Showing 213001 words to 216000 words out of 407268 words
Daga haka munaya ta mik'ama Galadima wayar tana cigaba da share hawaye.
Hankalinsa atashe yace, “miyasa zakimata alk'awarin zuwa? bayan kinsan ga halin da kike a ciki”.
“kayi hak'uri yalla6ai, gara ka barni Na tafi
shine mafi a'ala, tun farko y'ar uwata bata 6oyeminba ta sanarmin naje gida Na haihu, idanma baka kainiba to wahala kawai zanta sha anan d'in tunda hakan take buk'ata”.
Galadima jiyay tamkar ya make Munaya, ya haukace mata da masifa kaikace zai cinye
ta d'anya, “wannan ai canfin banzane da wofi, ALLAH shine kawai maiyi ai bawani alk'awarinku ba, shin Ku bazaku tausayama kanku baneba? yaufa kwannanki biyu kina wahalarnan, wane irin taurinkai ne wannan.......?”.
Dakatar dashi Momma tayi ta hanyar d
'aga masa hannu, ta dafa k'afad'ar munaya dake kuka tana fad'in “y'ata dama kinmata alk'awarin zakije Nigeria ki haihu ne?”.
“Momma ba alk'awari namataba, amma kusan 2months kenan tacemin gida zanzo Na haihu ko? nikuma bance mata komaiba”.
Murmushi Momma tayi, ta kalli Galadima dake tsaye yanata kumbura dan haushi. “Muh'd anemi ticket d'in Nigeria yanzunnan”.
Da sauri yace “Momma amma......”
Hannu ta d'aga masa alamar bata buk'atar jin komai. ya had'iye wani k'ullutu daya ts
aya masa a mak'oshi, shifa ba tafiyar tata bace matsalarsa, shima akwai tashi manufar da dalili, amma bashida ikon yin jayayya da Momma, waya ya zaro a aljihu. Ya lalubo wata number yay kira, ficewa yay daga d'akin.
Momma tacigaba da lallashin Munaya
daketa hawaye, ga zufa Na cigaba da jik'eta dukda AC dake aiki a d'akin.
Kusan mintuna talatin Galadima yashigo shida doctor, dannan aka shirya Munaya, nurses biyu suka kaita mota.
Wannan karon harda Momma rakkiya Airport, tanata jerama M
unaya addu'oi har suka isa.
Haka sukai wannan tafiya babu shiri, Galadima kayan tun safenema a jikinsa bai ko koma gida ya canjaba, hakama aunty Mimi.
A jirgi yana rungume da ita tanata murk'ususu idan abin ya motsa, wai danma waje Na musamma
n aka basu dankarta takura. idan nak'udar ta lafa sai barci mai dad'i ya kwasheta, da abin yamotsa kuma tata kuka kenan tana k'ank'amesa, dukta jimasa ciwo da farce, shikam tausayinta dukya cika zuciyarsa.
Yaa marwan ma cikin haushi yakira i
nna ya gaya mata abinda Munubiya tayi, inna taita fad'a tamkar zata ari baki, itada ta haifi su munaya ita tasan halin kowa acikinsu, tabbas a fili Munaya tafi Munubiya fad'a, amma a bad'ini Munubiya tanada ak'idar tsiya da tsatstsauran ra'ayi, lokuta da d
ama idan takafe akan Abu bata tankwaruwa, kuma dolene Munaya ta amince ayi kokuwa tasha wahala, dan idan Munubiya ta murd'e abin bazai ta6a ya yuwuba saidai idan Ubangiji ya juna mata ikonsa, to amma bata ta6a zaton shirmen nasu zai iya ta6a har lafiyarsu
irin hakaba.
Dole inna tashirya zuwa asibitin da kanta, taita zubama Munubiya dake fama da kanta fad'a, su mama Rabi'a da Maman Fauziyya sunata bata hak'uri, tunda dai anrigada an aikata, saidai kuma a kiyaye nagaba.
