Showing 159001 words to 162000 words out of 407268 words
Muryarsa c
an k'asan mak'oshi ya furta “my friend are you okay?”.
Banza na masa, nakuma k'i bud'e odon, lallai mutuminnan yacika d'an latsin rainin wayo number 1, yanzunan Galadima har yanada bakin yimin wannan banzar tambayar?, idona a rufe har yanzu na bud'e
baki cikin salon tsiwa zan maka masa bak'ar magana, amma saiya d'ora yatsansa saman bakina yana fad'in “shiiii!
🤫
” da bakinsa, shirun kuwa nayi kamar an rufemin bakin Dan Nina Na tuna illar yin tsiwar.(
😝😂
)
Ya matso dani jikinsa ya rungume, hannunsa
na buga gadon bayana k'ad'an-k'ad'an, ya d'ora bakinsa saitin kunnena, “yanzu kin gane banbancin Sameer da Munaya right?, idan kuma har yanzu baki fahimta ba to bakinki ya cigaba d'amin tsiwa OK?, nikuma bazan gaji da punishment nashi ba sala-sala yalla6iy
a
💋
”. ‘ya k'are maganar da sumbatar cikin kunnena’.
Babu shiri na k'ank'amesa dan har cikin kwalwar kaina naji sumbar nan.
Kad'an ya buga bayana sannan ya janyeni daga jikinsa ya sauka daga saman gadon.
“hasbinallahu wani'imal wakil” na
iya maimaitawa kawai, na k'ank'ame pillows d'in gabana ina rintse idanu da cije lips (copy copy
😝
).
Kusan mintuna 15 duk nazata yama fitane, sai kawai jinai an d'aukeni. a razane na bud'e idanuna, kallon ido cikin ido mukaima juna, da matuk'ar
Sauri na maida nawa na lumshe.
Wani muskilin murmushi Galadima yayi yana cije lips.
Ba shiri na bud'e ido, saboda jina cikin ruwan zafi, yunk'urawa nayi zan mik'e cikin 6ata fuska ya maidani ya zaunar yana fad'in “za6i ya rage naki, zama
kiyi da kanki, kokuma ni nayi miki..”
Banma bari yakai k'arsheba na koma na zauna ina kare k'urjina.
Kafad'a ya d'age sama yana ta6e baki da fad'in “hummm”.
Fita yay daga bathroom d'in ya rufe mata K'ofar.
Na kai tsawo
n lokaci a bayin ina Gasa jikina, dan nasan idanma banyiba kaina nama mugunta, saida naji ko ina ya saki sannan nayi wankan tsarki ina hawaye, bansan yanda zan fassara wannan muguntar ta Galadima ba kuma, wannan karon kuma tsautsayin zaice kokuwa ba yin Ka
nsa bane?.
Haka dai na kammala na d'aura towel d'ina, a zuciyata ina addu'ar ALLAH dai yasa ya fita, dan towel d'in guntune, bai gama rufe cinyoyina bama baki d'aya.
Da sand'a na fito, yauma inajin zafi kad'an-kad'an, amma ba kamar na ranar ba.
ganin baya d'akin saina ida rufe k'ofar na tako cikin d'akin sosai.
Ina neman kaya a wardrobe ina share hawaye, indai rashin tsiwar dayake fad'ace na daina masa, dan bazan zauna ya illatani a banza ba, wannan k'addararren cikinma daya hanamin ganga
r jiki hutawa da ciwuka ya isheni, basai na cigaba da 6alloma kaina wata muguntar tasa ba.
wata 'yar riga mai d'an nauyi-nauyi na samo, na cirota dan sanyi nakeji, juyowar da zanyi saina gansa zaune bakin gado yana danna laptop, hannunsa d'aya rik'e
da glass cup yana shan fresh milk hankali kwance.
Saida nad'anja baya, nakuma bud'e rigar ina kare jikina.
Duk abinda takeyi yana kallonta ta gefen ido, amma yawani share kamar baima San da itaba.
Da bin bango da sand'a na koma bayin,
ta gaba kuma ina karewa da rigar.
Saida ta shige ya d'ago kai yana kallon k'ofar bayin, saikuma ya girgiza kai yana murmushin gefen baki. cigaba yayi da aikinsa a nutse.
Barci nakeji, ga zazza6i yafara rufeni, hakan yasa ina gama saka rigar na fi
to, naci serious kawai sannan na fito.
d'ago idanu yayi muka had'a ido, da sauri nad'an rankwafa inajan rigar barcin k'asa wai danta rufemin cinya zuwa kwauri.
Baki ya ta6e yana wani janye ido cikeda basarwa. Irin shi baiga abin kallo d'in nanba
.
