Showing 147001 words to 150000 words out of 407268 words

Chapter 50 - Raina Kama COMPLETE

kuke k'ok'arin Comments sai bana iya barinku banyiba

😃

, ina godiya kwarai

da gaske, I love you all

🥰🥰🥰🥰🥰

🤝🏻👍🏻



_*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu

😭🙏🏻

_*

*_Typing

📲

_*

*_Haske writer's asso...._*

💡



*_



RAINA KAMA......



_*

_{Kaga gayya}_

*_Bilyn Ab

dull Ce_*

🤙🏻

~Book 2~

👉🏻

7



................Gaba d'aya ya rikice ya rikita Nurses d'in da jama'ar wajen, cak ya d'auki Munaya, gadonma da aka kawo masa domin d'orata ko kallonsa bai yiba. Wani d'aki suka nuna masa ya shiga da ita.



Da sassarfa doctor dazai duba munayar ya iso, dan dogaran Galadima tasoshi gaba sukaje sukayo.

Kai tsaye Galadima yace baya buk'atar namiji mace yakeso ta duba masa matarsa.

Hak'uri doctor d'in ya bashi, sannan yakira wata likita mace mai su

na doctor Farida.

Isowarta yasaka Galadima da yay bake-bake a k'ofar bata hanya ta shiga.

Duk yanda taso yabata waje tayi aikinta yak'i, gashi duk yabi yagama rikitata da tsawarsa.

Doctor d'in da Galadima ya hana ya duba Munaya ne ya matsa

kusada su harun yana fad'in “dan ALLAH sir Ku lalla6a yalla6ai ya fito danta samu damar aikinta, wlhy dukya rikitata”.

Murmushi Nuren da isowarsa kenan asibitin aka masa bayani shima yayi, suma su harun duk murmushi sukayi.

Nuren ya kalli baba

k'arami yana murmushi, “Abbanmu inharfa bakai kamasa magana ba bawai zai fito baneba”.

Shikansa baba k'arami murmushin yakeyi, koba komai hankalinsu Yakuma kwanciya da zaman 'yarsu inda suke tunanin anfi k'arfinta.

Bayan doctor yabi zuwa d'

akin, Galadima dake zaune, kan Munaya na bisa cinyarsa sai murza tafin hannunta yakeyi wai kozata farfad'o, yayinda doctor Farida ke k'ok'arin lik'a mata oxygen ita kuma”.

Shima baba k'arami da k'yar ya lalla6ashi ya fito.

Tsawon lokaci doc

tor Farida tana ciki bata fitoba. Galadima dukya damu, danma ankawo masa kujera ya zauna, amma sai jan tsuka yakeyi time to time.

Hankalin 'yan gidansu Munaya ma duk a tashe yake, jiran fitowar doctor Farida kawai akeyi dan aji mike damun munayar.



Innarsu Munaya kam gefe ta koma tana sharar kwalla, itakam batasan yazata misalta wannan tsakaniba, miji da 'ya'ya duk babu lafiya, Munubiya ma fa sunacan ana k'ara mata ruwa.

Fitowar doctor Farida yasaka kowa mik'ewa anason jin bayani, Galadima

dai yana daga zaune ya zuba mata idanu shima. Doctor Farida tace su kwantar da hankalinsu ta farfad'o, amma tamata allurar barci, yanzu tanason ayo gwajin jinin Munayar data d'iba.

Galadima ya lumshe ido yana ambatar “Alhmdllh” akan la66ansa.



Sauban ne ya kar6a suka tafi shida Sarkin mota lab d'in.

Dr Farida ta kalli Galadima tana murmushi, “ranka ya dad'e zaka iya Shiga ka ganta yanzun”.

Nuren ya kalli Galadima ya jinjina masa kai alamar yaje.

Saida yaja wasu seconds sa

nnan yamik'e cikin takun nan nasa na k'asaita da izza, duk idon jama'ar wajen akansa yake, yana birge kowa.

d'akin ya tura ya shiga, ya taka har gaban gadon da Munaya ke kwance, idanu ya tsura mata, tayi wani fayau da ita, ya jawo kujerar dake waja

n ya zauna, har

yanzu idonsa na kanta, cikin cije lips da lumshe idanu ya d'ora hannunsa bisa sumar kanta da d'ankwalinta ya zame ta fito, saikuma yasaka d'ayan hannunsa ya shafi kumatunta, a kan la66ansa ya furta “sorry my friend, ALLAH yana tare da masu

hak'uri kinji”.

Daga haka bai sake cewa komaiba, ya janye hannunsa daga kanta ya mik'e ya fito.

