Showing 369001 words to 372000 words out of 407268 words
“Lafiya lau, sai kewarku, ya kuka baro manasu da autana?”.
“kowa lafiya, Autanki nacan nama inno ta6ara, bakiga yanda yay k'iba ba ma”.
Momma tayi dariya tanacewa, “Ja'iri, da yanata zum6ure-zum6ure bazaijeba, bagashi haryaci wa
ta kusan uku ba, kwana nawa zai gama”.
“Dama ai shagwa6ace Momma”.
Momma tayi murmuahi tana maida kallonta ga jakadiya dake maganar ga abinci.
Sannu Tamata, ta kalli Galadima daya jingina da kujera ya lumshe ido.
“Muh'd tashi ga
abinci ko, kasamu ka kwanta ka huta”.
Idonsa ya bud'e yana mik'ewa, saiga Samha da aunty Mimi sun fito suma. momma tace, Samha ta kira Munaya tazo taci abinci.
Galadima yanaji amma baice uffanba, saima maida hankalinsa yayi ga abincin da Aun
ty Mimi ke zuba masa.
Ya faracin abincin Samha da Munaya suka fito, kallo d'aya yamusu ya d'auke kansa zuciyarsa na mamakin miya kaita d'akin Momma?.
Duk Momma na kula dashi.
Itama Munayar kallonsa tad'anyi ta d'auke kai.
H
aka akaci abincin duk hirar dasu Momma sukeyi da Munaya Galadima baice uffanba, cin abincin sa kawai yakeyi, baima wani ci da yawaba ya matsa gefe alamar ya k'oshi.
Aunty Mimi tace, “my K'ani Yaya dai?”.
Yad'an yamutse fuska da fad'in “Alhmdl
lh ya isheni”.
“Ai kai dama tsiyar murarka kenan wlhy Sameer, ta jigataka ta hanaka cin abinci, ALLAH ya kara sauk'i”.
Cikin lumshe ido ya amsa da amin a saman la66a.
Muma duk sannu mukai masa, ya d'aga mana kai kawai.
Koda muka had
'a ido saiya zubamin wata harar gargad'i, murmushi nayi na kauda kaina gefe tamkar ban ganiba.....................
✍
🏻
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*
😭👏🏻
*_Typing
📲
_*
*_
💡
HASKE WRITERS ASSO...._*
*_
♦
RAINA KAMA...!!
♦
_*
_(Kaga gayya)_
*_Bilyn Abdull ce
🤙🏻
_*
*_BOOK 3_*
👉🏻
2
⃣
6
⃣
.................Momma dai ta kasa ta tsare ta hanani hawa sama, idan abu Galadima ke buk'ata saitace Samha ta kai masa, tsakanina dashi saiya sakko gaidasu ko
zaije massalaci, ya kumak'i nuna hakan ya damesa, sosai mamaki ya kamani, dan kwanakinmu hud'u kenan da dawowa, da farko na d'auka kawai shariyar tasa ta k'asaitace ta motsa, amma zuwa yau dayake shirin zuwa Kashmir sai abin yafara bani tsoro, dan ina zaun
e bakin gadon Momma ina shayar da Abdurraheem ya shigo, Momma ta fita kitchen.
'Dago ido nayi ina amsa masa sallamar da yayi, amma saiya d'auke kai tamkarma bai ganniba, ya k'araso kusa dani ya rissina ya d'auki Amaturrahman dake kwance tana motse
-motse.
Duk'owar dayay saitasa k'amshin turarensa bugomin a hanci sosai, na lumshe idanuna sannan na bud'e akansa, magana yake ma Amaturrahman ahankali cikeda k'asaitarnan tasa, saikace wata babba.
Da kamar nima zan shareshi, saidai na daur
e nace, “Ina kwana”.
“Lafiya”. Ya amsa batareda ya kalli inda nakeba.
Hakan yamin ciwo a rai, na dangwarar da Abdurraheem d'in akan gado batareda ya k'oshiba, aiko saiya saka kuka, banbi takansaba na shige bathroom abuna.
Da kallo Ga
ladima ya bita cikeda takaici harta shige, ya cije lips nashi tamkar zai huda da hak'ori, idanunnan harsun kad'a da 6acin rai. Yana k'ok'arin tashi ya d'aukeshi Momma ta shigo d'auke da k'aramin Kofi ma Magani daza'a basu. K'arasowa tai dad'an hanzari tana
fad'in “shikuma wannan mi akai masa?”. Ita bama ta lura da Galadima ba, amma taji k'amshin turarensa.
Kwafar da yayi yasaka Momma juyowa ta kallesa bayan ta d'auki Abdurraheem d'in. “Wai dama kana d'akin amma yake kuka? Ina Munayar ne?”.
