Showing 324001 words to 327000 words out of 407268 words

Chapter 109 - Raina Kama COMPLETE

kuka saboda tsoro. Rikicewa daddynsa yayi yana tambayar mi aka masa? Badai yay musu komaiba ba ko?.....

Katseshi Galadima yayi da fad'in “Zandai yimasa, Dan kaima yanzu d'anka zai wuce Inda Na Alhaji Bana yatafi”.

“kai kai dakata please

ka dakata, nidai Na yarda zan mik'a wuya, karka ta6amin yaro kaji Na rok'eka”.

Cire bindigar Galadima yay yana maida kunamar da fad'in “shawara mai k'yau, lallai kanason d'ankan nan, ka tambayi abokanka, Wanda bazai mik'a wuyanba saiya fad'a yanzun n

an”.

“karka ta6a mana yara please, duk zamu mik'a wuya”.

Galadima ya tuntsire da dariyar da wanima zai iya rantsewa bai ta6a ganin yayiba, yace, OK, good dattijan k'asa, saina jiku acan”.

🤣🤣

ana shagali a Nigeria yau kam

🤸🏻

‍♀

🤸🏻

‍♀

🤸

🏻

‍♀

🤸🏻

‍♀

amma Nigeria novel ba tamuba

😜

.

Su Alhaji balala dai kam sun mik'a wuya, da Kansu suka kai Kansu police station mafi kusa, daga can suma d'aukesu zuwa inda IG yace.

Galadima yay hamdala ga ubangiji dukda bawai komai yagama k

ammaluwa bane, amma lallai an d'akko hanya.

Ya bada Umarnin tashi suyi sallar La'asar, kafin a dawo a cigaba da gashi

😜

.

....................................



Bayan sun idar da salla C.P ya kira Galadima, suka shaida masa su Alhaji Bana

suna hannunsu yanzu haka.

Galadima dake tsaye yace, “Alhmdllh, zuwa safiyar gobe kuma sai a kai case d'inmu Court, Dan inason komai yafarune cikin gaggawa ya k'are, bana son jan jiki a aiki”.

C.P ya kalli IG Dan jiran amsa.

Kai IG ya

jinjina masa alamar za'ayi hakan.

C.P ya shaidama Galadima amsar IG.

Galadima yace, shikenan, shi yatashi daga aiki, saikuma safiyar gobe.

C.P zaiyi magana I.G ya dakatar dashi alamar ya barsa kawai.

Ta6e baki Galadima yayi yana

yanke wayar, ya maida kallonsa gasu Muftahu da duk suna maidashi television, gira d'aya ya d'age musu, sukuma sukai masa jinjina

👍🏻

.

Kauda idonsa yayi ya maida ga yaran, yace, “yaya akwai mai buk'atar wanka ko barci?”.

Gaba d'aya suka amsa

da duk suna buk'ata.

Kallon Ameer da Saleem yayi yabada Umarni da ido.

..............................



'D'aya bayan d'aya suka dinga kaisu suna wanka, duk Wanda yagama sai abashi lemo, batare daya San miye acikiba saiya shanye, daga s

ha ko mintuna 3 basa k'arawa suke 6ingirewa barci

🤣

.



🤣🤣

ho Galadiman mu kasan takan tsiya, Zuma kenan, ga zak'i ga harbi

🤸🏻

‍♀

, kaga Na Munaya baban triplets, bada kanka a sare kaje gida kacema su mama Fulani an k'illesa

👌🏻😜😂

.

Da

akazo kan Harun k'in tankawa yayi, Dan haka Galadima yace su barshi kawai, amma harsu Malam Saminu da Alhaji Darma su Farhat duk sunma Kansu gyad'ar dogo sunje sun mik'e zasu huta.

Nuren ya kalli Galadima cike da tausayi yace, “Brother kaima kad'an

je ka huta mana”.

Murmushin gefen baki Galadima yayi, yajawo lap-top gabansa yana girgizama Nuren kai alamar a'a.................



