Showing 243001 words to 246000 words out of 407268 words

Chapter 82 - Raina Kama COMPLETE

yay yanama mom sannu



Idonsa akan yaron yana kuma sumbatar goshinsa cikin lumshe idanu ya k'araso inda nake dana zuba

musu idanu cikeda sha'awa.

Kusa dani ya zauna ya d'ora minshi akan cinya. nima rungume kayana nayi na sumbaci goshinsa, inason bashi abinci amma inajin kunyar Galadima, gashi ya zubamin ido yak'i tashi.

Lura da hakan dayay ya sakashi yin miskil

in murmushi ya mik'e yabar wajen.

d'an hararan bayansa nayi ina fad'in mugunta dai babu k'yau a kan la66ana..................



🏻

“Hummm fans nasan kwace wai ina Harun ne?

🤔

, kumuje zuwa dai danjin ina ya shige haka? Ita kuma sarauniya Z

ulfah (uwar gidan Sarki mike matsalarta)?.

😨😏

*_Ya Rabbi ka gafarta ma iyayenmu_*

😭👏🏻

*_typing

📲

_*



💡

*_HASKE WRITERS ASSO....._*

*_



RAINA KAMA.....!!



_*

_(Kaga gayya)_

*_Bi

lyn Abdull ce

🤙🏻

_*

~Book 2~

👉🏻

2



8



............A yanda Na kula har yanzu bayajin dad'in jikinsa, dan komai a d'an wahalce yakeyinsa, koda ya fiddo kayan daga wardrobe saiya dawo bakin gadon ya zauna ya dafe Kansa, kallonsa nayi cikin damu

wa nima, Na cire Abdurraheem Na kwantar, sannan Na mik'e zuwa garesa, durk'usawa nayi Na d'ora hannayena akan gwiwarsa, “yalla6ai lafiya?”.

Shiru yamin kusan minti 1, harna fidda ran samun amsa ma na yunk'ura na mik'e da nufin barin masa d'akinma d

uka.

Hannuna ya rik'o, na juyo na kallesa, har yanzu yana yanda yake baiko d'ago motsa ba.

Na cije lips ina had'iye kukan dakeson zubomin, rayuwar nan tasa bana sonta wlhy, ni y'ar dangi Ce, nariga natashi gidan yawa, dukda gidanmu bahagon gidan

e mukanyi hira koyayane, amma shifa magana ma idan bai ra'ayiba wahala take masa, Abu na damunsa a rai amma bazai iya fiddashi yaji sauk'iba, Momma ta had'ani da aiki, a watannin baya kad'an kamar yafara canjawa, amma gashi yakuma birkicewa yanzu, tayaya M

omma take tunanin zan iya canja Galadima? murd'ad'd'en mutumne shi mai wahalar sha'ani, ga tsantsar mulki da k'asaita da suka zama jinin jikinsa, s.........

Tunanina ya katse lokacin danaji an jawoni, nai firgigit saboda fad'awa danayi jikinsa, sh

ikuma yay baya ya fad'a kan gadon, kad'an ya rage mu danne Amaturrahman, yad'an kauce kad'an yana sauke ajiyar zuciya.

Uffan bai ceminba ya maida idonsa ya lumshe.

Mamakin wannan lamari ya kamani, hannu yasaka ya kwantar da kaina a k'irjinsa ya

na d'an buga bayana da d'ayan hannun, zanyi magana ya d'ora yatsunsa hannunsa uku na tsakkiya akan bakin alamar nayi shiru. banida za6in daya wuce yin shirun, nabisa yanda yakeso.

Yanayin da zuciyarsa ke bugawa sai yabani tsoro, na saka hannuna na

danne wajen sannan na d'ora kaina bisa hannun, ajiyar zuciya yayi yana cizar lips..

Tsawon mintuna 3 muna a haka, har knocking d'in k'ofa akayi amma baiko motsaba bai barni na motsaba, na yunk'ura zan tashi ya maidani.