Baice komaiba sai bayi ya nuna mata da hannu, hakan yasata fahimtar ransa a 6ace yake, ta zauna tana shafa bayan yaron, yayinda shikuma ya daina kukan.
A kausashe Galadima yace, “Momma idan bazata iyaba na nemo masu kulamarmin da yara, dan baza
n d'auki wannan wulak'ancinba, ta k'auracemin na k'yaleta tayi duk yanda ta gadama, shine yanzu kuma abin akan yarana zai dawo, nifa wlhy......”
Dakatar dashi Momma tai ta hanyar d'aga masa hannu, “ya Isa haka Muh'd, Munaya dai matarkace, kuma lafi
yar ALLAH kuka dawo k'asarnan, aganina tun washe garin dawowarku kaga batazo inda kakeba yakamata ka tambayeta miye dalili? Amma ka share tamkarma hakan bai damekaba, shin mulki haukane Muh'd? Indai kace zakaima mace izza da mulki wlhy kana tare da wahala,
dan ba kowace mace bace zata d'auka, gaka da zuciyar tsiya saikace kuturu, ni nasan minene matsalarkune balle na sasantaku? Kuka Sani, inma zaku shekara a hakane kuyita zama babu ruwana wlhy”.
Shiru Galadima yay yakasa magana, zuciyarsa sai zafi
take masa.
Momma kam ta d'auki Abdurraheem da maganinsu tayi ficewarta tabar musu d'akin, sumaci Kansu ita babu ruwanta.
Kansa ya dafe cike da takaici, shi yarasa gane kan Munaya, da farko yabartane yaga iya gudun ruwanta, a tunaninsa ko kunya
ce, amma daga baya saiya fahimci ba haka bane, wani tsirin ne kawai take Neman k'irk'ira, kud'i ya ajiye mata shima ya fice d'auke da y'arsa a kafad'a.
Munaya dake a bayi tana kuka ta wanke fuskarta ta fito danjin alamun ya fita.
Kwanciya tay
i saman gadon wasu hawayen na zirarowa, itafa koma mizaiyi tana akan bakanta, dolene saiya kar6a laifinsa sannan koda zai sameta yanda yakeso.
A can falo Samha yabama Amaturrahman yay musu sallama ya fita.
Shareshi momma tayi, sai aunty Mim
i ce tace, “Dan ALLAH Momma Ku tsaida shirinan naku keda mom, kubashi matarshi, yanzune hankalinsa ya kwanta yadace yasami cikakkiyar nutsuwa da iyalinsa, amma kunbi kun kankane, haba dan ALLAH Momma ”.
Da 6acin rai Momma ta kalli Aunty Mimi, “To m
ai d'an uwa, yanzu ke idan Sauban ne a matsayin Munaya zakiso wani yazo ya auresa a sigar da d'an uwan naki yayi? Miyasa kukeda son kanku, wlhy kinji na rantse inhar bai gane kuskurensa ya nemi yafiyartaba ta yafe masa bazan ta6a bashi itaba, idan yagadama
ya cika gidannan da fushi, kuma aiga y'ay'ankunan mata kun haifa, ba kuma zakuso a aikata hakan agaresuba ince?”.
Aunty Mimi ta tausasa murya ganin ran Momma ya 6aci, “tokiyi hak'uri Momma, ni aganina a zaunar dashi a karanta masa laifinsa, ki
nga shi yanzu dukma baisan dalilinkuba wlhy”.
Banza Momma Tamata, ta ajiye Abdurraheem ta tashi takoma d'akinta.
Binta kawai da kallo aunty Mimi tayi, tasan akan gaskiya su Momma suke, to amma sai a tausayama Sameer ai shima, akuma sanar dash
i laifinsa, tasan halin Momma akan son kwatarma mai gaskiya gaskiyarsa, bakuma zata ta6a tank'waruwa ta sauk'iba, balle ga mom a gefe na angizata.
****************
Ran Galadima a 6ace yay wannan tafiya, sauk'inma da yaje yaga jikin
Abie ne sai nutsuwa ta saukar masa, har yanzu yanata samun kulawa ta musamman, bakuma a shiga inda yake, amma kullum Dr Erfan cikin ma Galadima albishir yake akan cigaban da ake samu, yauma sosai ya labarta masa komai gameda ga66an Abie da ayanzu zasu iya
fara aiki, zasu barsane yad'an k'ara kwanaki domin k'arfin jikinsa da abinda ba'a rasaba, dama ciwo shike shiga lokaci d'aya, amma sauk'i sai a hankali.
Kwanan Galadima biyu yadawo new Delhi.
Ranar kamar wasa Munaya da Samha suka shiga
kitchen wai zata koya mata tuwo, har Momma na musu dariya da tsokanarsu yau zasuci tuwon y'an gayu.
