Showing 75001 words to 78000 words out of 407268 words

Chapter 26 - Raina Kama COMPLETE

/>
akan Galadima d'in, domin aganinsu sunyi sake d'an zaki ya girma, kuma Galadima na neman zame musu *RAINA KAMA......*

★★★

.



.



.

★★★

Gidanmu kam tunda aka kammala d'aurin aure labari ya shigo gabana yashiga luguden daka, rungume juna muka

yi ni da Munubiya muka fashe da kuka mai ban tausayi, Wanda muka saka jama'a dayawa kukan, ciki kuwa harda Innarmu da mama Rabi'a. babu wanda yace mu bari, aka barmu mukayi mai isarmu, dan kowa yasan dolene muyi irin wannan kukan na rabuwa, dan yau babu fa

shi dolene mu Rabun, abinda baita6a faruwa agaremuba, kullum a gado d'aya muke kwana muke tashi, kowanne aiki tare mukeyin sa, komai namu iri d'ayane, daidai da pants & bra iri d'aya muke sakawa, idan d'aya bashida lafiya saika d'auka muduka bamuda lafiyar

, babu abinda ke banbantamu sai hali, amma yau gashi aure zai banbantamu, jinai inama muma mazane tamkar su Aiyaan, yanda babu mai rabamu d'in.

Haka dai wannan yinin biki akayishi a wani iri, mu cikin damuwar rabuwa, matan gidanmu cikin hassada da b

ak'in cikin mun fisu.

danma Su Abba sunyi dogon gargad'i akan wlhy duk wacce tasake tada finina a gidan sai dai ta k'arasa bikin a gidan su.

Wannan furucinne yasaka kowa yin likimo, sai dai fa ta ciki na ciki

🙊😂

.

Hotunama da akayi na

family wasu fuskar tasu tamkar kashin farar safiya

😖

🥴

, Innaro kam ai mune nagaban girarta a yau, sai dama-dama takeyi damu, dama komai akayi saitace an kaima Ai'sha dai ko, (

😂

su innaro anga banza).

Wannan abun datakeyine keta kuma hasala matan gida

nmu da 'ya'yansu, itakam ko a ha6ar kallabinta, warkajaminta kawai takeyi na murnar auren jikoki.

Yayinmu mazane kawai babu ruwansu, duk suna cikin farin cikin wannan aure.



Bayan la'asar sakaliya saiga sak'o daga masarata mutane biyu d

'auke da akwatina biyu wai sun kawo kayan da zansa awajen dinner ni da Munubiya, sun shirya dinner d'inne mu biyu kawai banda sauran amaren.

Wannan lamari kam ya sosa zukatan mutane da yawa, ni kaina banji dad'in hakanba gaskiya, dan banason su d'auk

a kamar mun banbanta da sune yanzun, gaskiya da ace inada Number Galadima dana kirashi nace a fasa wlhy, saboda muma anan gidanmu yayunmu sun shirya mana dinner d'in gaba d'ayanmu, duk da ni dama ban saka ran zuwan Galadima ba a wajen.

Gashi kuma ga

te pass guda 30 kacal suka kawo, alamun basa buk'atar mutane dayawa a wajen kenan, ikuma na nace inhar bada sauran 'yan uwana ba ban zuwa nima d'in.

Lallashin duniya anyi nak'i sauraren kowa, nakafe akan bazan jeba.

Matan gidanmu kam cewa suk

ayi munafurcine kawai.

Zancensu bai dameniba, nidai ina akan bakana bazanjeba. su Ayusher sun rasa yanda zasuyi dani, dama akwai number Galadima saisu kirasa su sanar masa halin da ake ciki.

Innarmu kam ko k'ala batace daniba, yitaima tamkar ba

tasan mi akeyiba, mama Rabi'a da Aunty Salamah sai fad'a sukemin kamar zasu dokeni, hakama innaro, sai jaraba takemin harda dungure min kai.

cikin ikon ALLAH kuwa ana cikin haka saiga kiran Samha yashigo wayata, Ayusher ta d'auka suka gaisa, azaton

Samha nice, saboda muryar Ayusher ma tana kama da tamu. Tace, “Aunty gimbiya ya hidima?”.

Murmushi Ayusher tayi danjin sunan nawa harya canja, tace “ba ita baceba Ayusher ce”.

Cikin jimami tace Aunty gimbiyar fa?”.

Labarin komai Ayusher ta

bata, sannan tace “dan ALLAH ko zaki had'ani da Galadima?”.

Samha tace “babu damuwa bara na dubashi, duk da nasan yana tare da abokansa yanzun”.

Godiya Ayusher Tamata sannan suka yanke wayar akan idan tagansa zata kira”.

Masifa naha

u yima Ayusher akan miyasa zatace saita fad'a masa, nidai koma miye babu inda zanje.

