Showing 21001 words to 24000 words out of 407268 words
da dai bawani sake masa nayiba ya burgeni.
Su Ayusher sunata tsokanata, nidai ban kula suba.
Washe gari da safe kuwa
saida abin yazama fad'a, wai ankama wasu suna gulma akan rashin zuwan sauran anguna, kuma dangin momy Hadiza ne, aikam sosai aka zuba rikici, har saida abbanmu ya tsawatar.
Aranar aka shirya kai amare, dole sai dai a rarrabu, tun la'asar aka fara kaw
o motoci, baba k'aramine yabada shawarar ahad'a tafiyar kawai gaba d'aya, su aunty Hauwa'u suma su siyama rakiya, sannan suma haka.
Haka kuwa yayima wasu iyayenmu mata dad'i, dan kobabu komai saji yanda gidan kowacce ya kasance.
mun fara kai su
Siyama da Zarah, wad'anda babu alamun kuka a idanunsu, gidajensu jere da juna, sunyi k'yau masha ALLAH, kayan gado dai duksu Abba sukayi, kuma kud'insu d'aya, saidai kowa da za6insa, kayan kitchen ne kowa uwarsa tayi da sauran tarkace, ananne kowa ya ware
ido dan aga kwazon uwar mutum, nidai agareni babu makusa, gidansu Zarah duk yayi.
Mun ajiyesu tareda k'awayensu, mukuma muka tafi kai sauran.
Daga Nan sai gidan aunty Rahaima, itama masha ALLAHU wlhy, saidai mak'iyi, gidanta yayi k'yau, sai da
i tanada kishiya.
Saikuma gidan aunty khaleesa, itama dai d'in zamm zamm wlhy, daga nan sai aunty Ramlah, wlhy itama yayi d'as, itama tanada kishiya. Aunty Hauwa'u ce k'arshe dan itace babba, itama gidanta yayi k'yau sosai.
Nidai aganina babu
wadda mahaifiyarta batayi k'ok'ari ba wlhy, amma hakan bai hana sauran gumtso gulmarmakiba aka taho da ita.
Kasancewar duk babu Inda muka zauna aka taho gida da wuri, harzamu wuce Fu'aad daya d'akkomu yace bari yashiga Birnin gayu plaza damu.
Nace a'a muwuce gida kawai, kar aga kowa yadawo mu bandamu, gashi lokacin har 8:30pm ya wuce.
Ayusher ce tace indai bazamu dad'eba ashiga, saimuce muna gidajen su siyama mu, mun zauna jiran anguna.
Kamar dai nace a'a amma nayi shiru, sabo
da naji munubiya da feena suma sun bada goyon bayan mu Shiga, sannan Fu'aad yace bazamu dad'eba.
Ya kalleni murya k'asa-k'asa yace, “ginbiya bakice komaiba?”.
Murya a sanyaye nace, “indai bazamu wuce 1hour ba muje”.
“insha ALLAHU my luv ba
zama mu kaiba”.
A kasalance Na d'aga masa kai saboda agajiye make ti6is.
Haka yashiga wajen nidai zuciyata Na dukan uku-uku daban San Na miyeba.
Munshiga cikin plaza d'in, bansan takamaimai miyasa Fu'aad yace mushigo wajenba, tu
nda dai bawani abin ci ake saidawa a wajenba.
Mun shiga 6angaren kayan kwalliya, yace kowa yaza6i abinda yakeso.
Nidai nace masa a'a mun Gode.
6ata fuska yayi yana hararata, ya maida kallonsa gasu munubiya dake tsaye “please dan ALLAH karku
biye mata, kuje Ku d'auka”.
Badan suma sunasoba suka amsa da to.
Ya kalleni yana fad'in “mujeto ni na d'ebar miki”. bance masa komaiba nabi bayansa ganin kamar yayi fushi, wayarsa aka kira, ya zaro daga aljihu, saida yad'an saci kallona yaga h
ankalina baya kansa sannan ya d'aga, murya k'asa-k'asa tamkar mai gulma yace, “nagama aikina”.
