Showing 105001 words to 108000 words out of 407268 words
/>
“mikenan?”.
“Saka miki desire tabs dakikace, kiduba
yanda kikace yadamu sosai, Munaya kofa saka mikin yayi babu laifi, tunda hakinsane, sadaki yabiya ya aureki, inma banda wautarki koda auren Contract d'inne kukayi ai ba'a fatar sakin ko. atunaninki innarmu wane tashin hankali zata shiga idan ance aurenki
ya mutu cikin kwanaki 5 kawai da arenmu, ni yanzun shawarar dazan baki ki kwantar da hankalinki kuje India d'in, ki duba mahaifinsa, saikiga tarbar da parent nasa zasu miki, daga nan samu san mafita, idan sakin zaki nema kinga saiku rabu, idan kuma zaki iy
a zama da shine shikenan, saimuyita addu'ar ALLAH ya dasa masa sonki a zuciya”.
“Humm, Munubiya kenan, kinga kuwa tashin hankalin danake ganowa a masarautarsun nan, wlhy akwai babban lauje cikin nad'ifa, bazan iya wannan rayuwarba gaskiya, dan tan
ada wahalar gaske, shi kansa ba ta6a sona zaiyiba, dan tun farko dawata manufa ya aureni ai”.
Murmushi Munubiya tayi mai sauti, tace “amma ke kina sonshi?”.
“ALLAH ya kiyaye, ni wlhy bana sonsa, kuma ban tunanin zansoshi ko anan gaba”.
Dariya Munubiya tayi, harda kwantawa a gado, cikin dariyar take fad'in “to badai asan maci tuwoba sai miya ta k'are, kika sanima kona samu baby's d'ina a jiyan”.
Kwafa nayi kawai, nace can dai a bakinki, kedai mukema fatan ALLAH yasa mun samu,
ki shirya min kayan dad'i gobefa zanzo kinji Sweetheart ”.
“karki damu habibati, a gaidamun Galadima ango”. tayi maganar cikeda tsokana.
Aiko sai Munaya ta saka mata kuka.
Dariya ta tuk'e Munubiya tayanke wayar tana mamakin yanda Mun
aya tayi sanyi, dawuya Munaya kaga ta zauna yima Abu kuka, koyafi k'arfinta tanada jimirin wahala, lallai Galadima baije da wasaba ashe.
😆👁
Koda tayi sallar isha'i saida ta saka 'Yar uwarta a addu'a, fatanta wannan auren ko igiya d'aya karta sam
u rauni barema akai ga saki. ta d'au alk'awarin cigaba da sakata a addu'a a kowacce sallarta.
Nima ina ajiye wayar tashi nayi nayo alwala nayi sallar isha'i d'in.
Kallon hotuna na zauna yi awayarsa, duk kusan ma bawasu pictures bane na
azo agani, daga hoton wayoyin salula sai na kamar kayan waya Daba a had'aba da computers, mamaki ya kamani, saikace mai k'era waya?, nidai gajiya ma nayi na ajiye wayar, har barci ya kwasheni ban kuma jin labarin Galadima ba.
Shikam tunda
yabaro wajen mai martaba suka fita shida sarkin mota, birnin gayu plaza yaje, yayi wasu 'yan abubuwa sannan ya gana da ma'aikatan wajen. Sai kusan around 11 ya dawo gidan, ko sashena bai kallaba ya shige d'akinsa, abinda duk zai buk'ata yad'an harhad'a, ya
kira Wanda zai kira awaya akan wasu harkokinsa sannan yay shirin barci ya kwanta..
Washe gari da asuba ko tadani bai zoba kamar jiya, ALLAH yasama nariga da na saba da tashi sallar tun a gidan mu, dan haka akan lokacin na tashi nayi kayana. barci na
kuma komawa, ban tashiba sai 9am.
Wanka nafarayi, ina tsaka da shafa mai yashigo da sallama ciki-ciki, na zawo hijjab da sauri na saka.
Bakinsa ya ta6e yana kauda kai gefe. “ki shirya zamu fita”. ya juya ya fita.
Da kallo na bishi ina g
irgiza kai, oh ni, saikace anmasa dole sai yayi maganar?.
Dukda bansan inda zamuba saina d'okantu da fitar, kobabu komai nasha iska ai, danni gidannan jinsa nake tamkar wata duniya daban ba duniyarmu ta mutaneba, yo komaifa gidan akwaishi, makaranta
ne asibiti k'aramine, wajen wasan yarane, babufa yanda zaka fita waje inba doleba, musammamn ma mu matan aure, garama mazan da masu fita karatu kuma.