Munkai mintuna 7 sann

an ya zameni ya kwantar ya mik'e zaune, batareda ya kalleni ba ya sauka daga gadon, bathroom ya Shiga, babu dad'ewa ya fito, nidai kallonsa kawai nake da mamaki, Dan fuskarnan amatuk'ar d'aure take tamkar baisan minene dariyaba a rayuwarsa, ya shinfid'a ab

in salla, domin rama sallolin da suka riskesa yana barci.

6oyayyar ajiyar zuciya na sauke, na tashi zaune idona akan yaran, duk sun koma barci, na tsurama Abdurraheem ido, saboda fitar numfashinsa ta banbanta dana y'an uwansa, tunani nai ko yanayin

nasa barcin kenan shikuma, saboda wahalar da suka sha,

d'aukar ledar kayan da mom ta kawo nayi, na fiddasu na saka, ban jira ya idarba na fice abina.

Nayi mamakin da yanzu babu kowa, harsu Munubiya sun tafi, haushi ya kamani kamar zanyi ku

ka, aidai sa jira na fito mu gaisa ko? hawayen da suka zubomin a kumatu na share, namafi jin haushin Munubiya wlhy.

Sallamar da akeyi na amsa da k'yar, sannan na bada izinin shigowa, cikin bayina ne guda biyu, zubewa k'asa sukayi suna gaisheni.

Cikin girmamawa d'aya tace, “dama ance mu gani idan kin fitone”.

Nace, “Hummm”.

Fahinmatar iya amsar dazan iya basu kenan ya sakasu mik'ewa suka fita, zamewa nai na kwanta cikin kujerar ina cigaba da zirar da hawaye.

Kusan mintun

a 5 saiga Samha ta shigo, ta durk'usa gaban kujera tana sharemin hawayena, d'ago ido nayi na kalleta, namata murmushin k'arfin hali ina tashi zaune.

Muryarta da alamun tasha kuka itama tace, “Aunty Uncle Sam na kiranki”.

Kai na jinjina mata kaw

ai, na tashi gaba d'aya na d'auki mayafi muka tafi tare.

Koda mukaje k'ofar falon bata Shigaba, nikad'ai na Shiga ita kuma ta juya ta fice daga sashen gaba d'aya.



A falo na iskeshi cikin doguwar kujera a kwance, ya kifa yaron d'aya a k'i

rjinsa Wanda nake k'yautata zaton Abdurraheem ne, wayace manne a kunnensa, amma a hankali yake magana koni danake tsaye cikin falon banaji, na kalli abincin da aka jere a tsakar falon ina zama a kujera.

Bai dad'eba ya kammala wayar, idonsa dake jaji

r har yanzu ya d'ago yad'an kalleni, jijiyar kansa dukta tashi rud'u-rud'u. saida yad'an lumshe idanu kafin ya motsa la66ansa ahankali yace, “kici abinci inji inno”.

Dukda maganar taban haushi haka na danne, wato inji inno ma ba injishi ba ko?. Sakko

wa nayi k'asan lallausan carpet d'in, d'aya bayan d'aya na bubbud'e kulolin da kwanikan, a rai na ina tunanin ina zamu kai wanna abincin haka?.

Tashi nayi zuwa ga show glass d'in dake falon, wadda aka jera mugs and glass cups, mug d'aya na d'akko, naj

e wajen wanke hannu dake a wajen dinning, Wanda babu tebirin cin abincin ba'a sakaba, bansan dalinsa nak'in sakawarba, wanko mug d'in nayi na had'o kayan tea a ciki dake a wajen show glass d'in suma, na zubo ruwan zafi daga dispenser na dawo, yana kwance y

anda na barsa, yanzuma garda su lumshe idanu yanata shafa kan yaron zuwa bayansa.

Na kallesa a d'arare Dan yaune karan farko dazan aikata hakan, komi yake buk'ata yakan yi da kansa, ko ruwa wannan inhar bana manta ba bai ta6a cewa na d'auka masaba, s

ometimes ma sai idan yasaka Samha ko Sauban su masa Abu saini na tashi nayi idan naga rashin dacewar hakan, amma dai dakansa yace Munaya yimin kaza, gaskiya bai ta6aba. muryata na rawa nace, “bismillah”.