Banza Ayusher tamin tamkar batasan inayi da itaba ma.

Kusan muntuna 7 saiga kiran Samha yasake shigowa, Ayusher ta d'aga, maimakon taji muryar Samha saitaji t

a Galadima cikin k'asaitar nan tasa da izza.

Nutsuwa Ayusher tayi sosai ta gaisheshi, sannan ta masa bayanin komai.

uffan bai ceba saida ta kai ayar zancenta, lips d'insa yad'an cija kafin yace “had'ani da ita”.

A kunne Ayusher ta sa

kamin wayar, yayinda kowa yafice daga d'akin aka barni ni kad'ai saikace wata mayya.

Dagani har shi kowa yayi shiru, shi yanajin kansa nima hakance, kusan minti 4 yaji banida niyyar tankawa saiya yi guntun tsoki, “shin ke baki iya gaisuwa bane?”.



Dukda naji ban k'yautaba saina ta6e baki, cikeda dakiya nace, “ina yini”. muryata a dishe take saboda kukan danaketa sha tun jiya.

Bai amsa gaisuwarba yace “wane sak'o kika bada a bani?”.

Saida na tunzuro baki sannan nace “yoni minace abak

a?”.

Lips d'insa ya lasa yana fad'in “nikikema wannan abun?”.

Banza namasa danni bansan mina masaba kuma.

Yaja guntun tsoki, “ki kama kanki fa, karkiga auren contract mukayi, akwai sharid'd'a acikinsa, bana buk'atar ganin kowa awajen i

nba keda sister d'inki ba, haka na tsara, kuma babu mai canjamin ra'ayina, zuwa anjima wadda zata shiryaku zatazo, idan kin gadama karki bari a shiryaki, nikuma zakiga mi zan yi akai..”.

d'if ya katse wayar, cirota nayi daga kunnina ina dubawa tam

kar zan ganoshi acikinta. naja tsaki ina fad'in “aikin banza kaje ka koyo R sannan kamin wannan ikon, nifa baka isa takani ba acikin auren contract...... ”

Sauran maganar ta mak'ale a mak'oshina saboda shigowar munubiya.



Zama tayi akusa

dani, “sweetheart zan iya neman alfarma a wajenki?”.

Kai na d'aga mata.

Ta gyara zamanta sosai tareda kamo hannayena duka acikin nata. “inason kima mijinki biyyay kiyi yanda yakeso, yanzu hakkin bin dokarsa tarataya a kanki dole inhar bata sa6a

ma addini ba, kina kaucewa kuwa zaki had'u da fushin ALLAH, tunda yace haka yakeso ayi kiyarda kawai, awa nawane anyi an tashi kowa yakama gabansa”.

Alk'awarin Dana mata yasani amincewa zanje tilas amma badan raina yasoba.

An tsara wad'and

a zasuje, dan haka aka damk'ama kowa gate pass d'insa a hannu ya Adana. dukda wasu gani kwaf zasuje kuwa.

Bayan sallar isha'i saiga masu mana shiri sun iso, babbar magana wai d'an sanda yaga gawar soja.

Jama'a ni kaina bamma gaskata ce

war nibace ballan tana Ku 'yan kallo, saika rantse kace dama can mud'in jinin sarauta ne, munyi k'yau har mun gaji, gashi dandanan akayi aka gama, har kusan 9pm muna jiransu, gidan yayi tsitt duk wad'anda zasuje dinner sun tafi, wad'anda zasu bimune kawai

tare damu muna jiransu Galadima, dan shima yaa marwan d'in baikai ga isowaba.

Sai around 9:15pm sannan mukaji dirar mitoci a k'ofar gidan.

Aunty Mimi ce da kanta tashigo itada wasu bayi guda hud'u, saida ta gaisa dasu innarmu sannan aka mata iso

d'akinmu, wani dad'ine ya ratsa zuciyarta, dukda batasan wacece matar k'anin nataba acikinmu, amma muntafi da imaninta, jitai inama natane wad'an nan twins, ALLAH yasa haihuwar farko na haifo musu irinmu.

Daga ni har munubiya rissinawa mukayi muka ga

idata cikeda girmamawa, dan munsan a haife ta haifemu, dukda bawai sa'ar innarmu bace, ko mama Rabi'a ma ta girme mata.

Hakan damukayi yamata dad'i kuma mun birgeta, ta kama hannayenmu tana yaba k'yawun damukayi, wasu turarurruka ta fidso kala uku a b

ag d'inta tashiga feshemu dasu, dukda uban turaren da aunty salamah tamana wanka dasu zance, dan itama haka taita zazaga mana su d'azun, ni saima hawarmin kai sukeyi wlhy.

Wasu alk'yabbu masu azabar k'yau iri d'aya aka saka mana, takalman dake k'afar

mu kansu abin kallone.