Dawowa yayi wajena bayan ya katse wayar, da kansa yake za6ar mini duk abinda yadace.
Su munubiya ma sunacan suna d'auka, kamar ance munubiya ta
bar wajen saita zagaya tabaya, a dai-dai wannan lokacinne shikuma yake tunkarowa shida wasu matasan samari guda biyu, da alama yana zagayene kowani abun daban. tafiya yake cikeda nutsuwa da sarauta, sai sautin takunsa dakakeji, tunkan su iso gareta k'amsh
in turarensa ya iso.
Waige-waige munubiya tafara, tanason tuno mai wannan k'amshin. bata ankaraba saijinta tayi tatafi suuuu santsi ya kwasheta.
Shi mutumne mai yawan tausayi da taimako, da sauri yayo kanta kafin taje k'asan, Dan yasan fad'uwart
a a wajen babban had'arine, yakai hannu zai rik'eta itakuma ALLAH yabata ikon dafe wasu tarin baskets dake wajen. Cikin runtse ido da sauke ajiyar zuciya ta furta “Alhmdllh”.
Janyewa yayi daga rankwatowar dayay kanta tamkar zai rungumeta, batareda ya
ce uffanba yafar wajen.
Muduka akan idonmu komai ya faru, wad'anda suke tare dashine sukaima munubiya sannu, mukuma muka k'araso da sauri gareta muna tanbayarta babudai wata damuwa ko?.
“babu komai Alhmdllh”. ‘tafad'a tana gyara tsayuwarta’.
Nace, “kunga kuzo mu tafi hakanan, wlhy inajin tsoron agane bama gidansu siyama”.
Duk suka amsa da gsky mu tafi, da k'yar muka yarda mukaje wajen biyan kud'in. yabiya sannan muka tafi.
ALLAH ya taimakemu ba'a mana fad'aba.
Duk cikinm
u babu Wanda yakuma maida hankali akan abinda yafaru a birnin gayu plaza, saidai abin yakasa barin raina, kamar zuciyata tana cikin fargaba, amma bansan ta miyeba, ita kanta Munubiya wani sukuku nake ganinta, bandai tanbayeta ba Na share.
Washe gari
Monday, muka tashi da shirin makaranta, saida muka gama gyara gidan tsaf sannan muka tafi harsu Ayusher, dayake lectures d'inmu Na yau sai 1:30pm ne. yauma sauran 'yan uwanmu bakowa yaje school d'inba ma har fauziyya.
Tun muna tsaye abakin titi muna
jiran taxi naga wasu tsirarun mutane nabinmu da kallo. ban kawo komai arainaba muka samu taxi.
Driver ma yana tuk'i yana kallonmu ta madubi, sainaga kuma ya kalli takardar dake saman cinyarsa. d'an fara tsarguwa nayi, amma saina dake ina zaton irin d
irobobin nanne masu shegen kallon tsiya.
Da muka sauka cikin makaranta ma bata sauya zaniba, kallonmu akeyi har ana nunamu, wasu da jaridu a hannu wasu kuma waya.
Munubiya tace, “Manaya bakiga abinda ke faruwaba tundaga fitowarmu gida zuwa
nan ne?”.
“nagani wlhy Munubiya, bansan miyakawo wannan kallon k'urilla d'inba, dama bakiga kallon da direban can yake manaba ni da ke harya saukemu, ko sanda muke sallama dasu Ayusher idonsa Na kanmu kyam kuma yana kallon wata jarida dake cinyars
a”.
Muduka kallon jikin junanmu mukeyi, babu wanda shigarsa tazama aibu acikinmu, sannan bama tareda wani abin kallo,
Hannun juna muka kama muka cigaba da tafiya cikin tsantseni da nazartar kallonda 'yan uwanmu d'alibai suke mana.