Su Munaya sun iso Nigeria lokacin tsakkiyar ranane anan, dan irin 1pm d'innan ne, dayake yakira su sarkin mota ya sanar dasu time d'in dazasu iya isowa, tun wajen 11am ma suna airport d'in..
Tunda Galadima yafara sakkowa daga matakalar jirgin
rungume da Munaya akan idonsune, hakanne yasaka sarkin mota matso da motar bisa alfarmar ma'aikatan wajen, suna gama sakkowa k'afarta ta rik'e, dole ya d'auketa daga ita har nauyin cikin ya k'arasa da ita motar, mutane duk tausayinta yakamasu.
Tunfa
a mota labari yafara canjawa, dan Munaya tafita hayyacinta sosai, Galadima sai tsawa yakema sarkin mota, ALLAH daine kawai ya kaisu asibitin lafiya, aiko suna shiga dogarai suka shiga da gudu cikin asibitin kiran doctors.
Tunima Galadima ya kuma su
nkutarta yayi ciki, a hanya yagamu da nurses da gadon d'aukar marasa lafiya, bai d'orataba, yawucesu abinsa, doctor Farida ta nuna masa d'akin da aka canjama Munubiya.
Gadon da aka tanada dan Munaya ya d'orata, Munubiya tashiga mik'o mata hannu tana
kuka, itama a wahalce tamik'a mata nata, dan gadon kusa da kusa aka sakasu....
A tare suka dinga Neman yafiyar junansu suna kuka, sai tausayinsu ya kamasu Galadima.
Da k'yar doctor Farida tasamu Galadima ya fita suyi aikinsu, dama haka tash
a dagama da Yaa marwan shima, saida ma Abbansu yamasa magana, Dan shima yana asibitin.
Munubiya da Munaya Haka suke rik'e hannun juna kowa nashan azabar nak'uda, (wannan k'auna dabance gaskiya, nak'uda ba abun wasaba amma suna son jin junansu a
kusa, wato koma mutuwace tazo musu a tare?
😽
).
Haihuwar Munubiya ce tafara gadan-gadan, Dan haka Munaya ta k'ank'ame hannun y'ar uwarta tana kuka da kiran sunanta a galabaice, itama sai labarin yafara canjawa, Nurse da doctor Farida and doctor Zai
nab dake Kansu duk suka maida hankali ga Munubiya, cikin rahamar ubangiji saiga jinjiri yayi sallama duniya da kuka. tamkar jira itama Munaya ta kar6a, a time d'in Munubiya tayi shid'ewar wucin gadi, amma hannunta na cikin na Munaya datake shan azaba itama
. Ba'a d'auki tsawon lokaciba itama tata mace tafito, saikuma sabuwar nak'uda ta tashi a tare suduka, yanzu Munubiya mace Munaya kuma namiji, na Munaya na fad'owa wani yakuma biyo baya
😳
.
Turk'ashi, ALLAH sarkin rahama da tausayi, maiyin yanda yaso
kuma ga Wanda yaso, Munubiya ALLAH yabata k'autar tagwaye mace da namiji, yayinda Munaya keda uku, maza biyu mace d'aya.
Su doctor Farida duk sun kacame da murna da k'ok'arin gyara yaran, kaikace su akama haihuwar.
Dandanan aka shiga goge y
ara da zaitun, amma cikin hattarar kar a had'esu agaza ganewa..
Su Munaya ma dai kulawa ta musamman aka basu, amma Munubiya ta suma, kuma bata farfad'oba, hakanne ya tada hankalin su doctor Farida suka rufu akanta suna bata dukkan wani taimako,
sama-sama Munaya ma kejin 'Yar uwarta tashid'a, hakanne yasata kuma k'ank'ame hannunta hawaye na zurara mata, itama bawani k'arfine da itaba, Dan ko idanu dak'yar take iya d'agawa, dishi-dishima take ganin komai.
Lamarin yana san zama babba, Dan s
aida wani babban doctor ya shigo dole, ganin shigi da ficinsu doctor Farida yayi yawa yafara ankarar dasu Galadima.
