Showing 351001 words to 354000 words out of 407268 words

Chapter 118 - Raina Kama COMPLETE

ya dace.

A na

nma Galadima ba zama yayba, washe gari yabaro Kashmir shida Akash suka dawo India, Dr Ajay kawai suka baro can, wasu kud'ad'en ya fara turawa dake hannunsa, Dr Erfan Fahad yafara treatment d'in Abie.



**************************

Busy d

a Galadima yayi yasaka shi da Munaya waya sai time to time sukeyinta, a koda yaushe kuma cikin kwantar masa da hankali take, a Daren da zasu wuce Niger nema suka d'anyi doguwar hira, yayta shinfid'a mata dokoki akan yaransa, ita dariyama abin yayta bata, t

a dai danne da binsa da to Dan a zauna lafiya, ta d'ira da masa godiyar hidimar da yasaka Muftahu ya kawo musu da sunan tsaraba da dukkan abinda zasu buk'ata, wai ba sai sunje sunkaima mutane nauyiba.

Washe gari suka Nufi Niger Republic cike da zu

mud'in son kasancewa da ahalin mahaifansu.

Tafiyace da sukayi cikin isassun motoci babu takura, Dan Galadima motoci ya aiko musu har hud'u, wad'anda zasu iya jurar dukkan wata wahalar shiga sahara, tareda kwararrun driver's da sukasan hanya. gashi ba

suda matsalar Abinci dan sun tanadi abinsu. Tafiyar sassafe sukayi. Dukda sakko da sukayi basu sami shiga Agadas ba a ranar, dole suka sami mafaka suka kwana, ranardai kam babu maganar waya da kowa dake Nigeria, balle kuma su Galadima. Sosai Munaya taji ke

war mijinta, balle da taga su Munubiya nata soyewarsu, hasalima d'aki d'aya suka sauka a masaukin, itakam itada laraba saboda kula da yara.

Ya Marwan kam shi ai gaba ta kaishi, dan wannan damar ya samu ya more amarcinsa, Dama an dad'e ba'a had'uba

🤭

.

Dukda magiyar da Munubiya taita masa akan yabari saisun koma gida amma yace Sam bama ta isaba, yaudai saiya lasa, dole ta barshi yayi yanda yakeso harma da bashi gudunmawa, dan sunyi missing juna, saidaga baya taita masa zun6ure-zun6uren baki, shi

kam yayata mata tsiya da gwalo.

Da safe Munaya yanayinta kawai ta kalla taita shek'a dariyar mugunta, harda Munubiya ta tsargu. Su Feena nata tambayar Miye?.

Munaya tace, “kuma Ku gano da kanku, dan babu ruwana”.

Su Ayusher dai basu fa

himci komaiba, har Munaya tagama shak'iyancinta tayi shiru a motar.

Yau d'inma dai sai yammaci lik'is suka isa Cikin Birnin Agadaz.

Dan anata kiraye-kirayen sallar Magrib.

Tunda suka shigo garin inna tai zugum tana tuna wasu shud'ad'd'u

n shekaru da abubuwa masu yawa suka faru, babu inda tagane saboda dad'ewar da sukai da barin tushensu, garama ita, mama Rabi'a ma bata fahimci komaiba ita, dan wayonta a wancan lokacin baikai Na inna ba.

Kula da damuwar da inna take cikine ya sama

Abba kama hannunta ya rumtse a nashi alamar lallashi. Batace dashi komaiba, sai d'ora kanta datai gefen kafad'arsa.

Driver dake driving motar dasu innar suke ciki yace, “Hajiya ina muka dosa to?”.

Shiru Inna tayi takasa magana, saboda kuka daya

taho mata, tana fargabar ko zasu sami k'ar6a daga ahalin nasu kokuwa sa6ananin hakan, gashi harda uwar gayya sukayo.

Mama Rabi'a ce tai k'arfin halin cewa “Zamuje masarautar garinne”.

Daga Abba har Abbansu Feena kallonta sukayi da matuk'ar m

amaki, mama Rabi'a dai tai k'asa da kanta, dan batada bakin amsa musu dukkan tuhumarsu. Inna kam ai saita fashe da kuka k'asa-k'asa.

To Mudai bamusan ina aka dosaba, kallon gari kawaine namu, ni inata fama da Abdurraheem ma dake kukan gajiya, nasan

wanka kawai suke buk'ata, shine zaimin bore, ALLAH ma ya soni Sauran basu d'auki amshiba, dan duk suna hannun su Feena da muke tare a motar.

Innaro dai tanata baza ido da ta6e baki, burinta dai a Isa taga abinda yasa aka tasosu daga wata uwa duniya

.



🤣

innaronmu ta mutunci badai za'a canjaba kam.