Daga abin wasa sai Munaya ta zage tayi nutsetstsen tuwo da miyar ganye, tamusu juns na kayan itatuwa, gamawarsu kenan sukaje zasuyi wanka, Momma d
a Aunty Mimi na zaune afalo suna jiran suyi wankan azo abasu tuwo suci, su Abdurrahman duk suna tare dasu aunty Mimi na yanke musu k'unba, Yayinda jakadiya ke tayata, babu Wanda ya sanarma zaizo, sai kawai sukaga ya shigosa da sallamar nan tasa ciki-ciki.
Duk juyowa sukai suna kallonsa da mamaki, jakadiya ce kawai tasami damar amsa masa, sai Khaleel dake wasa ya tafi da gudu yana masa oyoyo.
'Daukar yaron yay ya d'aga sama, dukda yayi girma masha ALLAH.
Ya k'araso cikin falon Jakadiya na
gaisheshi, amsa mata yayi da kulawa, sannan ya zauna a kujera yana rik'e da hannun Khaleel.
Momma tace, “wai dama kana tafe?”.
“Wlhy kuwa Momma”. Yafad'a cikin sauke numfashi, itama ya gaisheta.
Itama aunty Mimi suka gaisa, tana masa sa
nnu da tambayarsa jikin Abie.
Cikin fad'in “Alhmdllh” ya amsa musu, yabasu labarin cigaban da aka samu, farin ciki na manaye zukatansu.
Ajiye ruwan da baiwar tamasa yay dai-dai da fitowar Munaya cikin matsakaiciyar kwalliyar data k'ara mata
kwarjini da cikar haiba, dan zani da rigane na atanfa, ta fito asalin bahaushiyarta jinin buzaye tawani fannin.
Lokaci d'aya idonsa ya sark'e cikin na juna, kowanne sirrikan kewar d'an uwansa na fita daga cikin nasa, Munaya tafara d'auke kanta, yayin
da shima Galadima ya janye nasa cikeda basarwa. Jitai tamkar karta k'araso, amma kowa yarigada yaganta, tadai k'araso tana masa sannu da zuwa. Amsawa yay cikin halin ko in kula.
Ita Momma dariyama suka bata, hakama aunty Mimi data maidasu television
.
Ajiye Abdurraheem d'in yayi yatashi wai zaije ya watsa ruwa.
Munaya tabisa da kallo a sace, sanye yake cikin k'ananun kaya, wando ruwan toka da farar riga mai d'ishi-d'ishin ruwan goro.
Tad'anyi 6oyayyar ajiyar zuciya tana kauda id
onta lokacin daya juyo, dan jiyay a jikina kallonsa akeyi, aiko saigashi ya kama yalla6iyarsa dumu-dumu.
Baki yata6e ya ida hayewa yana sak'ama zuciyarsa matakin daya shirya d'auka akanta.
********
Ba'a zauna zaman cin tuwonba saida Gal
adima yay wanka ya sakko, duk suka hallara wajen cin abincin, Momma tama Munaya nuni da ido tayi saving nashi.
Babu musu tabi Umarnin Momma, yanata latsa waya tamkarma baisan hidimar da sukeba, ga fuska cinkus babu walwala, dukda zuciyarsa na kwad'ay
in fara cin abincin da k'amshin ya addabi hancinsa tun d'azun.
Tana gamawa takoma mazauninta da Samha ta shiga tsakkiyarsu, ya ajiye wayar yana kuma wani d'aure fuska dacin Magani, yayi mamakin ganin tuwo, dukda dai Dama akanyi musu amma sai time t
o time, shiyyasa yake sonsa sosai.
Hannunsa ya wanke a ruwan da aka ajiye masa, baici da tsokalin data ajiyeba. Tun a laumar farko kunnensa ya nemi tainkewa, 100% yaji yakamata ya baima mai wannan girkin maki.
Momma da Aunty Mimi dai kam kasa
hak'uri sukayi, suka shiga santi da yaba wannan tuwo, Galadima dai yayi tsitt, sai a zuciyarsa yake yabawa, cikeda tsokana Momma tace, “wasuma dai santin nasu na shirune, suna tsoron yin magana dad'in ya yanke”.
Dariya su aunty Mimi sukayi, Munaya
ta saka d'ankwali ta kare bakinta tana murmushi, dan kowa yasan dashi Momma take.
Galadima da yasan dashi Momma take shima saiya murmusa yana satar kallon Munaya.
Saida suka gama tsaf Momma ke cewa lallai d'iyata sannu da k'ok'ari, ra
bon danaci tuwo irin wannan mai dad'i tunna inno, har k'yauta yau saina miki”.
A kunyace Munaya tace, “godiya nake Momma”.