A k'ofar d'akin ya iske Doctor Farida tsaye, kallonta yayi cikin maganarnar tasa mai kama da an masa tilas yace “zata iya kaiwa wane lokaci bata f

arkaba?”.

“Ranka ya dad'e inaga daganan zuwa kamar awa d'aya”.

Kansa ya jinjina mata, bai sake magana ba yanufi d'akin da Abba ke kwance. ya Tatar da doctor d'in dake kula da Abban a d'akin.

Da sauri doctor yabashi kujera ya zauna, k'afa

d'aya kan d'aya ya d'ora ya Ciro waya a aljihu yana danne-danne. batare da ya kalli doctor ba yace, “kunyi gyaran karayar?”.

Doctor yace, “eh ranka ya dad'e duk an gyara, saidai na hak'ark'arinsa yaso kawo matsala, amma Alhmdllh komai ya dai-daita”

.

“humyim, maganar bayanan danace a tattara minfa?”.

“shima komai ready ranka ya dad'e ”.

“o right, insha ALLAH zuwa jibi nakeson mu tafi, amma wai har yanzu bai ta6a farfad'owa bane?”.

“ai ba'a sume yakeba, allurar damuke mas

ace kawai takesakasa yawan barci”.

d'ago ido Galadima yayi yana kallon doctor d'in, yace “amma danme ake masa?”.

“ itace ke taimaka masa wajen rage masa rad'ad'in ciwukan, dan maganar gaskiya yana cikin matsanancin ciwo”.

Cije lips

Galadima yayi kawai, yace “ALLAH ya bashi lafiya”.

“amin ya rabbi”. ‘cewar doctor.

Daga haka suka fito shida doctor d'in.

Inda Harun yake Galadima ya nufa, “brother yau ba zakaje aikiba kenan?”.

Kallon agogon hannunsa Harun y

ayi, sannan ya kalli Galadima, “ka rikitamu ne ranka ya dad'e shiyyasa ban kula time ya tafi hakaba”.

Murmushi kawai Galadima yayi amma baice komaiba.

Harun yay musu sallama ya fita da nufin zuwa anjima idan yatashi aiki zai dawo.

Su ya

a Hameed sukai masa godiya da fatan alkairi sannan yatafi.

Daddy ya kalli su yaa Hameed d'in yace ai kuma da tafiyar kukayi, karku makara wajen aiki”.

A ladabce suka amsa masa da to, suna shirin barin wajenne saiga motocin su waziri sun shigo

, dole su yaa hameed suka dakata.

Waziri ne da matawalle, sai Garkuwa da baraya, sai kuma wasu manya-manyan 'yan majisar Sarki. dogarai duksun kasa sun tsare, wasuma zato suke sarkinne yazo da kansa.

Su daddy ne suka musu iso har d'akin da A

bba yake kwance, sosoi suka nuna tausayawarsu gareshi, sunja doguwar addu'ar samun lafiya da fatan alkairi ga Abba. Sannan suka Isar da sak'on Sarki.

Sun d'an jima a d'akin suka fito da nufin tafiya, a dai-dai time d'inne kuma doctor Farida ta iso ga

ban Galadima cikeda sassarfa. Bakinta a washe tamkar

gonar auduga. Wani dogari Na k'ok'arin dakatar da ita Galadima ya d'aga masa hannu alamar ya barta tazo.

Cikin girmamawa doctor Farida tace “wannan asibiti da dukkan jama'ar cikinsa suna taya masa

rautar gagara badau murnar samun k'aruwa daga jikin gimbiya Munaya, insha ALLAH nanda watanni 7 dawasu satittika zata zama uwa, ma'ana tana d'auke da cikin wata 1 da sati uku”.

Atare dogarai suka d'auki kabbara, Galadima dake tsaye baki bud'e ciki

n tsantsar mamaki ya kafe doctor Farida da idanu, sai kawai yashiga zame agogon hannunsa mai masifar tsada da k'yau ya mik'ama doctor Farida.

Sauban yazo ya rungumesa, hakama matawalle.

'Yan gidansu Munaya sai suka koma 'yan kallo kawai, amma

bakin kowa yakasa rufuwa.

Doctor Farida ta kalli Galadima cikin mamaki da al'ajabi, “ranka ya dad'e ni Na cancanci wannan agogon mai d'unbin tsada kuwa?”.

Wani murmushin Daba a cika gani Galadima yayiba ya saki, ya gyara tsayuwarsa yana fad'in

“idan duk abinda na mallaka a duniya kike buk'ata zan baki shi, saboda wannan shine albishir Na farko da aka ta6amin Na farinciki a rayuwata, kifad'i dukkan abinda kike buk'ata inhar baifi k'arfina ba kafin nabar asibitinnan za'a kawo miki shi”.