Shiri nayi cikin zani da Riga na atanfa, sunmin kau sosai, danni fa saima naga kamar fatata ta
wani d'an murje hakannan
👁
..
A falona na iskesa zaune, muka had'a ido kowa ya janye nasa cikeda basarwa, saida yagama k'asaitarsa da mulki sannan yatashi, sanye yake cikin milk d'in shadda datasha ainahin aikin masu sarauta, takalmansa ma hakan
ne, sai fidda k'amshin turarensa mai narkar da mutane yakeyi, sajennann ya kwanta luf bisa face nashi, hular na hannunsa bai sakaba.
Gaba yayi nabisa abaya ina takuna d'ai-d'ai, takalmana masu sauk'in tsini sai bada sautin kwas-kwas sukeyi.
Mun tarar da motocin dazamu fita dasu a shirye guda 3, an wankesu sai d'aukar idanu sukeyi, gaisuwar da hadiman gidan suke mana muketa kar6awa, nikam banason abunnan wlhy, amma shi ko'a jikinsa.
Bud'e mana motar akayi muka shiga, nida shi muna
baya, sai sarkin mota agaba, yayinda mota biyun kuma dogarai suka shiga.
Babu Wanda yay magana tunda muka fita, nidai kawai kallon hanya nakeyi da mamakin ina muka dosa?, mun Isa immigration office Ashe passport za'amin, abinka da manya, cikin 1h
our aka kammala min komai. Bamu bar office d'inba saida harun yazo ya kar6i passport d'in domin nema min visa, daga nan muka fito.
wani dad'ine ya rufeni danaga mun doshi hanyar gidan mu, shi kansa ya hango farin cikin dake shinfid'e a face d'ina,
ya janye idonsa daga kallona ya maida kan kallon mutanen anguwar daketa hada-hadarsu hankali kwance.
A dai-dai k'ofar gidanmu motocin suka paka, da hanzari na nemi 6alle murfin zan fita.
Caraf ya damk'e hannuna, juyowa nayi ina kallonsa tam
kar zanyi kuka, idonsa a lumshe yake tamkar ma baisan miyayiba.
“dan ALLAH ka sakar min hannu naje”. ‘nayi maganar tamkar zanyi kuka’.
Banza yamin, saida yamula dan kamsa sannan yabud'e idonsa a kaina yana hararata, “ki nutsufa, ko an fad'a m
iki haka akeyi?”.
Baki na tunzuro gaba.
Ya janye idonsa daga kallona yana kuma matse hannuna cikin nasa.
Ni ban saniba Ashe wai dole sai an nema masa ison shiga gidan namu, sarkin mota dai tuni yafita dama.
'Yan anguwarmu suny
i cirko-cirko suna kallon motocin, jira kawai suke suga Wanda zai fito aciki, dukda sunga masu jajayen riguna a tsaitsaye, alamar daga masarauta ne.
Muna a haka saiga yaa hameed yafito daga cikin gidanmu dad'an hanzarinsa, inaga yazo gaidasune, dan
kullum Safiya duk sai sunzo shidasu yaa Shafi'u.
Jikin motar damuke ya k'araso, sarkin k'ofa yay knocking d'in glass d'in 6angaren Galadima. duk da yasan yana kallonsu shi.
Sauke glass d'in yayi a hankali, sannan yama sarkin k'ofa nuni
daya bud'esa, har yanzu hannuna yana cikin nasa kuma. Ya d'auki hularsa ya saka.
Cikeda fara'a Yaa Hameed yake masa barka da zuwa, sai lokacin ya saki hannuna, sannan yazura k'afarsa d'aya yafito, nima dogari d'aya yazagayo da sauri yabud'emin, n
a fito, handbag d'in hannuna dogarin ya kar6a yana zubomin kirari.
Kallofa Yakoma sama ga 'yan anguwarmu, kowa sai kallona yake yana fad'in ashe munaya Ce, kai masha ALLAH, kugafa auren sati d'aya harta canja kamanni, lallai sarauta dad'i.
In
da yaa Hameed da Galadima suke na zagayo, suna rik'e da hannun juna sunyi musabaha, fuskar yaa Hameed a washe, yayinda ta Galadima ke d'ukeda wani munafukin murmushi.
Cikin murna nace “yaa Hameed I miss u”.
“miss u too Darling sister. bism
illa ranka ya dad'e kumuje ciki to”.
Atare muka shiga ciki, ina gaba suna bina a baya shida yaa Hameed.
Matan gidanmu kowacce na mak'ale jikin window d'inta tanason ganin Galadima, yayinda Aryaan da Aiyaan suka shek'o da gudu kaina, ganin
haka suma sauran yaran sai suka shek'o, duk na tarbesu cikeda farinciki da kewa.