🤦🏻

‍♀

Duhun da dare ya farane yasa bamu fahimci inda muka iso ba, inna tasan baza'a ta6a barinsu shiga masarautarba kai tsaye, Dan haka ta fita daga motar, takai mintuna kusan 20 tana fa

ma da masu tsaron k'ofar, amma sunk'i aminta da shigarsu, dukda kamaninta da suke hangowa dana ahalin masarautar.

Ana cikin haka saiga wani matashin saurayi dabazai wuce sa'ansu Yaa Marwan ba. Yanda yake tafiya cikin tsari da Isa zai tabbatar maka sh

i jinin gidanne, masu tsaron k'ofar duk suka zube k'asa suna masa barka da fitowa, bai amsa musuba sai inna da yaketa faman bi da kallo, itama dai idonta na'a kansa.

Kamannin mahaifinta take kallo tsaf tattare da saurayin, yayinda shima dai take masa

tsananin kama da nasa ahalin, ya d'auke kai da nufin barin wajen batareda ya tankama innarba, murmushi tayi kawai, Dan shariya da Isar mulki wannan jinin gidansune, shiyyasa mafi yawan lokaci ba hak'urine kawai ke sakata share haukar y'an gidansuba, harda

wannan halayyar data zama jinin jiki.

Cikin harshen buzanci tamasa magana.

Cak ya tsaya, kusan wasu seconds sai kuma ya juyo yana kallonta.

Inna tace, “dukda banida hurumin tambayarka wanene kai a masarautar nan, domin yanayinka ya tabba

tar min kasancewarka jinin gidan, ina rok'onka alfarmar tambaya da kuma taimako”.

Nanma kallonta kawai yake, tamkar bazaiyi maganaba saikuma ya matso gabanta, alamar yana saurarenta.

Sunayen mutum uku ta lissafo masa akan ko sunada rai.



Da mamaki sosai yake kallonta, dukda yanayinta ya nuna ita buzuwace, amma ba mazauniyar wannan yankinba, Dan suturarta da wasu abubuwa da dama ya banbantata al'ummar yankin, gashi kuma ta lissafa masa sunayen manyan mutane masu daraja a masarautar.



Shima cikin harshen buzancin hace, “baiwar ALLAH ked'in wacece?”.

“ta hanyar shiga damu wannan gidan kawai zakasan wacece ni”.

'Dan jim yay alamar tunani, zuwa can sai yace, “ina zuwa to”.

Kai inna ta jinjina masa, ya koma ciki, inna

kuma tadawo jikin motarsu tana bama su Abba hak'uri.

Sukace karta damu, tabi ahankali.

Kusan mintuna 30 saiga saurayinnan ya dawo tare da wasu tsoffi biyu, inna Na hangosu ta nufosu itama, bata ganesuba, amma haka ta risina tana gaishesu cikin

yarensu.

'Daya a cikinsu tamata wasu y'an tambayoyi, duk inna ta amsa mata kai tsaye, mamaki ya kamata, takuma jeho mata wata tambayar, nanma dai inna ta amsa.

Tsohuwa tayi murmushi, sannan tabama masu tsaron k'ofar umarnin barin motocin su

inna shiga cikin masarautar.

Inna taji dad'i sosai, taita mata godiya.

Shigarmu katafaren gidan mai yalwace da haske a ko inane yabamu mamaki, bayan driver's d'in sun faka motocin inda aka nuna musu duk muka fito, mudai kallon kallo muk

a koma a tsakaninmu, Dan munga abinda ya girmi tunaninmu, hadimai sai kai kawo sukeyi dukda duhun dare.

Iya abinda zamu iya buk'ata kawai aka fidda mana a motocinmu, tsaffinan da matashin saurayi daya maidamu television sukai mana iso wani Sashe, ba

bu kowa amma cike yake da komai Na buk'atar rayuwa, yayinda kwanmu da kwarkwatarmu zai ishemu mu sakata mu wala.

Mun gaida tsoffi nan dukda bamu da tabbacin sun iya Hausa, amma a mamakinmu duk sai suka amsa mana, suka kuma mana sannu da zuwa sannan

suka fita, amma banda wannan saurayi daya koma gefe ya zubama dukkan wani motsinmu ido, musamman ma mu hud'unnan, Ni munubiya Ayusher Feena, bansan miyake kallo tattare damuba, nidai damun had'a ido dashi saina zuba masa harara, yakanyi murmushi ya d'auke

kai, Ashe sauran y'an uwanama hakance ke faruwa a tsakaninsu dashi. Yaa Marwan da Fadeel kuma suna lura daduk abinda ke faruwa, amma suka k'i cewa uffan. Dan yak'ima kowa magana a cikin mu, shiyyasa muma duk mukayi watsi da lamarinsa, babu Wanda ya tanka m

asa.

Babu jimawa saiga tsoffi nan sun dawo tare da wasu y'ammata kusan goma, kowacce abinda ke hannunta ta ajiye, sannan duk suka durk'usa suna gaishemu.