Tund
a muka shigo cikin class sai duk aka zubo mana idanu, kuma anata k'us-k'us. yanzu kam hankalinmu yatashi sosai, wai mike faruwane? saikace yau mutane suka fara ganinmu? shin yaune muka fara shigowa makaranta?.
Bamu da mai bamu amsar tanbayarmu, muka n
ufi Bilkisu dake zaune itama tazubo mana idanu, ga jarida agabanta, kamar yanda muka gani wajen sauran 'yan department d'inmu, wasu narik'e da jaridu wasu wayoyi, sunyi group group kuma suna k'us-k'us.
Da sauri Na k'arasa zan d'auki jaridar gaban Bilk
isu amma saitayi saurin d'aukewa............
✍
🏼
Babbar magana, shin mike faruwane? kallonmi jama'a kema su Munubiya? Sannan mi ake kallo a jikin jaridar da wayoyin kuma?
🤦🏻
♀
.
Nasan masu karatu ma wannan amsar suke son sani
🤔
*_ALLA
H ka gafartama iyayenmu_*
😭👏🏻
[4/16, 9:53 AM] +234 811 277 0720: *_Typing
📲
_*
*_HASKE WRITERS ASSO...
💡
_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_
♦
RAINA KAMA......!!
♦
_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce
🤙🏻
_*
👉🏻
9
⃣
.......K'yaleta nayi najuya sit d'in bayanmu Na fusge ta hannun wani guy, rubutun farko dage jikin jaridar a shafin farko na tsirama idanu.
*_BABBAR MAGANA, GALADIMA SAMEER RUNGUME DA MATASHIYAR BUDURWA A PL
AZA 'DINSA SUNA SUMBATAR JUNA!!_*
sai kuma hoton dake k'asan rubutun shima har kala biyu, Na farko abinda yafarune na fad'uwar Munubiya a birnin gayu plaza, har Galadima yay yink'urin taimakonta amma tadafe baskets ko ta6ata ma baikai gayiba, amma
abin mamaki da al'ajabi a hoton galadima ya rungume munubiya ne bakinsa akan nata.
Hoto nabiyu kuma ni da shi ne afilin idi lokacin damukayi karo har wayarsa ta fad'i, ko kad'an bai ta6aniba, ko waya daya kar6a a hannuna hannuna danashi basu had'uba,
amma anan an nuna hoton yana rik'e da hannuna duka biyu muna kallon juna.
“Innalillahi” nafara maimaita jikina har yana rawa, gawata uwar jufa data fara jik'a sassan jikina, lallai dolene duk inda muka gitta abimu da kallo.
Ju yowa nayi na kal
lo munubiya dake tsaye a bayana, itakam hawayema takeyi.
Jikina a sanyaye nakama hannuta muka fita daga cikin hall d'in, kallon da ake Manama ayanzu yafi na d'azun, Dan labarin sai kuma yad'uwa yakeyi yanzun.
Muna fitowa muka samu taxi sai gida.
Tunda muka sauka naga wasu gungun samarin dake layinmu a majalissarsu sun zubo mana idanu gaba d'aya, tuni zuciyata tafara tsitstsinkewa, kenan labarin harya iso nan?. Dagani har Munubiya jamukai muka tsaya, saboda ganin dukkan ahalin gidanmu tsaye c
irko-cirko a tsakar gida, hardasu yaa hameed anguna, ga bak'i dabasu gama tafiyaba, innarmu kwance akan tabarma maman fauziyya namata fifita, ga Abbanmu kusada ita tsugunne yana shafa mata ruwa.
Jaridar dake hannun baba k'arami mukabi da kallo, bans
an sanda wani kuka yatahominba nima, sa6anin da munubiya kawai keyin kukan.
Da gudu mukayi kan innarmu, amma sai yaa hameed ya daka mana tsawa, “karku sake Ku ta6ata wlhy, idan bahakaba jikinku kuwa saiya fad'a muku”.
Babu shiri mukaja burki, a
mma sai muka durk'ushe ak'asa muka fashe da kuka.