Aikam bamu fitaba saida tamana hotuna, afaloma saida aka mana muda su innarmu.

A waje muka iske motoci guda uku masu k'yau, da alama sauran motocin sun d'auki jama'a sun tafi.

Saida mukaje jikin motocin sannan a

unty Mimi tayi murmushi tana kallonmu, to karnayi abin kunya, wacce ta my k'ani? wacce ta Marwan?.

K'asa mukayi da kanmu saboda kunya, saida ta kuma maimaita tambayar sannan munubiya tayi k'arfin halin nunani, kunyarmu takuma birgeta sosai, hannun m

unubiya ta kama tana fad'in kece babba ai, zoki fara shiga”. a motar farko ta sakata, sannan tadawo takama hannuna ta sakani a ta biyu.

Rufe k'ofar tayi takoma motar bayanmu tashiga. yayinda kuyangin nan hud'u suma suka shiga motar k'arshe.



Tunda nashigo k'amshin turarensa yadaki hancina, ta gefen ido na saci kallonsa, kishin gid'e yake a kan kujerar motar tamkar yasamu gado (dan bansan yama zan musalta muku tsarin motarba nikam, ammafa komai abin kallone) k'afarsa d'aya a k'asa d'aya akan ku

jerar, kansa na gab dani, dan dazai zame ko motsawa dolene saiya ta6a jikina, sanye yake cikin wasu Fararen suit masu azabar k'yau, sunyi mugun fidda ainahinsa matsayin cikakken namiji mai aji da gayu, aikin danna wayarsa kawai yakeyi tamkarma baisan na sh

igo motarba, dan ko sau d'aya bai d'ago ya dubeniba.

Nima basarwa nayi nayi tamkar bansan dawata halitta acikin motarba bayan driver.

Shikuwa tun shigowa ta k'amshin turarena yabigi hancinsa tareda shiga magudanar jininsa, a rayuwa yana matu

k'ar k'aunar k'amshi, lumshe idanunsa yayi yana lasar lips, amma jinkai da k'asaita ta hanashi d'agowa yako dubeni.

Itakam munubiya tana shiga bayan aunty Mimi tarufe k'ofar yaa marwan jawota yayi jikinsa, tareda sumbatar gefen kumatunta. ta matse

jikinta waje guda saboda tsorata, muryata na rawa ta gaidashi.

Ya amsa yana wani kuma shinshina wuyanta da bata wasu kisses d'in.

Mamaki da al'ajabine suka kamata, anya kuwa wannan yaa marwan d'in nanne mai shegen muskilanci da share mutane?,

kanta bai ida kwancewa ba saida taji hannunsa indama batayi zatoba, tamkar zatayi kuka tace “please yaa marwan kayi hak'uri dan ALLAH, cikin motane fa”.

Rungumeta kawai yayi batareda yayi maganaba.

A wannan yanayin mukaji motocin sun tsaya.



Bayan an bud'e mana duk muka firfito, tsakanina da Galadima kuwa babu Wanda yacema wani kanzil har muka fito.

Yaa marwan da Munubiya ne agaba rik'eda hannun juna, saini da nawa d'an hayak'in Mr k'asaita abaya, harmun fara tafiya Aunty Mimi tamasa

magana. banji mitace ba saboda da Indianci tayi maganar

😜

.

Jinai kawai wani lallausan hannu cikin nawa, dagani harshi babu shiri muka kalli juna saboda shock d'in daya jamu a time d'aya.

Shine yay azamar janye nasa idanun yana cije lips, kafi

n nima na janye nawa cikeda kasala da luguden zuciya.

Mamakine ya kamani lokacin da muka shigo hall d'in, inda sauran 'yan uwanmu sukene Ashe, sainaji dad'i sosai wlhy.

Nandanan mc yashiga sanar da isowarmu, tunda muka shigo kallo gaba d'aya

yadawo kanmu, musamman mutane dake son ganin Galadima a yau.

Can saman hii table muka isa muma, mazaunin daya kasance namu, su Safara'u tamkar su saka ihu saboda ganin yanda muka had'u tamkar bamuba, duk sai suka raina nasu kwalliyan dukda suma sunyi

matuk'ar k'yawu kuwa..

Bayan mun zauna angunan suka taso suna kawo gaisuwa wajen Galadima, fuskarsa d'auke da murmushi yake amsa musu tareda mik'a musu hannu suyi musabaha, koda sun nok'e saiya kamo hannun nasu da kansa.

Bak'in ciki tamk

ar yakarsu Halimatu, ganin angunansu suna kai gaisuwa wa Galadima, basusan hakan dole bane agaresu kodan kasan cewarsa d'an masarauta wandama ake da yak'inin zama sarkin gobe idan da rai, idanma badan hakan ta kasanceba ta ina suka Isa ganinsa balle ma har

suyi gaisuwar Baki da baki harda musabaha. Aishi adaline ma tunda harya iya halartar taron nasu.