Nanfa suka fara turkesu da tambayar ko lafiya?, sukuma suna basu amsa da babu komai, kowa dai bai yardaba, dukda suna jiyo kukan jarir
an.
An d'auki wasu adadin mintuna kafin numfashin Munubiya ya dawo, ajiyar zuciyar da Munaya tasaki duk saida yasaka su doctor Farida kallon ta da tausayi, dukda tana cikin wani hali itama, amma hankalinta nakan 'Yar uwarta.
Sun kimtsasu tsaf,
daganan aka musu allurar barci dansu sami Hutu, yara dai kam Alhmdllh, duk da sun lura d'aya daga cikin na Munaya bai cika kuzariba, kamar sauran mace da namijin sun fishi lafiya, amma basuda tabbas tunda basu bincikaba. Nurse d'aya tafito ta kar6i kayan
haihuwar takoma, duk an saka musu, dukda basu zama iri d'aya ba tunda sunzo babu tabbacin miza'a haifa, musamman ma su Galadima, gara su Yaa Marwan sunsan ita Munubiya dama biyune.
Tunda su doctor Farida suka fito Galadima dake ta kaikawo shi
da Yaa marwan da Muftahu suka maido hankalinsu Kansu, Galadima bai iya matsawa ba, saisu aunty mimine suka k'arasa ga su doctor Faridan.
Kowa yana k'ok'arin tambayar abinda ke faruwa.
Doctor Farida tayi murmushi, tace, “to ai bakine bazai iya
fad'a ba ma, inaga kawai angunan k'arnin su shiga daga ciki, idan sun fito kwaji komai”.
Yaa marwan da Galadima suka kalli juna, kowa yana fargabar abinda zai tarar d'in.
Aunty Mimi ce takama hannayensu tana fad'in “kuje mana, mi kuke tsorone
wai?”.
Kowa tamkar an doke masa gwiwa haka suka nufi d'akin, Yaa marwan ne gaba Galadima a baya.. Duk sukayi sororo a k'ofar d'akin suna bin gadajen matan nasu da jariran kusa dasu da kallo.
Badan kowa yasan kayan jikin matarsa ba dabasu iya
banbancewa ba (kunsanfa mu 9ja 'yan gargajiyane
🤭
, kod'an canja kayannan na asibiti bamayi
🤣
).
Galadima da Yaa marwan suka kuma kallon juna, kowa ya kasa cewa uffan, doctor Farida dake bayansu tamkar ta kwashe da dariya, tadai daure ta danne.
Ra6asu tayi ta shigo ciki sosai, ta tsaya tsakkiyar gadajen tana kallon hannun Munaya da Munubiya dake had'e da juna har yanzu, sunyi-sunyi su saki amma sunk'i, sai suka saka musu lokar asibiti a tsakkiyar aka d'ira hannayen Dan kar suyi sanyi.. Juyowa
tayi ta kallesu da murmushi a fuskarta, tace, “wannan itace Munubiya ga babies d'inta nan 2 mace da namiji, wannan kuma Munaya ga nata 3 maza biyu mace d'aya. Ina muku fatan alkairi gaba d'aya, ALLAH ya rayasu akan sunna”. tana gama fad'a ta juya ta fita t
abarsu.
Binta sukayi da kallo harta fice, sannan suka maido ga iyalan nasu, saikuma kowa ya k'arasa da hanzari ga matarsa.
Yaa marwan yasaki murmushi yana d'aukar macen, sanan ya d'auki namijin shima, dukya rungume.
Galadima kam dur
k'usawa yay gaban gadon yasa gwiywoyinsa a k'asa ko k'yank'yami bayayi, dukda angyara wajen tsaf tamkarma ba'a haihunba.