🏻

*_ALLAH ka gafartama Iyayenmu_*

😭👏🏻

[8/3, 3:38 PM] +234 813 221 4515: *_Typing

📲

_*

*_

💡

HASKE WRITERS ASSO...._*

*_



RAINA KAMA...!!



_*

_(Kaga gayya)_

*_Bilyn Abdull ce

🤙🏻

_*

___________________

*_Na gaisheku, gaisuwa irinta musamman d'innan. Makaranta buk d'in RAINA KAMA dake JAMI'AR KUST dake W

UDIL, alkairin ALLAH yakai agareku, ALLAH ya yalwataku da ilimi mai tarin albarka damu baki d'aya._*

Ina inyinku irin Trillion's d'innan my guys

🤸🏻

‍♀

😘😘😘😘

❤❤

.

____________________

*_BOOK 3_*

👉🏻

1



7



...................Abin surutu lallai y

a samu, mak'iyan Galadima kuwa duk sun kasance a tsorace, Dan ba kowane ya fahimci inda shirinsa ya dosaba, hakama a cikin masoyan nasa, wasu suna ganin daidainsa wasu kuskurensa, kowa da irin fahimtar dai da yayma lamarin.

Yauma dai haka suka kwa

na zagaye da police.

Amma su IG duk sun tafi, d.p.o ne kawai tare da tawagarsa, kamar kuma yanda ya buk'ata sunakan tattara case d'in zuwa Court.

6angaren su Baffi kuwa lauyan Abie dukkan shirye-shiryen shiga Court suma suna akanyi. Dan dukkan

shirin Galadima yasan dashi tsaf, hakan yasa koda yagani baiyi mamakiba, kisan Ahmad daine da akace yayi yabashi mamaki, dukda zuciyarsa bata aminta Galadima zai iya kashe yaro ko d'ayaba. Amma lallai hakan ya sakashi a rud'ani, harma ya kira sir Isa suka

yi maganar. Sir Isa yace shima yagani a labarai amma gaskiya bai yardaba, akwai dai abinda duk basu saniba, Dan Galadima bazai aikata hakanba.

Da wannan maganar ne Baffi yad'an samu Nutsuwa yacigaba da tattara bayannsa daduk abinda zasu kafa hujja da

shi a court.

Duk abinda ke faruwa Momma tasan komai. Dan Galadima ya sanar mata, baya kuma 6oye mata dukkan shirinsa akan wannan case d'in dama, amma sai tayi lup tamkar batasan anaiba, koda labari yazo musu saita taya su Aunty Mimi rud'ewar itama

, harda pretending d'in kukanta tana Neman number Galadima, amma sai tak'i wucewa.

Daga Baffi har mai martaba babu Wanda ya kirata akan batun, duk a nufinsu Na 6oyemata kar hankalinta ya tashi balle Na mahaifinsa dake kwance yana fama da kansa.



Amma saiga kira daga mama Fulani, tafad'ama Momma maganar daduk yazo bakinta ta 6atanci akan Galadima, itadai momma cikanki batace da itaba, har tayi ta gama ta yanke wayar.

Saiga gimbiya Zulfah ma ta kira Momma, itakam ai harda kukan makirci irinna y

'an duniya. Itama dai tayi kid'anta tayi rawarta Momma Na saurarenta.

Koda ta Yanke wayar saita kira munaya. Taita kwantar mata da hankali da lallashinta akan ta kwantar da hankalinta. Insha ALLAH komai zaizo k'arshe, kowace rayuwa takan tafine da jar

abawa. Babu wani rai dazai rayu cikin farinciki da samun yanda yakeso 100%, dolene kowacce rayuwa akwai NATA k'alubale, nakowa kuma akwai ta hanyar dayake fuskantar nashi.

Sosai Munaya ta gamsu da nasihar momma hakannema yad'an samu mata nutsuwa tad'a

n rintsa a wannan dare.

.................................