Dukda Galadima ya fahimci girkin Munaya tayishi baice k'alaba, saima ya d'auki waya yay kira, ya mik'e ya fice harab
ar gidan.
Aifa nan suka shiga gulmarsa suna dariya, Samha harda cewa tana ganinsa yana lumshe ido lokacin fayakecin tuwo.
Aiko mizasuyi inna dariyaba.
Koda yagama wayar bai koma cikin gidanba, saiyay ficewarsa saboda gabatowar lokacin sa
lla.
*_9:30pm_*
Galadima ya sakko daga samansa, fuskarsa kawai zaka kalla kafahimci yana tare da damuwa, sanye yake da kayan barci farare sol, wandon yaje har k'waurinsa amma baikai k'asaba, sai k'amshi mai sanyi yakeyi.
Cikin san
d'a ya tura k'ofar Momma yad'an lek'a kansa, Munaya kad'ai ya hango zaune abakin gado tana tofama yaran addu'a a tafin hannunsu tana shafa musu a jiki, ya kalli ko ina babu alamar Momma saiya ida shigewa.
Shigowar Mutum kawai Munaya ta gani, tsor
ata tayi, ta kware baki zatayi ihu yay azamar saka tattausan hannunsa ya toshe bakin, k'amshin turarensa ya sakata fahimtar shine, d'aukarta yay gaba d'ayanta tanata mutsu-mutsu da k'afafu dason yin magana amma babu dama.
Yanufi k'ofa da ita zai fi
ce Momma ta fito daga bayi, daga bayansa kawai yaji ance,
“Sannu shugaban masu iya satar mutane, to saika ajiyeta ai”.
Fad'uwar gaba da kunya dukta lullu6eshi a lokaci d'aya, ya dire Munaya yana susar k'eya saboda kunya, yama kasa kallon Mo
mma d'in.
Itakam bata kuma cewa dashi komaiba tazo ta gabansa ta fita d'akko abu.
Yana ganin Momma ta fita saiya juyo ga Munaya da hanzari. A matuk'ar fusace yay kanta, “K! y'ar rainin hankali ALLAH yau saikin sanarmin minayi miki, inba hakab
a a d'akinan zan kwana, bar ganin Momma ta tsaya miki”.
Ja da baya Munaya tayi ganin yana Neman maketa, idonta cike da kwalla tace, “Ai kaima kasani”.
Hannu ya d'aga tamkar zai maketa saikuma ya fasa, ya dunk'ule hannun, “ke wai wace irin mutu
mce birkitacciya?, ba'a ta6a zama dake lafiyar ALLAH?, kinsan ALLAH wannan karan Abban zan kira Na sanarmawa idanni kin rainani.......”
Cikin kuka munaya ta katseshi, “Dama kasanar masa ai shine ya kamata, kaga shima zaisan tayaya ka aurar masa ya
rinya, Papi da mai martaba zasusan Neman auren shekara biyu sukaje suka nema kuma suka d'aura.....”
Kansa ya dafe cikin tsantsar takaici, miye kuma nadawo da wannan maganar bayan ta wuce? Kai yarinyarnan y'ar matsalace. Duk a zuciyarsa yake zancen.
Momma da dama duk cikin shirinsune ta fita tai saurin shigowa tana fad'in “Minakeji haka? Waye yayi auren shekara biyu?”.
Duk kasa magana sukayi, munaya Na kuka shiko kunya da nadama dukta rufeshi.
“Waishin bakujini baneba?!”. Momma ta
yi maganar a tsawace.
“Momma please cool down”.
“Nayi cool down a ina Muh'd, dama abinda ka aikata kenan bamu saniba? Yanzu nan da hankalinka da iliminka Na addini da tarbiyyar da muka baka zakaje kayi auren yarjejeniya da d'iyar mutane? Sheka
ra biyu ta cika kasaketa saboda son zuciya? Wannan d'abi'ar daga ina kuma ka samota? Danba koyarwar addininmu bace balle al'adarmu”.
Jiki a sanyaye Galadima ya zauna a bakin gadon kansa a dafe, itama Momma saita zauna tana kiran Munaya data mak'ure
jikin bango tana kuka maiban tausayi. Takowa tayi tazo inda take, saita zauna a k'asa kusada ita.
Momma ta kallesu dukansu, saima suka bata tausayi, Dan takula kowannensu yakamu dason d'an uwansa Na gaskiya, tad'anyi gyaran murya tana fad'in “Muh'd
!”.
Kallonta yayi idonsa ya kad'a zuwa jaa kad'an, jijiyoyin kansa da gashin jikinsa duksun mik'e saboda damuwa, sai faman cizar lips yakeyi.
Momma datasan bazaiyi magana ba tunda yahau sama saita cigaba da maganarta, “Muh'd ka fad'amin gask
iya ya akayi ka auri Munaya?”.