Shiru kamar bazai bud'e idonsa ba saikuma ya b

ud'e d'aya yad'an kalleni ya kauda kansa. cikin k'asaitar nan tasa yace, “miyasa?”.

“miyasa kuma?”. ‘nakuma maimaita maganar ina k'ok'arin janye hannuna’.

Carab ya rik'e hannun nawa, ni tsoroma ya bani, na kalli hannunsa da nawan ga mug cikeda

ruwan zafi yanata turiri, kuma zafin yana ta6amin gwiwar yatsuna, idonsa a lumshe har yanzu, idona harya fara tara kwalla, nayi alk'awarin koda hannun zai toye gaba d'aya bazan tanka masaba, ai yasan abinda yake dai-dai da akasin haka.

Saida mukayi

1minute a haka kafin ya maido face d'insa inda nake yana kallona, ya d'age gira d'aya yana fad'in “da zafi ne?”.

Humm lallai Galadima akwai rainin wayo, na fad'a a zuciyata, janye idona nayi daga kansa na maida kan Abdurraheem dahar yanzu yake kw

ance a bisa cikinsa.

Ya yamutse fuska yana sakin hannun, cikin basarwa yace, “inason jarumta”.

Had'iye kukan dake k'ok'arin tahomin nayi, na ajiye Mug d'in na cigaba da zuba masa farfesu a k'aramin bowl batareda nayi koda tariba.

Tashi y

ay zaune yana jije lips, yayinda hannunsa ke rik'e da yaron, d'ayan kuma ya dafe saitin zuciyarsa, a wahalce yake fisgo numfashi kafin ya fesoshi, tun kuma d'azu na lura da hakan, kalmar zafi daya fad'amin na shiga fassarawa, har na fahimci da manufa ya fa

d'a, hakanne ya Sani murmusawa batareda na d'agoba ina zuba masa farfesun nace, “tabbas duk zafi sunansa zafi, amma akan samu banbance-banbance wajen banbancesu, wani zafin a gangar jiki muke jinsa, wani ko tawani sashen jikin ake samunsa, wani zuciya, wan

i rayuwarma gaba d'aya Ce ke tsintar kan a zafi, saidai babu zafi mafi rad'ad'i daya kai na Mutuwa, idan da zamuyi nazari zamu fahimci rayuwa tana a tsare ne mataki-mataki, sannan iri d'ayace ga kowanne launin halitta na mutum ko aljan ko dabba, Dan mukan

tainci kanmune akusan mizani d'aya, dukda ubangiji ya banbantamu ta halitta da ayyuka da tunani ko nace kaifin basira, ko'a jinsi launi biyune, akwai namiji akwai mace, dukkan rayuwa takan farane da mafari yalla6ai” na d'ago ina sake mik'a masa mug d'in te

a d'in again, a mamakina a yanzu saiya kar6a, na lashi lips d'ina na k'asa ina gyara zama sosai da maida hankalina wajen juya kunun dana zuba a cup da tsokali, cikin nisawa nacigaba da fad'in, “mafarin rayuwa shine dasuwar bawa a cikin mahaifiya, mukanyi w

annan rayuwarne a cikin halin su wanene mu? daga nan sai matakin haihuwa, shigowa duniya a bisa bigiren wane ahali muka kasance, dukkan ahalin daka Sani sunada matsalarsu, saidai tawasu tafi tawasu zafi, daga ranka ka iso filin gwagwarmaya wato duniya, shi

kenan littafinka dayazama rubutacce tun a cikin mahaifiya saiya fara aiki, mala'iku masu kula da fitar numfashi su dasa alk'alaminsu, masu kula da abinci suma haka, masu kula da ruwa ma haka, masu kula da magana ma haka, masu kula da kallo ma haka, masu ku

la da ji ma haka, masu kula da duk wani motsinka ma haka, tafiya, zama, kwanciya dadai sauransu, kowa ana haihuwarsa tsaftatatccene, iyaye suke fara juya akalar rayuwa, walau mai k'yau ko sa6aninta, (kaga kenan akwai hisabi tsakanin iyaye da y'ay'a ma kena

n?) daga nan rayuwa zata cigaba da yad'o kamar d'an duma, tun ana maka, harka koma koya, harka fara iyawa da kanka, harma ka kware ka koyama wani, (wanne ka iya? ko ka koya? yarage ruwanka) duk Wanda kaga an masa a farko to tabbas za'a k'ara masa a k'arshe