Ni kuma na dalla masa Harara ina k'ok'arin hayewa gadon.
“ji mana”. ‘yafad'a cikin izza’.
Banza na masa zan haye gadon.
Yace “iyim, bakije daddarawa ba kenan yarinya, saina sake kaiki yanzunnan....”.
Kafin ya rufe baki nama
iso gabansa na tsaya.
d'agowa yayi yana kallona yana kur6ar fresh milk nashi, ya d'agamin gira d'aya.
Baki na turo masa ina share hawaye.
Ya kamo hannuna ya zaunar kusa da shi, “nikam yalla6iya karki haifomin abin cikin kwan da halin kuka,
bana son ragwan taka, 'yata ko macece jaruma za'ayi, irin wadda labarinta zai zaga lungu da sak'o na duniya”.
Harara na balla masa, yay saurin rik'e cup d'in hannunsa dayake zuba frash milk a ciki, “eh me, malama karkisa hantar cikina fitowa, irin wa
nnan harara haka”.
Kad'an yarage banyi dariya ba, da gaskiyar Momma, halin Galadima d'aya da Sauban, tsantsar harmutsine da sanya damuwa a rai ya lullu6e halinsa na barkwanci, hakan kuma yanada nasaba da rashin samun mai jansa a jiki yana d'auke mas
a kewa da rage masa rad'ad'in damuwarsa. Momma hankalinta nakan jiyyar Abie, Aunty mimi kuma rainon Sauban, mom kuma tayi aure lokacin dayake buk'atar makusanci, s.......
Firgigit nayi saboda hancina da yaja, na kalleshi ina tura baki.
“maida wu
k'ar yalla6iya, abin bana fusata bane, wace duniyar kika tafi hakane da nisa inata magana?”.
Marairaice fuska nayi ina shirin fara kuka, “please ka barni na kwanta barci nakeji”.
Kofin hannunsa ya mik'amin, na waro idanu ina girgiza masa han
nu alamar a'a”.
Shima saiya waro nasa idanun yana fad'in “why?”.
“kawai ni bazan sha bane, aje a zubamin wani abu”.
“hakane kuma”. ‘ya fad'am yana kamoni ya jawoni jikinsa’.
Saman cinyarsa na zauna, da hanzari nafara k'ok'arin mik'
ewa. shima saiya kama hannayena ya maidasu baya yanda bazan iya kata6us ba, madarar ya d'auka ya guntsa da yawa a bakinsa.
Waro idanu nayi ganin ya nufo bakina gadan-gadan, duk yanda naso kauda fuskata ya gagara, na datse hakwarana da sauri, shi kum
a saya toshemin hanci, hakan yasa ni bud'e baki dole, dan ina buk'atar shak'ar numfashi. Tas ya juyemin fresh milk d'in abakina, sannan ya kuma rufe hancina saida na shanyeta sannan
ya janye bakin, ni dashi duk muka hau sauke numfashi, kuka na sanya masa,
amma hakan bai hanashi kuma guntsar madarba ya kuma juyemin a baki na, haka yayta min, ya kuma k'ara rabin kofi kuma, saida yaga ta kwalin ta k'are sannan ya sakarmin hannu na tashi zaune.
Bansan kawai na fara kaima k'urjinsa k'ananun dukaba, ina fad
'in wlhy sai ALLAH ya sakamin, kai bama zan yarda ba fa, saboda k'azanta kaita had'a yawunka da fresh milk kana d'uramin, ni bazan yardaba”.
Shagala kawai yayi yana kallona, yakasa kare kanshi balle yunk'urin hanani, saida nayi mai isata sannan na
fad'a k'irjin nasa ina raira kuka.
Lumshe idanunsa yayi yasaka hannayemsa ya zagayeni sosai yana kuma sakani jikinsa sosai. Nima sainayi luf Ina shak'ar k'amshinsa da yariga ya mannema fatarsa.
Munja wasu times a haka, ni ina kuka shi kuma idon
sa a lumshe yana shafa kaina da saurarena.
Jiyay kawai jikinta ya saki, alamar barci ya d'auketa, sai ajiyar zuciya da take ta saukewa, bud'e idonsa yayi, sannan yakai bakinsa a hankali ya sumbaci sumar kanta dake tare da danshin ruwa har yanzu. zafin
zazza6inta dake ratsa 6argon jikinsa ya sakashi fidda huci yana kuma sumbatar kanta.
Dr Farida ta sanar masa babu abinda zai hanata wannan zazza6in, koda tasha magani ya sauka saiya dawo, sai idan cikin yayi kwarine maybe ta daina ma gaba d'aya, amma
mai juna biyu ba'a rabata da k'ananun ciwo makamantan haka. jiyay ya kuma k'aunar Momma d'insa a ransa, a hankali ya furta I love you my Momma”.