Ni nama manta dawani Galadima muke tare, Ashe shi yanata kallonmu cikeda sha'awa.
yaa Hameed yamasa jagora zuwa falon Dady.
Nikam ai d'akin Innarmu sha, ta
reda gayyar 'yan tarbata.
A zaune na iske innarmu tana ninke kayan su Aryaan, da alama wankewa tayi, sai tausayinta ya kamani, yanzufa kowanne aiki dole itace zatakeyi, babu mai tayata, jikinta na fad'a ina hawaye.
Itakam tace “kajimin ja'ir
ar yarinya, to miye abin kukan kuma? wai nikam yaushe kika lalace da sauri kuka haka Munaya?”.
“innarmu kewarku cefa wlhy”. nashiga gaidata, cikeda farincikin yanda na koma a kwana 6 kacal take amsamin, sai jero hamdala take a zuciyarta.
Zainab k'anwar Fauziyya tashigo d'auke da tire an d'oro zo6o da ruwa akai.
“inyee, kaga su zee anzama 'yan matafa, kace bad'i sai aure kenan?”.
Fuskarta ta rufe tana fad'in kai Aunty kibari please, innarmu kice ta daina”.
Innarmu
dariya take mana itakam, saiga Rahma itama tashigo, saiga Ameenatu da Khadija ma, lallai bad'ima Ashe zamu aurar da yawa, a kwana ki 6 d'innan sainaga yaran duk sunmin girma a ido. Nasha mamakin su na zuwa gaisheni, dan bansa akaba nikam, araina nace ko ja
ma'ar gidanmu dun fara canja haline dai?.
Muna haka saiga innaro tamkar an jehota, kowa ido ya zuba mata, dan shigowa tayi tana masifar wai bamu fara shiga gidan taba nida Galadima.
Na kalleta a d'age ina ta6e baki, “yo banda abinki innaro
ai sai nafara ganin Uwata, dan banida kamarta kaf duniya”.
Ha6a tarik'e tana kallona “eh lallai kam, yo ai Dama ke halin uwarki gareki, ba mutuncine dakeba, ballan tana yanzun kuma ido yak'ara fetsarewa ansan komai na aure”.
Zan maida mata m
urtani innarmu ta harareni, shiru nayi na k'yaleta badan nasoba.
Shima Galadima yana falon Dady yasamu tarbar mutunci daga maman Fauziyya, dan matan gidanmu babu wadda ta aika masa dako ruwa, yaji dad'in tarbar daya samu kuwa, musamman yanda su A
bba suka nuna masa tamkar d'ansu, baiyi dubi da sarautar dake kansaba ya duk'a har k'asa yakwashi gaisuwa wajen iyayena uku.
Hakan yamusu dad'i, domin ya mutuntasu, kuma sun kuma tabbatarwa shid'in mai tarbiyyane.
Anan yamusu bayanin munzo m
usu sallama ne zamu tafi India.
Fatan alkairi su abbanmu sukai mana da k'yak'k'yawar addu'a, daga nan sukad'an ta6a hira dashi, dukda yana nonnok'ewa saboda kunya irin ta jinin hausa Fulani.
Nikam can innarmu ta iza k'eyata nashiga kowanne d'
aki na gaidasu, sai kallon k'urulla suke bina dashi, anason ganin wata makusa a jikina, amma sai basuganiba kuwa, komai sai sambarka. Aikam bak'in ciki tamkar ya karsu, kowa hassada nacin zuciyarsu (kai jama'a ALLAH yarabamu da cutar hassada komai k'ank'ar
tatta
😢🙏🏻
)
Na dad'e d'akin maman Fauziyya sosai, dan acanma naci abinda tad'an girka mana mara nauyi, yaa Hameed yazo ya d'auki na Galadima da kansa.
Sashenmu na dawo inatama innarmu shagwa6a, duk nabi na nanik'e mata, dukda tureni datakeyi
. Nashiga tsohon d'akinmu harda kukana, komai nanan yanda yake, harma dawasu 'yan tarkacenmu daba a gama badawa ba, haka
kawai bamu mutuba d'akinmu Yakoma kango, anan na d'akko cajata da wayar Galadima daya barmin a filin idi, sai wad'ansu 'yan abubuwa dan
ake buk'ata.
Na fito ina tambayar innarmu waye ya d'auki wani hotonmu dake saman mirror nida Munaya?, tacemin maybe Ameeran inna lami Ce ko Bilkisu, dan taji suna rigima akan d'aukar Horton.