, kodai silar tsufa, ko ciwo, kokuma iftila'in rayuwa, kokuma na k'arshe shine hidimar gawarka, a dukkanin dunk'ulalliyar rayuwar da kowanne bawa yakanyi zakaga cike take da k'alubale masu zuwa da zafi kala-kala, yalla6ai kasan mike taushe wannan rad'ad'in

zafin kuwa?”. nayi maganar ina d'ago ido na kallesa. A mamakina sainaga ya girgiza min kansa. na murmusa ina janye idona daga kansa na maida ga kofin tea d'in ina masa alamar yasha mana.

Yamutse fuska yay irin kalar tausayinnan.

Nima sainayi kwa

l-kwal da ido kamar zanyi kuka, na had'e hannayena waje d'aya alamar rok'o

🙏🏼

..

Lips d'insa yad'an ciza kafin yafara shan tea d'in. Nayi salute nashi ina masa jinjina

👍🏻

.

Basarwa yayi, nima saina kad'a ido ina tunzura baki gaba, sannan naciga

ba da fad'in, “Abinda ke taushe wannan rad'ad'in zafin shine *_HAK'URI_*. hak'uri muhimmun sinadarine dake jagorantar garkuwar jiki ta kowacce launin halittar jiki na d'an Adam, walau a fili take ko a 6oye take, saidai babban makarinsa da taskar adanashi

shine *_ZUCIYA!_* a duk lokacinda k'arfin zuciya ya raunana to zaka samu madarar hak'uri ta salwanta, idan zafi yanata yawa babu wannan hak'urin bugu d'aya take duk wani ma'adani na cikinta saiya tarwatse, saikaga an rasa ayyukan jiki dana ruhi, shikenan w

ane yazama labari. daga lokacin da rad'ad'in fitar rai ya kusanci bawa dukkan mala'ikunan da suka kasance tare dakai a randa kazo duniya saisu fara janyewa daga gareka, wani bawan kafin ranar mutuwarsa zakaga ya daina cin abinci, hakan na nufin mala'ikan d

ake kula da abinci ka yagama aikinsa, domin ya zagaye duniya kaf duk yawan abincin dake cikin ta babu rabonka koda kwayan gero ne, ka gama cinyewa, wani kafin ranar Mutuwa ya daina shan ruwa, aikin mala'ikan dake kula da ruwa shanka yagama k'arewa kenan, d

uk yawan koramu da tafkuna na duniya bakada sauran rabo na ruwa, ka shanye naka, wani kafin Mutuwa ya daina magana, mala'ikan dake kula da furucinka yagama aikinsa, babu sauran wata kalma data rage harshenka ya furta, wani kafin Mutuwa ya daina ji, mala'ik

an dake kula da jinsa ya gama aikinsa, babu wata kalma data rage kunnensa zaiji, wani kafin Mutuwa ya daina gani, mala'ikan dake kula da ganinsa ya gama aikinsa, kwayar idonsa baza

ta sake kallon wani abuba, wani kafin Mutuwa ya daina tafiya, mala'ikan dake

kula da tafiyarsa ya gama aikinsa, haka-haka wad'annan mala'ikun zasuyita ja baya suma barinka, har yarage sai mai kula da fitar numfashi kawai, daga ranar da UBANGIJI yace yana buk'atar ganinka shikenan takuma k'are, sai rundinar mala'iku su had'u su tak

ewa kwamandan mala'ikan d'aukar rai baya, idan kai mutumin kirkine fararen mala'ikune, idan na banzane mala'iku masu azaba zasu take masa baya, sauran al'amari kuma sai Wanda ya haliccemu yasan ya zata kasance