Yayunama duk saida sukazo suka gaisa dashi, mazan da matan, sannan mukayi hotuna, su Zarah da siyama matan 'ya'yan senator kam ai yau saikikaji tsit babu

felek'e, dan mazajen nasuma ko zuwa basuyi wajenba, kamar yanda basu halarci tasu dinner d'inba lokacin aurensu.

Aunty Mimi dakanta ta kar6i microphone tabada hak'uri da neman alfarmar tafiyarmu, saboda suma mutanensu nacan suna jiran isowarmu, dam

a munzone domin kar6ar excuse.

Hakkane yad'an rage fushin wasu, sannan mun tafi dawasu acikin yayunmu maza.

Mun tafi kowa yana yaba tsarin namu.

Yanzuma haka muka tafi tamkar wasu kurame, saidai yanzu a zaune yake, yajingina kansa

da kujera ya lumshe idanu.

Nikam gefe na maida kaina ina kallon titi.

Yanzun kam koda motocin suka tsaya bamu fitaba, sai kusan mintuna 10, Ashe lokacin harsu munubiya da yaa marwan sun shiga, saura mu kuma.

Bamu fitoba saida akayi knoc

king glass d'in gefensa, ahankali ya sauke glass d'in batareda ya bud'e idonsa ba, wanine yalek'o yana fad'a masa mu fito, duk bud'e mana motar akayi dagani har shi sannan muka fita.

Zagayowa yayi inda nake tsaye, a mamakina da al'ajabi sai kawai n

aji ya sak'alo Hannunsa a k'uguna, cikeda firgici nad'ago na kallesa, saiya sakar min harara dawani munafikin murmushi, saika rantse da ALLAH kallon soyayya yamin, nikam dukda kwarjini dayamin saida na turo baki gaba da hararsa a kaikaice, ALLAH ma yasoni

baiga hararba.

Ahankali muke tafiya saboda Alk'yabbata, yayinda kuyangin ke watsa wasu flowers masu k'amshi a inda zamu taka, aunty Mimi kam da wata daban santaba suna feso mana Abu mai k'amshi.

Kai jama'a wajen taronnan fa ya had'u, k'arshe

n had'uwa kuwa, an k'awata wajen da kwalliyar white and Golden colors, yayinda kwalliyar jama'ar wajenma white and Golden colors ne, (suma mutanemu dasukazo wajen dama ankawo musu kaya irin kalar).

Mazan sunsha wankan white suit, takalmansu da agogun

a zuwa tie duk golden, matan kuma white gown ta material sai d'ankwali golden.

Yayinda tamu shigar ta kasance golden gaba d'aya, su Galadima kuma sun saka white suit, komai nasu white ne shida yaa marwan.

Tunda muka shigo wajen ya d'auki tafi,

yayinda aka saki wak'ar da aka raira domin mu. (Bara nad'an raira muku kad'an

🤥😜

).

*_Alk'awari yacika munubiya alk'awari yacika.... yacika yacika munaya alk'awari yacika amarya...._*



🙄

iya nan na iya to

🥴



🏻

‍♀

Gaba d'aya sai wani

tsoro da kunya ya kamani, nafara tafiya ahankali tamkar kazar da kwai ya fashema aciki.

Bansan lokacin da Galadima ya rankwafo kainaba, dan tunanina yatafi wajen mamakin yanda suketa shiryama auren shekara 1 wad'annan bidi'oin.

Jinai kawai an

d'aukeni cak, ihu kawai aka sanya awajen da uban tafi, yayinda aka kuma sakin sabon kid'a na musamman.

Runtse idanuna nayi kawai zuciyata na kai kawo tamkar zata fito waje saboda mamakin munafuncin Galadima. (Yo inba munafuci ba miye na d'aukata aga

ban jama'a, bayan ni da shi ko magana bata had'amuba

😏

).

Bai direniba sai a kujerar da aka tanada domin mu.

Anan d'inma zama yayi yasakani jikinsa, kunya da haushi duk sun cikani, wlhy badan karna kunyatashi ba dayasha mamaki. Gashi sai wani maga

na yakemin k'asa-k'asa kai kace ta arzik'ice, nanko duk gargad'ine wai na kama kaina karnayi abinda wani zai fahimci ba auren soyayya bane a tsakaninmu.

Baki na tunzuro gaba dan haushi, yasaka d'an yatsa ya d'alli bak'in nawa.

Naji zafi wlhy kum

a.

😏

Abun ALLAH wadai bai k'areba saida akazo yanka cake, bayan su munubiya sun gama nasu cikin mutunci

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login