Innro tace, “kwayi kuka kuwa munafukai, ahiyyasa ai ANNABI yace a auri mace tagari, Dan 'ya'ya susami uwa tagari, yo wannan aimu ba sabon abu baneba agaremu, tunda dama halin uwarku kenan, itama saida
tagama tambad'arta a titi aka k'ak'abama d'ana”.
Rintse idanu nayi saboda yanda maganganun innaro ke sukar zuciyata. Dady yakatseta da fad'in “dan ALLAH inna kiyi hak'uri kibar maganarnan”.
“hameesu barni nafad'i gaskiya, wannan abin kunya
har ina, wai jikokinane yau aka buga ajikin jarida namiji rungume da d'ayarsu a titi” ta face hanci tana share hawaye da bakin zani, “ALLAH ya wadaran irin wannan rayuwa taku kuda uwarku, kun jawo mana abunkunya, yanzu dawane ido duniya zata cigaba da kal
lonmu” feeet, takuma fyace majina”.
Mudai ni da munubiya muna durk'ushe rungume da juna Luna rairai kuka maiban tausayi dacin zuciya, yayinda 'yan gidanmu da sauran 'yan biki suketa k'us-k'us a tsakaninsu.
Isowar likita yasa aka kama innarmu aka
maida falon Abba, a sank'ame take tamkar gawa....
★
.
★
.
★
.
★
.
★
.
★
.
★
.
★
.
★
.
★
.
★
.
★
.
★
.
★
*_GAGARA BADAU PLACE_*
Shirye-shiryen komawa India yakeyi hankalinsa kwance, Dan yau zai koma ga mahaifansa da 'yan uwansa dake can, jirgin k'arfe 8pm zaibi.
Yana gama had'a 'yan abubuwan dazai iya buk'ata yadawo falo ya zauna, sanye yake cikin farare k'al d'in kayan Adidas na training, dogon wando da Riga mai dogon hannu, yasaki hular abaya, kayan sun masa k'yau sosai.
Kallo d'aya yayma abincin dak
e kan center table d'in ya d'auke kansa, cikin k'asaitacciyar muryarsa mai cikeda isar masu mulki naji ya furta “Saykin k'ofa”.
Kai kace anmasa dolene saiyayi maganar.
Da hanzari sarkin k'ofa yashigo falon, ya zube a k'asa “barka da hutawa ya
shugabana”.
Kansa kawai ya jinjina, sannan yace, “waye yakawo abinci nan ne?”.
“ya shugabana bansan daga ainahin wane 6angare bane, amma bayin dasuka kawo daga 6angaren sarauniya Zulfah ne”.
Baice komaiba ya d'aga masa hannu alamun
yatafi.
Sai da yad'an rissinar da kansa alamar girmamawa sannan yamik'e, dokace agareshi shi bayason kirarin da akema 'yan gidan sarautar. dan haka basa yimasa shi, Saboda gudun 6acin ransa.
zamewa yayi yay kwanciyarsa akan doguwar kujerar
ya lumshe idanunsa batareda yabi takan abincinba.
Sallamar sarkin k'ofa tasakashi bud'e idanunsa akansa, ya amsa sallamar bisa la66ansa, sarkin k'ofa yazube agabansa, cikeda girmamawa yace, “ya shugabana yalla6ai Muftahu yace amasa iso gareka”.
Alama yamasa akan yabada izinin ya shigo.
Fita sarkin k'ofa yayi. babu dad'ewa saiga Muftahu yashigo da sallama, Galadima yabud'e idonsa yana kallonsa tareda amsawa.
Zama yayi kujerar dake kallon Galadima, yace, “yalla6ai barka da hantsi”.
Murmushi Galadima yayi, ya tashi zaune sosai yana fad'in “my man daga ina haka naganka ayikice? bakaje aikibane?”.