Hannunsa d'aya ya d'ora agoshin Munaya da duk yaga ta masifar rame masa yau, d'ayan kuma yafara tsafa kumatun yaran d'ai-d'ai, haw
aye masu d'umi Wanda shikad'ai yasan ma'anarsu suka fara sauka a kumatunsa. Cikin lumshe ido ya matsa ya sumbaci goshin Munaya da hancinta, sannan ya dawo kan babies nashi yana sumbatarsu.
Yaa marwan ma yanacan ya duk'ufa kan matarsa yana mata kalam
ai masu dad'i acikin kunne k'asa-k'asa, kai kace idonta biyu tana jinsane
😹
.
Galadima ya share hawayen fuskarsa, cikin murmushi yace, *“UBANGIJINA ka gamamin komai, yau nine da k'yautar abin cikin kwan d'ai-d'ai har 3 a lokaci d'aya, badan
k'arfina kabaniba, bakuma Dan nafi sauran bayinka ka baniba, suma y'ay'a jarabawace ga iyaye, ya Mahaliccinmu kabamu ikon bama yarannan tarbiyar da zasu zama cikin alfaharin MANZON ka da addininmu mu da mahaifansu mata, ka rayasu bisa turbar addinin islama
, ALLAH yasa suzama masu tausayi da jink'ai gana k'asa dasu damu kanmu, su zama masu girmamawa da mutunta na sama dasu a duk inda suka shiga, ya RABBI ka rinjayar da zukatansu ga bautarka domin rabauta a duniya da lahira, ka nisantar da zukatansu da gangan
gar jikinsu ga sa6onka komin k'ank'antarsa dagasu har 'yan uwansu gasunan guda biyu da k'annensu masu zuwa da dukkan y'ay'an Al'ummar musulmi. I love you so more and more my Darling children's, ina muku barka da isowa duniya gidan gwagwarmaya, ALLAH yabaku
damar cinye jarabawar da ubangiji ya k'addaro a cikin tsawon rayuwar da zakuyi a dunia kafin Ku koma garesa”.*
Yaa marwan ya amsa da amin shima fuskarsa d'auke da murmushi.
Tashi Galadima yayi yaje gareshi suka rungume juna.
Galadima ya
ce, “d'an uwana ina tayaka murna”. Yaa marwan ma yace, “ranka ya dad'e nima ina tayaka murna”.
Sakin juna sukayi suna dariya, saikuma suka kuma cafke hannun juna cikin musabaha da nuna tsantsar farincikin dake baibaye da zukatansu a yau d'innan.
Aunty Mimi kasa hak'uri tayi ta danno kai d'akin babu ko sallama.
To shigowarta cefa ta fallasa komai, kowa yasan d'unbin alkairin daya sauka a wannan families guda uku a yau. Dan danan labari yafara karad'e asibiti da gidajen su Galadima Dana s
u Munaya.
Masarautar gagara badau, masarautar su papi, su Momma duk labari ya Isar musu harda hotunan babies gaba d'aya, kafin kacemi labari yafara zagaye social media, *FANS NA RAINA KAMA FA* babu ala, dama duk sungama shirinsu, (danma ansamu sa6ani
masu tafiya india
🤣
, Wanda basu kai ga tafiya ba ALLAH ya taimakesu saiku tattala kud'in jiyginku babu ruwana
😹😂🤸🏻
♀
).
Bakin Galadima da Yaa marwan da dukkan ahalin wad'annan dangi kam yakasa rufuwa, hardamu ma masoyansu.
Yauma dai su doc
tor Farida da jama'ar asibiti sunsha k'yaututtuka, Dan Muftahu ya baza abin mamaki, ( lokacin da su sarkin mota zasu fitone yagansu kamar a rikice, shikuma zai fita daga masarautar shine ya tambayesu, sarkin mota ya fad'a masa, bai bisuba saiya wuce asibit
i, shine yasaka aka canjama Munubiya d'aki, aka tanadi gadon Munaya kuma). dukda Galadima yayi mamakin ganinsa hakan bai sakashi tambayarsa ba ko katse masa hanzari, ko'a fuskama bai nuna mamakiba.