*_WASHE GARI_*



Nasara ta farko da aka wayi GARI da ita shine farfad'owar Abba cikin hankalinsa, saidai har lokacin baya sanin Wanda yake a tare dashi, hakanne yas

aka likitocin fad'in a k'ara masa lokaci yasamu isashen hutu.

Ahalinsa sunsamu Kansu a farinciki ainun, hakama masoyansa, shikansa Galadima Yakuma samun kwarin gwiwa da karsashi akan aikinsa.



An kuma shigar da case d'in Court

kamar yanda Galadima ya buk'ata, abinka da lamarin manya har antsaida washe gari a matsayin ranar da za'a zauna Court d'in.



Yinin ranar zubur Galadima baiyi magana da police ko d'ayaba, koda sun buk'aci magana dashi saiya had'asu da Muftahu ko

Nuren. Daga k'arshe dai dolensu suna k'yaleshi.





★★★★★★★★

*_



RANAR SHIGA COURT_*



Yau ta kasance ranar zaman court, shari'ar su Galadima Ce kuma farko da za'a fara saurara a court d'in, lallai wannan shari'a ta m

anyace, Dan court d'in ta cika da manyan k'asa wad'anda sunfi kud'i wahalar gani, amma yau gasu available, y'an jaridar ma manya-manya aka bari, k'ananun suna awaje sunyi tururuwa domin rajin nemawa d'an uwansu hak'insa wato Alhaji Auwal fharuk dayake a as

ibiti har yanzu cikin halin ni y'asu.

Mukuwa talakawan gari y'an jiran jin yazata kaya mu sai dai gani a tv



.

Yo Wayaba asibi laya ubanta ba malam ba

😬

, ai ko babama da babansa aradu

🤕

.

*_Court_* d'in tayi tsit babu abinda kakeji sa

i gudun fankoki da tarin manya jefi-jefi, dan babu alamun fara'a a fuskar kowa.

Daga masarauta dai k'anin mai martaba ne yazo wato Garkuwa Hayatudden Abubakar, sai wasu daga tawagar y'an majalissar Sarki, harda waziri dayazo bisa tirsasawar mai marta

ba.

Daga masarautar su Papi kuwa yarima mai jiran gado mahaifin su Nuren wato Wambai Abubakar Abdul-fatah Wanda yagaji sunan kakansu Galadima marigayi Abubakar kenan. Saikuma wasu daga jiga-jigan masarautar suma.

Fitowar alk'alin alk'alai Ot

hman Ibraheem gwannu tasaka dukkan jama'ar Court d'in mik'ewa domin girmamawa a garesa, (dan shima Alk'ali baba uban su babane shima

🤭😝

).

Saida ya zauna sannan yabada izinin kowa ya zauna, Court d'in tayi tsit kowa ya Zubama alk'ali dake karanta tak

ardar k'arar hankali kwance ido, kusan mintuna 3 ya d'ago yanabin Court d'in da jama'ar cikinta da kallo ta cikin eyeglasses nashi daya jawo k'asan ido, d'auke idonsa ya ya maida ga Lauyoyi dake zaune suna jiran kule, suce cas.

Gyaran murya yayi yan

a maida idonsa ga takardar da fad'in “Ina wad'anda suke k'arar da kuma wad'anda akai k'ara? Idan kuma Lauyoyine to na masu k'ara da wad'anda ake k'ara suna inane?”.

A tare Baffi suka mik'e shida abokan aikinsa su uku, cikin girmamawa ga alk'ali ya

risinar dakai yana mik'a gaisuwa da fad'in “yamai girma mai shari'a sunana Barrister Usman Audu Tsanyawa, nine lauya mai kare Wanda yake k'ara, tare dani akwai Yohan Emanuel, da Bilkisa Ibraheem Musa (kutu melesi su bilyn Abdul anzama lauyoyin novel

🤸🏻





😎🤣😜

).

Bilkisu da yohan suka risina alamar girmamawa.

