Showing 378001 words to 381000 words out of 407268 words

Chapter 127 - Raina Kama COMPLETE

Ba k'aramin firgita nayiba, badan karnayi k'arya ba danace har wutar bala'i Nagano a idonsa tana ci, wannan bawa akwai zuciyar t

siya, idan zai zama jami'in tsaro da k'asarmu ta amfanu da yawa.........

Da k'arfi ya girgizani, saboda ganin saboda rainin wayo tunanima na tafi..........

A firgice nace “yi hak'uri zauna zan fad'a maka”. na fad'i hakanne dan kawai ina ganin

itace mafitar dazan nema ya fasa had'iyeni. a mamakina kuwa saiya tashin ya zauna yana dafe k'irji hawaye nabin kumatunsa.

Tsantsar tausayinsa ce ta kamani, na tashi na d'akko ruwa na dawo kusa dashi na zauna, addu'oi na shiga tofawa a ruwan, yana za

une dafe da kansa, da alama kuka ma yakeyi, dan ajiyar zuciyar da yakeyi ta yawaita.

Saida na gama na dafa ka fad'arsa, tamkar bazai d'agoba saikuma ya kalleni, ruwan addu'ar na basa, babu musu ya kar6a ya shanye, duk da baima san mita bashiba,

idanma poison ne dai gara ma yasha ya mutu ya huta.

Mintunansa biyu zuwa uku dasha yafara sauke ajiyar zuciya mai k'arfin gaske, saiya zame kuma ya kwanta, kafin kacemi barci ya saceshi a haka.

nima ajiyar zuciyar nayi ina girgiza kai da share

hawayen dake silalomin, ina rok'on ALLAH ya kawoma wannan bawan nasa sauk'i da rangwame cikin gaggawa da warwarewar al'amura.

Dagashi har yaran tausayi suke bani, nayi zurfi a tunani wayarsa tayi ring, kamar zan share saikuma Na tuna maybe Momma ce,

tashi nayi zuwa inda wayar take, aikam dai itace, nayi picking jiki a sanyaye, dan tunanina kota gamajin komai, amma sainaji sa6anin haka, da y'ar raharta ma tace, “Muh'd duk hidimar sunance haka?”.

“Uhm Momma bashi bane nice”.

“a'a d'iyata

kece?”.

“eh Momma, kuna lafiya? ya jikin Abie?”.

“Alhmdllh d'iyata, ya k'arfin jikinki kema? ina yaran?”.

Gabana ya fad'i, Na had'iye wani yawu da k'yar, cikin in ina nace, “lafiyar kowa k'alau Momma, shima y... yana barcine”.

Dag

acan Momma ta murmusa tana gyara zama a harabar asibitin, dan batason Abie yaji wayar da zatayi, tace, “humm d'iyata kema 6oyemin zakiyi kenan? yanzu koda mutuwa yaran sukayi dashi kansa kowama saiya shiga fargabar gayamin?”.

Na had'iye yawu dak'yar,

“kiyi hak'uri Momma, ki gafarcemu”.

“Bakumin laifin komaiba ni, hakan da Muh'd yay shine dai-dai, dan lokaci yayi dazai daina zama jiran sak'on mak'iya ko zuwansu, shine yakamata ya fita farautarsu domin kawo k'arshen komai, na yarda dake 100% Muna

ya, nakumayi imani insha ALLAH kece zaki sauyamin yaro daga k'uncin dayake ciki zuwa farin ciki, tamkar yanda Na fad'a miki tun farko karki ta6ama Muh'd sanya ko nuna tsoronsa, lokacin dazaki kwantar masa dakai kizama kowacce irin mace a agidan mijinta har

yanzu baiyiba, kada ciwonsa yasakaki fargabar fad'a masa gaskiya, rayuwa da mutuwa duk Na ALLAH ne, ko ayanzu Muh'd yabar duniya bazanyi bak'in cikiba, domin ya nuna musu shi jarumine, kuma ya haifi wad'anda zasu iya zama magadansa su sauya komai koda ba'