Tashi yay d'auke da Munaya a hannu, ya kwantar da ita sannan yaja bargo ya lullu6a mata. tare da sunku
ya wa ya sumbaci goshinta ya shafa cikinta da hannunsa sannan ya mik'e ya koma inda yake.
Ya cigaba da aikin dayake a laptop Wanda ban fahimci komaiba a ciki, tsawon lokacin yana aikin, saida ya fara hamma sannan ya kashe. bayi ya shiga ya d'auro alwa
la, ya gabatar da nafila kafin yay shafa'i da wutiri yaja doguwar addu'a da kirari wa Ubangijin talikai, harda hawayensa sannan ya mik'e.
Ya kuma daidaita hasken fitilar d'akin sannan ya hau gadon shima ya kwanta, yay musu addu'a ya shafe cikin munaya
(
😂
Galadima saboda tsaro ba tsoroba ko
🥺
).
a zatona zai rungumeta, sai naga ya gyara kwanciyarsa kawai a gefenta yaja bargo shima.
Galadima asuba ta gari, (ni dai rungume nawa mijin zanyi aradu
🤫🙈
⛹
🏻
♀
).
Ga bannin asubahi
zazza6in munaya ya sauka, hakanne ya sakata samun dad'in barci sosai, ta kuma kanainaye Galadima, wanda shi da kansa ya mirgino har inda take cikin barci ya rungumeta, dukda zafin zazza6inta nata ratsa nashi jikin yakasa barinta. ahaka kiran sallar farko y
a riski kunnuwansu.
Kusan a tare suka farka, ganinsu manne da juna yasaka kowa barin jikin d'an uwansa da sauri, munaya dai kunya ta sakata juya baya, amma boss ko a kwalar rigarsa, saima tashi da yayi yana wani ciccin Magani ya shiga toilet.
Alwala ya yo, baiyi mata magana ba ya fice abinsa.
Munaya ta raka bayansa da harara tana fad'in Girman kai dai rawanin tsiya wlhy. tashi tayi itama ta shiga bayin, amma sa6anin shi ita harda wankan gasa jiki (lallai kinji basawa Munaya
🤭
, wannan gasa
jiki dabaya k'arewa haka
🤥😂
).
Fitowa tayi tanata kumbura fuska, ni dai na lalla6a na shige bayinta danna dandalo arzik'i
😝
lol (koya kukace fans
🤷🏻
♀
😂
?).
****************************
Ban sake jin d'uriyarsa ba sai around 9:30am.
Tashina a barci kenan na rarrafa zuwa bayi da k'yar nayo wanka, dan banajin dad'in jikina gaba d'aya, danan ya saki sai nan ya kama ciwo.
Motsin mutum naji a bayana dan haka na waiga, Galadima ne cikin Farin wando da t-shirt itam fara ta
s, ya d'aure k'ungunsa da Navy blue d'in belt, sannan ya kawo jacket navy blue itama ya saka, babu takalma a k'afarsa, sai dai k'afar fes tamkar ba'a takata a k'asa, sai agogon azurfa mai k'yau d'aure a tsintsiyar hannunsa.
hummm dan k'yau kam dai ya
yishi, sai dai ni bawai ya birgeni bane
😏
(ho Munaya banda zuk'i ta malli dai
🤥🤣😝🙆🏻
).
Janye idona nayi na maida kan gyaran gashina da nakeyi.
Shima baice uffanba ya wuce wajen frigate, fresh milk ya d'akko yatako gaban mirror inda nake
zaune. a saman mirror ya ajiye kwalin madarar ya jingina bayansa shima, idonsa a kan gashina danake gyarawa. ya d'au madarar ya zuba a cup d'in daya d'akko tare da mik'omin.
“ni ba ita zan shaba”. na fad'a ba tare da na kalleshi ba.
“mikenan?
”. shima yafad'a cikeda k'asaita.
Yanzunma ban kalleshi ba nace “tea”.
Kofin ya dire saman mirror yana tattare hannun rigarsa, “salon ki k'onamin idon abin cikin kwan kenan, to za6i ya rage naki, sha da arzik'i ko kuma d'ura”.
Babu shir
i na d'auki kofin na kwankwad'e, dama iyayine inajin yunwar.
Kofin na mik'a masa ina 6ata fuska tamkar zan fasa ihu.
Ya d'agamin gira yana fad'in “taimakon kai my friend”.
Gefe nayi da fuskata ina fad'in “kai duk salon mugunta ka sani a
i”.