Tsoffi suka sake zama muka gaisa, sannan suka nunamana d'akunan barci, dacewar mu hu

ta zuwa safiya koma mikenan dai saji.

Innaro dai bin kowa take da ido, ga gajiya Na cinta ga tambaya fal ranta, dasun had'a ido da inna saita sakar mata murmushi kawai, hakama Abba da abbansu Ayusher, saibin matan nasu suke da kallon tuhuma, amma s

u inna sunk'i bada dukkan k'ofar da kowa zai fahimci wani Abu.

Saurayinan ya fice bai tankama kowaba, yana fita muka shiga ta6e baki. Amma bamuce uffanba dai.

Nace, “Ni dai bata abincinnan nakeba, nasami ruwa nayi wanka shine matsalata”.



Hararata mama Rabi'a tayi, tana fad'in “Baki da tausayi Munaya, wad'annan bayin ALLAHn ai suke buk'atar duk wannan bakeba, musamman Abdurraheem dashi baima son takura Na kula”.

“Yo mama nidai kaina Na sani wlhy”.

Rankwashi Yaa Fadeel ya zuba

min akai, Na dafe wajen idona Na cikowa da kwalla, “Amma Yaa Fadeel da zafifa?”.

“Ai dankiji zafin namiki”.

Yanda nahau matsar kwalla duk sai suka haumin dariya, hardasu Abba, haushin hakan yasani tashi Na shige d'akin dake kusa da inda muke

zaune.

Kutt d'akine k'ato, d'auke da makeken wani irin gado mai k'yau, saida nayi bismilla sannan Na fad'a saman gadon, Dan tsayawa muku lissafin had'uwar d'akin 6ata lokacine, ahaka Ayusher ta shigo ta sameni, muka 6ararraje abinmu.



*B

ayan awa 3*

Duk d'inmu kowa yayi wanka ya canja kayan barci, yaranma an musu, munci abincin dai sama-sama, Dan ba irin cimar da muka saba baceba, amma dayake akwai fruits dawasu abubuwan irin shigen abincinmu sai muka harhad'a mukai nak, garin dad'an

sanyi gaskiya, aka nad'e su Ameen cikin kayan sanyi su duka, kowa d'akin da yay wanka yakoma ya kwanta a matsayin masauki.

Mudai tare da innaro da laraba muka kwana, saboda matsalar yara.

To dayakema kowa gajiya taci k'aniyarsa lafiyar ALLAH mu

kasha barcinmu, amma wlhy akwai d'an karen sanyi, Dan zuwa asubahi harda wata iska mai azabar sanyi daban tsoro, ALLAH ma yasomu akwai manyan barguna a d'akunan, gakuma ko ina ruf an d'auki mataki, da alama sun saba da kayansu su dama.

Tunda saf

e sosai aka kawo mana karin kumallo a kuloli masu k'yau.

Mudai kam bama mu tashiba, saisu innarmu, koda hadiman dazasu mana gyaran sashe. Sukazo sai komawa sukayi, dan barci muke, su Abba ne kawai suka tashi dasu innarmu.



Kusan awanni

biyu da kawo abincin tsoffi nan sukazo kiran inna, sai suka tafi da mama Rabi'a, mu munatama barcinmu bamusan duk anayiba.

Tunda suka fito idon Inna ya cika da hawaye, yau sune a mahaifarsu, bayan tsawon shekaru da suka d'auka basannan, sosai masarau

tar ta canja, an k'awatata fiye da da, abubuwan cigaba masu d'unbin yawa sun yalwatu a cikinta, ga gine-gine Na k'awa da akayiyyi cikin masarautar.

Itama dai mama Rabi'a bata tuno komai dan sanda sukabar masarautar bama tasan kantaba.

Sun i

sa wani Sashe mai girman gaske da k'awa, kamar yanda kowanne bango yake da hoton Rak'umi haka shima wannan, an k'awatashi da hoton rak'uma har Uku, hadimai sai mik'a gaisuwa suke gasu inna, nasudai d'aga hannu da murmushi, Dan ita inna ta mance abubuwan da

yawa da suka shafi tsarin masarautar tasu, to bama wayaune da itaba awancan lokacin, sai y'an abubuwan daba'a rasaba.

Sun Isa katafaren falon daya k'awatu da kayan alatu irin Na yankin nasu, basu tsaya ananba sai a wani dake gabansa.

Buzuwar t

sohuwa ce k'yak'yk'yawa, mai cike da d'umbin kamala da halin dattako, tana zaune bisa wata darduma ruwan goro, hadimai biyu namata hidima.

Batako d'ago kai ta kalli kowaba, dukda tasan da shigowar su inna, Tsoffi nan guda biyu suka rissina suna sa

nar mata zuwan su inna.