aso, nanda kwanaki biyu komai ya gama lafawa ki tabbatar kin masa maganar tafiya wanka gida, wannan shine target d'inmu Na k'arshe akan rayuwar zaman aure na dindin, kowacce irin birkicewa zai miki akan bazaki jeba, kema ki birkice masa, dan nasan abinda y

afaru zaisashi dagewa akan yaran bazasuyi nesa dashiba, idan kuma har aka cigaba da tafiya a haka, kowane irin dana Sani zai iya biyo baya”. Momma ta share hawaye dake kwarara a idanunta, taci gaba da fad'in “ALLAH yayi miki albarka Munaya, dake da abinda

kika haifa, yanda kikamin biyya wajen k'autata kar6ar Abu mai wahala (duk da bani na haifekiba) kema ALLAH yasa y'ay'anki sumiki biyyaya fiye da wannan, ALLAH yasaka hannu adukkan lamarinki keda mijinki da sauran y'an uwansa, nusar dashi abinda duk baki

gamsu dashiba shine zai rage ma zuciyarsa baraza, dan tarawar yagani a lokaci d'aya shine mafi had'ari Munaya, zuciyarsa zata iya bugawa a lokacin, kiyi hak'uri nasan bak'yajin dad'in zama da Muh'd ko kad'an, domin ni kaina mahaifiyarsa wataran gaza gane k

ansa nakeyi, amma inaji a jikina akwai sauyi maiban mamaki dazai zo ya rusa komai, ki sameshi fiyema da yanda kikeso, ALLAH yayi muku albarka, idan ya tashi ki kirani naji ya jikin nasa”.

Bata jira nayi magana ba ta yanke wayar, da alama kukane yaci

k'arfinta. nima saina fashe da kukan ina kallon Galadima, insha ALLAH zan cikama baiwar ALLAHr nan burinta, koda ace mun rabu dashine, dan maganar gaskiya bazan iya rayuwa da mutum murd'ad'd'e mara yarda irin Galadima ba, labarinsa kawai kukeji, amma halin

sa saika zuna dashi, Mara hak'uri zai iya gundurarsa ne cikin awanni biyu kawai, dan zaka dinga kallonsa a matsayin mai wulak'anci ko dizgi, girmankai da sauransu. Na sauke ajiyar zuciyarsa ina maida kallona ga Abdurrahman dake motsin tashi, nasan dukansu

saisun tashi inhar d'aya ya tashi, saina lalla6a na kwanta kusa dashi na saka masa nono a baki.



********************

Har akayi la'asar Galadima bai farkaba, Nuren yazo shida Sauban, da Saleem har sau biyu suka iske yana barci, hakama Mom

da inno da mama Fulani. Gashi su inno 4:30pm zasu wuce ma, laraba tazo tama yaran wanka, dan tuni sun farka, Nima nakumayi sannan naci abinci, kaina ciwo yakemin sosai, dan haka Sauban yafita ya samomin Magani nasha na kwanta, munyi sallama dasu Mom, zasu

dawone kawai idan Galadima ya farka kafin su tafi. yaran kam duk d'insu suna can an kaima papi su tun d'azun.

Nidai barci yay awon gaba dani, daga nankuma bansan wainar da aka cigaba da toyawa ba a gidan.



*******************

Baya

n la'asar kad'an Galadima ya farka, ganin shi kad'aine a d'akin ya tashi zaune bakinsa d'auke da addu'ar tashi barci, jin k'irjinsa yayi sakayau yasaki babu nauyin kamar d'azun, saidai abinda ba'a rasaba, yatashi zuwa bathroom yay wanka da alwala.

Sa

llan zuhur da la'asar ya rama, tareda addu'ar neman sauk'i akan wannan lamari da samun k'arfin zuciya, dolene saiyayi yak'i da dukkan abinda zai zama makamin barazana a agaresa inhar da gaske aikin zaiyi, falo ya fito bayan ya kimtsa, zamansa da mintuna ba

ifi 2 ba saigasu inno.

Basu jira isoba suka shigo, a zatonsu yana bedroom yana barci, sunsan Munaya kuma tana d'akinta tana barci tunda daga can suke. ganinsa a zaune ya saka fuskar kowannensu fad'ad'a da murmushi. Shidai kallonsu kawai yake d'ai-d'

ai.

