an, yayi k'yau sosai, sai tashin k'amshi yakeyi, saidai fusakar kam babu alamun yasan miye dariya.

A haka ya iso sashen

Munaya, babu kowa daga ita sai yaranta da Khaleel dake barci a gefensu, itako wayama take latsawa, da alama game takeyi Kodai wani Abu.

Sallamarsa ciki-ciki da k'amshin turarensa ya sakata d'ago ido suka kalli juna, yawani Basar yana shan k'amshi,

hakanne yasaka Munaya sake kama kanta, ta gaisheshi, sau d'aya ya amsa ya zauna a bakin gadon yana shafa kan yaran d'ai-d'ai harda Khaleel.

Handbag d'inta da mayafi dake ajiye alamar lokaci take jira kawai ya kalla, baki ya ta6e ya d'auke kai.



Key d'in mota guda biyu ya fiddo a aljihu ya jefa min akan cinya.

Ni harma Na tsorata na kalli keys d'in sannan Na d'ago na kallesa.

d'auke Kansa yay daga inda nake, cike da k'asaitarnan tasa yace, bak'in kibama Abba, d'ayan kuma ki ajiye a w

ajenki, motar tana can, saboda ko wani abu yataso musamman kai yara asibiti sai wani ya kaiki cikin yayyenki, ki kulamin da yara, kuskure d'aya kikayi a kansu zand'au mataki mai tsaurine, duk abinda zuciyarki batayi na'am dashiba ki gaggauta kirana na sani

, ki kula da Abdurraheem sosai, banda barinsa yana dogon kuka saboda doctor ya sanar mana yana d'auke da ciwon......”.

Saikuma yay shiru yana furzar da iskar bakinsa.

Masifar tsura masa ido nayi zuciyata Na bugu tamkar zata fad'o dan tsoro, s

ai tsuma nakeyi, babu shiri na taso na dawo inda yake, durk'ushewa nayi gabansa tamkar mai neman gafara, “Yalla6ai ciwon mi? Please ka k'arasa fad'an dan ALLAH”.

lumshe idanunsa yayi yana cizar lips, “Ba abin tada hankali baneba ai, domin ALLAH daya

d'ora mana yafimu sanin hikimar hakan, bagashi ni nakai lokacin da Magauta basuyi tunaniba”.

Maganganunsa ya nuna minta cewar Abduraheem Na d'auke da Ciwon zuciya? kenan shima yayo gadon mahaifinsa?”.

Matsowa nayi na fad'a jikinsa na sanya ku

ka, bashida za6i saina kar6ata shima ya rungumeni cikin yima Ubangiji tasbihin Neman dauriya da kar6ar jarabawa a duk yanda tazo. Bai hanani kukanba saida nayi mai isarta sannan na share hawayenna. d'agowa nayi daga jikinsa zan tashi amma saiya hanani haka

n, cikin kunnenna yace, “Baki da kunya gaskiya, ban ta6a ganin uwa mara kawaici akan y'ay'an fariba saike”.

Kunyace ta kamani, na 6oye kaina a jikinsa ina murmushi.

Galadima ma murmushin yake yana shafa bayanta.

Sun dad'e a haka sanna

n na tashi daga jikin nasa gudun kar khalel ya farka ya ganmu a haka, shima ya fahimceni, dan haka bai hanani ba.

Yace, “Addu'arki yake buk'ata da taka tsantsan, dukda ba wayonmune zai hana Ubangiji ikonsa ba idan yaso, sai yakai watanni 6 zai fara

ganin doctor insha ALLAH, ya mik'a mamin ATM d'insa, ga wannan dukdai abinda yataso saiki cira, amma a bimin kud'i a sannu ni talakane mai yawan buk'atu, ga Abdurraheem ya k'aru shima, to idan bawa bai nema kud'iba ai yagama shiga uku a wannan zamanin daba

kowa ya damu da damuwarka ba, inadai kuma gargad'inki ki kula min da yara, yau zamu koma India, amma kwanaki uku zanyi insha ALLAH na dawo”.

Nace, “ALLAH yabashi lafiya da dukkan al'ummar ANNABI, nagode sosai, saidai kuma inason kawai idan na ta

fi shi.......”

Hannu ya d'aga min, “karki damu nasan maganar Aurenmu ne, kamar yanda na alk'awarin inhar komai ya fito kan shekara zamu rabu, inkuma ba a samu yanda akesoba shekara biyu inakan Sani, sauran bayani kibani lokaci zuwa kammala abinda ke

gabana OK?”. ‘yay maganar yana kallonna’.

Kaina kawai na d'aga masa ina had'iye abinda ya tokare mak'oshinna.

Bai sake cewa komaiba ya mik'e yana kallon agogon hannunsa bak'i, “ku fito”. yafad'a yana ficewarsa.

Da kallo kawai nabisa idonna

yana cika da k'wallan dabasan na minene ba.

**************

Munaya tasamu rakkiyar wasu daga masarautar, bisaga jagorancin Galadima da suke zaune a mota d'aya, daga ita har shi babu Wanda ya tankama wani koya kalli wani, shi tundama suka fito

latse-latsen System yakeyi hankalinsa kwance, itama ta basar gefe tana kallon waje dukda glass d'in mai duhune.

Sun Isa k'ofar gidan k'arfe 5:24pm, bayan su Aunty Mimi sun fita duk suka shige cikin gidan tareda Kuyangi.

Munaya tayi yunk

'urin fita amma sai taji motar a kulle, Sarkin Mota ta kalla sai taga harya fice, ta dawo da kallonta ga Galadima daketa aikinsa tamkar ya manta a mota yake.

Shareshi nayi kamar nima bazanyi magana ba kamar yanda ya basar, amma saina kasa, na kuma

kallonsa murya a sanyaye nace, “ka bud'emin mana, miye ma'anar zaman namu? Wanima saiya zargi wani Abu ai?”.

Banza yay mani tamkar bazai tankaba, kusan mintuna biyu sannan yace, “idan sun zarga laifine? Naga Sadaki na biya”.

“Hummm”. Munaya t

a fad'a kawai tana d'auke kai.

Saida ya gama shan k'amshinsa sannan ya ajiye lap-top d'in gaban motar yana matsoni. da mamaki na kallesa, “yalla6ai lafiya?”.

“ita ta kawo haka”. ‘yafad'a yana wani ciccijewa da jawoni jikinsa’.

Tamkar z

an tsala kuka haka naji, dan naji zafi, mukaima juna kallon ido cikin ido, idona da kwalla tafara taruwa sai wani marmar yakeyi, matso da fuskarta yay sosai, cikin magana rad'a yace, “kin fara kewata ne?”.

Baya naja

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login