Alk'ali ya jinjina kai alamar gamsuwa, su Baffi suka zaune, lauyan wad'anda ake k'ara shima ya mik'e, ya rissina tamkar yanda Baffi yayi, sannan yace, “ya mai girma mai shari'a sunana B

arrister Adam Sadiq Adam, nine lauya mai kare wad'anda ake k'ara, tare dani akwai Barrister Aliyu Sa'adu yaro”.

Barrister Aliyu ma ya mik'a gaisuwa ga alk'ali sannan suka zauna.

Alk'ali yabama Baffi damar tashi domin yin magana.

AL

LAH Sarki dattijon kwarai kenan, masu wahalar samu cikin k'asa a halin yanzu, ya gyara hularsu ta lauyeyi dake Kansa, tare da farin eyeglasses d'insa dan rayuwa taja, ijiya duk sun raunana, ya kalli jama'ar cikin Court d'in sannan ya dawo da kallonsa ga al

k'ali, yace, “yamai girma mai shari'a! Kamar yanda kowa yasani Muhammad Sameer Saifuddin Abubakar (Galadima) shine yake Neman son sanin miya saka wad'annan mutanen 11 yin gamayya wajen kama surukinsa harsu wahal dashi? Bayan kuma shikeda alak'a dasu bawai

surukinsa ba?”.

Kai Alk'ali ya jinjina, cikin sauke numfashi yace, “Lauyan wanda ake k'ara gareka”.

Barrister Adam Sadiq Adam ya mik'e shima yana fitowa fili, yayinda Baffi Yakoma ma zauninsa ya zauna, Brr Adam Sadiq Adam yace, “yamai girma

mai shari'a wace irin tambayace ke fitowa daga bakin lauyan mai k'ara? Ai sune yakamata ayima tambayar minene dalilin shi Galadima Na kama yaran wad'annan mutane 11 yayi Garkuwa dasu yau tsawon kwana biyu? harma da kisan wani a cikin su.........



A hanzarce Baffi ya d'aga hannu sama yana mik'e da fad'in “yamai shari'a tambaya akaima lauyan mai k'ara, amsa kuma yakamata ya bamu baya sakko tashi tambayarba”.

Hannu Alk'ali ya d'agama Brr Adam Sadiq Adam, yace, “Brr Adam ka gyara, amsa muke buk'a

ta, kanada dama kaima kayi taka tambayar daga baya”.

Brr Adam Sadiq Adam ya risinar dakai alamun ban hak'uri sannan ya gyara tsayuwarsa yana fad'in “Yamai girma mai shari'a akwai abinda ke hannun Alhaji Auwal Fharuk Wanda mallakin su wad'annan mutan

e 11 ne, shine sukeda buk'atar kar6a”.

Baffi yamik'e yana fad'in “yamai girma mai shari'a ko zamu iya sanin minene wannan Abu da suke tuhumar Alhaji Auwal Fharuk akansa, dahar suka kasa mik'ashi ga sharia domin kar6a har sai sunbi ta hanyar nuna k'ar

fin ikonsu?”.

Brr Adam Sadiq Adam yay shiru yakasa cewa uffan, dan ganin tun a tashin farko yana shirin zurmawa.

Ganin yak'i cewa komai Baffi ya kuma cewa “ya mai girma mai shari'a idan baza'a samu amsaba ina buk'atar d'aya daga cikin y'an

wad'annan tawaga domin ya amsamin tambayata idan shi Barrister bai saniba”.

Alk'ali ya jinjina kai yana bada Umarnin tasowar d'aya daga cikin su Alhaji Mansur.



Dukfa abinnan dake faruwa Galadima yana kallon komai kai tsaye ta Comp

uter, danshi baizo Court d'inba, babu damar hakan, yana fitowa a gidan police kamashi zasuyi, wannan yasa tukan zaman Shari'a Alk'ali yabada wannan damar ta had'a video call d'in da Galadima zai iya ganin komai da za'ayi kamar yanda IG ya buk'ata bisa umar

nin shi Galadima d'in, kamar yanda ya shard'anta ko amasa hakan koya jeho gawar yaro d'aya ko yarinya. Hakan yasa sukai masa babu gardama.