Inno ta mangari kansa tana fad'in “ja'iri baka sanmu bane halan?”.

Hannunta ya rik'e yana kallonta, cikin maganarnan tasa ta k'asaita yace, “Inno wai ina zakuje ne?”.

“inda muka fito mana”. Inno tafad'a tana zama kujerar kusa dash

i.

“saikace wad'anda ake kora?”.

“A'a wazai koremu nida gidanmu, komawar dai ne yafi cancanta, dan takawa ma yace a gaisheka basai ya shigoba, zakuyi waya, idan ka murmure kaje yana nemanka”.

“To shikenan ALLAH ya tsare hanya, mun god

e sosai da sosai”.

“Amin” inno tafad'a tana shafa kansa ta ciga da kwararo masa addu'oi shida matarsa da yaransu, falon kowa tana amsawa da amin, itama mom tayi nata.

Yace, “mom hada ke wai?”.

“eh mana Sameer, zaman mi zanyi to? tund

a ALLAH ya iyakance komai cikin sauk'i, nanda y'an kwanaki kuma basai na zagayo naga masu jego ba da jikin naka, a dai dunga kulawa sosai, gasu laraba nan da bayi 2 anbar muku, dukdai wata kulawa insha ALLAH zasu taimaka wajen badata akan yaran, dan yakama

ta dukkan bayi da kuyangin sashen nan naka ka sallamesu kawai”.

Kansa ya jinjina mata alamar amsawa.

A gurguje sukad'an kuma tattaunawa da kwantar masa da hankali suka fito, dukda yaso musu rakkiya suka dakatar dashi. Abincin da mom ta zuba mas

a takumace yamata alk'awarin zaici ya dage yaci sosai, sannan Sauban daya dawo rakkiyarsu d'auke da y'an uku shida bayinnan biyu yabashi magani yasha, kar6ar Amaturrahman yayi, Sauban kuma na zaune dasu Abdurraheem yana musu wasa wai dole sai sunyi dariya,

(nace, “aiki jaa kenan, inba dariyar k'udaba ta jarirai idan suna barci keyi aiko ka dad'e baka ganiba Uncle triplets

😂

).



Galadima ma madai yatsansa d'aya ya saka cikin hannun Amaturrahman yana wasa dashi, dukda idonsa a lumshe yake ya jingina

kansa da kujera, maganganun Munaya na d'azun kawai yake nazari dalla-dalla.

Ana cikin haka Samha tayi Knocking, Sauban yace ta shigo, saida ta gaida Galadima damasa ya jiki.

Ya amsa mata batareda ya kalleta ba, tareda tambayarta Khaleel fa?.

Tace, “yana 6angaren Ummu hasheem”.

Baice komaiba, itama ta k'araso ta d'auki Ammaurrahman data rik'e yatsansa gam tak'i saki..

d'agowa Galadima yay yana kallon yarinyar, Samha dai dariya takeyi, har Sauban shima ya farga da abinda ke faruwa

ya shiga tayata. Galadima ya zare yatsansa yana murmuahin gefen baki da lakatar hancin Amaturrahman.

Har Magriba suna nan sun shashance akan yaran, yayinda Galadima ke zaune yanata cud'awa da tantancewa, lokaci-lokaci yakan kallesu dagasu har yaran

. Tunda ya tambayesu Munaya sukace tasha Magani tana barci bai sake tambaya ba.

********

Ban tashiba saida suka fara kuka, a time d'in har magrib tama wuce, nagama shayar dasu na lek'a Galadima, na iske doctor jalal tareda Dr Yaseen da Akas

h Wanda yake shirin komawa gobe, sai Muftahu da Nuren.

Muka gaisa dasu suka kuma tambayata jikinsa? na Amsa musu da Alhmdllh. fitowa nayi na barsu, da aka kawo mana abinci ma can nace akai musu, Sauban yazo ya kwashi yaran bisa Umarnin Galadima, docto

rs zasu kuma duba lafiyarsu.