Ka

nta ta shiga girgizawa, kafin ta d'aga agogon ga mutane su gani.

Mamaki ya cika kashe matan gidansu Munaya hassada da al'ajabi ya cika zukatansu, tunma ba'a haifi cikinba Galadima yake wannan rawar kan inaga an haifoshi?, Kansu bai kuma kwanceba said

a sukaji waziri da baraya Na sanarda tasu k'yautar ga doctor Farida, hakama matawalle da Nuren.

Doctor Farida fa ta rikice, itakam yau taga farar rana, (

🙄

idan ta ALLAH ake niya kamata abama wad'annan k'yaututtuka ma

😏

).

Nuren da matawalle suk

a hau rabon kud'i a asibitin, tamkar basu San ciwonsu ba.

Waziri kam d'akin da Munaya take kwance aka musu rakkiya, sun mata addu'a kafin su fito, kowa bakinsa a washe, wasukam ta cikin Na ciki kawai

😳🤭

.

Kafin kace mi labari yagama zagaye asi

bitin, gidan Sarki kam kafin su waziri su Isa labarin cikin Munaya yaje.



hakama Sauban ya kira su Momma ya guntsa musu, Momma saida tayi sujudar shukur.

Abie bakinsa yakasa rufuwa, kamar daga sama sukaji yace “ALLAH ya inganta”.



Dukda a hankali yayi maganar hakan bai hanasu ganin motsawar la66ansa ba, Khaleel dake kusa dashi yace “Lah Abie yayi magana Momma!!”.

ba momma ba hatta da jakadiya sakin kwanon hannunta tayi ta waigo tana kallon Abie. Aunty Mimi ta tura laptop d'in

gabanta tafad'o, hakama Samha wuntsilowa tayi daga kujerar datake zaune tayo inda gadon Abie yake.

Gaba d'aya suka rufu akan abie, kowa yanason sanin gaskiyar batun Khaleel, murmushi Abie yamusu yana jinjina kai alamar gaskiyane, sannan a hankali ya

kuma furta “da gaske Khaleel yake”.

Ai yau babu kunya Momma ta rungume Abie a gabansu aunty Mimi ta fashe da kuka mai ban tausayi.

Aunty Mimi ta had'a momma da Abie d'in ta rungume itama.

Jikin Samha har 6ari yakeyi takira Number Gala

dima ta Nigeria.

Ya rako su waziri da zasu tafi kiran Samha ya shigo, bai d'auka ba, itakuma bata gaji da kira ba.

Saida su waziri suka wuce sannan yaciro wayar a aljihunsa cikeda haushin wanene mai nacinnan. yana dubawa yaga Samha Ce.

Mur

mushi yayi kawai sannan ya kirata da kansa, bugu d'aya Samha ta d'aga, kuka kawai ta fashe masa da shi, zuciyar Galadima tashiga tsitstsinkewa. tsawa ya daka mata yana tambayar lafiya?.

Share hawayenta tayi, murya Na rawa tace, “Uncle Sam wlhy Abie

yayi magana, yanzun nan da Uncle Sauban ya kira yace aunty gimbiya nada ciki sai Abie yace ALLAH ya inganta”..

Galadima ya ciro wayar a kunnensa ya kuma kallon number, tunaninsa wasune kawai keson masa yawo da hankali, ganin dai da gaske number Sa

mha d'in ce saiya maida a kunnen, cikin sanyi murya ya kira ainahin sunan Samha, “Zeenah! banason wasan banza kema kin sani”.

“wlhy Uncle ba wasa nakeba, ga Momma ma kaji awajenta”.

Kafin yace wani Abu yaji muryar Momma namasa sallama, yanayin mu

ryarta yasakashi lumshe idanunsa. Momma tace, “Muh'd! Yau ranace dabazamu manta da itaba a tarihinmu, k'yautar abinda kud'i baya saya, ALLAH kuma yabama takawa damar magana, narasa yanda zan musalta farin cikina Muh'd”.

Wasu hawayene suka gangaro a

kumatun Galadima, ga murmushi yak'i barin fuskarsa, cikin nutsatstsiyar muryarsa yace “Momma ko yanzu Ubangiji ya d'auki raina yagama min komai, Momma mizanyi duniya tasan ina cikin tsantsar farincikin da tunda nazo duniya ban ta6a riska ba?”.