“martabar gudan jinina nake karewa”. yay maganar yana k'ok'arin ficewa.
Baki na na ta6e ina harar bayansa, su gudan jini anji jiki kuwa.
Ganin zai fice nai saurin cewa “nifa inason zuwa kitso, kuma zan koma school”..
T
sayawa yay cak daga yunk'urin fitar da yakeyi, Batare daya juyoba yace “babu wannan tsarin a masarautar gagara badau”.
Yana gama fad'a ya ida ficewarsa.
Tamkar zan fasa kuka nayi jifa da cumb d'in hannu na ina fad'in “ina ruwana dawani tsarinku n
i, makaranta ta nakeson komawa ehe”.
Yana jiyota amma ko'a jikinsa yaci gaba da k'ok'arin fitarsa hankali kwance.
★★★★★★★★★
Tunda Aryaan ya shigo da gudu inna ta tareshi tana fad'in “kai lafiya? minene na gudu?”.
“innarmu wlhy Uncl
e ne yace ki shirya mana kayanmu ni da Aiyaan zai aiko gobe a kaimu wajen Auntynmu”.
Inna tayi d'an murmushi kawai, dan ita bata d'auki maganarma serious ba.
Su dai su Aiyaan sunata murnarsu, sun tafi d'aki sun hau had'a kaya.
Babu dad'ewa
da yin haka saiga daddy ya shigo da sallama, inna ta amsa masa tana gyara zama, shima zama yay kujerar dake kusada k'ofa, ganin haka inna ta fahimci da magana yazo, dan haka ta maida dukkan hankalinta Kansa.
Bayani yamata dalla-dalla akan zancen da s
u Galadima sukazo dashi, ya d'ora da fad'in “saiki shirya dan zamuje ai miki passport”.
Inna tace, “amma dadynsu nake ganin ai da kud'in kukaje kamar zaifi”.
Murmushi Dady yayi, yace “Ai'sha nasan miyasa kikeso zamewa, to ai kaf cikin matan
yayan kece ya cancanta kije koda ace bawai Galadima ne ya biyaba, maganar ciwo Muke bawai jin dad'i ko gutsiri tsomar wasu ba, ki shirya dan zai turo wanda zamuje immigration office d'in”. daga haka ya tashi ya fice.
Shiru kawai inna tayi, itadai i
nda ta itace da antafi da ko innaro, dan tasan wannan tafiyar dukda ta ciwoce sai ta janyo 6acin rai a gidan.
Aiko tamkar inna tasani, dan ana fad'ama innaro tace “bata amince ba, ita ta haifi auwalu kuma da ita za'aje tayi jiyyar yaronta, baza
ta bama kowacce mace acikinsu wannan ragamarba.
Shiru baba k'arami da daddy sukayi, taci masifarta ta gama tayi shiru.
Baba k'arami yace, “amma dai inna kinsan jinyar Yaya sai da matarsa a kusa, kekuma k'arfinki ya k'are ya za'a d'ora miki d'aw
ainiyar da matansa ne keda hakki a kai?”..
“yo d'awainiya ba tare da kai za'a tafiba? Kai basai kamasa ba. ni dai fa ban amince Ai'sha tajeba, dan wlhy bazan ta6a son Ai'sha ba komi zata zama, tunda dai ta silar jikokinane balle amin ilimi. k'ila
ma itace ta jefeshi dan taga ta kama k'asa 'yarta Na auren d'an Sarki, t........”.
“innaaaa! haba mana, dan ALLAH karma ki bari maganar nan ta fita, waishin minene laifin Ai'sha a gareki? duk cikin matanmu banga wadda take girmamaki da d'aukarki matsa
yin uwaba irinta, inna ya kamata wannan k'iyayyar ta koma soyayya hakanan, a baya kince dan basuda asali, kin dawo kince juya ce bata haihuwa, gashi kuma yanzu har ALLAH zai fidda jikoki daga tsatsonta, to miye kuma matsalar?”.
“toko zaka shak'eni
Na fad'a makane Hameesu?”.
“a'a inna, ALLAH yabaki hak'uri”.
“kaidai ka Sani, ni yanzu bara Na tashi Na shirya Ku kaini inama kace, imagesa nema ko uwarmi oho”.
Daga Dady har baba k'arami babu Wanda ya tanka mata, tana shigewa baba k'ara
mi ya mik'e yana cema dady “yaya ka jireta, bara naje mutafi da maman 'yan biyun, kota fito kace naje shiryawa ne”.
Kai Dady ya kad'a masa yana murmushi, baba k'arami ya fita da hanzari.
Bayan wasu mintuna saiga