😭

. zakasha mamaki idanfa nace maka duk wannan

zafin k'aramin zafine acikin kashi-kashin na abinda ya shafi haluttu, shi wannan zafin ana kiransa zafin na za6in kai, kokuma zafi na a haka tsarin yazo, ma'ana kaine ka had'ama kanka wannan zafin, kokuma wanine ya had'a makashi. Abu na biyu shine zafi na

rad'ad'in Mutuwa, dolene kowa saiya d'an d'anashi, walau kafiri ko Musulmi, saidai akwai banbance-banbance na awanne tsari ka koma ga ALLAH, ba wannan zafinne kawai ke jiran d'an Adam ba, akwai zafin na *_BARZAHU_* shi ake kira kwanciyar kabari, mika tanad

a, mi zaka tarar shine abin tambayar, wannan kam ALLAH ne mafi sanin wad'anda zasu d'and'ana wannan zafin (ALLAH ka datar damu

😭

)”.

Akan la66a Galadima ya amsa da amin, Munaya ta share hawayenta, ta cigaba da fad'in sai zafi mai gaba d'aya, shine na

makoma, *_WUTA KO ALJANNA_*, yalla6ai wad'annan jimullar zafin ga d'an Adam tilas ne, na cikin rayuwa shine zafin da zaka iya controlling nashi ta hanyar hak'uri, to Ashe bai kamata ka tasirantar da wannan zafin ya cigaba da k'onaka ba, musamman idan zaka

yi dubi dawasu ni'imomin da ALLAH yamaka a cikin wannan zafin, ka kasance mai yawan hak'uri saikaga kanka cikin masu yawan riba, wlhy ta wannan hanyarne kawai zaka zama mai *_NASARA_* akan mak'iya ni..........”.

Maganata ta katse saboda knockin

g d'in k'ofar da akayi, kallon juna mukayi ni da shi, yay wani luuu da idanunsa ya lumshesu, hakanne ya sakani bada izinin shigowa kawai batare da na jira amsa daga garesa ba.

Sarkin k'ofane ya shigo, ya zube yana gaishe mu, nice kawai na amsa, bos

s kam hannu kawai ya iya d'aga masa, yay mana ya jiki again, nanma nice nakuma amsa shi, cikeda girmamawa yace, “ranki ya dad'e yalla6ai harun ne ke buk'atar iso”.

Saida gabana ya fad'i, na had'iye wani yawu mai kauri ina kallon galadima dayay biris

damu yanata shafa kan d'ansa, bud'e idonsa jajaye yayi akan Sarkin k'ofa, ya jinjina masa kai alamar ya shigo dashi.

Kallonsa nayi tamkar zanyi magana saikuma nai shiru, a raina ina mamakin wannan munafukin dami yazo kuma?..... ban kai k'arshen zance

n zucin ba Harun yay sallama, nid'ince dai na amsa cikin danne zuciya da fushina.

Ya zauna fuskarsa d'auke da murmushi.

Nima saina saki tawa ina fad'in, “barka da hantsi ranka ya dad'e”.

“Barka dai gimbiyarmu, ya jikin ki dana yalla6ai?”

.

Na kalli Galadima dayay shiru kansan jingine da kujera ido a rufe, “da sauk'i”, na fad'a ina mik'ewa na koma saman kujera, dan bazan ta6a barin falonba sainaji uwarmi ya kawosa.

Ya amsa da “masha ALLAH, ALLAH ya kiyaye gaba ya k'ara lafiya”.

“humm” na fad'a ina amsawa da “Amin dai”.



Hankalinsa ya maida ga Galadima, “Sameer ya jikin?”.

Bud'e idonsa yayi shima, ya ajiye mug d'in hannunsa a teble d'in dake gefen damarsa, batare da yace uffanba ya sauke ajiyar zuciya yan

a taunar lips.

Banga alamar damuwar rashin amsawar tasaba a fuskar Harun, dan yariga ya saba da halinsa.

Saidai idonsa k'uri akan Abdurraheem dake cinyar Galadima d'in yana barci, mik'ewa yay yana fad'in, “my son zo mu gaisa ko?”.

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login