Dariya

momma tayi, tace “godiyar ALLAH ta wadatar da komai Muh'd, lallai yarona zai zama baba”.

Galadima yayi dariya yana goge hawayen fuskarsa, “Momma bama Abie wayarnan”.

Cikin tsokana tace, “nawa zaka biya? kasan mu yanzu komai Na kud'ine”.



Sosai yasaka dariya, har jerarrun hak'oransa Na bayyana. Dogaransa duk sun saki baki suna kallonsa, duk da bajin maganar da yake sukeba, tunda suke da shi basu ta6a ganin yana dariya makamanciyar wannan ba, Sauban kan ai hotuna yaketa masa bai saniba.



“shikenan Momma, inhar baki had'ani da Abie ba kema kuwa d'iyarki bazata dawo India ba ashe?”.

“a'a miyay zafi? indai takawa ne gashi”.

Nanma dariyar Galadima yayi, Abie da tun d'azu yaketa murmushi shima saboda a Hans free momma tasak

a wayar duk sunaji, a hankali yace Daddyn Unborn!”.

Galadima baiji mi Abie ya fad'a ba, amma tabbas yana jiyo alamun motsi, da sauri yace, “Momma video call please ”.

Mota ya bud'e ya shiga, Sauban ma ya k'araso dan kuma taya d'an uwansa murn

ar k'aruwar daya samu. tunda aka bayyana maganar cikin Galadima bai samu Kansa ba, balle su ke6e.

Motar yashigo shima, ganin video call Galadima ya had'a dasu Momma saiya matso kusada shi sosai yana d'aga musu hannu.

Momma tace, “ho autana ina k

a shige wai?”.

“momma ina zaki ganni nazama Abban Unborn”.

Dariya sosai suka sanya, Galadima ya rankwashi kansa.

Wayar aka saka kusada Abie sosai, a hankali yace, “lallai wad'annan iyaye akwai zumud'i dai”.

Basuji miya fad'aba. A

mma sungane ta hanyar motsin la66ansa. cikin zaro ido Sauban yace “Abie!!”. Sai kawai ya rungume Galadima ya fashe da kukan farin ciki.



Humm masu karatu, nabama kowa damar k'iyasta wannan farin cikin a zuciyarsa shima

😁😉

.





*

★★

*



*





*



*

★★

*



A lokacin da Galadima suke can suna waya dasu Momma Munaya ta farka, doctor Farida ta cire mata k'arin ruwan danya k'are.

Ta kalli doctor Farida tace “doctor Abbana fa? karki cemin dai Abbana ya mutu Dan ALLAH?”.

Hannun

ta doctor Farida ta rik'o, fuskarta d'auke da murmushi tace, “gimbiyarmu Abbanki nanan da ransa, insha ALLAH kuma zai tashi, kedai kici gaba da masa addu'a kinji”.

Kai Munaya ta jinjina mata, sannan tace, “to zanyi fitsari”.

Doctor Farida ta am

sa da to, da kanta ta taimakama Munaya tashiga bayi, fitowa tayi tabata waje, saida ta gama sannan ta kuma taimaka mata ta fito.

“doctor 'yan gidanmu fa?”.

Murmushi Dr Farida tayi, cikin tsokana tace, “Gimbiya Galadima yakamata ki fara tambay

a ai”.

Murmushi Kawai Munaya tayi, amma batace komaiba, Dr Farida tace “to bara Na musu magana”.

Babu dad'ewa saiga 'yan gidanmu nata shigowa, yanda kowanne fuskarsa ke a washe sai suka bani mamaki, nakasa hak'uri nace, “Abba ne ya tashi? kuke

farin ciki haka?”.

“shima insha ALLAH zai tashi 'Yar albarka”. Cewar innaro tana dariya.

Ni duk sun kuma d'auremin kai da addu'ar da sukeyi suna fad'in ALLAH ya inganta.

Mamansu Fauziyya tace minakeso akawo min naci.

Nace, “ba

najin yunwa mama, ni sonake ma Na kuma ganin Abba”..

“karki damu, Abba yana barci ne, kedai kisamu kici abinci babynmu yak'ara k'ato kafin ki haifo mana”.

Ban fahimci maganar ta Fiddausi ba, Dan naga awajen akwai masu ciki da yawa, aunty

Ramlah, aunty Khaleesat, aunty Hauwa'u, Siyama, Zarah, aunty Raihana duk cikinsu ya tsufa, haihuwa yau ko gobe.

Na kalli innarmu dake tsaye batace komaiba, murmushi namata, itama saita mayarmin, nace, “wai har yanzu Munuhiya ba a cire mata ruwanba?

”.

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login