★★★★★★

Tunda Harun ya fita saiya kira wata Number lokacin daya k'arasa d'akinsa, dukkan abinda ya faru ya labarta mata, daga can tace k'aryane bahaka akaiba, ita an sanar mata lallai da Galadima aka kar6o yaran, ba

bu wasu police, amma itafa kamar tafara saka alamar tambaya akan wannan ficikar matar tasa.

Harun yace, “haba dai, wannan y'ar yarinyar mizata iya, akwai dai abinda bamu saniba, yanzu dai kibari zamuyi maganar daga baya, zand'an bincika yarannan dann

i na lurama kamar ba wad'anda muka saka bane sukayi aikinnan?”.

“sunefa gaskiya, abinda dai na lura dashi sun had'a aikin da wasune, shiyyasa suke 6oye mana Kansu, tunda kaga mudai baiwarnan bamu muka sakata ba, amma shi namijin yana cikinsu, nasan

sunyi luff ne sai k'ura ta natsa su fito”.

“ok shikenan to, zandai sake bincikawa, dan Sameer yanada wayo, shiyyasa naso bugar cikinsa akan batun, amma wannan shegen k'asaitar tasa ta rainin hankali ya hanashi tankamin, sai matarce ke bani amsa”..

“karka damu zamu sauke masa shine ai”...............



🏻

🤣

abin dariya, ku a naku zaton yaranku sun 6oye Kansu be?, to suna hannun Galadima, lafiya kawai muke jira ya samu ya yagalgalasu kuma ya cafkoku munafukai

🙄😏

.

*_

ALLAH ka gafartama iyayenmu._*

😭🙏🏼

[8/21, 8:44 PM] 0mmer Farouk: *_Typing

📲

_*

*_

💡

HASKE WRITERS ASSO...._*

*_



RAINA KAMA...!!



_*

_(Kaga gayya)_

*_Bilyn Abdull ce

🤙🏻

_*

*_BOOK 3_*

👉🏻

2



8



.........

........Har yamma Galadima bai dawo gidanba, abincin ranama da aka ajiye masa sai d'aukeshi akayi, sainaji inajin tausayinsa, dan nasan yanacan ba zaune waje d'ayaba, yawan harkoki dayakeyi kansa kullum yake yawo tamkar wata motar haya, shidai kullum burin

sa ya iya d'aukar nauyin ahalinsa, bai yarda zama rago ko jira daga waniba koda ace papi ne, ya yarda yasha wahalar nema amma ta gumin halak, sa6anin matasanmu da kullum burinsu nakan gwamnati ko alhajin anguwarsu ko d'an siyasa, ko alhajin da yafi kowa ar

zik'i a danginsu. Akwai wata kalma da Galadima yata6a fad'ama sauban Wanda akulum Na tunata tana k'ayatar dani. Lokacin inada tsohon cikinsu Amaturrahman, da yawan cin abincinnan Na masifa, aranar jikin Abie yad'an motsa, sai yakasance nikad'ai aka bari a

gida sai hadiman gidan, cikin barci yunwa ta addabeni, hakan yasani farkawar dole Na sakko k'asa da k'yar, kitchen Na shiga nasami madara Na d'umama kafin kuku yad'an girkamin wani Abu, fitowata daga kitchen d'in keda wuya sai Galadima da Sauban suka shigo

, da alama ya tuk'osane, dan idan yana cikin damuwar tashin ciwon Abie Momma hanashi driving takeyi. Da mamaki Sauban ya kalleni da cup a hannu yana fad'in “Yanzu nan Aunty duk hadiman gidannan saikin shiga kitchen da kanki a wannan halin? Aiko yau saisun

gane kuransu”.

Ya tafi fuuuu cikin fushi saina dakatar dashi ina murmushi. Nace, “A'a Yaa Sauban, kabarsu please, nice ban sasunba nayi da kaina, amma aiga shican nasaka kuku wani aikin”.