Ajiyar zuciya Muftahu ya sauke, yacije le6ensa na k'asa yana mik'ama Galadima jaridar dake hannunasa, “nafita wlhy sainaci karo
da wannan jaridar data fito a safiyar yau”.
Cikin halin ko inkula Galadima yace, “Miye had'ina da jayidan to?”.
“Kayi hak'uri ka kar6a ka duba”.
A shafin farko yay karo da abinda yasakashi sake kallon Muftahu, kai Muftahu ya d'aga
masa alamar yacigaba.
*_ANYI WALK'IYA...., GALADIMA DA AIKA-AIKA A FILIN IDI_*
cikin hanzari yabud'e shafin farko, nankuma an saka.
*_BABBAR MAGANA, GALADIMA SAMEER RUNGUME DA MATASHIYAR BUDURWA A PLAZA 'DINSA SUNA SUMBATAR JUNA!!_*
sai hoton farko dana biyu, wad'anda suka d'aure kansa, danshi gaba d'ayama ya manta daduk abinda yafaru, tundaga na birnin gayu plaza harna filin idi d'in. d'agowa yay yakalli Muftahu sannan ya maida kallonsa ga dogon rubutun da akai akan sharhin hotunan.
bazai iya karanta rubutun ahakaba, saiya fara waige-waigen neman medical glasses d'insa.
Fahimtar haka da Muftahu yayi yace, “ina yake in d'auka maka?”.
Da hannu ya nuna bedroom d'insa ba tare da yace komai ba.
Mik'ewa Muftahu yayi yanufi
bedroom d'in, babu dad'ewa saigashi yadawo, ya mik'a masa sannan yakoma inda yake da ya zauna yana fad'in “ko ka kawo na karanta maka”.
Nanma baice uffanba yamik'a masa jaridar, kansa ya maida jikin kujerar ya jingina ya lumshe idanunsa.
Tir
yan-tiryan Muftahu yafara karanto k'aryar da aka jera jikin jaridar, ko sau d'aya bai motsaba, amma yana saurarensa.
Muftahu yagama cikin sauke ajiyar zuciya, Amma tabbas wannan wata k'ullaliyace, ai ba abinda yafaru kenanba jiya a birnin gayu, ni na
ma rasa mizan cema wannan gidan jaridar wlhy”.
Galadima ya bud'e idonsa dake a lumshe, ya kad'a yay jajur saboda 6acin rai, akan Muftahu ya saukesu batareda yace komaiba, tuno abinda yafaru a filin idi yayi kusan sati 4 kenan, tabbas sunyi karo da
yarinya, wadda ayanzu haka ko fuskarta bazai iya tunawaba, dan ko'a waccan ranar kallo d'aya yamata, a jiya kuma ko ta6a yarinyar baiyiba ALLAH ya kareta daga fad'uwar dazatayi. jinjina kansa yayi cikeda 6acin rai da mamaki.
Muryarsa a sark'e yace,
“Muftahu imason bayanai akan yayannan najikin jayiday su duka”.
“ok yalla6ai, amma ai yarinya d'ayace duba kagani”.
Kar6ar jaridar yayi yakuma kallon hotunan, tabbas duk yarinya d'ayace, wannan ya sake tabbatar masa da an shirya masa hakann
e.
Mik'ewa yayi yazari mukullin mota batareda yace ma Muftahu komaiba, ganin haka shima Muftahu saiya mik'e yabi bayansa.
Cikin sauri dogaren dake binsa inhar zai fita suka taso gareshi, amma saiya d'aga musu hannu.
yana k'ok'arin bud'
e motarne Jakadiyya ta iso inda yake...
Cikin rissinawa tace, “barka da hantsi galadima”.
Bai iya amsa mataba, sai hannu daya d'aga mata kawai.
Kuma rissinawa tayi tace, “Galadima takawane yabani izinin in kirayeka”.
Kallonta yayi za
iyi magana saikuma yay shiru ya maida motar yarufe tareda cillama Muftahu dake bayansa kyes d'in.
Muftahu ya cafe.