Shigowar Galadima da yaa Hameed tasaka innarmu y
in shiru, nikam ban daina daddaga k'afa k'asaba ina k'unk'unin miyasa tabari suka d'auka?.
Galadima dake k'ok'arin zama yad'ago ido yad'an kalleni sannan ya janye.
Yaa Hameed ne yace kekuma lafiya?.
Fad'a masa nayi tamkar zanyi kuka, ya
ce “to kuka zakiyi?”.
“ALLAH yaa Hameed inason hotonfa”.
“ai saiki hak'ura yanzun tunda sun d'auka ko?”.
Innarmu da Galadima dai gaisuwa sukeyi, babu Wanda ya tanka mani. shi saima mamakin ta6arar danakeyi yake a zuciyarsa.
Nika
m bansan yana yiba.
Sosai yaji innarmu ta burgesa, yakula ko kad'an ba halinta nabiyoba, dan ita tanada sanyi, dagani batada hayaniya, amma nikam ai sai addu'a.
Yad'an jima anan dukda ba hira sukeba, kowa kunya na cinsa, a raina nace dama y
anda kunya guy d'inan ashe?.
Alkairi mai yawa ya ajiyema innarmu, dawata leda da yaa Hameed yabiyosa da ita, sannan yafita innarmu na saka masa albarka yana amsawa cikeda jin dad'i, jinta yake tamkar Momma d'insa.
Daga nan saida yashiga k
owanne d'aki, sannan yaa Hameed ya rakashi gidan innaro.
Abba ne yashigo yana fad'in a tattaro lefena muwuce da kayanmu.
Na marairaice fuska nace Abba abarsu anan, kagaba tafiya zamuyi can d'in babu kowa.
“a'a Munaya bazai yuwuba, idan
mun ajiyesu anan mizamuyi dasu?, kitafi da kayanki, duk randa dai kuka dawo suna d'akinki ai.
Badan nasoba na amince, amma naje wajen kayan ina fitar da wasu, ni saima yau naga lefen, gaskiya su Galadima sun zuba kud'i a wajennan.
Duk matan gid
anmu atanfofi na fidda musu, maman fauziyya kam guda biyu, sannan yaran gidanmu 'yan matan yanzu kowa nafidda masa wani abun, su Aryaan ma dukda mazane kowa na fidda masa abinda zai iya amfani dashi.
Sai su Ayusher da inna lami da Ameera, Bilkeesu ma
da nata, hakama mama rabia, na ware akwati guda na lodama Munubiya kaya sosai aciki, aunty salamah ma da nata, sai gwaggo Safiyya da yaranta mata, itama innaro jarabatu na fidda mata, su Abbanmu ne dai narasa mizan basu aciki.
Innarmu na kira taga
ni, ta kalleni tana fad'in “munaya bazasuga an kwashe kayanba?”.
“a'a wlhy innarmu bazasu ganiba, kowafa da sashensa a gidan, kuma babu mai shiga harkar wani, idan na barsu mizanyi dasu? Kayan sunmin yawa ai”.
“to shikenan, ALLAH ya saka da
alkairi”.
Na amsa da ameen ina fad'in “ganaku nan keda su Aiyaan innarmu”.
“a'a ni bazan d'auki komaiba, bakiga yama kawomin abuba, ga kud'i dama bansan ko nawa bane”.
Kuka na Sanya mata akan saita kar6a, babu yanda ta iya ta amsa, amma s
aida tarage. Sai dai tana fita na maida mata harda k'arima.
Zainab Ce ta kaima kowa nasa, kowacce rai babu dad'i ta amsa, sotayi ace daga 'ya'yantane wannan abun arzik'in yafito bawai innarmu ba, (basusan shi Ubangiji babu ruwansaba, yakan azurt
a Wanda yaso Yakuma k'ask'antar da Wanda yaso a lokacin dayaso).
Babu wadda tazo godiya sai maman fauziyya, nace “oho dai, aikin banza wai talaka ya girmi sarki
🤷🏻
♀
”.
Banyi maganar su d'auki motarba, dan sonake nasami cikon d'ayar nabasu
su duka ukun.
Nima naje na gaida innaro, dasu Abbanmu, naje gidan innaro lokacin su Galadima harsun fito,, na iske Ashe gwaggo Safiyya tama koma jiya, sai d'iyarta Habiba datake zawarci aka bari anan.
Munsha hira da ita, tanata yaba k'yan da n
ayi.
Innaro kam dukda jana datake ajiki sai basar da ita nakeyi, amma hakan bai hanata yaba Galadima ba, catake wai na more miji, nafi kowa morewa a gidanmu.
Nidai banda ta6e mata baki da bak'ar magana babu abinda nakeyi, bata