Galadima dake zaune saman kujera ya d'aura k'afa d'aya

kan d'aya idonsa a lumshe tamkar baisan mi mukeyibama ya bud'e baki cikeda k'asaitar nan tasa yana fad'in, “Ai duk Wanda ya dogara da k'arfin wani to lallai nasa na cikin jerin k'arewa a sahun marasa amfani, dan zai dawwama cikin bibiyar samu daga waninsa

shikuma bai amfanu datasa fik'irarba, kazama mai k'arfin zuciyar gina kai ba zaman jingina da bangon waniba”.

Yana gama fad'ar haka ya tashi ya haye sama, dagani har Sauban da kallo kawai muka bishi, kowa na fassara zancensa dalla-dalla, ni abinda na

fahimta kai tsaye bada Sauban d'in yakeba, akwai abinda yafaru daga can inda suka fito, amma saiya za6i mu yamana sharhi bisa dalilin dashi yabarma kansa Sani. (ALLAH dai ya ganar da matasanmu domin tashi su nemi na Kansu ta hanya mai k'yau basu cigaba da

dogaro a bangon wasuba.

👏🏻😢

).

Tun d'azun yake tsaye akanta amma bata saniba, ta Lula duniyar tunani mai zurfi, ga Abdurrahman dake gefenta yanata mutsu-mutsu da k'ananun kuka amma batama jishiba.

Agabanta yay wani durk'uso mai birgewa, yak

ai fuskarsa daf da tata yana hura mata iska a saman ido zuwa hanci.

Wata sassanyar ajiyar zuciya na sauke tareda dawowa hayyacina cikin zabura, yay azamar damk'e hannuna da fad'in “My Mata!?”.

Ajiyar zuciya na sauke tareda dai-daita dan fahi

mtar shine, na zuba masa idanu cikin mamaki nace, “Yaushe ka shigo?”.

Murmusawa yayi sannan yamik'e daga durk'uson dayay agabana, batareda ya bani amsaba ya fara k'ok'arin cire farar rigar suit d'insa. Mik'ewa nayi na taimaka masa, sannan nadawo gab

ansa na warware tia.. 'Din da bottoms d'in pink d'in rigarsa ta ciki. Sai wani faman lumshe idanu yake da bud'esu akaina, bansan miyake tunaniba.

Ina cire bottom d'in k'arshe na rigar ya rik'e hannuna, idanu na d'ago na kallesa, ya sakarmin wani k'a

saitaccen murmushi yana matsoni jikinsa sosai, a saman la66a ya furta “Kinyi k'yau sosai, amma mikike tunani haka?”.

Da mamaki na kalli kaina, sanye nake doguwar rigar shadda milk color, anmata simple aiki da brown d'in zare, an k'awatashi da stones

, Wanda sune suka fidda ainahin k'yawun d'inkin, sai siririyar sark'a data kwanta a wuyana d'as, nayi d'aurin Maryam babangida daya kuma fidda ainahin suffata ta bahaushiyar asali mai rik'o da al'ada. Yanda nake bin jikina da kallo haka Galadima kebi shima

da idanunsa, na maida kallona ga face d'inshi dake kadaran kadahan, bai d'aureba kuma babu walwala sosai tare dashi.

Gira d'aya ya d'agemin sai kuma yad'an ta6e baki yanajan hancina da had'e yatsunsa biyu na k'arshe

👌🏻

alamar komai yaji.

Nad'a

n murmusa ina k'ok'arin barin wajen dan naga alamar miskilawan suna kusa.

Ruwa naje na had'a masa, na fito ina goge hannuna da towel.

Durk'ushe na iskeshi gaban Abdurraheem da cup d'in ruwan dana ajiye danshi a hannunsa. Ya d'ago yana kallona

dad'an murmushi a face d'insa, “kinsan minake gani a jikin Abdurraheem kuwa?”.

Kaina na girgiza masa alamar a'a.

Kallonsa ya maida ga yaran yana cigaba da murmushinsa. Yace, “Kamannin Abie”.

Takowa nayi Inda suke Nima Ina murmushi mai sa

uti da fad'in, “Nadad'e da wannan tunanin a raina, saidai nabarma zuciyatane har sai randa zan gansu a waje d'aya, Ashe kaima kana lura?”.

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login