Mayafin dake yane da jikinta Na yadin lafaya irin kayan buzaye ta janye saboda rufe mata rabin fuska da tayi, ta d'ago kai tana kallonsu inna Wanda suma itad'in suke kallo.

Wani Murmushi ta sakar musu Na musamman,

yayinda idonta ke binsu da kallon k'urilla mai nuna alamun kallon kamannin wani a jikinsu.

Cikin yarensu Na buzaye tama tsoffin da hadiman Umarnin ficewa.

Saida suka fita sannan ta yafito su inna alamun su matso gareta.

Inna da mama Rabi'

a suka matsa inda take, ta kamo hannayensu ta rik'e a nata tana murzawa, kusan mintuna biyu, sudai su inna Na kallonta, tamusu nuni da subata tafin k'afarsu ma.

Inna a ranta tana mamakin kenan har yanzu canfe-canfe da muguwar al'adar gidan Na nan da

i?.....

Tunaninta ya katse lokacin dataji hannun tsohuwarnan bisa fukarta, kallon juna sukayi itada mama Rabi'a, sannan suka maida kallonsu ga tsohuwar da idonta ke a rufe tana murmushi da cigaba da shafa fuskokinsu.

Kusan mintuna biyu sannan

ta bud'e ido akansu, race, “lallai kud'in ahalin wannan gidane Na gaskiya, masu tafe da babban abin al'ajab da ba'a ta6a samuba a wannan masarautar, barkabku da dawowa hamshak'iyar masarauta mai d'unbin tarihi da yalwar arzik'i, minene sunayenku?”.



Cikin had'iye yawu inna tace, “Ni Ai'sha, itakuma Rabi'a ”.

Tsohuwa tayi murmushi mai k'ayatarwa, sannan tajawo kaskon wuta dake cike da rushi gabanta, ta bud'e wani kasko mai k'yau ta zuba garwashi kusan bakwai sannan ta saka turare mai d'unbin ya

wa a ciki, dandanan wani k'amshi ya baibaye falon, gabansu inna ta tura kaskon, ta jawo wani mayafi ta mik'a musu da musu nuni su rufa dashi.

Basuyi musuba, Dan ita inna duktasan hakan al'adar masarautar suce. Haka suka shige mayafin k'amshin yanata

baibayesu, kusan mintuna biyar ta bud'esu da kanta.

Babu Wanda yay magana tsakanin ita da su, saiga mutane sun fara shigowa d'ai-d'ai cikin falon.

Kowacce cikin shiga ta alfarma irinta cikakkun Buzaye, hakama mazan, kowanne fuska a nad'e cikin

rawani.

Dukkan mai ruwa da tsaki saida yagama hallara, adadin wasu mintuna saikuma ga wani dattijo mai cike da tarin kamala ya fito ta wata k'ofa daban, a tare dashi da mata biyu suma cikin nutsuwa, kowa saida ya mik'e a falon har wannan tsohuwa.



Dattijo ya zauna bisa kujera dake gefe, sannan kowama ya zauna, cikin risinawa sukaita gaisheshi, kansa kawai yake jinjina musu, hakanne yasakasu inna fahimtar lallai wannan shine Sarki mai mulki a wannan masarauta yanzu.

A cikin nutsuwa yay maga

na, idonsa nakan mama Rabi'a da inna.

“Lale marhabun da dawowarku wannan masarautar mai d'unbin tarihi da dattako, mai takaici dakuma dana sanin farrak'a mafi yawan ahalinta bisaga bahaguwar al'ada mai durk'usar da kowanne irin ahali”.

Idon In

na cike da kwalla, da d'okantuwa da furucin wannan adalin Sarki mai kama da jirwayen nadamar kasatuwar abinda ya wanzu abaya dama Wanda basuda tabbacin faruwarsa ko dakatawarsa.

“Muna godiya mai cike da girmamawa da farin cikin waiwayen bayanmu duk

da muna tare da fargabar koza'a kar6emu, amma lallai an ciremu daga wannan fargabar da muka shigo da ita wannan yanki”.

Dattijo ya jinjina kansa yana murmushi.

Tsohuwar d'azunce ta kalli dattijon Sarki, ta buk'aci shigowar sauran tawagar b

ak'in dasu inna sukazo dasu.

Kai tsaye yabada izini.

Kwammu da kwarkwatarmu muka shigo, hardasu Aiyaan dasu Innaro, duk muna d'auke dasu Amaturrahman, nanma dai abin kallon muka gani da mamaki, tamkar yanda muka baro wasu abaya, mun kasa fah

imtar inane su Innarmu suka kawomu kuma?.

Gaisuwa mukaiyi irin wadda muka iya, hakama su Abbanmu da aka bama wajen zama Na musamman a gefen wannan dattijo.

Duk sun kar6a mana a

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login