Alhaji Abdul-Naseer dake farkone ya taso, ya shiga inda aka tanada domin buk'atar hakan, ya fad'i sunansa da m

atsayinsa, sannan Alk'ali yabama Baffi damar masa tambayar.

Baffi ya k'arasa jikin katakon d'aya shiga tsakaninsa da Alhaji Abdul-Naseer, idonsa a kansa yace, “Alhaji Abdul-Naseer, nasan kana d'aya daga cikin y'an wad'annan tawaga, shin kozaka iya a

msa mana tambayar da lauyanku ya kasa?”.

Murmushin Alhaji Abdul-Naseer yayi, cikin kwarin gwiwa yace, “Brr Usman, a ganina wannan sirrinmu ne, koma mi muke buk'ata a hannun Alhaji Auwal Fharuk mukeda alak'a dashi ai ba kowaba ko?”.

Baffi ya

shiga jinjina kai yana murmushi, yayi taku d'aya biyu saikuma ya juyo ga Alhaji Abdul-Naseer, yace, “lallai wannan gaskiyane Alhaji Abdul saidai kuma dalilin sanin Court yanada alak'a da samo Alhaji Auwal Fharuk a hannunku, wanda ta silar kama y'ay'anku da

surukinsa yayine kowa yasan hakan, saikuma gashi shi wannan bawan ALLAH Alhaji Auwal Fharuk a jiya daya farfad'o dukda baya cikin hayyacinsa, amma yana ambatar sunan Alhaji Halluru da jaddada lallai koda zaku kasheshi bazai bada wannan camera ba, domin s

hekarunma da kuka d'auka kuna ma rayuwarsa barazana bai bakuba balle kuma yanzu da lokacin Isar da ita ga Wanda akace ya Isar yayi, kenan Alhaji Auwal Fharuk k'arya yayi?”.

Da sauri Brr Adam Sadiq Adam ya mik'e yana fad'in “ya mai shari'a wannan ai

tamkar titsiyene Brr kema Wanda ake zargi, dan babu yanda za'ai la'akari da mutumin da baya cikin hankalinsa kamar yanda ya fad'a.....”.

Shima Baffi azamar dakatar dashi yayi, yace, “yamai girma mai shari'a Barrister Adam bashida hurumin yanke hukun

ci akan yanayin Alhaji Auwal, sai ya bari bayanin likitoci ya tabatar mana hakan”.

Alk'ali yay gyaran Murya da buk'atar ganin likitan dake kula da Alhaji Auwal Fharuk (Abba).

Cikin mintuna 3 saiga doctor ya shigo.

An sakashi d'a

yan wajen, ya fad'i sunansa da aikinsa, sannan Alk'ali yace, “kaine likitan da ke duba lafiyar Alhaji Auwal Fharuk? ”.

“eh nine yamai shari'a”.

Alk'ali yace, “kozamu iya sanin wani Abu dangane da jikin Alhaji Auwal Fharuk? ”.

“kwarai

kuwa ya mai shari'a, an kawo mana Alhaji Auwal Fharuk cikin hali irinna suma, amma babu wani alamar duka ko harbi a jikinsa, saidai bincikenmu ya nuna an shak'a masa wani Abu. Daya saka numfashinsa Nisan zango, sai ajiyane bisa hukuncin ubangiji ya farfad

'o, wad'annan kalamai sune abinda ya farka dasu a bakinsa, kuma kwakwalwarsa ras take, abinda aka shak'a masanne kawai bai sakesaba har yanzun, danma yanada jini mai k'arfine”.

Cikin wad'anda suke zaune ma'aikatan Court d'in d'aya yaje ya kar6i way

ar doctor da yay recording ya kaima alk'ali.

Alk'ali ya kunna recording ya saurara, ya ajiye wayar gefe da sallamar doctor cikeda gamsuwar

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login