***************
Mama Fulani Na kishin gi
d'e bisa kilisarta kuyanginta Na bautar da suka saba, Wambai na gefenta yana nuna mata pictures na gidaje dayake son za6ar d'aya daza'a gina masa shima acikin masarautar, don mama Fulani tamatsa suyi aure, shi matawalle yamace bazai zauna da matarsa a k'a
sarba. Amma mama Fulani tace dolene saiya zauna.
Wata baiwace ta shigo jikinta sai 6ari yake, ta zube a gabansu tana huttai, Wambai ya daka mata tsawa.
Firgita tay tayi baya zata fad'i, Mama Fulani ta d'aga masa hannu alamun ya barta.
“hab
a Granny kina ganinfa yanda ta shigoma mutane a haukace, saikace wasu sa'ointane a wajen?”.
Uffan mama Fulani batace masaba, sai wani k'asaitaccen murmushi datayi tana kallon amintacciyar baiwarta, alamu tamata da ido na ta tambayi mi dattijuwar ta
zo dashi?.domin itace dama mai kawo ma mama Fulani duk wata gulma takowane 6angare a masarautar, Dan ita babu sashen dabata da 'yan lek'en asiri, kuma wannan dattijuwar baiwa itace shugabarsu, komai suka tattaro ita zasu fad'awa ita kuma takawo ga mama Ful
ani.
“mike faruwa tulluwa?”. Amintacciyar baiwar mama Fulani ta fad'a tana kallon dattijuwa tulluwa dahar yanzu jikinta baibar 6ariba.
“Ranki ya dad'e ki gafarceni da abinda nazo fad'a, banida za6in daya wuce hakan, domin da kiji a bakin wasu
gara kifara ji abakina danki tabbatar nasan aikina”.
Mama Fulani ta hura hanci, yayinda izzarta ta k'aru, sosai ta tashi zaune idonta akan tulluwa.
Batareda tace uffanba tulluwa tacigaba da magana, Dan tasan ma'anar kallon ta cigaba da maga
na kenan.
“ranki ya dad'e yanzunnan labarin haihuwar matar Galadima ta iso wannan masarauta, ba haihuwar baceba abin girgiza abinda ta haifanne, idan kinbani izini sai na fad'a uwar gijiyata”.
Wani kakkauran yayu mama Fulani ta had'iye, Wamba
i daya cika yay fam da haushin wannan shegiyar baiwar ya Dalla mata harara, “dalla malama kifad'a kinwani zauna cancana magana kamar wata zuma”.
“ALLAH ya huci zuciyarka ranka ya dad'e, maganarce tanada nauyi. dama labari ya iso ta haifi yara uku n
e maza biyu mace d'aya....”
Wambai yay masifar razana harda mik'ewa, mama Fulani kam ko motsi batayiba, sai wani k'ayataccen murmushi na k'asaitattun mata masu izza da mulki tayi, ta d'ago ido ta kalli Wambai cikin harara tace “kai kuma miye na mik'
ewar?”.
Tunawa yay akwai kuyangi saiya saki murmushi basarwa, yace “mamaki mana Granny, 'ya'ya uku fa a 1 time, dolene na taya d'an uwana murna ai”. bai jira cewarta ba yafice da hanzari.
Lumshe idanu mama Fulani tayi bayan Wambai ya 6acema
ganinta, ta kalli amintacciyar baiwarta fuska d'auke da murmushi nan tace araba k'yaututtuka, takuma sallami kowa.
K'yaututtukan da mama Fulani tasaka a rabama bayin gidan yasaka zancen haihuwar munaya yakuma karad'e lungu da sak'o na m
asarautar, masu murna nayi masu kuka nayi, dan kowa dai yasan magadan masarautar gagara badau sun iso, tunda kowa yasan Galadima ne magaji mai jiran gado, _(karku manta haryanzu sarkin yanzu sarautarsa ta ruk'on kwaryace, Dan mahaifin Galadima tsohon Sarki